Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 42022 words

Chapter 6 - BAKIN GIDA BY FATIMA SULEIMAN UMAR.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

*FATEEMAH* *S* *OMAR*


*PAGE* 25-26




.....................πŸ“–"Karku damu indai akan wannan ne ni nasan matakin da zan dauka kutashi ku tafi gida karkusa komai aranku" mikewa hajiya Sareena tayi ta 'dauko ko kudi tabawa hajja tace "sai mujiki hajjarmu" dariya hajja tayi tace "zakuji alheri kuwa" daga haka sukayi salama suka huce gida




yau alhamis gobe yakama tafiyar su Deedee dan haka Abba yace a kira mishi su
zama sukayi a parlour Abba kan kowa a 'kasa
Abbane ya kalesu yace "naji dadin ganin wannan rana me albarka duk da sai gobe zaku huce amma yau nake da time 'din da zanmuku nasiha" kalon Aliyu yayi yace "kaine babba kai zan fara ta kanka karike kanwarka da amana duk abunda zatayimaka kayi hakuri kuruciyace kaga ita yarinyace kuma ka kare mutuncinta duk iya rintsi ko huya kar ka bari hani abu yasameta na rokeka Aliyu karka cutarda kanwarka kayi hakuri ka rungumi matarka kuhada kanku kuyi hakuri da fatan ka gane abunda nake nufi" kan Aliyu a 'kasa yace "insha Allah zanyi abunda kace" kansa Abba ya shafa yace "Allah yayi maka albarka" "ameen Abba" kalon Fateemah Abba yayi yace "Fateemah kece 'karama kece zakiyiwa mijinki biyya kuma ki kula dashi duk abunda baya so ki nisan ceshi duk abunda yake so kema ki soshi sannnan banason rashin kunya da hakewa nagaba da ke kiyi hakuri zakiga ribar zaman duniya" muryarta na rawa tace "nagode Abba Allah yasaka da alkari kuma insha Allah zaka sameni meyin biyayya" dafata Abba yayi yana murmushi yace "ameen 'diyar arziki Allah yayi miki albarka" "ameen" tace sannan Abba ya dauko kudin rafa 'yan dubu dubu guda 5 ya mikawa Fateemah ta dago ta kaleshi a tsorace murmushi yayi yace "ki amsa nakine ba ayi miki laifeba kinga ba a barki hakaba hakkinkine a baki" kin amsa tayi tace "a'a Abba kabarshi walahi na yafe" fuska Abba ya hade yace "ba nason gardama ki amsa nakine ko kinyafe dulene ki amshi wannan ai ba biyanki lefenki akayiba ko rabi ba a biyakiba" tana hawaye ta amshi kudin tayita godiya har saida Abba ya bata rai ta daina ya salami Deedee ta tafi ya kali Aliyu yace "nasan kai ba karamin yaro bane kasan abunda kakeyi inaso ka tsananta tsaro akan iyalinka dan kasan halinda *gidan* nan yake ciki karkayi la akari da kayi nisa dashi a'a shi mugu ko ina kashiga binka yakeyi dan haka ka sa ido sosai akan iyalinka kuma karnaji karna gani" "insha Allah za'a kiyaye Abba" "to Allah yasa Allah yayi albarka" "ameen nagode Abbana" "to zaka iya tafiya Allah ya kiyaye kila kan natashi kun huce" "ameen" yafada haka yana mikewa yayiwa Abba salama ya huce




Deedee tana zuwa 'dakin Ammi ta zubewa Ammi kudin akan cinyarta saurin kalonta Ammi tayi tace "wannan kudin daga ina?" Deedee na dora kanta a kafadar Ammi tace "Abbane ya bani wai ba amun lefeba ba abarni hakaba" fuska Ammi ta hade tace "dan bayi miki lefe ba za'a dau irin wannan kudin abaki kema da kike da hauta kika amso" cikin shakwa'ba Deedee tace "saida naki amsa Abba yaita fada saida na amso" "hmm shima yaya da aikin yara yake walahi, jeki aje kudin gobe zan maida mishi abunsa sai kuntafima bare yace indawo miki dasu" tashi Deedee tayi ta bude drower tasa kudin ta dawo kan cinyar Ammi tayi kwanciyarta har bacci ya 'dauketa






