Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 84785 words

Chapter 7 - Farar Wuta Book 1 Complete Hausa By Aisha Aliyu Garkuwa .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

gaban kayan akwai dukkan tarkacen dake cikin aljihunsa a wannan ranar, muƙullin mota, chewing gum, chapet, biruka da kuma wallet ɗinsa, wallet ɗin ta dauko sannan ta rufe wardrobe ɗin ta dawo gaban Hajiya Salamatu ta miƙo mata ita.
Sanin halinta sarai yasa Hajiya Salamatun ta karɓa ba tare da ta tambaya ba, ta ware cikinta, kuma bayan tudun kuɗin da taji a ciki da kuma jerin credit cards, wani hoto da aka maƙala a jiki shi ya ɗauki hankalinta, samari biyu ne a jikin hoton wanda kallo ɗaya kawai zai shaida maka cewar wa da ƙani ne, don bayan girman da ɗaya yafi ɗaya, akwai kammani sosai a fuskarsu. Suna dariya mai cike da nishaɗi yayin da babban ke miƙo hannunsa kamar zai naushi ƙaramin.
Ƙaramin Ma'aruf ne Hajiya Salamatu ta sani, babban kuma...
"Jamal..." Sassanyar muryar Hajiya Kilishi ta furta tare da tunanin Hajiya Salamatun.
"Jamal shine ƙalubale na kuma shine rauni na Salamatu, shi yasa na rufe idanuna nayi abinda ya kamata akansa, don haka kamar kullum zan gaya miki cewa ki yarda bani da wata matsala a duniyar nan yanzu idan ba kuma ƙaddarar ubangiji ba. "
Ta fadi hakan yayin da take tsaye akanta, Hajiya Salamatun ta ɗago ta kalle ta, wannan murmushin na baya ya tafi, idanunta sun canja ta yadda ko ɗigon raha babu a cikinsu.
"Kar ki ƙara lissafa Ma'aruf a cikin ƙalubale na Salamatu, don kinfi kowa sanin matsayinsa a waje na."
Kuma a cikin idanuwan nata, Hajiya Salamatun ta shiga hango abubuwan da suka faru wasu tarin shekaru da suka wuce!
******
11:20 Am
"Inalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Wai baka da imani ne Ishaq? Tun da na tashi kake ta masifa a gidan nan kana mita, nace maka wallahi ko ganin yarinyar banyi ba balle inyi mata wani abu, do I have to bury myself before you believe?" (haƙa kabari zanyi in shiga kafin ka yarda dani?)
Ma'aruf ya fada a lokacin da yake zaune kan dining table din falon gidansu, inda ya samu ya ture wasu litattafai da kuma kayan wankin Ishaq ya dora plate ɗin abincin da yake ci.
Ishaq na tsaye daga cikin falon shima rike da nasa kofin shayin da kuma remote ɗin da yake kokarin chanja channel daga ta labaran da Ma'aruf ya kai.
"Ka gayawa wani ba ni ba, na san halinka sarai B, hankalinka ba zai taba kwanciya haka ba idan har ba kayi abinda kake so ba. I'm just advising you (shawara nake baka) komai zai iya faruwa idan har maganar nan ta lalace kuma Baffa ya san da saka hannunka."
Ma'aruf yayi murmushi a hankali sanda yake jin zafin faten dankalin dake sauka cikin maƙogwaronsa wanda motsawar Adam's apple ɗinsa kadai zai shaida maka hakan.
"Wai ina zaka je ne ma? Yau asabar fa?"
Ya canja akalar zancen nasu ba tare da ya kalle Ishaq ɗin ba, don tun da farko kayan jikinsa sun riga sun nuna masa cewa Office zai je. Babu adadi na lokutan da zuciyar Ma'aruf ke motsawa a duk lokacin da yaga Ishaq na yin wani abu da ya danganci aikinsa, aikin da yake so kuma abinda shine mafarkinsa ya fito dashi zahiri kuma yake yi ɗin. Shi nasa burin da kuma mafarkin sun dade da kaɗewa shekaru goma da suka wuce. Abinda yake yi a yanzu, ba rayuwarsa bace ko kaɗan, wata rayuwa ce da ta zama dole ya ƙarasawa mai ita.
"Thanks to you, nayi missing tarin ayyukan da dole inje in san halin da ake ciki kafin Monday, Idan ciwon ka ya sake tashi Ma'aruf wallahi ka nemi mai raka ka asibiti."
Murmushi Ma'aruf keyi har a lokacin yana cigaba da cin abincinsa yayin da ƙamshin curry da kuma naman dake cikin abincin ke gauraye ɗakin, ya kai hannu yana cusa yatsunsa cikin gashin kansa, wani abu da ya riga ya zama ɗabi'arsa kafin yace.
"Ka san me Mami take ce min yanzu? Wai inyi aski kafin in shiga gida, don Inna Danejo na tashi da safen nan abinda ta tambaye ta kenan."
Ba shiri Ishaq shima yayi nasa murmushin kafin ya gyaɗa kai don har ya hango irin rigimar da za'ayi da Ma'aruf din da ba zaiyi askin ba da kuma Inna Danejon da ba zata haƙura, don kafin tafiyarsu London ta kawo dalilai sun fi ashirin na cewar rashin lafiyar Ma'aruf tana maƙale da gashin kansa ne, Baffa ne kawai bai bada goyon baya ba da tuni sai dai Ma'aruf ɗin ya tashi yaga kansa ɗal!
"Hular sanyi kawai zaka dauka, in zaka shiga wajenta ka saka kace anyi askin ba'a bude kan ne."
Ya faɗi hakan lokacin da ya gama neman abinda yake so a jikin Tvn don haka ya ajiye remote din ya juyo ya kalle shi.
"Za'a kawo maka motar ka ne?"
"Eh, na kira direban Office tun dazu nace yaje ya ɗauka ya kaita Carwash, I'm sure kafin 12 zai dawo da ita."
Ishaq ya gyaɗa kansa.
"Shikenan mu haɗu a gidan, nima can na nufa idan na tashi insha Allah."
Ya faɗi hakan yana juyawa hanyar ƙofa, idanun Ma'aruf suka bishi da kallo yana tunanin wani abu, kuma sai da ya isa ƙofar da zata fitar dashi waje har ya buɗe ta sannan yayi saurin kiran sunansa.
Ya kuwa juyo a take kamar shima dama jiran kiran yake yi. Ma'aruf ya girgiza kansa yana kallonsa.
"Wallahi ban ga yarinyar ba Ishaq, kawai dai na bata wani saƙo ne da na san dole ba zata taba yarda ba."
****
11:30Am.
"Na yarda!"
Kalaman guda biyu suka fito daga bakin Amina lokacin da take tsugunne a gaban iyayenta guda biyu da dukkan fuskokinsu ke haskawa da tsananin mamaki.
Tata fuskar fayau take, ba abinda zaka iya tsinta a jiki.
Ta gyara zamanta sannan ta sake maimaitawa kamar wani ya sata.
"Na yarda zan aure shi Baba."
Maimaitawar ta fiyo tare da faɗowar flask ɗin ruwan zafin da Amma ta ɗauko don juyewa Baba ruwan wanka, ya subuce a hannunta ya faɗi har ƙasa, kwalbar ciki ta tarwatse yayin da ruwan zafin ya fallatsa akan dukkaninsu.
*
Me kuke tunani yasa Amina ta yarda da auren Ma'aruf?
Wacece ainihin Hajiya Kilishi?
Me ya faru da Jamaal?
Shekarun cikin labarin sun wuce da wasu abubuwa da zamu fara kwance su daga Babi na gaba insha Allah...☺️
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
BABI NA BIYAR.
~~~~~
Ana gobe sallah ne ranar, ita da Maryam sun je kasuwa siyayar mayafai da takalmi, tun kusan sha biyu suka fita har mutane suka fara alwalar sallar la'asar basu gama siyayyar ba.
Maryam dake riƙe da ledar kayan da suka siyo kalli tsinken kwakwar da suka auno tsawon kafar Hafsa dashi tace.
"Ai wallahi dama na san takalmin yarinyar nan shi zai bamu wuya, kafa kamar ba ta mutane ba ƴar firit da ita."
Amina ta share gumi a gefen fuskarta tace.
Har tunani nake ko ba daidai na auno ba wallahi gashi mun kusa gama siyen komai..."
Bata karasa ba ta tuno da sakon garin da Amma tace su siyo zata yi teba dashi da daddare.
"Kin san na manta da garin Amma... zo muje wancan layin na san zamu samu."
Maryam ta girgiza kanta.
"Mu raba tafiyar kawai lokaci ƙara wucewa yake, ga wani kantin takalma can, bari naje na duba idan ma ban samu ba zan jira ki sai kizo ki same ni anan."
Da haka suka raba tafiyar, Maryam ta tsallaka ta cikin cunkoson mutanen ta nufi kantin ita kuma tabi layin gefensu inda nan ɗin ma turuwar mutanen ce wadda dama sun riga sun shirya mata, don tun ana saura sati ɗaya sallar suka so zuwa kasuwar amma rashin haɗuwar kudin yasa dole sai yau suka samu suka fito.
Ga rana, ga azumi amma yadda mutane suka hargitse baza kace kowa a gajiye yake ba. Da kyar ta samu ta ɓulla layin da masu garin suke, kuma akan ragin naira hamsin ɗin da zasu yi kuɗin mota dashi, sai da ta kusan shanye layin tana tambaya da ƙyar ta samu wani acan ƙarshe yace zai rage mata.
Tana tsaye yana ƙoƙarin auna mata, wani yaron shagon nasa ya shigo, irin samarin nan ne masu magana, yana shigowa ya haye kan ɗaya daga kantocin shagon yana fadin.
"Allah na tuba a yadda ake wannan ranar ga azumi ai wallahi komai talauci na ba zanyi aikin sauke gari ba, don mugunta kaga yadda suke jefo musu buhun nan daga sama, wani har sai ya kai ƙasa wallahi kafin ya ɗago."
Maganar ta ɗauki hankalinta, tana hango yadda nauyin buhun gari yake ace mutum ya dauka a wannan ranar.
"Yau ma mota ta sauka ne?"
Mai shagon ya tambaya yana miko mata ledar garin.
"Gata can yanzu ta tsaya, ka san shi Auwalu ko da goma yaga sunyi ƙasa sai yayi aike."
Ta miƙa masa kuɗin tana faɗin ta gode, amma kafin ya karba saurayin yayi saurin miƙo hannu ya karba sannan ya miƙo mata yana mata murmushi, irin halin ƴan kasuwa.
A kofar shagon kuwa tana fita taga motar ana ta sauke garin, tausayin masu yin dakon ya tafi har cikin ranta ganin yadda ko a ido buhun ke da nauyi, tana tafe tana ganin fuskokinsu lokacin da idonta ya kai kan fuskar da ta sa ba shiri hannunta ya saki ledar garin nan... Mahaifinta ta gani dauke da wani katon buhu yana ƙoƙarin kaiwa inda sauran ke saukewa, mahaifinta dai Baba, Baban daya shirya tsaf a yau ya fita suna yi masa a dawo lafiya.
A wannan lokacin yana gaɓar farfaɗo wa daga karayar arzikinsa ne, don duk da kokarinsa wajen yi musu kayan sallah, har saida aka haɗa da kuɗin Aminu kafin komai ya isa, bata san lokacin da hawaye ya fara biyo kuncinta ba, taga ya sauke ya koma sake ɗauko wani... Baba mutum ne mai tsananin son dogaro da kansa kowa ya sani, yayyensa duka sunyi kokarinsu wajen tallafa musu tunda al'amarin ya faru, amma babu wanda ya isa ya ɗauke maka cin yau da gobe sai Allah, don haka ta san nauyin ya cigaba da tambayarsu ne yasa har ya kawo kansa yin wannan aikin don kula dasu.
Hawayen ya cigaba da bin fuskarta yayin da zuciyarta ke rawa a kirjinta, tunanin ta ɗaya ne a lokacin, idan har mahaifinta zai iya sadaukar da girmansa yayi wannan aikin don kawai ya fita kunyarsu meye su baza suyi don fita tasa kunyar a duniya da kuma lahira ba?
Ta share hawayenta lokacin da wani mai wulbaro ke miko mata ledar garin da Allah yaso bata fashe ba. Kuma bata fadawa Maryam abinda ta gani ba, bata fadawa Amma ba, bata fadawa kowa ba, don ta san hakan wani abu ne da Baban ba zai taɓa so waninsu ya sani ba.
Kuma a wannan daren sai gashi ya dawo da ledar kaza har guda biyu ta miyar sallah, su Hafsa suka yi ta tsallen murna yana binsu da nasa murmushin shima.
Wajen karfe biyun dare bayan kowa ya kwanta, ta hango shi ta ƙofar ɗakinsu a wajen banɗaki yana miƙe bayansa, kukan da tayi a cikin filonta a wannan daren Allah kaɗai ya san yawansa, abu ɗaya kawai ta sani shine tayi wa kanta alƙawari a wannan ranar cewa ko abinda yafi rayuwarta ne zata sadaukar a duniya don farantawa mahaifinta.
*
"Wallahi gani nake yi kamar zaki ƙyalƙyale da dariya ki gaya min wasa kike yi."
Fatima ta faɗa tana kallon Amina data idar da sallah a gabanta.
"Ke ma kin san ai ban taɓa miki irin wannan wasan ba, da gaske nake Fatee, don yanzu haka ma Baba ya tafi gidan Kawu Mallam ya faɗa masa."
"Ya fada masa cewa kin yarda zaki auri wanda yake da matsalar ƙwaƙwalwa Amina...? inalillahi wa'inna ilaihir raji'un Amina kin san Allah ko da nake cewa ki rabu da Abdallah ki samu wanda yafi shi ba irin haka nake nufi ba, ya za'ayi kiyi irin auren da ake bada labarin ire-iren sa a sigogi mara sa daɗi?"
Fatiman ta ƙarashe muryarta na karyewa. Amina ta cire hijabin sallar tana kallonta,
"Ban gane me kike nufi ba?" Ta tambaya tana kallonta. Fatima ta girgiza kai kafin ta gyara zamanta.
"Amina duk wanda yaji batun auren wallahi shaidar da zaiyi miki daban, kowa cewa zaiyi auren kuɗi zaki yi, musamman ƴan unguwar nan da kin san daman ƙiris suke jira akanki."
Amina ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta, abinda Fatiman ta faɗa gaskiya ne ta sani, kuma maganar iri ɗaya ce da maganganun Amma na jiya, duka su biyun ƴancinta suke nemar mata, amma a wajenta darajar mahaifinta itace a gaba da ita kanta don haka ta riga ta gama yankewa kanta hukunci, ta gayawa zuciyarta cewa zata tsaya tare da mahaifinta koda zata mutu sau biyu idan ana yi.
"Fatee na tabbata ba fa ba wai matsala ce sosai ba, kawai sun faɗa ne saboda kinga a aure ba'a ɓoye komai, kuma ma Baba yace baza'a bari maganar ta fita ba, kema kin san ba zan iya ɓoye miki bane."
Ta faɗi hakan yayin da idanunta ke hango takardar data cusa cikin kayanta a jiya, babu wanda ya san da ita, babu wanda ta gayawa hatta Amma kuwa duk yadda kowanne abu mai hankali a cikin kanta ya tsorata da maganar dake rubuce, amma ta sani cewar in har iyayenta suka ji hakan dole zai iya sake zama wani ƙalubale musamman ma a wajen Amma don haka ta yanke hukuncin ɓoyewa tunda ba zata taba fatan abinda zai hadassa mahaifinta yaji kunya ta dalilinta ba.
Kuma kafin Fatiman ta sake cewa wani abu suka tsinci sallamar Ummi daga tsakar gida, ƴar Kawu mallam wadda suke kusan sa'anni da Aminan.
"Ina amaryar take?" Muryarta ta fito da fara'a bayan ta gaisa da Amma da kuma Maryam wadanda suke kitchen, ta karaso ya ɗage labulen ɗakin tana kallon Amina bakinta a washe.
"Yarinyar nan da tsinannen wayo, sai dai muji kawai wai zaki yi aure?"
Sai dai Amina tayi wani guntun murmushi kafin tayi mata sannu da zuwa.
"Ni ba zan amsa ba wallahi, tunda sai da muka ga meeting ɗin su Kawu yayi tsawo sannan da kyar muka san me ake ciki, da ake ɓoye mana naga wanda zai raka ki siyayyar kayan bikin ai."
A cikin maganar ta Amina ta tsinci wani abu, cewa da gaske Baba yake a ɗazu daya shaida mata cewar kowa zai ji maganar auren ne ta fuskar alkhairi, babu wanda zai san me ake ciki, gashi kuwa ko iyalan Kawu Mallam ɗin da ake taruwa a gidansa basu san komai ba, zurfin maganar ya tsaya a iyakar Baba da yayyensa ne sai kuma Amma, Fatima, Maryam da Aminu da suka sani a yau. Ance zancen duniya baya ɓuya, amma har cikin ranta tana fatan zancen ya tsaya a iya wadannan mutanen kawai.
"Ai ni ban yi zaton har ɗan bokon naki ya gama makaranta ya shirya ba, shi yasa wallahi abun ya bamu mamaki sosai, har su Umma ma cewa suka yi koda wasa Amma bata yi musu zancen a kurkusa ba."
Amina ta girgiza kanta.
"Ai ba shi bane Ummi, wani ne daban."
Sai da Ummin tayi shewa kafin tace.
"Gaskiya ne yarinyar nan, kice da karfinki kika taso, Fatima bani labari don na san zanfi ji a wajenki, wane ne sabon kamun?"
Fatima tana take tace.
"Wallahi kin san al'amarin Allah ai, kawai komai a lokaci guda yazo."
"Eh, amma dai da maiƙon sa ko? Yadda komai ya taso a lokaci gudan ai na san a shirye yazo ko?"
Kawu malam mutum ne malami mai sauƙin sha'ani, amman sai Allah ya bashi matansu duka ukun masu azabar son kuɗi, kuma suka taso da ƴaƴansu ma gabaɗaya akan hakan, gashi mata sunfi yawa a ciki don haka a zaune yake cewa basa auren kowa sai mai abin hannunsa ire-iren ƴan kasuwa, gasu da surutu da kuma kauɗi, hakan yasa duk kusancinsu dasu Amina basu fiye shiga cikinsu sosai ba don halayensu sun banbanta duk kuwa da cewa suna da mutukar kirki.
"Ai kuwa dai yana da kuɗi gidansu ma haka."
Fatima ta bawa Ummin amsa har a lokacin tana murmushin yaƙe.
"Kice dole ne mu raƙashe a bikin nan, wallahi azo a saka mana rana ma nan kusa Momi tazo mu fara shirye-shirye, zaki yi anko?"
Amina taji wani abu ya tokare mata a maƙoshi, don ita har ta yanke hukunci bai taɓa zuwa kanta cewar ma biki za'ayi ba, gani take kamar jana'iza kawai za'ayi akaita, kuma sai Allah ya taimake ta kiran Amma yazo a daidai lokacin don bata san amsar da zata bawa Ummin ba.
Amma ta kalle ta bayan ta isa kitchen din, fuskarta fayau tace.
"Kizo ki zuba muku abinci gashi nan an sauke."
Ta haɗiye yawu a hankali tana ƙarasawa ciki, lokacin da flask ɗin ruwan zafin nan ya faɗi daga hannun Amma, sai ya zama kar ya fashe da dukkan irin hukuncin da take tunanin Amman zata dauka akan ƙin bin maganarta da tayi, don a lokacin bata ce komai ba, juyawa tayi kawai ta bar wajen yayin da Baba ke saka mata albarka, kuma bayan taje ta same ta a ɗaki, abu daya kawai tace.
"Rayuwarki ce dama Amina, na nuna miki kuskuren dake ciki ne kamar yadda yake alhaki na a matsayin uwa, kuma tunda har kinga zaki iya dauka, ga fili ga maidoki nan, zuciyata ba zata riƙe ki da komai ba, Allah ya baki sa'a."
Daga haka bata ƙara cewa komai ba, kuma bata yi fushin da Amina tayi zato ba, harkokinta ta cigaba da yi a gidan kamar dama maganar bata taso ba, kamar dai shekaranjiya da Baba bai ko ziyarci gidan Hajiya Kilishi ba, balle su san da komai.
Ta zuba abincin ta kai musu, suna ci Ummi na daɗa bada bayanin yadda abubuwa zasu kasance wanda daga ita har Fatiman yaƙe kawai suke suna amsa mata, wajen la'asar ta tafi, lokacin ma Fatima ta daɗe da tafiya asibiti inda tace yau za'a sallamo kakarta.
Wajen ƙarfe biyar, Aminu ya shigo gidan riƙe da wani flask lokacin da take wanke-wanke ita kaɗai a gidan, don Amma ma ta shirya ta tafi gidan wata ƴaruwarta a Goron dutse ta shaida mata al'amarin.
"Ina yarinyar nan take?"
Ta san Maryam yake nema don haka tace.
"Ta tafi makaranta tun ɗazu."
Sai ya ajiye flask ɗin a ƙofar kitchen sannan ya ƙaraso ya tsugunna a kusa da ita, muryarsa ɗauke da nutsuwar da zaka shafe rabin rayuwarka kafin kaji ta a wajen Aminu yace.
"Hukuncin da kika yanke yayi daidai Amina, ba don Amma ba daidai ta faɗa ba, sai don kare mutuncin Baba da kika yi, kuma na tabbata Allah zai duba hakan ya kyautata rayuwarki."
Kwalla ta taru a idonta lokaci guda, don haka ta gyada kai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads