Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 84785 words

Chapter 12 - Farar Wuta Book 1 Complete Hausa By Aisha Aliyu Garkuwa .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

lalace ba kamar yadda yayi fata a farko, sai kawai ya mayar da hankali kan aikinsa kuma yawan aikin ke sa shi sha'afa da zancen auren sai wasu abubuwa kamar wannan sun faru da zasu tuna masa cewar shima yana jiran faruwar auren ne don ya fara nasa sabon binciken da har cikin zuciyarsa yake jin cewa wannan hanyar zata iya kaishi ga nasarar da ya shafe shekaru yana lalubenta a cikin duk wani abu da ya danganci kayan Jamal.
Misali irin lokutan da Mamin ke kiransa ta bashi wasu bayanai na cewar an kai kaya gidansu yarinyar ko kuma ya turo da wani adadin kudi za'ayi abu a kaza, abubuwan da suke sa shi yana jin cewa da gaske auren zai yi don Baffa ma ya kafa sharaɗin cewa gidan zai dawo ɓangaren da Baba Alhaji ya taɓa zama, yaje kamar yadda Aa ya marta har sau biyu yaga gyaran da ake yi, amma daga haka bai kara tunawa ba ya cigaba da harkokinsa don damuwarsa ba sai ta komai yayi daidai bane, ta ya iya kammala abinda ke gabansa ne kafin lokacin don ya sami nutsuwar da zai yi dukkan bincikensa akan yarinyar.
Ya cije leɓɓensa a hankali yana tuno kalaman da Faruk ya faɗa masa kwanakin baya.
"Sake yin aurenka shawara ce mai kyau B, amma me yasa sai wannan yarinyar? Kace mahaifinta ba wani bane, kuma kaima ba saninta kayi ba balle ince kana sonta ne, beleive me akwai tarin ƴaƴan masu kuɗin da har layi zasu yi idan kace zaka zaɓa."
Ya faɗi hakan ne ranar da Baffa yasa aka raba katin ɗaurin auren ga kowa a Office ɗin kuma mamaki ya kama su ganin cewa har da sunansa, don haka Faruk ɗin yayi wannan ƙorafin ne bayan ya shaida masa yadda al'amarin ya kasance. Kuma kallonsa kawai yayi a lokacin da dukkan tunanin da bai zo kansa ba, cewar iyayen yarinyar ba masu arziƙi bane, ya sani cewar maza irinsa basa aure a irin waɗannan gidajen, misali aurensa da Ruƙayya shine daidai, don ko irin manyan mutanen da suka halarci ɗaurin auren nasu daga bangaren mahaifinta ma wani abu ne.
Amma baya jin ko bashi da wani abu da yake nema daga yarinyar hakan zai dame shi, don ba auren ko itace a gabansa ba, kuma kuɗin mahaifinta ba abinda zasu tsinana masa kamar yadda na mahaifin Rukayya ma basu kare shi da komai ba sai abinda yake ganin yanzu har dasu a silar sa. Tuna cewar bai ma taɓa ganinta ba har yanzu yasa ya jinjina kansa a hankali, bai sani ba idan ya kamata a kira wannan al'amarin auren gaske bane wannan.
"Ina kika baro masu yin cin-cin ɗin ne da kika biyo ni?"
Yaji Mami na tambayar Samirah bayan ta ajiye wayar, sai dai bai bari ita ɗin ta bata amsa ba ya miƙe tsaye, muryarsa da zurfi yace.
"Zanje in dawo."
Sai ta girgiza kanta..
"A'a, kaje ka kwanta ka huta kawai, ni zan kwana da ita anan, ka tafi da Samira ka ajiye ta a gida sai ta ɗebo min ƴan kayan kayan da zamu buƙata zuwa, zan kira Malam Sani ya kawo min."
Ya cije leɓɓensa kaɗan yana bin maganganun nata kafin ya gyaɗa kansa sannan yayi mata sallama ya juya tare da ɗaukar hularsa da ya ajiye daga kan wata drawer a gefe.
Samiran ta biyo bayansa, kuma har ya isa waje jikin motarsa, zuciyarsa na riƙe da yadda muryar Mamin ta fito da tsantsar damuwa da kuma kulawar da ba mai iya ƙiyasta yawanta, a lokuta da yawa yasha ƙiyasta yadda zuciyarta ke iya ɗaukar damuwar tarin mutane da tarin kyautatawa ga duk wani mahuluki da zai shigo hanyarta balle kuma shi da kowa ya sani cewa matsayinsa daban ne a wajenta.
Ya san itace ja gaba akan komai na bikin nan, amma duk da wannan hadaniyar ta tsallake ta zata zauna, bai san irin son da yake yiwa Hajiya Maimuna mahaifiyarsa ba bayan tsananin girmanta da yake gani, amma Mami zai ajiye ta ne gefe ya tara dukkan ƙaunar waninta a wani gefen, don yana daga cikin abinda yasa yake son yayi tsawon rayuwa mai kyau don ya kyautata mata.
A sanda lokaci ke wucewa da wannan tunanin a zuciyarsa, a lokacin Hajiya Kilishi ke girgiza kanta daga cikin ɗakin asibitin bayan fitarsu, zuciyarta na ƙara gaya mata cewar ba haka tsarinta yake ba, ita ke da ikon ƙaiyade duk mutanen da zasu shigo rayuwar Ma'aruf, don haka bata zana cewar abubuwan da ya rasa a baya zasu waiwayo shi nan kusa ba. A tunaninta yadda yarinyar tayi masa nisa haka tayi a zuciyarsa ma, a tunaninta ko zai neme ta sai shekaru sun ja tukunna a lokacin da hakan ba zai shafi tsarinta ba, amma har me tayi a yanzu da duniyarta zata fara girgizawa?
Ta ƙara girgiza nata kan a fili tana cigaba da kallon fuskar Hamidan da kuma yadda ɗan ƙaramin ƙirjinta ke ɗagawa wajen fitar da numfashi mai nauyi, a ɗaya gefen ƙwaƙwalwar ta tana hango idanun Ma'aruf da suka tafi ɗauke da tsananin damuwa da kuma ƙaunar yarinyar dake nunawa ƙarara.
Ta kuma girgiza kanta wannan karon a hankali, ai alƙawari ne cewar ba zata taɓa iya raba zuciyar Ma'aruf tare da kowa ba, sau nawa zata zana cewar shi nata ne ita kaɗai? Ba har da tsoron wannan yasa ta haɗa aurensa da yarinyar data san ba zata taɓa tasiri akansa fiye da ita ba? Ko uwar data haife shi a yanzu ta isa ta raba soyayyar sa tare da ita ne balle kuma wannan sabuwar halittar? Ta ƙara gurgiza kanta, ba lokacinta bane yanzu, ba lokacin da zata shigo rayuwarsu bane yanzu, bata tsara mata waje ba sam.
Numfashin yarinyar har yanzu take kallo tana so ta kai karshen lissafinta... Lissafin da ta fara tun a lokacin da wayarta ta suɓuce daga hannayenta a lokacin da Ma'aruf ɗin ke mata bayanin samun yarinyar. Kuma wucewar wasu sakanni kawai, tunanin nata ya kai kan gaɓar da kwakwalwarta tayi tanadinsa tun a gida...
Gaɓar da take shirin faruwa da zaren wani makamancin tarihin da ta taɓa ja a baya, fuskar Jamal ta haska a cikin kanta a ranar da ya shiga har cikin ɗakinta ya gaya mata cewa bata isa ba, wani murmushin ya suɓuce a fuskarta cike da fatan ruhinsa ya iya ganin yadda lokaci ke bata tarin damar dake ƙaryata kalamansa, tana fatan ace kabarinsa zai buɗe don yaga sabon saƙon da zata aika masa a daren yau wanda zai ƙara ƙaryata kalamansa fiye da cikin masaki.
Ta miƙe a hankali ta nufi wajen da ta ajiye jakarta, kan teburin da Ma'aruf ya ajiye hularsa, zata yi komai ne hankalinta a kwance don ɗakin asibitin shi zame mata mafaka mai kauri daga duk wani tunanin da zai iya taɓa farinta.
Ta gama tsara hotunan komai a cikin kanta har tayi musu fenti ma, sannan hannunta ya jawo jakar da niyyar buɗe ta....
***
A cikin ɗakin, da misalin ƙarfe goma na safe, Ruƙƙaya ta kalli mahaifiyarta da fararen idanunta dake shaida tashin hankali da kuma fargaba ƙulli-ƙulli, ta girgiza kanta tana share hawaye.
"Wallahi Maamah Hanan ƙawata ce ta haɗa ni da ita, tace ta taɓa yin aiki da wata ƴaruwarta suna da ƙoƙari sosai, shi yasa banyi tunanin komai ba na ɗauke ta a lokacin, kuma itama ta taɓa fada min inda take amma na manta."
Kukanta ya ƙaru lokacin da ta sake cewa.
"Na shiga uku Maamah, idan na rasa Hamida ya zanyi da rayuwata? Da me Ma'aruf zai sake kallona idan har babu ita?"
Hajiya Nafisa, mahaifiyar Ruƙayya na zaune a cikin ƙaton falon gidan na ƙasa, sanye take da wata doguwar riga irinta larabawan dubai, kanta daure da ƙaramin mayafin rigar yayi da wayarta ke riƙe a hannu.
Idanunta na kallon Ruƙayyan ne da tsananin takaici bayan tashin hankalin da suka tashi dashi na ɓatan Hamida, sai jiya da daddare jirginta ya sauka daga Paris, don haka ko da ta dawo ta hawo samanta bata nemi kowa ba tunda maigidan ma baya ƙasar. Sai a safiyar yau da ta tashi ne sannan ta san Ruƙayya bata gidan saboda haka ta nemi Hamida da mai aikinta Mary amma sai su Jamila da Aisha masu share-share na gidan suka shaida mata cewar ai kwana biyu kenan Mary ta fita da Hamidan kuma bata dawo ba.
Saboda haka kai tsaye ta kira Ruƙayyan ta shaida mata cewar ba'a san inda Hamida da Mary suke ba, kuma wucewar minti talatin sai gata ta ƙaraso cikin tashin hankalin da yafi nata, kuma a zaton ta da tazo kai tsaye zata kira Maryn ko kuma ta bita zuwa address ɗin gidansu ta karɓo yarinyar amma sai gashi tana gaya mata wai lambar Maryn bata shiga kuma ita bata san inda take ba.
Allah ya sani idan har tana da wata matsala a rayuwarta to akan Ruƙayya ne, don babu abinda ta nema ta rasa a duniyar nan illa haɗin kan ƴar tata, ita kaɗai ce mace kuma babba a cikin maza huɗu amma a abubuwa da yawa ta kan gwammace mu'amalarta da mazan akan ita.
Ta sani cewa tun daga lokacin da Ruƙayya ta fara hankali a duniya ta rasa ta, don daga lokacin da ta ɗauki zuciyarta ta danƙa a hannun Ma'aruf shikenan take zaune da ƙirjinta fanko, don bata kara marmarin saka wani a zuciyarta har ta kalle shi da daraja ba kamar shi, tun yana cikakkensa na mutum har ciwon da zata iya kira na hauka yazo ya same shi, haka akayi auren tana murna su suna jiye mata baƙin ciki, kuma ko kafin ta haihu takaici iri-iri sun sha shi, sai da ya juye ƙwaƙwalwar ta tsaf ya goge wannan Ruƙayyan da take a baya, ƴar gayu mai cike da izzar da ko a cikin ƴaƴan manya ake samun masu kwaikwayon ta.
Ya canja mata yarinya zuwa bagidajiya irin matan da basu san komai ba sai zaman aure, ɗaya daga cikin abubuwan da ba zata manta ba shine lokacin aurenta har Lagos tasa aka nemo mata wasu ƙwararrun chefs(masu girki) mata bama maza ba don sanin halin Ma'aruf ɗin, amma wucewar sati guda Ruƙayyan ta bugo mata waya cewa ya sallame su yace shi girkinta yake so, kuma duk ƙin Rukayyan da girki haka ta ajiye ra'ayinta pa gefe ta shiga makarantar koyon girki tsawon watanni don kawai farin cikinsa, abubuwan da ta canja a rayuwarta don Ma'aruf baza su lissafu ba, don a abubuwa ne da ko na nesa zai hango su balle na kusa.
Don haka a lokacin da ta fahimci cewa da gaske tana shirin rasa ƴar tata, a lokacin ta miƙe tsaye tayi wani yunƙuri da bai bawa Rukayyan zaɓin komai ba illa bin umarninta, kuma sa'arta ta zarce har bayan rabuwar tasu ta cigaba da jin maganganunta zuwa yardar da tayi ta auri Alhaji Ahmad, amma zata rantse cewar zamanta baiyi nisa a gidan Alhajin ba fitinanniyar zuciyarta ta sake karkatowa zuwa shafin da take zaton sun barshi kenan har abada wato Ma'aruf, don haka auren bai je koina ba ta fito.
Ƴarta Hamida bata taɓa damunta ba don a tunaninta ita ba tasu bace, da tayi wayo ne mahaifinta zai karɓe ta koma wajensa, don haka bata ko waiwayarta a al'amuranta ta Ruƙayyan take yi. Ashe duk ub*n shirin da suke yi mata ita da ƙawarta akan alaƙarta da yaron nan Jawad a banza suke kashe ƴan kudadensu, ashe har yanzu zuciyarta bata dawo daga inda ta juya ba, Tunani take zata sake komawa wajen wannan yaron da a wajenta kudin da yake dashi ne kawai banbacinsa da wani mahaukacin.
Har ta buɗe baki zata yi magana, Ahmad, ƙanin Ruƙayyan dake bin Ashraf (wanda yayi aure) ya hawo saman daga shi sai gajeren wando da riga.
"Wai Maamah ki dawo ƙasar nan baki gaya mana ba. Sai da na shigo wajen 12 maigadi yake ce min ai kin dawo."
Ya faɗa yana ƙarasowa kusa da ita ya zauna, kuma sai a lokacin idonsa ya kai kan Rukayya dake kuka.
"Me ya faru?" Yayi tambayar ga dukkansu biyu.
Hajiya Nafisa ta nisa sannan ta bashi amsa.
"Hamida ce ba'a gani ba, ita da mai kula da ita."
"What? Ta yaya? Tun yaushe?"
"Itama bata gidan ai, sai da na dawo tukunna."
Ransa a ɓace yace.
"Me nake gaya mata a gidan nan Maamah, don me zata dauko wata ƙedara wai ita zata dinga kula da ƴarta, wai don ta iya turanci? Turancin banza su Hausawan ba su iya turancin bane?"
Hajiya Nafisa ta girgiza kanta.
"Ajiye wannan zancen Ahmad tunda komai ya faru, yanzu nemanta ne a gabanmu. Ya za'ayi?"
Kafin ya bada amsa, Ibrahim ya shigo riƙe da wayarsa a hannu yana faɗin.
"Is it true yarinyar nan ta ɓata? Umar just called me now wai ya ganki a waje ɗazu kuna tambayar Hamida."
Hajiya Nafisa ta gyaɗa kanta don ita yake kallo sanda ya shigo yana tambayar.
"Ƴansanda ɗin dake gadi a bakin titi muka tambaya suka ce mana tun shekaranjiya Maryn ta fita da Hamidan kuma basu dawo ba."
"Ya salam! This is bad, yanzu me ake ciki?"
Tambayar tasa Ruƙayya sake fashewa da kuka.
Ahmad yace.
"Akwai wani abokin Ashraf da ya taɓa zuwa nan yace min ya san ita mai aikin, ban ɗauko wayata daga ɗaki ba, Ibrahim kira shi."
Ya kalle shi.
"Wa zan kira?"
"Ashraf ɗin zaka kira kace ya baka number B-man."
Wayar Hajiya Nafisa tayi kara a lokacin, ta kalli number dake kiran nata, mahaifinsu ne don lokacin da Rukayyan ta dawo tace bata san inda Maryn take ba shi ta kira ta gaya masa halin da ake ciki. Ta ɗauki kiran ta kara a kunnenta, gaya mata yake yi cewa yasa an turo da ƴan sanda gidan zasu zo su nemi bayanai don su kamo Maryn.
Kuma bayan ta sauke wayar kallon Rukayyan ta cigaba da yi a lokacin Amir ɗan autansu ya shigo rike da kofin shayinsa ya zauna a gefenta yana bata hakuri.
Gayawa zuciyarta take yi cewa ba zata sake kuskuren rasa ƴarta ba a karo na biyu, bata son Ma'ruf amma idan har yanzu shine zaɓin Ruƙayya, shi abinda zai daidaita rayuwarta, to zata hakura kawai ta karɓi wannan ƙaddarar, zata dawo mata da Ma'aruf cikin rayuwarta ko ta wace hanya.
***
"Allah yayi miki albarka, Allah ya haskaka rayuwarki, Allah yasa ki zama haske a cikin gidan aurenki, Allah yayi riƙo da hannayenki wajen kyautata zaman ibadarki, Allah yasa ki zama sanyin idaniyar mijinki, Allah yasa masa tausayinki a zuciyarsa, Allah ya bashi ikon sauke nauyin duk wani hakkinki, Allah yasa ku zamewa junaku inuwar salama har a ranar alƙiyama, Allah ya sanya albarka a zuri'ar da zaku samu, Allah ya tashi rayukanku cikin rahamar ibadarku a lokacin da zaku koma gare shi..."
Duk wannan addu'ar tana fitowa ne yayin da ruwa ke sauka akan Amina daga bakin wata dattijuwa ƴaruwar Amma mai suna Gwaggo Balkisa da suka zo daga Nijar a lokacin da gidansu Amina ya cika da ɗimbin jama'ar dake shaida Kamu ko kuma wankan amarya da a ƙa'idar zuri'arsu Amma ake yinshi kwanaki kafin ɗaurin aure, al'amarin da yazo musu babu shiri don kwatsam suka samu baƙoncin ƴanuwan Amman tun daga Nijar mutane har motoci biyu.
"Bikin ƴarki ta fari guda kice ba sai mun zo ba Halima? Idan kince ku komai yazo muku cikin gaggawa an gaya miki mu yanzu muka fara tanadi ne? Har a aika da katinan ɗaurin aure amma ace wai iya maza ne kawai zasu taho? Yau ko Amina ba ƴarki ta sunna bace kina tunanin zamu ƙi halartar bikinta ko da kuwa tsakaninmu daku nisan bangon duniya ne?
Amina tana tuna yadda Amman ta sunkuyar da kanta tana saurare kafin tayi musu bayanin yadda al'amarin auren yazo, kuma fahimtar al'amarin ya kawo cece-kuce a tsakaninsu, waɗanda suke tsofaffi a ciki basu ga aibin komai ba don sun yarda cewa dama uba ke da ikon bada ƴarsa budurwa zamani ne kawai ya canja komai, amma sauran suma sai tunaninsu ya zama irin na Amma cewar tasirin taimakon da Hajiya Kilishi ke yiwa Baba shi ya rufe idanunsa saboda auren bai kamata ba.
Sai da aka kira Aminan ta tabbatar musu cewa ita ta amsa auren da bakinta sannan kowannensu yayi shiru. Ta faɗi hakan a lokacin da take kallon idanun Amma dake ɗauke da sauran labarin da bata ƙarasa musu ba, sauran labarin da ko ƴanuwan Baban basu sanshi ba, tana jin yadda zuciyarta ke bugu akai-akai cike da fatan kar nauyin kalaman su rinjayi zuciyar Amma a wannan lokacin, amma bata yi maganar ba, bata ce komai ba.
Kuma hakan yana tuna mata da matsayinta na Ammar su, matar da tunda suka taso a rayuwarsu babu wata rana da zasu iya ɗorar da saɓanin cewa faɗa ya shiga tsakaninta da mahaifinsu, kuma ba wai ba'ayi ba, ta tabbata ana yi ma fiye da tarin wasu gidajen auren, kawai babu ƙofar da zasu gane ne. Ta tuna watarana da taji ta tana yiwa Aunty Safiyya nasiha bayan wani saɓani da ya shiga tsakaninta da mijinta.
"Sirrin mijinki sirrinki ne Safiya, idan kika buɗe kamar kin tonawa kanki asiri ne, ko wa kika budewa littafin da wannan karatun zaiyi ta kallonki koda kuwa kin cigaba da zama ko kuma kin rabu dashi, mafitar matsaloli da yawa a hannunki suke, da wuya ake kaiwa gaɓar da wani ne zai iya magance miki damuwarki..."
Zata lissafa Ammanta cikin manya-manyan jajirtattun mata a gidajensu, zata lissafa ta cikin irin mutanen da mata da yawa ya kamata su kalla suyi koyi dasu, don ita kanta babban makamin da take taƙama dashi na shirin tunakarar sabuwar rayuwar da zata yi, halayen Amman ne.
Sai dai duk yadda ta kai ga dake zuciyarta, a wannan lokacin da Gwaggo Balkisa ke mata wannan addu'ar tana zuba ruwan ɗumi daga saman kanta, kuka take sosai, kuka mai nauyi, kuka mara sauti, kuka da zata iya cewa ya zarce na amare da yawa, don nata kalolin taraddain dake cikinsa basu da adadi, ba na barin gida ne kawai ba, bana shirin fuskantar wata sabuwar rayuwa bane, wataƙila idan tace na shirin mutuwa alhali tana numfashi ne, hakan zai iya fassara rabin abinda take ji.
Tana sanye da wani farin saƙi dasu Gwaggon suka taho dashi, anyi mata ɗaurin ƙirji dashi kawai, yayin da gashinta mai laushi da yawa ke mannewa a fatar kanta da kuma wuyanta saboda ruwan dake bi ta cikinsa,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads