Showing 27001 words to 30000 words out of 84785 words
Chapter 10 - Farar Wuta Book 1 Complete Hausa By Aisha Aliyu Garkuwa .txt
faɗa lokacin da Fatima ta shigo gidan da daddare, don tun safe tace mata zasu je bikin ƴaruwarsu.
Sai dai maimakon Fatiman tayi dariya kamar yadda ta zata sai kawai tace.
"Go slow ne wallahi ya rike mu a wajen Gandu."
Da haka ta juya ta gaishe da Amma dake yankewa Hafsa farce anan tsakar gidan sannan a lokaci guda ta jawo hannun Aminan dake jikin durum tana kokarin ɗiɓan ruwa a buta suka yi soro.
"Amina dama wanda zaki aura da kika ce min ɗanuwanku ne shine wani Ma'aruf Bakori wanda gidansu yake a sharada?"
Sai da gaban Amina ya faɗi duk da bata san me zata ce ba, ta gyada kai tana kallonta da fararen idanunta da ake gani tar a cikin rashin hasken soron.
"Eh, baki gani a jikin katin? Me ya faru?"
"Bikin da muka je a sharada ne Amina, kuma a layin gidansu, ƙanwar amaryar ce take gaya min cewa ta san duka ƴan gidan kuma da gaske bashi da hankali."
Sai ta girgiza kanta.
"Su Baba fa sun gama duk bincikensu Fatee, har ganin sa ma sunyi, sun ce ciwon ba mai yawa bane, sun ce har aiki yake yi a kamfanin babansa, ba wai bashi da hankali bane gabaɗaya."
Fatima ta girgiza kanta.
"Amina baki san me tace min bane..."
Da sauri ta sunkuyar da kanta sannan ta shiga girgiza shi itama tana faɗin.
"Mutane sun iya yaɗa irin wannan jita-jitar Fatee, ba yau aka fara ba, musamman a sha'anin aure..."
"Yana da wa sunansa Jamal?"
Fatiman ta katse ta, ba shiri ta ɗago ta kalle ta yayin da muryar Baba ta kwanakin baya ke haskawa a cikin kanta, lokacin da Amma ke tambayarsa idan Ma'aruf ƙani ne a wajen wanda suka je bikinsa a shekarun baya.
'A'a, shine dai wanda kuka je auren nasa, ai ya rabu da matar ne daga baya. Wa ɗaya yake dashi sunansa Jamal kuma ya rasu shekaru goma da suka wuce...'
"Ya rasu shekaru goma da suka wuce ko?" Muryar Fatiman ta tambaya tana karashewa da tunaninta.
"Me ta faɗa miki?" Bata san lokacin da bakinta yayi tambayar ba yayin da zuciyarta da abinda take tunanin ƙasusuwanta ne suka shiga rawa ba tare da kwakwaran dalili ba.
"Shi ya kashe wan nasa Amina! Shi ya kashe Jamal ɗin shekaru goma da suka wuce!"
****
"Kar ki ɓata min rai Saratu, don me Allah ya halicce ki a mace? Me zaki yi da ƙwaƙwalwar da ake cewa ko shaiɗan na tsoron kaidin da zaki iya fitarwa ta cikinta?"
Muryar Hajiya Kilishi ta faɗa cikin shirun ɗakin yayin da wayarta ke kare a kunne. Ƙawarta da ta kira Saratun tayi ajiyar zuciya a cikin wayar kafin tace.
"Baza ki gane bane Kilishi, ba zaki gane yadda nake gaya miki cewa matar nan ta addabe ni ba, shi yasa naje wajen malamin nan, amma gashi yanzun ma kuɗin da na zuba na neman tafiya a banza."
Wani murmushi ya suɓuce a fuskar Hajiya Kilishin yayin da fuskarta take fayau! Sai dai a cikin murmushin akwai wani ɓari na sirrin mafi yawan nasarorinta.
"Tsafi gaskiya ne Saratu, amma gaskiyar da bata ɗorewa, kuma na sha gaya miki babu amfanin mallakar abinda ba zai ɗore ba, har wani ƙato a gefe ya isa ya magance miki matsalar da ke kike cikinta?
Sau nawa zan biya miki karatun nan ne? Shekarata talatin a gidan nan kin sani amma babu rana ɗaya da na taba takaws wajen wani malami da sunan taimako. Da yatsa ɗaya nake juya kowa a gidan nan yadda nake so kuma kin san ko ƴanuwana da muke ciki ɗaya su ma basu san wata fuskata bayan wadda Iyalan gidan nan suka sani ba. Shi yasa nake son ki gaya min meye amfanin buɗe miki cikina da nake yi ke da Salamatu? Ba don mu taru akan bigire guda bane? To don me a yanzu zuciya zata ja ki ki kauce?"
Tambaya ce, amma Hajiya Saratun bata amsa ba, don ta san halin Kilishin sarai, ranta ne ya ɓaci amma har a cikin ɓacin nata halayyar ta kan yi rinjaye a zuciyarta. Don haka tana jinta tayi ajiyar zuciya a cikin shirun sannan tace.
"Yanzu a ina kuka tsaya?"
"Yace ita zai mayar can Egypt ɗin Kilishi, ni uwar garke in zauna in kular masa da ƴaƴa."
Ta furta hakan tana furzar da wani irin huci da Hajiya Kilishin zata rantse tana jin zafinsa tun daga nan.
"Bi shi a hakan, kar ki sake ki nuna ranki ya ɓaci, kiyi kwalliya ki tausasa muryarki, ki gaya masa zaɓin da yayi daidai ne, ya duba ɗawainiyar yaranki ya taimake ki.
Sannan ki faɗaɗa murmushin ki a gabanta itama, ki gaya mata ko da ke ya zaɓa ba zaki bishi ba dama. Bayan haka kiyi mata ɗawainiya a lokacin da zai gani, misali, samu yaji da irin su busashshen tattasai kice tunanin amfaninsu kika yi musu, don kwana biyu ne abincin can zai gundure su. Idan kin aikata hakan, ki kira ni sai mu ɗora."
"Kina ganin zan iya Kilishi? Ba kowa Allah ya halittawa irin zuciyarki ba fa?" Muryar Saratun ta tambaya ɗauke da rauni da kuma wani irin tuƙuƙin dake cin ranta.
Sai ta sake wani guntun murmushin tana miƙewa tsaye kafin tace.
"Zuciyar da Allah ya halitta min nazo duniyar nan daban take da wadda nake da ita yanzu Saratu, ni da kaina na sami wannan zuciyar don haka kema ki tashi ki samarwa kanki abinda zai ɗore. Ki kira ni idan kin gama abinda na gada miki."
Da haka ta katse wayar tana mai taya kawar tata jin ɗacin dake faruwa a rayuwarta, da ace tana da ikon juya zuciyar Saratu yadda taga dama, tayi rantsuwa a ciki wata daya kacal zata gyara mata komai, ta samar mata fiye da ƴancin da take dashi a wajen mijin nata tun kafin sake aurensa.
Amma zuciya ce kowa da irin tasa duk yadda ka kai ga iyawa, wani a baki kawai zaka bashi labarin dukkan nasararka amma tasa zuciyarsa ba zata taba iya ɗauka ba. Ƙawayenta biyu kenan a duniya Saratu da Salamatu, kuma bayan abotar tasu, tana zana su ne a cikin wasu mutane da suka taka muhimmiyar rawa a rayuwarta, suka yi mata amfanin da zata rantse ko uwar data kawo ta duniya bata yi mata ba a wajenta, don haka su biyun ne kawai duk duniya kawai take iya buɗewa cikinta su ga ainihin kalolin da take ɗauke dashi bayan farar fatar ta.
Matsalar guda ɗaya ce a wajen kowannensu, zuciyar Saratu bata iya jajircewa abubuwa har tayi yaƙi da iyawarta kamar yadda ita kanta ta furta a yanzu, Salamatu kuma sun sha banban da abinda kowannensu ke wa kallon nasara, don ita yanzu ko aure bata dashi, tafi ganewa yawon kasuwanci ga manyan mutanen da zasu dinga bata kuɗin da suka fi ƙarfin kayan nata.
Ta ja tsaki a hankali tana nufar ƙofar wardrobe ɗin ta, yau ita ke da turakar Baffa, ta gama shiryawa tuntuni wayar Saratun ce ma ta tsaida ita, a cikin wardrobe din ta dauko wata baƙar ledar magani da kuma muƙullin ɓangaren sannan ta nufi ƙofar ɗakin ta buɗe, ta buɗe ta sanda hayaniya ta cika kunnenta, hayaniyar da a yanzu kullum cikinta suke saboda ƙaratowar bikin.
Mutane ne kawai ke zuwa musu Allah sanya alkhairi tun yanzu, musamman daga ɓangaren ƴanuwan su Baffan na can ƙauye, masu kwana ma babu adadinsu don wasu tun wancan satin suka taho ma da zugarsu wai sun zo taya aiki, aikin da kullum sai anyi musu bayanin babu shi.
Don daga harkar jere har harkar abincin da za'aci lokacin bikin da duk wata hidima, kuɗi suka biya a dunƙule wa mutane daban-daban da zasu ɗauki nauyin hakan.
Kamfanika biyu na interior decoration suka biya don su yi jeran gidajen amaren, kawai ƴanuwanta dana Hajiya Maimuna ne ke zuwa su sa ido akan aikin don a hada har da tunanin mata komai ya tafi daidai, don haka su ɗin da suka zo, ba abinda suke ma illa ƙara aikin, don in banda ci su da ƴaƴansu ba abinda suke yini suna yi, dadinta ɗaya kawai basu barwa ma'aikatan gidan komai ba dasu ake girkin da duk wani aikin da ya taso, shi yasa ba wanda ya kai Inna Danejo murna a gidan yanzu ganin duk inda ta juya kawai ƴanuwanta take gani.
Surayya ta fara gani a falon tana danne-danne a wayarta kafin dandazon matan da ke ta fitar da kaya daga kitchen suna yin waje.
Ta wuce Surayyan da bata ko dago ba zuwa tsakiyar falon inda suka fara ganinta.
"Hajiya sannu da fitowa."
Wajen mutum biyar dake rike da wasu manyan fanteku tun na aurenta suka fada.
"Yawwa, waɗannan kayan fa? Ina za'a kai su?"
"Sameera ce tace a fita dasu waje Hajiya, na aikin cincin ɗin da za'a fara ne."
"Cincin kuma? Ina ita Samiran take?"
Tana tambayar kuwa ta fito ita da wata sa'arta mai suna Khadija da take ƴar ƙanwar Hajiya Kilishin, suka fito suna jan ragowar wani buhun sukari da ya kusan kai kwata.
"Cincin ɗin me ake yi shirin yi a gidan nan Samirah?"
Ta tambaya tana katse dariyar da suke yi ta kasa ɗaukar buhun.
"Mama yara ne ke jin yunwa kafin a sauke abinci musamman da safe, shine nace bari ayi cincin sai ya dinga rage musu hanya."
Girgiza kanta kawai tayi tana kallonta, kowa da irin ƙaddararsa a rayuwa, ita tata ta abinci ce, don duk da science take yi a makaranta, amma course ɗin da take son yi a University shima ɓangaren girki ne, (Nutrition and dietetics.)
"Allah ya baku sa'a, kafin ku fara ki kawowa Baffa abincinsa yanzu, can zan je."
Ta faɗa sanda ta juya, a cikin zuciyarta tana lissafin layin da zata saka Samiran daya danganci ra'ayinta nan da shekara guda idan ƙwarya ta fashe!
Sahla ta fito daga ɗakinta a lokacin riƙe da labtop ɗin Munaya tana sake gyara gilasan idonta.
"Mami dan Allah ki bani 1000 muyi subscription, datar da muke streaming ta ƙare kuma Aunty Munaya tace mu kai mata labtop ɗin wallahi ba zata sake siya mana ba."
"Kije ɗaki, na ajiye wasu canji akan mirror ku ɗauka."
Ta san ita da Zahra ne don kullum suna manne da juna, shi yasa bata san me zai faru dasu ba nan da shekara ɗayan nan.
Ta fita daga ɓangaren zuwa harabar gidan kamar wata sarauniya, don duk ɗaukacin mutane kowa tsugunnawa yake yana mata sannu da fitowa yayin take binsu da murmushin da zuciyarta ta wanke shi tsaf, ta tace shi kafin fitowarsa. Kuma ɓangaren Inna Danejo ta fara biyawa ta kai mata maganin cikin ledar nan, na ciwon ƙafa ne wanda Innan tace tana jin daɗinsa saboda haka take sawa ana kawo mata duk wata.
Kuma bayan sun yi ƴar hira da sauran tsofaffin dake wajen da kuma tarin albarkar da Innar ke sanya mata, ta fito zuwa ɓangaren Baffa, kafin ta shiga ta hango Munaya daga gefen ɓangaren tana waya, sai gyara glasses ɗinta take alamun tana sauraren wani abu, kuma fuskarta kaɗai ta kalla ta san a rikice take tunda dama ita ko doguwar magana akayi yanzu zata rikice tace bata gane ba, duk kuwa irin mahaukacin ƙoƙarin da take dashi a ɓangaren karatu, don tun suna yara Jamal ke cewa Ma'aruf da Munaya sune Geniuses (masu kokarin) ɗin gidan.
Zuciyarta ta cunkushe a lokaci guda da ambatar sunan, shekaru goma kenan da shafewarsa a doron ƙasa, amma har yanzu yaƙi barin zukata su huta, don ƙaryane a gidan nan ance an shafe sati guda na kowanne wata ba'a samu wani ya ambace shi ba, hatta ita kuwa tunaninsa na yawan wulga mata a zuciya, ta tabbata da ace Jamal na raye har yanzu to da itace a bayan ƙasa, don ta daɗe da lissafa cewa shi da ita mutane ne da baza su taba rayuwa a lokaci guda cikin duniyar nan ba.
Ta zira muƙullin hannunta ta buɗe bangaren ta shiga. Komai yana nan kamar yadda ta sanshi, don dama ɓangaren a suna yake na Baffan amma ita ke da iko da komai na cikinsa, me ta gayawa Saratu ne ɗazu? Babu abinda ƙwaƙwalwar mace baza ta iya ba idan har ta saka kanta, ta tuno shekarun da ranta ke ɓaci idan ta ɗaga labulen ɗakinta ta hango kyakkyawar surar Hajiya Maimuna na shiga ɓangaren Baffan, idan taci kwalliyar nan tata za'a shafe tsawon dare ana musu da wani cewa bata ajiye kamar Ma'aruf balle ma wanda yafi shi a duniya ba, kuma da tayi tunanin cewa bata don ganinta a wajen lokaci yayi da zata bar mata bangaren ita kaɗai, me ya faru yanzu?
Tayi wani guntun murmushi lokacin da take kunna turaren wuta a jikin burner, a lokacin kuma Samirah ta shigo riƙe da katon tray ɗin dake shaƙe da kayan abincin da ita kadai ta san me ta dafa.
Ta ajiye su daga kasa kujerar da ta san nan ne wajen zaman Baffan sannan ta juya.
"Bana jin zan fito sai gobe kuma, kar ki daɗe a waje."
"To Mami." Cewar Samiran tana saurin fita, sai dai tana isa bakin kofar Hajiya Kilishin ta sake kiranta.
"Da gaske nake miki magana, kar ki wuce goma a wajen mutanen nan."
Kuma duk da ta amsa ɗin sai da taga yadda ranta ya ɗan ɓaci kafin ta fita. Dole ne ma ta ƙara dagewa wajen kokarin fara ɓanbare tarin abubuwa daga jikinsu, don komai ya kusa ƙarewa, wannan rayuwar ba dahir ɗinsu bace.
Fitar ta ke da wuya kuwa taji muryoyi daga wajen suna bin layin gaishe da Baffan da ta hango hasken fitilar motarsa da direba ya sauke shi ta labulen falon. Sai ta taho wajen kofar don ta bude, so take ya fara yin tozali da ita da kuma kwalliyarta kafin wani abu ma na ɗakin.
Sai dai kafin ta ƙarasa ɗin wayar hannunta tayi ƙara, ya kalli lambar dake kiran ke shigowa kafin ta dauka, Kuma abin da muryar cikin wayar ta faɗa tun kafin ta kai ga cewa komai, shi yayi sanadin da zuciyarta ta doka a cikin ƙirjinta sannan wayar ta zame daga cikin hannayenta ta faɗi kasa ta tarwatse!
***
Hasken safiyar ya shigo ta tsakanin fararen labulen ɗakin yana ratsowa har ciki zuwa kan gadon da shima komai a jikinsa fari ne, Rukayya ta motsa a cikin baccinta tana ƙara binne kanta a cikin filon amma tasirin wasu dogwayen yatsu dake shiga cikin gashinta suka hana baccin nata cigaba.
"J dan Allah mana.."
Muryarta ta fito a can kasan numfashinta.
Jawad ɗin dake tsugunne a gaban gadon sanye da singlet fara ƙal da kuma wandon gogaggiyar shaddar daya sanya bayan ya fito daga wanka ya sake motsa yatsun nasa cikin gashinta yana matso da fuskarsa kusa da ita.
"Na gaya miki ina da meeting by 10 a Abuja, ko so kike in tafi in barki anan?"
Bata bude idanunta ba tace.
"And what time is it now? (Kuma yanzu karfe nawa?)
"Eight tana dab da ƙarasawa, kamar yadda zuciyata take dab da shirin fashewa akanki."
Bata san lokacin da tayi dariya ba sannan ta bude idonta akansa.
"Sai yaushe zaka dawo?"
"Sai nayi kwanakin da kika yi Paris."
Ta juya idanunta tana jin yadda yatsun nasa ke ƙara shiga cikin gashinta.
"Ka san bani da matsala ko zaka ninka kwanakin ne."
Ya gyada kansa a hankali.
"Na sani Barbie, na san ni zan haukace..."
Sai kuma yayi shiru yana kallon kyawawan idanunta yayin da itama tayi shirun tana sauraren yadda sautin numfashinsa ke fitowa akan fuskarta.
"You never know what I went through da bakya nan Rukayya, zan iya tsayawa a gaban ko waye in faɗa miki ke daban ce."
Ta lumshe idanuwan nata tana murmushi, tana da tarin hujjojin da zata yarda cewar dukkan maganganun Jawad akanta gaskiya ne, yana ƙaunarta ne da gaske, sai dai maganganun basa taba ƙarasawa har cikin zuciyarta don bata so ya tsallake huruminsa, tafi so ya tsaya a iya matsayin da tsananin kulawarsa gare ta da kuma matsayinsa na ɗan gidan minister da mahaifiyarta ke kwaɗayi yasa ta bashi kawai. Amma akwai wajajen da duk yadda ta kai ga jin sa a zuciyarsa bai isa ya tsallaka ba, Ma'aruf ne kadai mai wannan ikon akanta.
Ta tuna da text ɗin da ta tura masa a jiya ta nambar da aka tabbatar mata tasa ce, wani text layi guda kawai da ta tattara dukkan fatanta a cikinsa tana fatan ya zama silar niyya da kuma ƙudirin da ta gama tsarawa a cikin kanta har ma tayi masa ado da ƙarin wasu kyawawan abubuwan da zuciyar tata ke so.
'M'aruf, Hameeda ta tambaye ka...'
Kuma sai bayan da ta tura ne sannan bangaren ƙwaƙwalwar tata mai hankali ya shiga jero mata kuskure tare da wautar ta, yana gaya mata kamar ba haka ne daidai ba, yana hasko mata tarin yarjejeniyar data yarda da ita a cikin doguwar takardar nan, lokacin da ta yarda tasa hannu akan komai yayin da zuciyarta ke cike da ɗokin rayuwa mai kyau a gaba kamar yadda mahaifiyarta tace, yana gaya mata cewa saboda ta sami saɓanin tunaninta hakan baya nufin cewa ta shirya fuskantar duk waɗannan sharaɗan?
"Jibi zan dawo, ki gaya min zan ƙara samunki dan Allah."
Muryar Jawad ta jawo ta daga tunanin yayin da yake ƙoƙarin ƙara matsowa. Sai kawai tayi murmushi sannan a lokaci guda ta shammace shi, ta ture shi ta miƙe tsaye tana dariya, yayi ƙoƙarin kamo ta amma ta kauce saboda haka shi ya faɗa kan gadon inda ta taso.
"Zo."
Ya faɗa daga kwancen yana kallonta, ta matse kafaɗarta ɗaya.
"Zanje in shirya ne kar kayi missing flight dinka."
"Wani abu zan gaya miki."
Ta ƙara matse kafaɗarta.
"Ka barshi sai na fito."
Da haka ta shige banɗakin tana murmushi yayin da Jawad ya dafe kansa da duka hannayen sa biyu yana jin wani abu kamar taraddadi akan abinda ke shirin faruwa.
Allah ya sani da gaske yana sonta, irin son da bai san adadinsa ba kuma bai san lokacin da ya shige shi ba, abinda ya sani kawai shine a matan da yayi mu'amala dasu a rayuwarsa Rukayya daban ce, komai nata daban ne ta yadda tun daga lokacin da ya santa, sanda suka haɗu a airport zuciyarsa ke bin ta kamar raƙumi da akala. Shi yasa a yanzu da iyayensa ke damunsa da maganar aure ya ture duk wani kokwanton zuciyarsa ya tsayar da abu guda, don ya tabbata idan yayi saɓanin hakan zai zama kamar an bar baya ba zani ne.
Saboda haka a lokacin da ta fito take tsaye a gaban mudubi tana shiryawa, sai ya ture komai ya jawo ƙwarin gwiwarsa ya