Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 84785 words

Chapter 3 - Farar Wuta Book 1 Complete Hausa By Aisha Aliyu Garkuwa .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

a ransa game da ciwon nasa ba tsawon shekaru goma da suka wuce, maganganun Ishaq suka sake haskawa a cikin kansa.
...idan komai ya cigaba da kasancewa yadda yake tafiya, kana gab da rasa hankalinka gabaɗaya Ma'aruf!
***
Alhaji Muhammad Mansour Bakori, sanannen mutum ne wanda yake da babban Kamfanin yin robobi a garin Kano tare da ƙaninsa Alhaji Usman, wanda su biyu ne kacal a wajen iyayensu, mahaifinsu ya rasu shekaru da daɗewa amma mahaifiyar su tana raye.
Alhaji Mansour Bakori yana da mata biyu da ƴaƴa goma sha ɗaya, yayin da Alhaji Usman bai taba haihuwa ba tsawon shekaru talatin da aurensa, wanda hakan ya faru ne sakamakon wani hatsari da yayi tun kafin tun yana saurayi har ya zame masa sanadin hakan, shi yasa kowa a danginsu yake girmama matarsa Hajiya Madina da kuma jinjina mata na zaman da take dashi a duk shekarun nan alhali ita lafiyarta ƙalau.
Matan Alhaji Mansour biyu, Uwargidan itace Hajiya Maimuna, wata mata mai kirki da kuma alkunya, ɗanta na farko Jamal ya rasu shekaru goma da suka wuce, daga shi sai Ma'aruf wanda shi a wajen kishiyarta ya girma, sai Shukra, Munaya, Abdurrahim wanda shi tun yana shekaru biyu a duniya ya kamu da matsalar rashin magana amma yana ji kamar kowa, sai kuma autarsu Zahra.
Hajiya Kilishi itace mata ta biyu a gidan, wata mace ce mai tsananin kirki da kyautatawa, don faɗa ko da na rana guda bai taɓa haɗa su da Hajiya Maimuna ba tun zuwanta gidan, wani irin zaman lafiya da mutunta juna ne a tsakaninsu tun farkon zuwanta gidan, hakan yasa basu kaɗai ba ko wanda yake nesa ba zai taba cewar su ɗin kishiyoyin juna bane idan ya gansu tare.
Ita ta raini Ma'aruf tun daga watannin da aka yaye shi har zuwa girmansa na yanzu. Hajiya Maimuna, mace ce mai hali irin na mutanen da, tsananin kawaici akan abinda suke ganin shine daidai, don haka tun daga ranar da Hajiya Kilishi ta karɓe sshi bata ƙara nuna cewa shi nata bane, a suna kawai Ma'aruf ya santa a matsayin mahaifiyarsa, amma a wajen Hajiya Kilishin da suke kira da Mami ya samu dukkanin wata kulawar da ɗa ke samu daga mahaifiyarsa.
Ita ta raine shi da ƙarfin jikinta da kuma na zuciyarta, har zuwa girmansa kuwa ya zama tsakaninsa da Hajiya Maimuna gaisuwa ce kawai amma Mami ce komai nasa, duk da ƴadda wasu daga cikin ƴanuwan Hajiya Maimunan suke nuna rashin jin daɗin su akan hakan a yanzu da ya zama shine kaɗai namiji babba a gidan.
Ƴaƴan Hajiya Kilishi biyar ne, dukkaninsu mata kuma dukkanninsu harafin sunansu ya fara ne da harafin S, Safiyya, Salma, Surayya, Samira da kuma Sahla kamar yadda take so, don a wajen Daddy babu ruwansa da raɗin suna, duk wanda iyayensu mata suka zaba shi zai saka ba ruwansa. Zahra ce ma kawai taci sunan Inna Danejo 'Fatima' kamar yadda Hajiya Maimunan ta nuna tana so a saka.
Hajiya Maimuna ta sami matsalar shanyewar ƙafafu bayan ta haifi ƴarta ta ƙarshe Zahra, kuma babu irin maganin da ba'ayi ba a ƙasashe daban- daban amma ba nasara, don haka a dole yanzu sai akan Wheelchair take yawo.
Gidan Alhaji Mansour dake unguwar NNDC quarters a garin Kano, ƙaton gida ne mai ɗauke da bangare-bangare, akwai ɓangaren iyalansa guda biyu wanda kowanne iri daya ne, ƙaton falo da ɗakuna hudu kowanne da banɗakinsa a ciki da kuma sauran wajaje irin Kitchen, store, courtyard da dai sauransu, sai bangarensa inda shine waje na farko a gidan mai ɗauke da ɗakuna biyu da falo da kuma wajen meeting ɗinsa inda yake ganin baƙi a gida.
Akwai bangaren boys quarters inda masu a gidan suke zaune sai kuma wajen Inna Danejo kakar gidan, wato mahaifiyarsu Alhaji Mansour inda itama take da ƙaton falo, ɗaki ɗaya da kuma toilet, sai ɓangaren ƴan aiki, sai kuma bangare na karshe daga gefen hagu na harabar gidan, wato bangaren Alhaji Usman da suke kira da Alhaji Baba, wanda shima da a gidan yake tare da matarsa daga baya sai ya siyi wani gida gaba dasu kaɗan ya koma, don haka wajen a ƙulle yake babu kowa.
Ishaq abokin Ma'aruf ne kuma ɗan'uwansa, don da Mahaifiyar Ishaq ɗin da Hajiya Maimuna iyayensu ɗaya, asalin mahaifinsa ɗan Kaduna ne kuma shi kaɗai iyayensa suka haifa, mahaifinsa ya daɗe da rasuwa amna mahaifiyarsa sai da yazo matakin shiga Jami'a ne sannan Allah ya ɗauki ranta, don haka da shawarar Mami, Hajiya Maimuna ta tambayi Alhaji Mansour da kowa ke kira da Baffa, Ishaq ya dawo gidansu da zama daidai lokacin da Ma'aruf ke kokarin shiga Jami'a.
Mamin tayi haka ne don ganin ta samowa Ma'aruf sauki akan halin alhinin ɗanuwansa da har a lokacin bai gama warkewa daga ransa ba, don haka tare da Ishaq ɗin Baffa ya ɗauki nauyin karatunsu a wata Private University dake London har suka kammala, kuma hakan ya sanya shaƙuwa sosai a tsakaninsu duk da cewar ɓangare daban-daban suka karanta. Ma'aruf ya karanci harkar Kasuwanci ne yayin da Ishaq ya karanci ɓangaren aikin lawyer kamar yadda yake da buri tun yana yaro.
***
Washegari...
No. 58 Mafara Street, NNDC Sharaɗa Qauters.
.07:30 Pm.
Tun daga ƙofar gidan zaka gane cewar anyi wani taro ne a gidan an watse, don hatta gate din a bude yake gabaɗaya sannan ga motoci daga ciki suna kokarin fitowa.
Idan ka biyo ta cikin mutanen, zaka wuce ko'ina hanya ta kai ka har ɓangaren Hajiya Maimuna inda taron mutanen yafi yawa musamman a ƙaton falon ɓangaren da zaka tarar wanda yake cike da tarin mutane gabaɗayansu mata, kowa na zaune da abokin hirarsa yayin da ƙamshin turarukansu ya haɗe da ƙamshin daddaɗan abincin da aka gama ci a falon, don ga tarin plates nan wasu ma har da ragowar abincin sannan kuma a can gaban Tv stand na ɗakin akwai wasu manya-manyan flasks cike da snacks kala-kala ga duk wanda yake so ya diba.
Sai dai duk wannan ba shine abin kallo a dakin ba, tarin akwatunan dake zube a makeken carpet din tsakiyar falon ne, an buɗe kowannensu dake cike da kaya fal.
Lefen Babbar ƴar Hajiya Maimunan mace da suke kira da Shukra ne, amma ba zaka banbance adadin yawan ƴanuwan Hajiya Maimunan ko kuma na Hajiya Kilishi a falon ba, sun riga sun zama ɗaya dukkanninsu don ko a sati biyu da aka karbi lefe biyu na ƴaƴan Hajiya Kilishin Safiyya da Salma, duk sune dai a wajen, shi yasa a yanzu ma rabi hirarsu ta shirye-shiryen bikin da aka saka nan da wata guda mai zuwa ce.
Hajiya Kilishi ta ratso ta cikin mutanen, sanye take da wata doguwar rigar lace daya sha adon stones sai wulgawar kyalli yake a cikin hasken fitulun dakin, ta karaso inda Hajiya Maimuna ke zaune akan kujerar Wheelchair dinta tana hira da wata ƴaruwarta, ta sunkuyo daidai saitin fuskarta sannan tace.
"Hajiya su Ma'aruf sun iso, yanzu na tura Malam Sani (direba) ya ɗauko su daga airpot, mukullin store dinki zan karba na ajiyemusu abinci ɗazu, Hajiya Madina ce tace zata tafi nace idan direban nata ya sauke ta sai ya karasa ya kai musu abinci don na san baxa su shigo yau ba."
"Toh Alhamdlilah, Muƙullin yana hannun Sameera ita ta karba dazu wai sun ajiyewa ƙawayenta abinci su ma."
Hajiya Maimunan ta amsa a hankali itama. Dukkaninsu sun sani cewa a duk tarin jama'ar gidan babu wanda bai san abinda Ma'aruf ɗin yayi ba da kuma cewar baya ƙasar don labari baya taba ɓuya, amma duk da haka gwara ace basu fallasa zancen ba duk kuwa da cewar duk ƴanuwa ne a gidan, amma hakan ba zai hana cece-kuce ba.
Daga nan ɓangarenta ta nufa, inda babu mutane sosai, kuma ƴanmatan gidan da wasu kawayensu suka tare suna ta hayaniyar da jiran a ragu don suma suje su buɗe nasu babin kallon kayan. A falo ta tarar da Zahra da Sahla ƴan autan gidan kuma sa'annin juna sun baje litattafansu suna ta aiki kamar basu san da bidirin da ake yi a gidan ba, dama yayyensu sun riga sun manna musu sunan Allazi boko 1 da kuma Allazi boko 2, don mayun karatu ne kamar ba gobe, yanzu suka shiga SS1 amma abinda suka sani ko Abdurrahim da yake SS3 bai sani ba, kwanaki har Surayya dake level three suka koyawa wani abu a Biology.
Har Hajiya Kilishin zata yi musu maganar abinci sai ta kula da plate din snacks dake tsakiyar litattafansu, ta sana aikin Mama Rabi ne hakan, wata dattijuwa ma'aikaciyar gidan da har yanzu bata daina kula dasu ba kasancewar ita ta yaye su tun suna ƙanana.
Don haka ta amsa sannu da shigowar da suka yi mata kawai ta wuce. Ta nufi kofar dakinsu Salma inda ƴanmatan suke, hayaniyarsu tun daga falon zaka ji ta, cike da raha da kuma nishadi kamar an fara bikin, kuma duka hirar da suke ta tsare-tsaren bikin ce da suka daɗe suna yi tunda wannan shine karo na farko da za'a aurar da mata a gidan, kuma har guda uku a lokaci guda.
"A'a ranar kunshi ne fa za'ayi style iri daya, ranar Kamu kamar kowa zaiyi style dinsa ne ko?"
Muryar Munaya ta tambaya cikin hayaniyar.
"Ranar kunshi fa shi babu anko Munaya kin manta ne kowa kayansa zai saka, da Kamu ne za'ayi har style ɗaya."
Wata kawar Salma, mai suna Aysha ta bata amsa.
Hajiya Kilishi ta buɗe kofar dakin daidai lokacin da Munayan ke gyara glass din idonta tana kallon wayar Sameera dake hannunta inda take ƙoƙarin banbace tarin atamfofi da kuma lesukan da zasu yi ankon dasu.
A ƙaton gadon ɗakin gabaɗayansu suke a baje dasu da tarin plate din snacks din da suke ci, sai wadanda basu sami waje bane suka zauna daga kan bedside drawers.
"Ni fa wallahi gani nake kamar wata ɗaya ba zai isa duk wannan shirye-shiryen ba."
Shukra ta faɗa tana danna tata wayar.
"What?!" Salma ta mike daga kwance tana kallonta.
"... Ai Ya Shukra kar ma ki fara wannan zancen don wallahi Imran ba zai taɓa yarda a ƙara mana ko sati ɗaya ba."
Salma ta faɗa wanda hakan yasa dukkaninsu yin shewa a lokaci guda, don duk cikin amaren tafi kowa ɗokin bikin, yayarta Safiyya ba ruwanta don ita dama ba mai magana bace tun farko, kuma wanda zata aura mai mata ne da ƴaƴan sa biyu duk da cewar ba wani manyan ta yayi ba. Shukra kuma dake kan matakin masters dinta a bayyane yake cewa hankalinta yafi tafiya ga Project work din da take kan gaɓar yi fiye da bikin, duk kuwa da irin rawar kafar da Suraj ɗin da zata aura ke yi shi, wanda dan wani abokin aikin Baffa ne.
Har Salma zata sake cewa wani abu Sameera dake gefenta ta daka mata duka, wani duka da idan zata yi ɓaram-ɓaramarta Mamin tazo wucewa suke yi mata shi, don haka a lokaci guda ta juyo ta kalli kofa inda Hajiya Kilishin ke tsaye tana kallonsu da murmushi.
"Mami ina wuni..." Duka kawayensu na ɗakin suka hada baki wajen gaishe ta don tun zuwansu basu ma ganta ba.
Da murmushin ta amsa musu sannan ta kira Sameera.
"Ina muƙullin store dinsu Munaya? Yayanku sun dawo yanzu, kizo ki tayani mu debo abincinsu a saka a motarsu Hajiya Madina."
Da wani irin murmushi mai faɗi Sameeran ta amsa, don Allah ya sani duk da kowanensu yayi waya dashi tun a jiya, da kuma hayaniyar gidan ta yau, suna cike da tunanin halin da Ma'aruf ɗin ke ciki, don abinda yayi wani abu ne da basu taɓa gani ba tsawon rayuwarsu duk da sun san cewa kuwa yana da wannan cutar.
***
Mallam Aminu Kano International Airport
08:30 PM.
"Wata nawa aka saka bikin yaran nan ne Malam Sani?"
Ishaq ya tambaya a lokacin da yake kokarin saka jakar kayansu cikin boot ɗin motar da Malam Sanin ya buɗe.
"Wata ɗaya aka saka wallahi, ai gidan ma har yanzu yana nan a ɗinke, shi yasa Hajiya tace ba sai kunzo ba, kawai in wuce daku gida."
Ishaq ya gyaɗa kansa yana rufe boot ɗin.
"Ai dama bamu da plan din zuwagidan nan yau, amma Lallai su Baffa sun shirya, har su uku ne fa a wata ɗaya kawai."
"To ai rufin asirin Allah ake ciki kullum kuma shi ke rufawar." Cewar Malam Sanin yana dariya.
Duk maganar da suke yi, Ma'aruf na zaune a cikin motar daga baya, wayarsa na riƙe a hannunsa haskenta na haska siririyar fuskarsa da a cikin ƴan kwanakin ta ƙara ramewa, message ne kawai ke tururuwar shigowa da kuma tarin emails tunda ya kunna wayar har zuwa yanzu, ya lumshe idanunsa kawai sai kallonsu yake a lokaci guda kuma yana jin hirar su Ishaq ɗin daga waje.
Allah ya sani gabaɗaya ya manta cewa shirye-shiryen bikin akeyi sai a jiya da Mamin ke tuna masa cewa yau ne za'a karbi lefen Shukra, kuma jin cewa gidan a cike yake yasa shima baiyi tunanin ya kamata su je ɗin ba, amma kuma ya kamata yaga Baffa a yau, idan yana gidan kuma fa? Sai yasa yatsan sa ɗaya ya share dukkan messages ɗin sannan ya lulubo nambar mahaifin nasa amma sau biyu ya buga bata shiga ba, don haka ya nemo ta Mami.
Bugu ɗaya kuwa muryarta ta shiga kunnensa.
"Mai gaskiya na, kun taho?"
Ta kira shi da sunan data laƙaba masa tun yarintarsa.
Sai ya sake lumshe idonsa ya koma da baya jikin kujerar lokacin da Ishaq da Baba Sani suka buɗe ƙofofin motar suka shigo.
"Eh Mami, Baffa yana gida kuwa?"
"A'a yana office shima har yanzu. Na bayar direban Hajiya Madina zai kawo muku abinci yanzu, wataƙila ma kuyi daidai dashi."
Wani abu ya motsa a kirjinsa, don yayi kewar irin wannan kulawar tata a ƴan kwanakin nan, sai dai kafin ya saurari abinda ta cigaba da cewa hankalinsa ya kai ga abinda Ishaq ke cewa cikin wayar sa da aka kira ya amsa.
"To shikenan gamu nan insha Allahu..."
"... Akwai maganar da zamu yi Ma'aruf, nima nafi son ka samu hutu sosai zuwa goben."
Sauran maganar Mamin ta shiga kunnensa bayan Ishaq ya kashe wayar da yake yi."
"Ma'aruf, kana jina kuwa? Da kaci abinci ka sha magungunan da aka baka "
Yaji ta sake faɗa lokacin da Ishaq ke cewa Malam Sani...
"Sakataren Baffa ne yakira, wai Baffan yana son ganinmu a office ɗinsa kafin muje gida, ka juya ta wanna U-turn ɗin sai mu koma."
Ba shiri Ma'aruf yaji wani abu ya zarce cikin maƙogwaronsa, don tun bayan farkawar sa sau ɗaya kawai yayi waya da Baffan, a jiya daya kira ta wayar Ishaq, ya tabbatar masa da cewar lafiya yake jin kansa shikenan bai kara nemansu ba, amma ko Baba Usman ya sake kira a safiyar yau kafin su taho.
Yana jin yadda Mamin ke cigaba jero masa tarin tambayoyi ta cikin wayar amma hankalinsa sam baya kanta har Malam Sani yasha kan U-turn din da Ishaq ya nuna wanda zai komar dasu baya zuwa hanyar Office ɗin Baffan, wani ƙaton branch na kamfanin su inda iya ma'aikata ne kawai a wajen.
"Muhammad..."
Muryar Baffan ta kira shi kuma a lokaci guda amonta ya ratsa har cikin kansa bayan sun isa Office ɗin, bayan sun shiga ciki kuma Baffan ya sallami wasu mutum biyu da yake tare dasu a lokacin, sannan bayan Ishaq ya dauki wata wayar ƙarya ya fita don dukkaninsu sun fahimci cewa dashi kadai yake son magana. Don haka ba shiri Ma'aruf yaji maƙogwaronsa ya bushe a lokaci guda, saboda Baffa baya taɓa kiransa da wannan sunan sai idan har wani zance mai muhimmanci zasu yi, kuma rana ta karshe da zai iya tuna ya kira shi da hakan shine ranar da aka daura auren sa.
Ya gyara zama a hankali yana jin yadda Baffan ya cika masa office din ta koina saboda kwarjini.
"Sun turo min da takarda wadda take bayanin ciwon naka."
Ya san takardar shima, sun tura ta email ɗinsa sannan sunyi printing ɗinta a cikin tarin takardun da aka sallamo shi dasu.
"Sun ce a cikin shekaru biyu kawai ciwon ka ya kara haɓɓaka har ya kai matakin karshe, shi yasa abinda kayi ya faru..."
Baffan ya faɗi haka sannan kuma yayi shiru, wannan dai al'adar ta manya. Ƙarar sautin shigowar saƙo daga wayar dake aljihun Ma'aruf ya cika shirun dakin kafin ya cigaba.
"Ko zaka iya gaya min a shekaru biyun baya kana ina Ma'aruf?"
Sai ya gyara zamansa a hankali, yana tuno ranar da Baffan ya naɗa shi a matsayin manajan kamfanin 'Bakori Enterprises' ranar da burinsa na farko ya fara cika a duniya.
"Baffa... Shekaru biyu baya shine lokacin da ka bani matsayin manaja a kamfanin nan."
Bai kalle shi ba, amma yaji sanda ya girgiza kansa.
"Ba wannan ba, rayuwarka personally Ma'aruf, kana ina?"
A yanzu ya rikice, yana jin kamar ma bai warke ba gabaɗaya, kamar ya sake bin jirgi ya koma asibitin nan ya kwanta.
"Ka manta?"
Ya tambaya amma bai bari ya amsa ba ya cigaba.
"... Bari ni na tuna maka, shekaru biyu baya kana tare da iyalinka Ma'aruf, shekaru biyu baya kana tare da matar da naje na karba maka aurenta har ma da yarinya, a shekaru biyu baya kai cikakken mutun ne mai kamala da mutunci a idon mutane, kuma a tsawon shekarun da kayi cikin wannan mutuncin, hankalinmu da naka bai taba tashi kamar yadda yayi a yanzu ba."
Wani abu ya zarce a maƙogwaron Ma'aruf, yaji wani ɓangare na ƙwaƙwalwar sa na gaya masa cewa wannan ce damarsa, yau shine lokacin da zai gayawa Baffa abinda shi da ishaq suka dade suna ɓoyewa, yau ya kamata ya gayawa Baffa cewa ba haka bane, abinda ya faru a zamansa da Ruƙayya har zuwa rabuwarsu ba yadda suke tunani bane sam.
"Na san da wannan tunin da nayi maka ka fahimci abinda ni dama duk sauran al'umma suka fahimta Muhammad, don haka kaje ka fara shirye-shirye, nan da wata guda zan karɓa maka wani auren tare da na ƙannenka."
Sai da aka shafe sakanni kafin maganar ta shiga cikin ƙwaƙwalwar Ma'aruf, da wani irin ƙarfin da sai da yayi da gaske kafin ya iya jawo iska ta shiga ƙirjinsa, sannan a karo na farko tun bayan fitar Ishaq ya ɗago idanu ya kalli mahaifin nasa.
Sai dai me? Maimakon fuskar Baffan, sai hoton wajen ya canja a idonsa da wani lokaci da ya faru a shekaru biyu da suka wuce...
Lokacin daya shaƙe wuyan Rukayya da duka hannyensu biyu, yaji ƙarar sautin karkarin da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads