Showing 66001 words to 69000 words out of 84785 words
Chapter 23 - Farar Wuta Book 1 Complete Hausa By Aisha Aliyu Garkuwa .txt
stand ɗin Tvn da dubu tamanin da biyar ta bayar aka siyo shi sannan tace.
"Gidan shiru ke kaɗai baki ko kunna Tv ba?"
Da wani murmushin a fuskarta tace.
"Ai ba'a hada Tvn ba har yanzu Mami."
Muryarta ta fito ƴar ƙarama a cikin shirun dakin, kamar tana son ta shaidawa Hajiya Kilishin ƙanƙanta da kuma rauninta.
"Baku gaya min ba ai, gashi jiya kuwa yaro mai gyaran satelite ya shigo har cikin gida, da ya karaso ya hada muku, amma a bar ki a gida haka shiru, shi ya fice ya tafi hadaniyar gabansa ba zai tuna da wani sha'anin Tv ba.
Sai ta sake girgiza kanta tana cigaba da murmushin.
"Ba komai Mami, duk sanda aka sa baza'a makara ba ai."
Ta fadin hakan lokacin da take kokarin mikewa, amma a lokaci guda Hajiya Kilishin ta tsayar da ita.
"Ina ziki je kuma?"
"Mami, kayan breakfast zan kawo miki."
Ta faɗa taka kallonta, sai ta girgiza kanta.
"Barsu nagode, dawo ki zauna."
Umarnin dake cikin muryar ya kaɗa hantar ta, taji wani abu yana ƙoƙarin ɓallewa daga cikin zuciyarta, amma sai tayi saurin ture hakan ta dawo ta zauna ɗin, hannunta na taɓa hannun kujerar gefenta kamar tana neman taimakon ta.
Kuma zaman nata sai ya zama kamar shine farawar wani shafi na farko a rayuwata, don watakila idan zata bada labari, zata fara ne ta kansa, daga lokacin da kafafunta suka sake komawa kan carpet ɗin nan da kuma lokacin da muryar Hajiya Kilishi ta sake ratsa shirun ɗakin da cewar.
"Amina kunyi waya da mutanen gida kuwa jiya?"
Sai da ta haɗiye wani dunƙulen abu da bata san sunansa ba a kirjinta sannan ta girgiza kai.
"A'a Mami, na kira su dai jiyan amma bai shiga ba."
"Ina wayarki?" Kai tsaye ta sake wata tambayar da ta fito kamar tsawa.
Kan Tv's stand ɗin nan ta nuna inda bayan fitowarta da safen ta saka ta a caji.
"To matso ki kira su."
Wannan karon sai da ta kalle ta tsawon wasu sakanni fuskarta na haskawa da mamaki sannan ta matso a hankali zuwa wajen wayar, lokacin da ta cire ta daga caji taji kamar hannunta na rawa amma tayi saurin fara dannawa ta lalubo nambar Amma.
Sai da ta sake kallon Hajiya Kilishin da murmushin fuskarta ya rage tasiri kafin ta kara wayar a kunnenta, kuma cikin wata iriyar sa'a, bugu ɗaya biyu sai Amman ta dauka, sautin muryarta kadai ya doka wani abu a ƙirjinta tun kafin ta fahimci abinda take faɗa.
"Amina yi haƙuri, tun jiya bamu kira ki ba, muna asibiti ne sai da safen nan muka fara samun nutsuwa..."
"Asibiti? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!... Me ya faru Amma? Me ya faru?"
A yanzu ta tabbatar hannun nata rawa yake, don tana jin yadda yake tafiya tare da bugun zuciyarta.
Daga cikin wayar Amma tayi ƙokarin gyara muryarta kaɗan sannan tace.
"Aminu ne mai mashin ya taka shi jiya da daddare a wajen aiki, amma sun ce jikin nasa da sauƙi kar ki ɗaga hankalinki, yanzu mu ma zamu shiga mu ganshi..."
Zancen ya katse a lokaci guda da Amina ta nemi wayar a kunnenta ta rasa. Hajiya Kilishin da a yanzu ke tsaye akanta riƙe da wayar tasa hannu ta ɓare bayanta ta fito da batirin ta jefar dashi gefe, sannan ba tare da ɓata wani lokaci ba ta karya wayar gida biyu itama.
Kuma taku biyu kawai ya mayar da ita baya kan kujerar da ta taso, ta cigaba da kallonta har a yanzu da ragowar murmushin nan a fuskarta kafin muryarta ta fito cikin wani irin sauti da yake ainahin halittar ta, sautin da yake manne a kirjinta tare da zuciyarta dake ƙawata mata tarin hanyoyin da kullum suke ɓullewa ga nasararta, sautin da a duniya kaf, mutum huɗu ne kawai suke sanin da kasancewarsa, sai a yau da ta zabi Amina ta zaman cikon ta biyar ɗin, cikon da take fatan zai zama mataki na ƙarshe da take da yaƙinin zai kai ga nasararta.
"Barka da shigowa cikinmu Amina."
Kalamai biyar ɗin data furta kenan wanda ta lissafa cewa adadinsu ya dace da lambar matsayinta, murmushi kan fuskarta cika taf da tarin kalaman da take shirin ɓare mata a yanzu wanda zasu sa ta fahimci wacece Kilishi tun daga tushe da kuma dukkanin abubuwan data aikata a rayuwarta.
***
Wane shiri Ma'aruf ke yi akan ƴarsa Hameeda da kuma Ruƙayya?
Me ya yankewa zuciyarsa akan Amina da har Ishaq ya fahimta?
Ku gaya min ina rayuwar gidan nan ke tafiya?
Munaya and Ishaq, me kuke tunani?
Hajiya Kilishi...
Ina gaya muku har yanzu sunan matar nan kawai kuke ji, next chapter zata buɗe muku abubuwa da yawa game da ita...
Babi na gaba zai nuna muku me ake nufi da ainihin kissa da kisisina irin ta mata kamar Kilishi, wanda suka yarda cewa kowacce mace zata iya samun duniyar da take so a tafin hannunta... Ba boka ba malam!
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
BABI NA SHA UKU.
~~~~~~~
There's a part of me that likes to beleive everything will be okay, then there's another that breaks down every chance it gets.
- Unknown.
**
Dukkan wata ma'ana ta mamaki da kuma tashin hankali shine yadda fuskar Amina tayi a lokacin da take kallon Hajiya Kilishi.
"Taɓa Aminu dana sa akayi tsaraba ce ga ƙwaƙwalwar ki Amina don ki saurare dukkan abunda zan gaya miki da kyau, ki yarda da dukkan kalamaina sannan kuma zuciyarki ta tabbatar da cewar Kilishin da zaki sani a yanzu da gaske take al'amuranta."
Tayi shiru bayan ta faɗi hakan hannunta na jawo wayarta da ta ajiye a gefe, babu ƙarar kiran dake shigowa alamun a silent ta saka ta.
"Ya akayi Awwalu?"
Muryar tata da ta canja tar ta tambaya cikin wayar bayan ta kara ta a kunnenta... Har a lokacin Amina bata motsa daga yadda take zaune ba, idanunta basu canja daga yadda suke kallonta ba, sannan ƙwaƙwalwar ta bata wartsake daga mamakin dake zagaye da ita ba, Ƙirjinta dake ɗagawa cikin numfashi mai nauyi shine kaɗai abinda zai sa ka san cewa idan ka taɓa ta ba zata tafi ta faɗi ba.
Wataƙila magana guda ɗaya aka fada a cikin wsyar wadda ta gamsar da Hajiya Kilishin, don bata ƙara cewa komai ba ta kashe ta kawai ta sake mayar da ita gefenta, sannan ta sake kallom Aminan, hasken fuskarta na yayewa alokaci guda
"Duk abinda zaki ji a yanzu ya zama tsakani dake ne Amina, idan ba haka ba a ƙarshen zancena zaki gane abinda zai faru idan har kika sako mutum na ukun mu a wannan zancen koda kuwa mahaifiyarki ce.
Da farko mu bar duk wani kewaye-kewaye mu tafi ga abinda yasa kika shigo gidan nan, tunda ni dake dama duk wani mai hankali mun san akwai dalilin aurenki da Ma'aruf..."
Ta gyara zamanta kaɗan sannan ta cigaba...
"... Cire mahaifinki ki ajiye shi a gefe, amma ko mahaifiyarki ta san ruwa baya tsami banza, a muryarta kawai na fahimci cewa irin zurfin tunaninta kika ɗauko Amina, ku duka kun san ba kowacce mace ce zata taka irin matsayin da kika taka a banza ba, zan ƙara tabbatar miki cewa shigowar ki cikin gidan nan dama cikin rayuwar Ma'aruf wani abu ne da ba don taimakona ba, ba zaki taɓa samunsa ba ko zaki mutu sau ɗari ki dawo, saboda a rana guda zamu iya samun mata dubu da zasu yarda da auren Ma'aruf ko da kuwa ciwon da yake dashi yafi haka tasiri, don ba'a wayewar kowacce rana mata ke samun namiji irinsa ba.
Kuma shi kansa Amina, da an bashi zaɓi na sani tsaf zai kawo macen da zata fi ki a komai don irinsu kawai ya sani kuma yake mu'amala dasu, amma sai nayi amfani da ƙarfina da kuma ikona nace ke kaɗai za'a bawa wannan matsayin wanda dole kowa ya yarda da hakan, don haka duk wata soyayya da kika ga kina samu daga mutanen gidan nan dama shi Ma'aruf ɗin da ya fara saurarar ki duka saboda ni suke miki ba don komai ba, ni na ɗora su akan turbar zuciyarsu ta so ki kuma hakan ya zame musu kar dole."
A yanzu Amina tayi ƙoƙarin sunkuyar da kanta tana kallon hannayenta dake faman rawa suna kakkarwa akan cinyarta, zuciyarta na bugawa ne kamar zata faso kirjinta ta fito yayin da kowanne kalaman Hajiya Kilishin ke shiga kunnenta da tsantsar rudani da kuma tashin hankalin da akace ba'a saka masa rana.
Kuma shirun da Hajiya kilishin tayi baiyi tsawon da zata iya fitar da komai ba lokacin da muryarta ta cigaba da cewa.
"Bari in ɗauko miki komai tun daga farko Amina, ta haka ne zaki fahimci zance na.
Lokacin da ina yarinya a wajen kakata na girma, ita ta raine ni tun daga lokacin yaye har girma na, a wajenta na samu tarbiyya da kuma tarin wayo da dabaru irin na zaman duniya, har yasa tun a ƙananun shekaru ina iya kallon rayuwar mutum na bashi shawara mai kyau da zata ɓulle ga matsalolin sa, hakan yasa ƙawayena dama mutanen unguwar a lokacin suka laƙaba min sunan ƴar baiwa.
Bayan wani lokaci sai wannan kakar tawa ta rasu don haka dole na koma gidanmu inda naje na tarar da tarin ƴanuwana, don mahaifinmu matansa uku ne kuma ƙaramar cikinsu wato mahaifiyata ce kawai mai ƴaƴa tara, sauran biyun akwai mai goma sha ɗaya da kuma sha uku.
Rayuwar gidanmu ba dadi sam, saboda a wajen kakata na saba komai namu mu uku ne kawai dani da ita da kuma wani almajirinta Awwalu da take riƙewa, don haka sai rayuwar gidan yawan tazo min a wuya, gashi babu ruwan kowa dani hatta mahaifiyata kuwa da hankalinta yafi karkata kan yayyena da suka fi girma a lokacin, don haka da lokacin shigata babbar sakandire yayi sai na samu mahaifina nace ya maidani makarantar kwana don zata fi mun daɗi, al'amarin kamar ba zai yiwu ba da ƙyar da rabo dai na samu na tafi.
A can na hadu da ƙawayena biyu kuma ƴanuwan da zan iya kira da na jini wato Salamatu da Saratu, wadannan mutane biyun Amina sunyi min duk wani gata a lokacin zama na a makaranta da ya kamata ace iyayena ne suka yi min, hatta kuɗin jarabawar karatuna tsaf su suka biya min har muka kammala, don ban daɗe da shiga makarantar ba mahaifina ya rasu abubuwa suka sake harigitsewa a gidanmu.
Kowacce mace taƙi fita tare da ƴaƴanta kuma aka ƙi a raba gado kowa ya koma yana zaman kansa ne da kuma zaman gasa a tsakani don kowacce mace tana so ne ace ƴaƴanta sune suka fi samun arziƙi, musamman Innata da take ganin itace ƙarama an riga an rainata ita da ƴaƴanta don haka bata damu da duk wata hanyar da yayyena ke bi su samo kuɗi ba indai za'a samun, burin kowacce kawai ace ita da ƴaƴan ta su ke ƙyallin maiƙo a gidan.
Abinda nazo na tarar kenan bayan na kammala makaranta na dawo, wani abu da tun bana saka shi a raina har ya zamo kwanci tashi nima tunanina ya karkata ga hakan, sai dai ni tawa ƙwaƙwalwar ta raina irin hanyoyin da suke bi, na kasa yarda cewa mutum ba zai iya magance matsalolin kansa a rayuwa ba sai ya tsugunna neman taimakon wani daban, don haka na shiga amfani da ƙwaƙwalwata wajen cimma manufata.
Almajirin da kakata ta riƙe Awwalu yana aikin masinja a wani kamfani, da taimakon sa da kuma dabara ta na samu aiki a kamfanin a matsayin mai gyara da kuma harhaɗa takardu... In taƙaice miki zance Amina, wata na biyu a wajen nan na fara karbar kuɗi sama da albashi na ba tare da kowa ya sani ba, kafin a shekara kuwa, ni da Awwalu muna samun daidai da abinda ma'aikatan wajen nan ke samu, ban taɓa bawa wani jikina ba sannan ban taɓa bin wani malami ko boka ba, da wayo da dabarata nake komai ta yadda babu mai zargina kuma dukkan wani bincike ba zai taɓa biyowa ta kaina ba.
Kuɗin da nake samu a kowanne wata sai da ya zama hatta a cikin gidanmu babu wanda ake kallo sai ni, mahaifiyata da ƴanuwana duk suka dawo suka raja'a a kaina, aka shiga bani wani irin girma da ban san yana wanzuwa a duniyar nan ba, ya zama zan iya taka kowa a gidanmu in zauna lafiya, nasa aka rushe ɓangaren ɗakunan mu aka gina mana danƙarere da ya tsone idon sauran ƴanuwana kafin daga baya suma su dawo su kwantar da kansu."
Muryarta tayi shiru a daidai wannan lokacin alamun ta tuna wani abu da ya saka ta murmushi, wani murmushi da har sautin sa sai da ya fito kafin tace.
"A wannan lokacin ne kuma na nemowa kaina mijin aure Amina, munyi ƙoƙarin canja kamfanin aiki ne ni da Awwalu don na yarda da karin maganar da hausawa ke cewa zama wuri ɗaya tsautsayi, don haka muka je kamfanin Bakori a wata ranar laraba, inda kafin mu shiga na hango Alhaji Mansoor ya fito daga ciki ya shiga motarsa, tun da na ganshi a wannan lokacin na sawa zuciyata cewa shine mijin aure na, don haka bamu nemi aikin ba nace da Awwalu mu juya, kuma kafin sati ya zagayo na bi hanyar da sani na ya manne a zuciyar Alhaji Mansoor.
Na kashe kuɗi sosai a wannan lokacin duk da ba sai na gaya miki yadda na aiwatar da komai ba zan gaya miki cewa sati guda na shafe ina siyan shafi guda a jaridar da Alhaji Masoor ke karantawa, ana wallafa hotona cikin irin ayyukan da na san dole suka ja hankalinsa.
Har da masinjan ofis ɗinsa da ma direbansa na haɗa baki dasu suna bashi labaraina, kuma bayan ya yarda da auren nawa, sai da na toshe bakin mutane da yawa wajen fallasa wani abu mummuna akaina.
Lokacin da na shigo gidan nan kuwa Amina da naga Maimuna, a lokaci guda na raina kaina na kuma ƙara yarda cewa sa'ata ce kawai ta shigo dani cikin rayuwar Baffa, don wanda yake da mata irin Maimuna babu abinda zai kaishi auren irina.
Amma ban damu sosai ba, tunda na san na shigo daular arziƙi ne kuma na ciri tuta a cikin ƴanuwana da a lokacin suka maida ni kamar mahaifinmu saboda biyayya.
Ban daɗe ba lokacin da Maimuna ta sami cikin Shukra ƴarta ta uku, don haka sai nayi amfani da hali irin nawa na ja ɗanta na biyu wato Ma'aruf a jikina, na so haɗawa har da Jamal ma amma shi da yake yafi wayo a lokacin sai ya mannewa uwarsa.
Ni na yaye Ma'aruf da hannuna Amina, ni na raine shi tun daga wannan shekarun har zuwa girmansa, don ko bayan haihuwar Maimuna bai bar wajena ba itama kuma bata yi magana ba saboda nauyi na da take ji a sannan, don a lokaci guda na zage na karɓi gidan, ni nake yin komai musamman da bata da lafiya, bayan tayi haihu kuma ni nayi ɗawainiyar da ƴanuwanta ma basu yi ba, hakan yasa a lokaci guda na samu soyayyar kowannensu, hatta Baffa kuwa, don sanda ya aure ni ba zan tantance irin son da yake min ba, amma a cikin shekara guda sai da na tabbata ni da Maimuna munyi kunnen doki a zuciyarsa.
Soyayyar kowa na siya tsakani da Allah don bana yarda da gaibu Amina, kamar yadda baba yarda da aikin wani boka ko malam da baya zuwa ko'ina, ni ina yin shiri na shekara da shekaru ne ba na wani ɗan lokaci kaɗan ba.
A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar mana har ta kai na fara haihuwa nima, a wanann lokacin tsananin kirki da kyautatawata yasa na kere Maimuna a zuciyar Baffa ta yadda ita kanta bata damu ba, don tana ganin cewar na cancanci hakan."
Tayi shiru wucewar wasu sakanni tana kallon Aminan kafin ta cigaba.
"Bari na gaya miki wani daga cikin babban sirrina don ki ƙara tabbatarwa cewa da gaske nake al'amarina... Nice na gurguntar da Maimuna..."
Babu shiri Amina ta ɗago ta kalle ta, idanunta na haskawa da tsananin mamakin da yake ƙaruwa akan wanda take ciki. Sai kawai tayi murmushi mai zurfi tana kallonta itama.
"Ƙwarai Amina, ni na saka Maimuna ta rasa ƙafafunta, kin san dalili?"
Ba ta bata damar amsawa ba ta cigaba.
"Na gaya miki Maimuna tana kyau, to labulen ɗaki na kawai nake ɗagawa in hango ta ranar girkinta ta nufi ɓangaren Baffa, idan tayi kwalliyar nan bana iya daurewa kishina dake tasowa Amina, rana daya na yanke cewar ba zan iya jurar cigaba da ganin zuwanta ba don haka takanas na tafi asibiti na samu wani ma'aikaci a ɓangaren ƙashi, na bashi maƙuden kuɗaɗen da a lokaci guda ya bani wani magani mai kama da poison wanda ke lalata har ƙashin mutum.
Kuma sai da na jira har bayan watanni huɗu da rashin lafiyar zazzaɓi ya kamata sannan na haɗa baki da wani yaro daga Nijar yazo har gida yayi mata allurar maganin nan a matsayin likita, kuma babu wanda ya san ni na dauko shi don nambarsa na sanya a wayar Baffa da sunan likitan gidan Dr. Ashiru, nace idan yazo yace Dr. Ashirun ne ya turo shi.
Kuma bayan yayi mata allurar ƙafafun nata sun lalace gabaɗaya na bashi kuɗi ya koma ƙasar sa Nijar, shi kuma Dr. Ashiru yazo yace bai san yaron ba, da aka duba lambar aka ga ma ba tasa bace dole aka haƙura don ko ƴan sanda basu iya samo komai ba.
Kuma bayan haka ni na zauna nayi jinyarta Amina, tun kafin a yanke ƙafafun har muka je India aka cire su gabaɗaya, shekara guda da rabi na ɗauka ina jinyarta, na hana kowa wannan ɗawainiyar hatta ƴaƴanta da ƴanuwanta tunda na san na samu abinda nake so, na san tsawo na da nata ba zai taɓa daidai a idanun Baffa ba, kuma hakan ya ƙara min ƙima a idanun kowa a gidan nan ta yadda nake cin kare na babu babbaka, kowa yana girmama ni da bani darajar dana siya a wajensu, hatta ƴaƴan Maimuna a idon kowa kamar nawa suke don babu adadi su Munaya zasu zo su faɗa min abinda mahaifiyar tasu ma baza su iya faɗa mata ba ko kuma su nemi shawarata akan abinda ita bata ma sani ba.
Don haka yanzu na san kin fahimci cewa saboda ni kika samu soyayyar kowa gidan nan, da kuma abinda nake nufi cewa duknwanda kika furtawa wannan zancen kamar kin bude masa kofar lahirarsa ne."
Muryarta tayi shiru a wannan lokacin,