Showing 54001 words to 57000 words out of 84785 words
Chapter 19 - Farar Wuta Book 1 Complete Hausa By Aisha Aliyu Garkuwa .txt
da Mamin ta taɓa gaya masa suna dawowa cikin kansa.
... Wannan ba irin ba irin Ruƙayya bace Ma'aruf, don nayi Imani yarinyar nan zata baka kulawar da kake buƙata.
Abinda Mamin bata sani bane, ita kanta Rukayyan tayi iya kokarinta a zamansu, don ta canja abubuwa da yawa a rayuwarta zuwa bukatarsa, matsalar kawai shine don son zuciyarta tayi komai, babu abinda tayi saboda shi ko don ta kyautata masa, don haka itama zai iya yiwuwa ta fara hakan ne don an saka ta, don bin umarnin da ya tabbatar shi tayi har auren nasu ya kasance, yaji zuciyarsa ta matse da wannan tunanin amma kuma sai ya samu sauƙi da hasashen cewa haka ba zai iya zama gaskiya ba.
Ta gama zuba lemon a wannan lokacin, ƙarar awarwaron dake hannunta ya janyo hankalinsa sanda take ajiyewa a gabansa daidai lokacin da wayarsa tayi kara daga kan kujerar nan, don haka tayi amfani da damar don miƙewa ta bashi waje amma sai muryarta ta tsaida ta.
"Ki zauna."
Fuskarsa fayau yana kallonta kafin ya juya ya dauki wayar. Ta haɗiye wani abu a makogwaronta a hankali sannan ta dawo da baya ta zauna ɗin, nesa kaɗan dashi kamar ɗazu.
Ya ɗauki wayar yana magana ta ciki, ta fahimci da wani yake magana kuma akan harkar aikinsu ne bayan hakan bata gane komai ba, amma kuma yanayin yadda yake maganar ya saka taji zuciyarta na sakewa da amon muryar tasa. Ya gama wayar ya ajiye ta a gefensa sannan ga mamakinta taji yace.
"Faruq ne, abokina ne a wajen aiki."
Sai ta daga kanta lokacin da ya sake kai wata lomar bakinsa sannan yace.
"Abincin nan yayi daɗi sosai Amina. Kinyi kokari."
Wani abu ya matse a zuciyarta daga yadda muryarsa ta ambaci sunanta, kamar zata yi magana amma kuma sai ta sake gyada kanta kawai tana wasa da karshen mayafinta. Kuma Yanayinta yasa Ma'aruf yaji a lokaci guda yana son suyi hira, aƙalla yau maganar tasu ta tsallake babin gaisuwa saboda haka yana kallonta yace.
"Munaya ta gaya min kina son karatu, tace ta samu wasu novels a wajenki. kina da litattafai da yawa."
Sai da sakanni biyu suka wuce sannan Amina ta yarda da maganar da ya furta saboda ɗan mamakin da ya kamata, ranar da take kokarin samawa litattafanta waje ne Munayan ta shigo ta ganta, a ciki har da wasu English novels dama na Hausa wanda take tarawa tun tana makaranta, shikenan sai suka shafe kusan rabin yinin suna hirar labarai kala-kala har ta ara mata wasu ma ta tafi dasu, don haka ta tabbata a yanzun ma ganinta yayi tana karatun ɗaya daga cikin wanda ta ɗauka.
"Wanne da wanne kika karanta?"
Muryarsa tana fitowa ne kamar yadda take jinta a kullum idan yana waya ko kuma da wani, amma a yanzu da ta san cewa ita yake wa magana sai take ji ta daban, tana saka ta ƴar rikicewar da bata shirya ba. A hankali ta daurewa hakan muryarta ta shiga jero masa sunayen littattafan da ta san sunyi suna amma da yawansu yace bai san su ba saboda yawanci akan Romance ne shi kuma yace ma yafi karanta Non-fiction, yana yi yana cin abincin cike da wani abu da zata iya kira da nishadi.
"Akwai wani 'The Life we had' na san zaki san shi.'"
Ta ɗaga kanta da sauri don ji tayi kamar hakan na kaɗe tasirin da muryarsa ke yi a zuciyarta, kuma a lokaci guda bakinta ya ɓalle da wani murmushin da bata shirya masa ba tana tuno yadda akayi ta karanta littafin a wani shagon bakin titin unguwarsu inda ake sayar da shi, zuwanta shagon nan bakwai kafin ta kai karshen littafin saboda yayi mata tsadar da ba zata iya siya ba, kuma wata ƙawarta da suka yi makaranta ɗaya da yawanci litattafan wajenta ma ita ta bata, itace ta dame ta zancensa, bayan sun bar makaranta ne a lokacin ita tana can Bauchi babu ta yadda zasu iya haɗuwa sai dai ta kira ta a waya tayi bata labarinsa. Tana tuna ranar da ta kai ƙarshen labarin da wani a cikin masu tsaron shagon ya gane ya tada ballin sai ta biya, da taimakon Aminu aka rufe case ɗin.
Bata sani ba ko shima murmushi yayi don kanta yana sunkuye amma taji muryarsa ta ɗan canja lokacin da yace.
"Ke ma kamar su Munaya ce ashe, ban san me marubucin littafin yayi da ya siye zuciyarku da yawa ba, babu wani abu da yake gaskiya a labarin nan."
Amina bata san sanda ta ɗago ta kalle shi ba tana girgiza kai, tace.
"Ai dama Fiction ya gaji ƙirƙire-ƙirƙire da yawa, shi yasa ya kirkiro komai ɗin don ya fito da ma'anar labarin sosai."
Ya girgiza kansa shima.
"Saboda kawai ya karya zuciyar mutane ne, shi yasa ma ya kashe su daga karshe, daga lokacin da na fahimci itama yarinyar mutuwa zata yi, na tsayar dashi ban ƙarasa kallo ba."
Sai ta sake ɗagowa ta kalle shi.
"Na zata novel ne."
Ta fada kamar tana tsoron labarin nasu zai banbanta, amma sai yayi saurin daga mata kai.
"Novel ne, amma lokacin da Munaya ta takura min da zancen labarin bani da time ɗin karatu, so sai kawai na siyo film din na kalla instead."
Ta gyada kanta sau daya sannan ta sake maida shi ƙasa ba tare da tace komai, yaji wani abu na shiga zuciyarsa yadda ta fara sakewa dashi a yanzu, don haka kai tsaye ya sake tambayarta.
"Baki kalli film din ba?" ya tambaya yana nazarin abinda bata faɗa ba akan furkar ta, kuma sai ta bashi amsar da ya riga ya sani ɗin ta hanyar daga kanta.
"Insha Allah zan kawo miki ki gani."
Sai ta ɗago ta kalle shi, yayin da hannunta ya tsaya da wasa da mayafin nata.
"Allah ya yarda."
Ta furta a hankali tana kallonsa, kuma a cikin idanun nata Ma'aruf yaga daren ya tsaya cak kafin ta sake sunkuyar da kanta a hankali, yaji wani abu yaji kamar tausayinta na bi ta kan zuciyarsa.
Tana da rayuwarta ya sani, watakila har ma da mafarkai na abubuwan da take son cimma, amma yanayin yadda auren yazo ya sani cewa yabi ta kan abubuwa da yawa a rayuwar tata, wanda da shine baya taɓa jin zai jurewa hakan, amma ita gata a zaune har tana kokarin yi masa hidima, yaji wani abu ya zarce cikin maƙogwaron sa a lokaci guda, a baya yana jin zai iya bin kowacce hanya don sanin meye haɗinta da Jamal amma tun a yanzu ya fara jin cewa ba zai iya yin abinda zata yi dana sanin haɗuwa dashi a rayuwarta ba.
***
Washegari da safe Hajiya Kilishi ta buɗe kofar ɓangarenta, fuskarta ta faɗaɗa da wannan murmushin nata mai armashi a duk lokacin da ta ganshi duk kuwa da cewar a jiya tayi ta kallon agogo cikin lissafin zuwansa amma bata ganshi din ba, dalilin da yasa a yau ta tashi da sassafe kenan don ta san yana da karbar magani a yau, don haka ta buɗe kofar zuciyarta na fatan ya kasance Ma'aruf ɗin ne, kuma fatan nata ya karɓu don yana tsaye a gabanta yana murmushin da take jinsa kamar ashanar dake ƙyasta zuciyarta wajen kamawa da wuta.
"Tun jiya muke kallon hanya Ma'aruf..."
Ta fada tana kallon idanunsa da kullum suke gaya mata shi daban ne a lissafinta ba sai ta rantse ba, zuciyarta tana yin fiffike ne ta tashi sama ta zagaya a duk lokacin da ta ganshi a gabanta irin haka.
"Mami I'm sorry, jiya aiki ne yayi min yawa kuma a gida naci abinci shi yasa baki ganni ba."
Maganar ta taho kamar wani gingimeman dutsen da ya faɗo daga kolulowar sama ya dira a tsakiyar kanta, a lokaci guda murmushin fuskarta ya ɗauke, idanunta suka tsaya akansa cak a sanda ya kara wayar hannunsa a kunne ya shiga yiwa wani Benjamin magana cewa yayi wa Legal Department ɗinsu bayani su ƙarasa shiryawa kafin ya ƙaraso.
Ya katse wayar ya juyo ya kalle ta a lokaci guda da yanayin nata ya baje, fuskarta ta cakuɗe da murmushin da yasa shi gyaɗa mata kai kafin ya wuce zuwa ciki, Abinda bai sani ba shine wannan karon murmushin ba nasa bane, na halittar da take hangowa a cikin idanunta ce... Amina!
A yau an ƙaraso gaɓar da take jira, a yau tsarinta zai fara ba sai gobe ba, bata wasa da lokaci balle har tayi sake da koda ƴar mitsitsiyar dama ce... A yau Amina zata shigo cikin ukunta!
A yau duk wani mahalukin da yake da kusanci da Amina zai shigo cikin lissafinta!
**
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
BABI NA SHA DAYA.
~~~~~~~
I've never fallen from quite this high
Fallin' into your ocean eyes
Those ocean eyes.
-Billie Ellish
A wannan ranar Amina na kwance daga kan gadon ɗakin tana sauraren wani shiri mai taken 'Allah ɗaya gari banban' da baya taɓa wuce ta daga cikin rediyon wayarta.
Idanunta kusan a rufe suke yayin da take sauraren maganganun mutanen dake gabatar da shirin, yau hira ake akan daya daga cikin garuruwan da take son zuwa a rayuwarta, Paris... Don haka sosai take jin daɗin duk wani bayani da baƙin da aka gaiyato suke yi na yadda garin yake da kuma tsare-tsaren su.
Sai dai duk yadda hankalinta ke kan shirin zuciyarta kuma nata zarya a can falon gidan inda ta kammala komai na abincin Ma'aruf ta ajiye masa kaar jiya, a yau ta riga ta tsarawa kanta cewa ba zata fita ba don Allah ya sani bata so yaga kamar tana kokarin shige masa ne ko kaɗan, ƙundubalar da tayi wajen yi masa abincin ta wadatar tunda har yanzu bata san manufarsa akanta ba.
Ko a jiya umarnin da ya bata ne kawai yasa ta zauna ba wani abu ba, yadda muryarsa ta furta 'Ki zauna' da kuma yadda ya kalle ta da idanunsa bai bata damar zabi ba ko kadan. Duk da cewa kuwa taji dadin hirar, tsaya... Ba hirar tasu ce ta mata daɗi ba, zancen cewa wannan labarin yana da film ne, don Allah ya sani zata so ganin yadda dukkan tunaninta game da komai na labarin zai fito zahiri.
"... Wato ina gaya maka samun gida a garin nan shine babban abu mai wahala, gidaje ba karamin tsada ne dasu acan ba..."
Hirar rediyon ta cigaba da fitowa yayin da zuciyarta ta fara lissafin kamar yau ya daɗe da yawa, don ko da safe bata ganshi ba kuma yau ita kadai ta yini a gidan, su Sahla da Zahran da suka yi mata alkawarin zasu sake shigo mata yau sun manta da zuwansu makarantar Haddar da suke zuwa shi yasa bata gansu ba.
Tun da tazo gidan basu shigo mata ba sai jiyan, kuma sai a jiyan ta gane ashe su ma suna da magana kamar su Samirah, a cikin gidan idan ta gansu da littafinsu kawai gaishe ta suke yi su cigaba da harkokinsu, amma jiyan da suka shigo tasha labarai kala-kala wanda mafi yawanci ba komai ta gane ba.
Don a baiyane yake yanayin rayuwarsu da tata ba iri ɗaya bane, abubuwan da suka taso suka sansu ita har yanzu saninta bai ƙaraso nan ba, yanayin makarantar su dama ƴaƴan masu kuɗin da suke mu'amala dasu ba iri daya bane da abinda ita ta taso ta sani. Ta tuno wata magana da Aminu ya taɓa gayawa Maryam ranar da yake tsokanarta bayan ta gama kurin cewa ai ita babu inda zata je a raina ta.
"... Nan bayan layin nan idan aka ƙarasa ba sai anje da nisa ba za'ayi iya ɗebo sa'anninki biyar da in suna hira ba zaki taba iya magana ba wallahi sai dai kiyi ta binsu da kallo kina wage baki."
Itama dai kuwan ta wage jiya, don murmushi kawai tayi ta binsu dashi kamar yadda take yi a wajensu Samirah, don har gwara su Zahran ma, su idan suka fadi wani abu sai ta biya shi sau biyu akanta kafin ta fahimta musamman Surayya da ta fahimci tafi su iyayi gabaɗaya. Suna da daɗin mu'amala sosai, da gaske suke sun karbe ta a cikinsu ba tare da tunanin komai ba,
Ta tuna sanda Samirah ke mata bayanin dalilin da yasa basu je gidansu da biki ba.
"Mu fa bamu san da bikin ku da Yaya ba sai ana saura two weeks da aka haɗa lefe sannan Mami ke gaya mana, kuma ko ranar dinner ma munso mu kai muku cards din. Yaya Shukra ce ma ta bani ranar luncheon na saka a jakar Khadija (wata kawarta) ita kuma sai tazo da wata jakar kuma ta manta bata ɗebo ba. A ranar ni kuma I was so busy kamar me, shikenan ban samu time munje mu ɗauko ba. Da na kira Yaya kuma na gaya masa cewa yayi kar mu damu kawai."
Amma duk da yadda ta fara sakewa a cikin nasu, tana kewar gida kamar ba gobe, abubuwa da yawa akwai su anan na duk wata buƙatar rayuwa, ga komai sabo koina ƙal-ƙal, gashi babu wanda ya taɓa ko haɗe mata rai har yanzu, idan ta shiga cikin gidan kowa haba-haba yake da ita, hatta su Salma amaren da akayi bikinsu tare dukksnsu sun gaisa a wayar Samirah, da Salman ma ba sau biyu suna gaisawa.
Ga Hajiya Kilishi da take nan-nan da ita kullum fuskarta dauke da fara'a tana fadin ita ƴarta ce, Ranar da taje ta gaishe da Baffa ranar ta fahimci dalilin da yasa Baba ya bada aurenta a gabansa ba tare da wani tunani ba, dattijo ne kamili mai nutsuwar da a fuska kadai kowa zaiyi masa shaidar hali na gari, don haka babu wata matsala da ta guskanta a gurinsa shima.
Sannan shi kansa uban gaiyar har yau ko haɗe rai bai taba yi mata ba, amma duk da haka, tafi son rayuwar cikin ƴanuwanta akan wannan, tunda har yanzu zuciyarta bata gama kwantawa da komai ba, tunaninta iri ɗaya ne da Amma dama kuma Fatima, dukkaninsu sun yarda cewa akwai wani abu dake tahowa wanda bai karaso ba, don ba'a ɗora turbar auren da cewar komai ya tafi daidai ba, sun sani cewa ba sun kawo ta cikinsu ne don su nuna mata kirkinsu ba dashi da ƴan gidan nasu, dole akwai wani abu da yake a ɓoye wanda har yanzu basu kai ga saninsa ba.
Su Aminu da Baba ne kawai hankalinsu a kwance don duk sanda suka yi waya da Baban, zai yi ta zubo mata tarin addu'o'in da suke karya zuciyarta, shi har yanzu zuciyarsa guda ɗaya ce game da auren, ya riga ya aminta da Baffa da ma Hajiya Kilishi ta yadda baya taɓa iya hango komai.
Ta lumshe idanunta a hankali tana jin yadda bacci ke shirin ɗaukarta a lokacin, ta shiga ƙokarin kore shi don aƙalla tana son jin lokacin da Ma'aruf zai dawo amma baccin mai nauyi ya ƙara karfinsa, don haka wata zuciyar ta gaya mata cewa zata iya ɗan runtsawa tunda tayi sallar isha kuma bata wani samu baccin safe ba sosai, da wannan lasisin da zuciyarta ta bata taji maganganun cikin rediyon nan suka zuƙe daga kanta a hankali, taji su suna yin nisa da kunnenta kafin a lokaci guda taga Aminu a tsaye daga bayan idonta.
"Me yasa kika kasa Amina?"
Kai tsaye ya tambaye ta yayin da idanunsa ke kallonta, kuma kalaman suka isa kanta amma suka kasa bada ma'ana saboda dukkan tunaninta ya tsaya cak tana kallonsa da dimbin mamaki, Yaushe yazo? Yaushe yazo ko kuma ita yaushe ta bar cikin gidan, don daga nesa tana hango duhuwar wasu dogwayen bishiyu, hakan yasa gabanta fadi da dukkan tsoron da zuciyarta zata iya dauka.
Tayi ƙokarin ta kalli kanta amma sai ta fahimci bata iya ganin jikinta kwata-kwata, kamar idanunta ne kawai a wajen suke ganin komai amma babu gangar jikinta, ta ɗago ta sake kallon Aminun da har yanzu ke tsaye a gabanta.
A lokacin ta kula cewa idanunsa sun canja, kalolinsu ba iri ɗaya ne daga yadda ta sansu ba, sun koma baƙiƙ-ƙirin dauke da kyallin kwalla yayin da fuskarsa ke nuna dukkan wasu kalolin tashin hankalin da bata taɓa gani a fuskar Aminun ba, Aminun mai raha da fara'a, Aminun data sani mai ɓoye damuwarsa a kodayaushe.
"Me yasa kika kasa Amina?"
Muryarsa ta sake tambaya da amon da ya kara hargitsa ta, kuma bata san lokacin da ya matso gabanta ba sai kawai taji ya riƙo hannunta na dama.
Ta kalli inda hannun nata ya kamata ya kasance, babu komai sai yadda yatsunsa suka riƙe ta, lokacin da ta ɗago da idonta sai taga ashe ya jawo ta ne har sun iso wajen duhuwar bishiyun nan, tashin hankalin ta ya ƙaru don tana jin yadda ƙafafunta da basa nan suke tafiya, da kuma yadda hannayenta ke rawa a cikin nasa.
Hankalinta ya kasu wajen nazarin bishiyun sanda suka tsaya a wani waje, ta juyo tana kallon yadda yanayinsa ke haskawa da dukkan raunin da bata taɓa hange ba, taji ta ƙara rikicewa, taji abubuwa da yawa suna tasowa cikin kanta, tambayoyi fal suna ihu da kokawar fitowa daga bakinta da ta san babu shi balle har ta iya furta su, kowanne lungu da saƙo na tunaninta ya cika da hanƙoro, kamar tana jiran wani abun da bata san meye ba.
Kuma kwatsam sai ta nemi bishiyun nan dake kewaye dasu duka ta rasa, warin ƙonewarsu ya cika hancinta amma babu su ɗin balle kuma alamun wutar, kuma babu wani ɓata lokaci kunnenta ya fara jiyo mata muryoyinsu, Maryam ta fara ji, tana ihu mai haɗe da salati, sai ta jiyo ta Hafsa da Adam ma, kowanne yana kuka mai nuna tsananin azaba, bata san ya akayi ta iya tsinto muryoyin su Fatima, Ummi har ma da ta wasu daga cikin ƴaƴan kawu Malam ba.
Kuma kafin wani abu ya sake giftawa a cikin kanta ta jiyo muryar Baba yana faman kiran sunayen su Maryam ɗin har ma da sauran mutanen da bata iya tantance muryoyinsu ba, hankalinta ya kara tashi duniyarta ta rikice, ihu da hargowar suka cika kanta kota'ina, kuma a lokacin da ta juya zata kalli Aminun sai taga babu shi, a yanzu Amma ce tsaye tana kallonta, fuskarta ɗauke da wani irin murmushi mai ciwo yayin da take kallonta da dukkan wani fata na duniya.
"Me yasa kika