Showing 15001 words to 18000 words out of 84785 words
Chapter 6 - Farar Wuta Book 1 Complete Hausa By Aisha Aliyu Garkuwa .txt
na cewar saboda maganarta Kawu mallam ya taso su a yau tun daga can suka zo, ganin yadda Babn ke kallonta yana son fassara yanayinta yasa ta maida idanunta ƙasa a hankali yayin da hannunta na dama ya kamo karshen skirt dinta da ƙarfi.
"Amina a jiya babu irin boren da mahaifiyarki bata yi min ba akan maganar nan, dukkan ku shaida ne cewa Halima mace ce mai biyayya gare ni, don tun daga ƙuruciyarku har yanzu babu ranar da ɗayanku zai ce kunji kanmu ni da ita game da wani al'amari a gidan nan, duk abinda na fada ko nayi daidai ne a wajenta, amma a karo na farko jiya mahaifiyarki ta bijire min akan wannan hukuncin, tace bata yarda ba, tace ba ni kadai na haife ki ba itama tana da nata haƙƙin akanki don haka ba zan siyar dake ga wasu mutane ba kamar yadda ta fassara al'amarin.
Kuma bayan zuwan su Kawu Ibrahim a yau sai suma duk suka goyi bayanta, da ni da Kawu mallam da Baban kurna Amina mune kadai muka hango wannan al'amarin ta fuskar alkhairi da kuma cigaban ki wanda su basa gani. Don haka na san a shekarunki da kuma hankalin yabzu zaki iya banbance daidai da akasinta, don haka muka yanke cewar matsayar tana gare ki yanzu, duk ɓangaren da kika zaɓa shi zai fi rinjaye kuma maganar ta zauna kenan har abada, kar ki ga cewar na amsa musu acan, ki faɗi ra'ayinki Amina babu wanda zai taɓa ganin laifinki don rayuwar ki ce, mu duk ƴan kallo ne kawai.
Don haka kije kiyi tunani daga yau zuwa gobe, saboda idan har ɓangaren mahaifiyarki kika ɗauka, ina so ne muje mu sami mutanen tare da su Kawu Ibrahim kafin su koma kuma kafin wani abu ma daga ɓangarensu yayi nisa. Kije kiyi tunani Amina."
Shikenan! Shikenan sai duk bayanin ya ƙare da wannan jimlar, lokaci kuma ya fara bugawa da adadin awannin da zasu tadda goben, goben da Baba ta furta kamar tsawonta na shekara guda ne.
Taji lokacin da ya miƙe ya zo ya wuce ta, taji shi ya zura takalmansa daga waje sannan taji ƙarar takunsa na nufar hanyar soro, sai kawai ta rufe idanunta gabaɗaya tana hadiye wani abu da bata sanshi ba a maƙogwaron ta.
"Duk abinda mahaifinki ya fada haka ne ya faru Amina, kuma ba komai yasa nayi hakan ba sai don nemar miki ƴancinki..."
Da wani sassanyan amo muryar Amma ta maye gurbin ta Baban tun kafin ta bude idanunta
"... Ƴancinki nake nemar miki Amina, don ni na hango abinda mahaifinki ya kasa ganowa, mutanen nan masu kudi ne da gaske, kuma duk tsananin kirkin mai kuɗi a zaune yake cewar baya taba son mu'amalar rayuwarsa da talaka kamar mu, zasu taimaka, zasu yi zumunci kamar yadda ita wannan Hajiya Kilishin ke yi amma aure Amina, aure babban abu ne da shine linzamin rayuwarka ta duniya har zuwa lahira, don haka kowa ya sani cewa hakan ba ƙaramin abu bane ga rayuwar mutum da zai haɗa shi da kowa.
Da ke muka je auren wani ɗansu a shekarun baya da suka wuce, kinga matar daya aura ai, kinga irin tarin dukiyar ubanta da danginsu, don ba a banza bahaushe ke cewa 'ƙwarya tabu ƙwarya ba... Kowa daidai dashi yake nema. Saboda haka Amina ko makaho yaji wannan zancen ya sani cewa mu ba daidai da mutanen nan muke ba, sun nemi aurenki ne kawai don son zuciyarsu..."
Sai tayi shiru kamar tana kokarin haɗewa wani abu da ya taso mata ƙirji yayi sanadiyar canjawar muryarta.
"Amina, ciwon yaron nan na 'Hauka' ne na tabbata suka yi masa ado da matsalar ƙwaƙwalwa kawai, kuma kin san wannan ba ƙaramar magana bace, kowa ya sani, su ma sun sani shi yasa basu tunkari kowa da wannan zancen ba sai mu, mu talakawa da aka mayar kamar ba mutane ba, mahaifinki dasu Kawu mallam suna ta danganta al'amari da ƙaddara, alhalin basu ƙara binciken komai akan yaron nan ba, amma ni nace idan har ƙaddarar ce me yasa basu kai ta ga irin ƴaƴan masu kudin da ɗaya ɗan nasu ya aura ba? me yasa sai a yanzu ne irinmu zasu yi musu amfani... Na sha gaya miki masu kuɗi basa kallon kowa sai kansu, suna ganin talaka kamar shi ya zaɓawa kansa rayuwar sa, kamar dama Allah ya halitto shi ne kawai don ya kawar musu da matsalolinsu.
Rayuwarki zaki sadaukar musu idan har kika zaɓi tafiya Amina, don aure ba karamar gwagwarmaya bace ko da mutum mai hankali kuma wanda kake so balle babu duk biyun a naki, rayuwarki zaki sadaukar musu a banza, dukkan wani mafarki da burinki sai ya mutu wajen yi musu bautar da baza su san kina yi ba, don wannan sigar auren a wajensu, bata da banbanci da cewar siyen ki suka yi..."
Ta sake yin shiru sakamakon yadda Aminar ta runtse ido da tasirin maganar, amma duk da haka sai ta cigaba.
"...Annabi yayi gaskiya da yace kudi sune masifar ƙarshen duniya, a karo na ba adadi wallahi na sake yarda da hakan, don ban taɓa tunanin cewa mutum kamar mahaifinki zai iya faɗawa cikin tarkonsu ba..."
Wannan karon kalaman suka daki zuciyar Amina da tasirin da yasa a lokaci guda ta ɗago ta kalle mahaifiyar tata tana girgiza kai. Ta sani dukkan abinda ta faɗa gaskiya ne, amma ba ta yarda da wannan hasashen nata na ƙarshe ba, ba zata taɓa yarda cewa kuɗi zasu rufewa Baba ido har ya mika ta ga inda zata cutu ba, haba mana! ta manta ne? Ta manta duk wannan tarin ƙaunar tasu dake tare dashi? Ta mata tarin sadaukarwar da yayi a rayuwarsa saboda su kawai?
Sai dai kallon da Amman ke mata yasa ta sake sunkuyar da kanta a hakali tana rufe idanunta da ƙwalla ta taru a cikinsu, dukkan maganganun da Amma ta fada gaskiya ne ta sani amma har a lokacin ta kasa gasgata zancenta na karshe don ta sani cewa ko da numfashinta na ƙarshe a duniya ne zata yarda cewa ba zai taɓa mika ɗayansu ga inda zasu cutu ba... A kullum shi mai son gyara rayuwarsu ne.
Ta kai hannu tana share idanunta lokacin da Amman itama tace.
"Kije kiyi tunani zuwa goben Amina, ki auna kowanne ɓangare ki ga wanda yafi rinjaye, ni dai a matsayina na mahaifiyarki kuma mace kamar ki na gaya miki abinda nake ganin shine daidai"
Ta rufe bakinta daidai lokacin sallamar su Adam daga makarantar dare ta kwararo a tsakar gidan. Shi da Hafsa ne suka karaso har cikin dakin bayan sun duba falon da babu kowa, da sauri Amina ta saka bayan hannunta ta share hawayenta kafin su ƙaraso da hayaniyarsu.
"Amma kaina ciwo yake yi." Muryar Hafsan ta ambata tun kafin ta shigo ɗakin da kalar ƙorafinta na kullum yayin da Adam shima ya shiga ƙaryata ta.
"Amma wallahi makaranta ce bata son zuwa gobe ƙarya take yi, yanzun nan fa har kusan faɗa fa suka yi ita da wasu a wajen ƴar tsohuwa, ba don nazo da wuri ba da ko kafi-kazan data siya ma baza ta samu ba."
Babu wanda ya lura da yanayin dakin a cikinsu sai bayan da suka ga Amman bata basu amsa ba, tayi shiru kawai tana kallonsu, wanda hakan yasa Adam yasha jinin jikinsa, ya sake kallon fuskar Amman da kuma ta Amina ya tabbatarwa kansa cewa basu yi daidai da lokacin da ya kamata ba, don haka ya nufi kofa, sai dai har yasa ƙafarsa ɗaya a waje ya tuna da saƙon da aka bashi.
"Au na manta wallahi, Yaya in kin fito ana kiranki a waje."
Da haka ya juya yayi hanyar Kitchen ayana fadin zai sake zuwa yaci abinci. Amina ta ƙara share hawayen idanunta, Abdallah ne ta sani, don dama tun jiya take tsammanin zuwansa dama don ta sani lokacin komawarsa makaranta yayi, sai dai yazo a lokacin da take jin bata son ganin fuskar kowa, maganganun Baba da Amma sun riga sun cike duniyarta ta yadda bata tunanin a cikin zuciyarta ma akwai wani waje komai kankantarsa da zai sake ɗaukan wani abu a daren yau.
"Ki tashi kije, ganinsa zai sa ki sake yankewa kanki hukuncin da ya dace Amina, daga daren yau zuwa gobe kawai kike dashi..."
Muryar Amman ta sake faɗa, taji kamar tayi ihu lokacin data ɗago ta kalle ta, Hafsa na tsaye har yanzu sai kallonsu take alamun rashin fahimta akan fuskarta, kuma daga yanayin Amman ta san ko ihun tayi ba zata canja maganarta ba don haka ta sake goge hawayen da bayan hannunta sannan ta miƙe a hankali tana jin yadda kowa ce kalma da iyayen nata duka furta tayi mata tsaye a zuciya bayan nauyinsu da take ji a kafaɗunta.
Akan igiyar tsakar gida ta tarar da hijabin da Maryam ta goge ɗazu don gobe za'ayi musu hotunan photo album ɗin sauka a islamiyyar su, na sallar idinsu ne, dogo har ƙasa kalar ruwan ƙasa, ta jawo shi kamar zata saka amma sai ta fasa, ta nufi ƙofar soron ta tsaya, ziciyarta na ƙoƙarin ƙulla ta yadda zata yiwa Abdallahn bayanin komai, komai ɗin da itama bata gama sani ba, taji ɓangare da yawa a cikin ƙwaƙwalwar ta na gaya mata cewa fitar ta a wannan lokacin ba alkhairi bace, don haka sai kawai ta dawo ta kira Adam dake karo da kwanuka a kitchen.
"Adam zo."
Ya juyo riƙe da plate yana kallonta kafin ya ajiye shi ya biyo bayanta, suka koma har hanyar soron.
"Adam dan Allah kaje kace masa bani da lafiya sosai, ya dawo gobe ba zan iya fitowa yanzu ba."
Kamar ya tambaye ta dama ta sanshi ne tunda bai taba ganinsa a gidan nasu ba, sai kuma kawai ya fasa ganin yadda idanunta suka yi ja ya san ba lallai taso tambaya a lokacin ba, ya juya ya fita, ita kuma ta tsugunna a wajen tana ƙara share hawayenta ba tare da ta fahimci kuskuskuren da tayi ba.
Lokacin da Adam ya fita, Ma'aruf na tsaye har a lokacin kuma ganin tahowarsa yasa ya ɗago da hannayensa duka biyu a hankali yayi baya da hular (hood) dake kansa, fuskarsa ta fito cikin hasken ƙwan fitilar barandar gidan,
"Yaya tace wai dan Allah kayi haƙuri bata da lafiya ba zata iya fitowa ba ka dawo gobe."
Ba shiri wani murmushin ya subuce a fuskar Ma'aruf, For real? Shine ma zai dawo goben? Bata san me ta tsallake bane, sai kawai ya gyada kansa tare da faɗin.
"Okay."
Har Adam zai juya yayi saurin tsayar dashi.
"Kana ji ko, ɗan tsaya ka bata wannan."
Adam ɗin kuwa ya tsaya, shi kuma ya buɗe ƙofar motar ya buɗe aljihun dake jikin dashboard ya zaro wata jotter da biro daya san Ishaq baya taba rabo dasu motarsa a matsayinsa na lawyer, ya yago takarda guda ɗaya ya ɗora daga saman yayi wani rubutu layi biyu da rabi kawai sannan ya rubuta sunansa daga ƙasa. Ya kalli abinda ya rubuta din yayi wani guntun murmushi kafin ya juyo ya mikowa Adam ɗin
"Nagode sosai kaji."
Ya faɗa yana sake yi masa wani murmushin, da fara'a shima Adam ɗin ya amsa yana masa a sauka lafiya kafin ya juya, shi kuma ya jefa kansa baya jikin motar yana cusa hannunsa na hagu cikin gashin kansa.
Ba haka yaso ba, amma hakan ma yayi... Ya riga ya gama da yarinyar nan ya sani, don abinda su Baffa ke tunani ba zai taɓa yiwuwa ba.
Aka ɗauke wuta a daidai lokacin, unguwar tayi wani irin duhu dinɗim kamar yadda yake jin zuciyarsa! Don haka ba shiri ya kunna motarsa ya shiga ya bar wajen.
"Gashi yace in baki."
Adam ya faɗa a cikin duhun soron bayan ya koma, Amina tayi saurin sake goge hawayenta kafin ta karbi takardar ba tare da tunanin komai ba don ta san ba wani abu bane Abdallahn ya iya rubuto mata fatan samun sauƙi dama, ta damƙe ta a hannunta sannan ta miƙe ta bi bayansa. A kitchen suka tadda Amma na kokarin kunna kyandir guda biyu Hafsa kuma na sake zuba abinci itama, kuma bayan ta amsa sallamarsu sai ta miƙowa Amina guda ɗayan yayin da Adam ya shiga fadan cewar Hafsan ta dauki farantinsa.
Ta wuce ɗakinsu kai tsaye, ta ajiyewa Maryam Hijabin akan katifarta sannan ta manna kyandir din akan wata kwalbar magani, a gabansa ta tsugunna hannunta rike da takardar, daga jikinta har zuciyarta daban take jinsu, wucewar awa guda kawai ta tafi da Aminar da take a baya, a yau da safe ma... tana jin zata rubuta dukkan abinda ya faru a daren yau a wajaje da yawa ta yadda ba labarinsa ba zai taɓa gogewa ba.
Ta sake goge wani hawayen sannan ta buɗe takardar a hankali, zuciyarta cike da fatan ta karanta wani abu mai rangwame daga Abdallan ko yaya ne wataƙila ya iya zaftare wani ɓangare na damuwarta, sai dai kuma rubutun da idanunta suka gani a jiki shine abu mafi tashin hankali fiye da duk maganganun da rayuwarta taci karo dasu a wannan daren.
Kar ki yarda da auren nan, da gaske ne abinda suka faɗa miki, I'm a psycho, zan kashe ki idan har kika shigo rayuwata. Ma'aruf B.
*****
11:15Am.
"Mai gaskiya kaci abincin kasha magunguna naka?"
Muryar Hajiya Kilishi ta tambaya cikin wayar dake kare a kunnenta, kuma a cikin wayar aka bata amsar data sa ta gyaɗa kanta kafin ta sake cewa.
"Zan kira Ishaq, zamu yi maganar komai dashi, idan zaka shigo kawai ka taho da magungunan duka."
Har tayi shiru sai kuma tace.
"Dan Allah Ma'aruf kafin ka shigo kaje ka aske gashin nan dan Allah, ko ɗazu da na shiga wajen Inna Danejo abinda ta fara tambayata kenan."
Amsar da Ma'aruf ɗin ya bayar mai tsawo ce, don ta dade tana saurarensa kafin tace,
"Shikenan idan ka shigo kayi mata wannan bayanin da kanka, akwai faten dankali a ɗaya daga cikin kwanukan abincin nan ka ganshi?"
Ya fadi abinda ya saka ta yin dariya kafin ta sake cewa.
"To aci lafiya, sannan idan ka wuce 1 baka shigo ba, zaka ganmu gabadaya gidan mun taho."
Ya fadi wani abun da ya kara saka ta dariyar da tafi ta farko tana fadin.
"Ai da ƴanmata zamu zo sai suyi muku sharar."
Da haka suka yi sallama, tana sauke wayar daga kunnenta.
"Wallahi na dade ina gaya miki Hajiya, da irin mahaukatan secret agent din nan na turawa ya kamata ki samu aiki, ko banza dukkanku zaku amfana da juna, ke da kudinsu su kuma da kissa irin taki."
Cewar Hajiya Salamatu, wata hamshaƙiyar ƴar gayu dake zaune daga gefen Hajiya kilishin.
Wajen ƙarfe goma sha ɗaya ne na safe a lokacin, kuma kasancewar ranar ta asabar ce kowa yana nan, gidan cike yake da hayaniya da kuma hada-hadar masu aiki da suka gama abincin safe suke kokarin ɗora na rana.
A cikin ɗakin da suke zaune an ɗage labulayen tagogin dakin guda biyu iska da hasken rana na shigowa yayin da a lokaci guda kuma filutulun ɗakin suke a kunne haɗe da fankar da aka ware har ƙarshenta. Hajiya Kilishi dake zaune itama cikin nata adon daidai misali ta ajiye wayarta a gefe sannan ta kai hannu ga robar ketchup ɗin dake kan katon farantin da aka zubo musu kayan breakfast akai, ta sake zubawa a farantin dankalin turawan dake hannunta ta sannan tace.
"Idan har zaki samo min me zai sa in ƙi sanya hannu Hajiya, kin san ai waje in dai da raɓa da kuma sirri ba na ƙinsa."
Hajiya Salamatu ta sake kai kofin shayinta baki tana girgiza kai.
"Ai kullum ina gaya miki al'amarinki abun mamaki ne Kilishi, wallahi duk yawona a doron duniya ban taɓa ganin mace irinki ba, yadda ba boka ba malam, kike juya komai da ɗan yatsa guda kuma hankalinki a kwance."
Hajiya Kilishin tayi wata guntuwar dariya alamun ta saba da jin hakan daga bakin ƙawar tata.
"Mu bar wannan zancen yanzu Salamatu, mu tafi ga abinda yasa na kira ki."
Sai da Hajiya Salamatun gyara zamanta a hankali tana ajiye kofin daga durowar gefen gadon, idanunta kaɗai zaka kalla ka san cewar da gasken ta tattara dukkan hakalinta ga abinda Hajiya Kilishin ke ƙoƙarin ɗorawa akan tsohon shirin da suka saba.
"Auwalu yana riƙe da ma'aikata har yanzu, sannan wannan auren kamar ya tabbata ne mu ajiye shi a gefe, me kika cigaba da shiryawa daga ƙarshen ƙullin da muka yi wa zaren, me kika tsara?"
"Tsari na da yawa Salamatu, farko dole ne in fara sakin manufata tun yanzu akan ita yarinyar, dole ne ta ɓoyayyiyar hanya in ƙara bincike akan zuciyarta ta yadda zan fara ƙawata tunaninta da miƙakkiyar hanyar da zata ƙulle ta a gaba.
Na biyu, dole ne a yanzu inyi taku mai nisa daga mahaifin yarinyar da kuma maigidana, zan ƙara zame hannuwa daga al'amarin na in zama ƴar kallo ta yadda ko ƙura ba zata hau kan farina ba, balle wani ɗigo na baƙi, amma zan kusanci mahaifiyar yarinyar dole, don haka ne ingantacciyar hanyar da kowa zai kalla a yanzu.
Sannan na san Ishaq zai shaida min dukkan sabon tsarin magungunan Ma'aruf, don haka wannan ma babu matsala, komai zai cigaba ne daga inda ya tsaya. Game da auren su Salma kuma wannan komai tsaftatacce ne don kin san bana taɓa haɗa ƙasa da gari waje guda. Daga Auwalu kuma, mun sake bude wani sabon account zai loda kudaden wancan watan..."
Ta faɗi hakan sannan tayi shiru a hankali, ramin bakinta na wasa da wani murmushi mai armashi.
"A yadda lissafin komai yake Salamatu, shekara guda tayi yawa kafin komai ya ɓare!"
Hajiya Salamatun tayi nata murmushin itama yayin da take kallon fuskarta.
"Na fahimta Kilishi nima na lissafa wannan adadin tun a wancan karon. Sai dai kin san a kullum nice mai hasko miki ƙalubalen da ke bakya ƙirgawa dasu. Ƙalubalen da duk zare ɗaya ne ya ƙulle su suke reto a jikinsa, ƙalubalen kuma da shine raunin ki Kilishi, shi kadai ne raunin da na san ubangijin ya halitta a ƙirjinki, Ma'aruf!"
Murmushin da kullum ke sauka a fuskarta duk sanda Hajiya Salamatun ta furta mata magana makamanciyar wannan shi tayi a yanzun ma, tayi shi tana ajiye farantin hannunta, ta jawo tissue a gefe ta goge maiƙon hannunta sannan ta miƙe, ta isa ga makekiyar wardrobe ɗin dake ɗakin ta buɗe waje na biyu, a ciki kayan Ma'aruf ne wanda ya cire daga jikinsa ranar da aka tafi dashi tafi London ba'a hayyacinsa ba.
A