shikuwa Aliyu a taren kasa bacci yayi sabuda tunanin irin amanar da kowa yake bashi ta Deedee ko xaimishi nasiha saiyace amana aka bashi Deedee amana dai amanadai kowa amana shikuwa ya zayi da wannan kayan akansa ko shi ba mutum bane da baza abata amanarsaba hmm kodan anga yafita zafin rai da xuciyane shiyarasa inama zaisa wannan amanar ko so ake ya goyata duk inda zashi ya tafi da ita shine amanar ohho




mikewa yayi yaje toilet yayo alwala yayi salah raka'a 2 ya roko Allah da yayemai kuncin dake zuciyarsa ya zaba mishi abunda yafi alkairi a rayuwar duniya yabashi ikon rike amanar da akabashi
cikin ikon Allah yana gama addu'o'in bacci yayi awan gaba dashi






washe gari 8:30am Aliyu ya gama shirinsa tsaf ya kira Usman sukayi magana akan zai 'karasa masa aikin daya bari anan sannan yarifo room 'dinsa yaje ya ajiye kayansa a but yanufi part 'dinsu






'dakin mommy yaje ya gaida ita ta amsa da fara'a tace "anfito kenan saitafiya" sosa kai yayi yace "eh mommy naso abari sai yamma ko zakuyi taro Abba yace ba'a gayaci kowaba karmuyi dare muhuce da safe kawai" "to Allah ya kiyaye" "ameen mommy" ya kali Hafsat dake kwace akan bed yace "jekice ta fito sauri nakeyi" "to" tace ta mike ta fice






shiga 'dakin Ammi tayi da suke ta faman artabu da Deedee taci abuncima taki sai kuka dataketayi tunda ta tashi da salama Hafsat tashiga 'dakin ta zauna kusa da Deedee tace "ya Aliyu yace ki ki fito ku tafi sauri yakeyi" kuka Deedee tasa harda buga 'kafa tanacewa "yatafi ni ba inda zanje" cikin hade rai Ammi tace "kinga Hafsat tashi kije kice kace yazo da kansa" mikewa Hafsat tayi Deedee tai saurin rukota tana cewa "ayya plc karkije na shirya bari na fito" mikewa tayi dama tayi wankanta ta sauya kaya isham ne yazo yafita da kayanta lokacin tagama shirinta tsaf tayi tana aikinta kuka






ruko hannunta Isham yayi zai fita da ita ta warce takoma gun Ammi tana kuka tace "kiyimin addu'a Ammita" hawayen da Ammi ke boyewa ne suka zubu ta dafata muryarta na rawa tace "Allah ya kiyaye yayi muku albarka" bata 'kara samun damar furta wata kalmarba sabuda kukan dayaci 'karfinta itama Fateemah kuka take sosai jokin Isham a sanyaye ya 'dago Deedee ya hadata da jikinsa ya fice da ita lafewa tayi ajikinsa tana kuka ahaka suka fita parlour gani kukan da take yasa mommy bata tsaya yi musu do guwar nasihaba tayi musu fatan alkari ta huce






Aliyu tun 'dazu yana jikin muta yana jiransu fitowa sukayi har lokacin Deedee najinki Isham wata iriyar faduwar gaba Aliyu yayi ganin yadda Fateemah ta lafe ajikin wani bashiba duk da yayantane uwa daya uba daya amma saida yaji ransa na suya wani irin tukukin kishi ya taso mishi yayi saurin karasawa fuska ba alamun rahama yaraba Deedee dajikin Isham ya kamo hannunta sata a mutar yashiga shima yabar gidan da mugun gudu






Zakiyya take jikin window tana lekensu tazube a gurin tasaki kuka me ciwo shikenan yau wata ta malaki Aliyu ba itaba
hajiya ce datajiyo kukanta tashigo ta dagota tace "kiyi hakuri tunda hajja tace zatasa abunyi xakiga yadda za ayi zuwan da dawowar" kwace jikinta tayi tace "ko me zatayi aidaga bayane tariga ta malaki Aliyu na ni yanxu na daina jira sai wata hajja tamun abu da kaina xan 'dau mataki" tana gama fadin haka ta huce tabar hajiya da sakaken baki






shi kuwa Annur yana can yana sheke ayarsa da baby Nafee amma yau tunda gari ya waye yakejin gabansa na faduwa wayoyinsa ya dauka zai kuna amma baby Nafee na hanashi kayansa ya shirya zai tafi gida amma saida baby Nafee tasan yadda tayi ta hana shi tafiya tace ya bari gobe sa taho gaba daya haka ya hakura badan yaso ba ya hakura amma hankalinsa yana can gida






a hanya kukan Deedee ya damu Aliyu ya rasa yadda zaiyi da ita janyota yayi jikinsa ya kwantar da ita a kafadarsa ya kamu hannunta yana murxawa a hankali lumshe ido sukayi a tare yana tuki da hannu dayan dayan yana cikin nata bacci ne yayi gaba da ita har sukace bata saniba




kalon fuskarta yayi yadda take baccin a takure a hankali ya zame jikinsa daga nata yaje ya bude gidan ya dawo ya dauketa ya kaita har bedroom ya kwantar da ita mikewa yayi zai tashi ta riko hannunsa cikin magagin bacci ta.................!




by
*XAHRA*
[8/27, 17:07] Anty Baby: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* πŸ“•πŸ–ŠοΈ
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )




*( F.W.A)πŸ–Œ*


https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/


☘🌷☘🌷
*BAƘIN GIDA*
☘🌷☘🌷


storry and writting
by
*FATEEMAH* *S* *OMAR*


*PAGE* 23-24




..........................πŸ“–Saurin rukota yayi ganin tayi baya zata fa'di kwantar da ita yayi a 'kirjinsa yafara taba fuskarta yana kiran sunanta a hankali
Hafsat ce taje ta dako ruwa a frige ta miko mishi harararta yayi ya bude bakin Deedee ya hankali ya zira nashi yafara hura mata iskar bakinsa ya 'dan jima kafin ta sake ajiyar zuciya tafara fitar da nunfashi a hankali kasa dauke bakinsa yayi daga nata saima kura mata ido dayayi yadda take bude ida nunta a hankali ta saukesu akansa






ajiyar zuciya ta sauke tana tuno abunda ya faru nunfashi ta sauke tare da janye bakinta a hankali rintse ido Aliyu yayi yana ta kaicin abunda yayi yanzu sakinta yayi ya mike yana kalonta yace "gidan ubanwa zakije da kika fito da gudu harda ture mutane" tana kuka tace "kayi hakuri bansan dakai a gurinba" tsaki yaja yace "to da bani bane bafa" fuska ta marairaice tace "ai dawani ne da sauki dan duk 'yan gidan nan sunfika hakuri" kalon da ya watsa matane yasa ta tuna me take cewa






hannu 2 tasa ta toshe bakinta ta mike da gudu tabar gurin
murmushi yayi ya girgiza kai a fili yace "matso raciya kawai" daga haka shima ya fice daga gidan






Fateemah 'dakin Ammi ta huce tana kuka ta zauna a kusa da ita tace "Ammi da gaskene ran juma'a ya Aliyu zai tafi dani zariya?" rungumuta Ammi tayi tana shafa bayanta tace "abunda nake so dake yanxu ki kwantar da hankalinki kar kisa damuwa a ranki wani ciwon yazo ya shigeki ko wa dakika gani yana rawuya a gidan mijinsa to walahi zaman hakuri yakeyi dan haka karki tada hanka linki dan ance zaki tare gidan mijinki fatana dake shine kizama me hakuri da biyya ga mijinki kinji" kai Deedee ta gyada tace "insha Allah bazan sa damuwa a rainaba kuma zanyiwa ya Aliyu biyya kamar yadda kikace" murmushi Ammi tayi tace "Allah yayi miki albarka *Fateemah* yadda kike mana biyya kike karbar duk 'kaddarar da tazo miki to Allah bazai ta 'bar dakeba duniya da lahira" murmushi Fateemah tayi tace "ameen Ammita" daga haka ta share hawayenta suka ci ga da hirarsu irinta uwa da 'yarta Ammi na bata shawarwari sosai kuma tana jin dadin hakan






a 'bangaren Aliyu kuwa tunda ya fita 'dakinsa ya nufa yaje ya kwanata ba abunda yake tunuwa sai laushi da taushin bakin Fateemah jiyake dama zasu dawama a haka walahi bazai kosawa tunani da bayasone ya 'kara fa'do mishi mugun ganin da ya kwamace makanta yayi ta 'dan lokaci shine ganin Fateemarsa matarsa kwance a kan wani 'kato duk annurin dake kan fuskarsa da farinci da feeling 'din da yakeji a kan Fateemah duk sai suka gushe sai tarin ba'kin ciki da damuwa mikewa yayi yashiga toilet yayi wanka ya fito ya sauya kaya yadau key 'din car 'dinsa ya bar gidan






suna ha'de duk 'yan matan gidan Deedee ce kawai babu
suna cikin hira Hafsat tace " 'yanmata al bishi rinki" cikin xumu'di sukace "goro" dariya tayi tace "to ran Juma'a munada casu dan Deedeenmu zata tare a gidan mijinta a zariya" ihu suka sa suna tafawa kowa yana dariya amma banda Zakiyya da ta daskare a gurin ba kalmar tariyace ta 'daga mata hankaliba ilah Zariya da akace zasu huce shike nan duk shirinsu ya wargaje mikewa tayi tana ganin dishi-dishi ta fice daga 'dakin ba wanda ya kula da halin da take ciki sai Hafsat jikinta ne yayi sanyi ta tunu irin tugun hajiya Sareena take na dama fada musu ce ta ziyar ceta mikewa tayi tana yake tace "ina zuwa" daga haka ta fice daga 'dakin




Deedee tunda Ammi ta kwantar mata da hankali ta saki ranta suka cigaba da harko kinta amma can kasan ranta tana cike da fargabar irin zaman da zasuyi da ya Aliyu shine kawai da muwarta yanzu






Zakiyya na fita ta nufi part 'dinsu tana kuka ta shiga parlour ba kowa ta 'karasa bedroom 'din hajiya tana 'kara sautin kukanta kamota hajiya tayi tana tan bayanta lafiya saida ta rage sautin kukanta tace "nashiga 3 haji ran Juma'a Fateemah zata tare gindan yaya Aliyu" "mtsasss" hajiya taja tsaki ta saketa ta koma ta zauna tana cewa "in banda abunki ai farin ciki yakamata kiyi burinmu ya kusa cika" baki Zakiyya ta turo tace "to kinsan a ina xata tare to gurin aikinsa zariya zai tafi da ita" "whattt" hajiya ta fada tana mikewa "kina nufin barin garin zaiyi da ita" kai Zakiyya ta gyada kamuta hajiya ta 'karayi tace "ki kwantar da hankalinki bari muje gidan hajja muji ya za'a 'bulowa al amarin" "to" Zakiyya tace tamike suka shiya suka tafi gidan *HAJJA*






suna zuwa gidan hajja ta tsakar gidanta a zaune tana ganinsu ko salama babu tace "hajiya barkanki da zuwa tunda na ganku haka nasan akai matsala ku shigo ciki muji ya za'ayi"




ciki suka shiga ta tanbayi ya me ya faru suka kwashe komai suka fa'da mata jimma tayi kafin tayi murmushi tace "..............




kuyi hakuri da wannan my fan's




by
*XAHRA*
[8/27, 17:07] Anty Baby: *FREEDOM WRITTER'S ASSOCIATION.* πŸ“•πŸ–ŠοΈ
( _Y'anci don cigaban Mata, y'an ci ya d'ara bauta, freedom writters._ )




*( F.W.A)πŸ–Œ*


https://www.facebook.com/Freedom-Writers-Association-110039363936693/


☘🌷☘🌷
*BAƘIN GIDA*
☘🌷☘🌷


storry and writting
by
*FATEEMAH* *S* *OMAR*


*PAGE* 29-30




.......................πŸ“–Gida Aliyu ya dawo bata parlour kaitsaye bedroom 'dinsa ya huce yaje ya watsa ruwa ya sauya kaya yafito yanufi kitchen ya tadda tayi abunci amma yana kalo ya dora wani ya dafa ya fito parlour yaci duk da ba dadi yayi maiba mikewa yayi ya shiga 'dakinsa har bacci yayi ya farka amma beji motsin Deedee ba mikewa yayi ya shiga parlour ta ba kowa ya 'karasa bedroom ya tura kofar yashiga a zaune ya tadda ita daga ita saiwa 'yar riga iya guwa ta kamata sosai tanata danna phone tana dariya






'kafarsa yaja a hankali sabuda tayi sanyi sosai ya 'karasa kusa da ita ya le'ka phone 'din yaga cart take a WhatsApp ya duba wanda takewa reply yaga Usman ne wayar ya warce ta mike a tsorace dan batasan ya shigoba kalon mamaki take binsa da shi yana huci yafara duba hirartasu da sauri ta kai hannu zata amsa ya rike hannu yana jifanta da mugun kalo kwala ce ta cika idonta tace "binkice fa ba kyau" "hmm sabuda ba abun kirki kuke fa'da ba ko" hawaye ta farayi yashareta ya zaro wayar yacigaba da dubawa






hannu ta 'kara kaiwa yaza amsa ya kauce haka suka rin 'kayi ajiyar zuciya yayi ya kaleta yaga yadda take kunbura fuska ya 'kara fito da phone 'din ta 'kara kawo hannu yarike hannu ya maida phone 'din aljiho takai 'dayan zata jawo yarikeshi yahadesu da wance ya rike da hannu 'daya ya kura mata ido yadda take kokawar kwacewa dariya ma tabashi amma ya maze ya daka mata tsawa yace "ke wai dani zakiyi kokawa?" "to dan Allah kabani phone 'dinta" sakinta yayi yajuwa zai fita tariko rigarsa






juyowa yayi ya fincike rigarsa ita kuma dayake bawani kwari gareta ba kawai saitayi luuuuuuuu ta fa'do jikinsa
ido ya rintse sabunda wani yarrrrrrr da yaji hannu yasa ya matseta ajikinsa har saida tayi 'yar 'kara san-nan cikin sexy voice yace "dama abunda kike so kenan kuma gashi inda jiki nane kin ta 'da" ido ta zaro tafara kokari kwace jikinta dan taji haushin abunda yace da ita






'kara matseta yayi yace "ina kuma zaki tunda jikina kike so kuma nace gashi saikiyi yadda kikeso dani" kuka Deedee ta fashe dashi tana dukan 'kirjinsa tana cewa "ni kasakeni banaso" murmushi yayi yace "kina so mana tunda kike ta'bani" "nifa ba ta'ba ka nayiba kuma inma kamanjikin naka mezanyi dashi kama ba sonka nakeba bare jikinka" zafin maganmagunta ne dayaji yasa ya tureta da iya 'karfisa ta fa'di kasa ta kwala 'kara yana huci yace "so what dan bakya sona nima inba kadara ba me xanyi da mezanci irinki me kai kanta 'dakin kato mtssss" ya fice daga 'daki a fusace






kuka me ciwo Fateemah tasa tana kukan ta 'daga hannu sama tace "Allah kaine kasan daidai Allah kana kalo kasan ni ba fasika bace Allah ka fita dani daga zargin da bayinka sukemun ya Allah ka bayyana gaskiya cikin gaggawa" ta mike tana cije lebe dan ba 'karamin dakuwa tayi a 'kasa ba ta hau kan bed ta cigaba da kukanta






Annur sai dare sosai ya isa Zariya agidan wani abokinsa da sukayi ABU ZARIYA ya sauka dan tunyana hanya ya sanar dashi ya kusa zuwa ko salah be yiba yai kwanciyar sa bai tashiba sai 9:00am ya tashi yayi breakfast yayi wanka san-nan suka zauna shida abokinsa Kamal ya kwashe komai ya fadawa Kamal dayake sai hali yazo daya ake abunta budar bakin Kamal sai yace






"ai kai kayi sokwanci Ibrahim tunfaro lokacin da ka tsara zakayiwa yarinyar shari to ba da gangan zakayi ba kamata yayi ka kusanceta da gaske ko ba ta yarda ba kaifa namijine inda halima kayimata ciki

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads