Header Ads
Showing 84001 words to 84785 words out of 84785 words

Chapter 29 - Farar Wuta Book 1 Complete Hausa By Aisha Aliyu Garkuwa .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

yafi karfin nasa, shi yasa nake rufe idona a duk lokacin da buƙatar in kwantar dashi ta taso min ina yin hakan."
Tayi shiru na tsawon wasu sakanni tana kallon yadda tasirin maganganun ke aiki a fuskar Amina kamar yadda ta zata kafin ta cigaba.
"Magungunan dake cikin jakar nan har America naje na nemo su Amina, magunguna ne dake birkita ƙwaƙwalwar mutum a lokaci guda ya fita daga hayyacinsa, kuma dama ciwon Ma'aruf abinda yake bukata kenan ya tashi, don haka duk sanda nake shirin yin wani abu da na san zai iya zame min ƙalubale, sai in kwantar dashi in gama duk abinda zan yi kafin ya dawo hayyacinsa."
Ta kai karshen maganar kamar bata karasa ba, don dukkansu shiru suka yi yayin da nauyin kalaman ke zagaye iskar dakin, ba irin ga Amina da taji hannayenta har rawa suke yi ɗauke da sabuwar rikicewar da maganganun suka sata, don yau ne karo na farko da ta ji ciwon Ma'aruf daga makusantansa, ko shi bai gaya mata ba, cewa kawai yayi 'I'm a mess Amina...'
Zuciyarta ta ajiye komai a gefe ta shiga gaya mata cewa har ta gama rayuwarta a duniya ba zata taba iya haɗuwa da wata muguwar halittar irin Hajiya Kilishi ba.
"Na san idan Ma'aruf yayi aure dole ne zargi zai shiga zuciyar wasu idan har na cigaba da rike magungunan sa, don haka wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sa na kawo ki gidan nan, daga yau magungunan nan sun koma hannunki.
Ki ɗauka ki tafi dasu, guda uku ne a ciki, ki ɓalli kowanne guda ɗaya ki bashi a gobe, don jibi zan fara aiwatar da abinda ke gabana kuma a sannan bana buƙatar ganinsa a kamfanin.
Wannan shine aikin ki na farko Amina, kuma idan komai ya tafi daidai, zaki fara ganin daidai bari nayi miki alkawarin farko tun a yanzu, idan na samu abinda nake so Amina zan sa a fitar da ɗanuwanki Aminu ƙasar waje a gyara masa kafafunsa su kamar yadda duke a da."
Shirun da ya sake ratsa ɗakin mai tsawo ne da babu abinda zaka tsinta a ciki kafin Hajiya Kilishi ta kai ƙarshen zancenta da magana ta karshe kuma mafi girman da daki zuciyar Amina babu zato, maganar da daga ita har Amma basu taba hango ta ba balle tasa ta a jerin tunanin Hajiya Kilishin, kuma duk da dauriyar da take da ita a lokacin sai da kalaman suka tasa allon kirjinta girgizawa da karfin da ta san har Mamin ta lura.
"Maganin dake gefe kuma naki ne Amina, ki dauka ki dinga shansa kullum, na san ba zan iya hana Ma'aruf kula ki ba idan har yayi niyya, amma kuma ba zan lazimci wani abu ciki ba don babu shi ko kadan a cikin lissafina!"
***
Yaya kuka ga sharaɗan farko na Kilishi??
Ta yaya kuke ganin Amina zata bullo musu??😅😅
Ta yaya zata sa komai ya faru ba tare da Hajiya Kilishi ta ɗorar da zargin da take mata ba??
Mu dai jira hukuncin Amma ko??
And the Uban gaiyar is over there going crazy akan ƙafafun Amina ba tare da ya san me ke shirin tunkaro shi ba!😅
Wani ya gaya masa cewa su Rukayya ma na can nayi masa nasu shirin suma...
Jawad ma kuma yana nasa!
A tsakiyar komai kuma dai, zamu samawa Ma'aruf wannan nutsuwar da yake nema insha Allah.😍😍
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
SANARWA.
~~~~~~
Assalamu alaikum.
Fatan alkhairi ga tarin Masoyan FARAR WUTA da ma duk wani littafi da ya kasance nawa. A lokaci irin wannan nakan nemi kalamai in rasa, nagode da dukkan support ɗin ku tun daga shafin farko na farar wuta zuwa in da na tsaya.
Ina kuma ganin tarin saƙonni da ƙorafin ku akan rashin samun update akan lokaci, ina jin kalmar HAKURI kamar tayi kaɗan, amman ita kaɗai nake da ita. Na fara littafin nan ne ba tare da na hango tarin uzururrukan da suka dinga taso mun ba, suka kuma zama dalilin rashin samun update ɗin da ba kwayi.
Na sani...
Na kuma fahimta tun kafin ku furta.
Kuyi HAƘURI, don saboda dalilai da yawa littafi na biyu (Farar Wuta 2) zai koma Paid Story cikin tsarin da nake fatan dukan mu zamu ji daɗin shi. Wanda na ɓatawa a farkon tafiyar nan zuwa yanzun, banda kalamai masu yawa sai neman afuwa da kuma bada hakuri.
Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kuma bamu aron lokacin sake haduwa dan karasa tafiyar FARAR WUTA.
Kar ku manta yanzu tafiyar ta fara...
Zan baku labarin yadda nasara ke samuwa babu boka ba Malam!
Zan baku labarin soyayyar Ma'aruf da wataƙila zata narkar da zuciyarku kamar ruwa.
Zan kuma baku labarin yadda mata ke samawa kansu mafita ta hanyar wayo da dabarar da Allah ubangiji ya halitta a ƙwaƙwalwar kowacce mace.
Ku tuntube ni ta wannan lambar. 08067794315.
Nagode muku fiye da yadda baki zai iya furtawa.
#AyshaShafi'ee
#fikrawriters
#FararWuta.

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads