Showing 69001 words to 72000 words out of 84785 words
Chapter 24 - Farar Wuta Book 1 Complete Hausa By Aisha Aliyu Garkuwa .txt
wucewar wasu sakanni sai kuma ta taso a hankali ta dawo kujerar kusa da inda Aminan ke zaune, kuma bata damu da rashin kallonta da har yanzu bata yi ba ta cigaba.
"Mu dawo kan abinda ya kawo ni, dalilin da yasa na aura miki Ma'aruf Amina, kamar yadda na faɗa ba don ki zo kiyi rayuwar zaman aure bane kamar yadda naga kin fara kokarin yi a yanzu, na kawo ki gidan nan ne saboda ki taya ni mu ƙarasa babban burin da nake dashi a duniya.
A farkonsa ban tsara dake ba, amma daga ranar da Baffa ya yanke shawarar cewa dole Ma'aruf ya ƙara aure, daga ranar kika shigo cikin lissafina Amina, don Ma'aruf ginshiƙi ne guda a cikin burin da nake son cimmawa a yanzu, ina ɗora shi ne akan matakan da zasu kaini ga yin nasara ɗaya bayan ɗaya, don haka idan har aka samu matar da zata raɓe shi wadda ba zan iya juyawa ba Amina abubuwa zasu lalace min ba kaɗan ba, shi yasa tun kafin kowa yayi wani yunƙuri musamman mahaifiyarsa dana san a tarin ƴanmatan dake danginsu zata iya haɗa shi da wata, na duba bayana na zaɓo ki."
Sai da ta sake gyara zamanta tana fuskantar Aminan dake zaune a gabanta ta sunkuyar da kanta sannan tace.
"Ɗago nan ki kalle ni Amina..."
Ta kuwa ɗago da kan nata amma bata kalle ta ba, gashin idanunta sun hade suna shaida jiƙewar hawaye alamun kuka take yi, wani murmushin yaso giftawa a leɓɓen Hajiya Kilishin amma ta tare shi, don da kukan Aminan da kuma shi ɗin, duka bata ga muhallinsu a yanzu ba.
"Sati guda zan baki kiyi tunani, idan har kika yarda dani, zan ƙawata rayuwarki da dukkan ƙawar da baki taba tunani ba Amina, zan miki liƙin alheri har sai hannayenki sun kasa tarewa, zan ɗaga ki ki zama tauraruwa a idon kowa musamman cikin danginki, zan kyautata rayuwarki da ta dukkan makusantanki idan har kika miƙo min hannunki na kama kamar yadda na tsara komai..."
Ta sake yin shiru tana kallon haɗewar gashin idon nata, sai kawai ta haɗiye yawun dake bakinta sannan ta ƙarasa furta abinda ke tahowa tun daga ƙasan zuciyarta, abinda take jin ko da duniya zata taru akanta ba zai canja ra'ayinta ba.
"... Idan kuma har kika zabi yin katoɓarar fallasa ni don ki tsira, na rantse miki da ubangijin da ya halicce mu rayuwarki zata dulmiya ne a baƙin ruwan da zaki yi ta yin ihun da babu wanda zai taɓa jiyo muryarki!"
***
Tun da ya shigo gidan jikinsa ya bashi akwai wani abu da ya faru, don fitilar falo ma a kashe take, iya hasken ta korido ne kawai yake a kunne, a falon ya ajiye wayoyinsa da su kaɗai ne a hannunsa sannan kai tsaye ya nufi hanyar koridon, ɗakinsa yayi niyyar wucewa ya watsa ruwa don Allah ya sani a gajiye yake, amma a lokaci guda idanunsa suka kai kasan ƙofar dakinta da nan ma fitilar a kashe take.
Har ya wuce ya dawo ya tsaya ya kwankwasa, kusan sau uku amma shiru bata amsa ba, sai yayi tunanin sallah take don a lokacin masaltai ke kiran isha'i, don haka sai kawai ya juyo ya dawo ɗakinsa.
Ya kunna fitulun ciki da suka gauraye da haske a ɗakin komai yana fitowa tar cikin kammalen da yake. Ma'aruf yana da tsaftar da duk wanda ya zauna dashi zai gane, don indai abu nasa ne to ba zaka taɓa zuwa kaga komai ba'a muhallinsa ba, sannan kuma yana da haƙurin da zai zauna da wanda bai damu da hakan ba, shi yasa ya iya zama da Ishaq dake wular da komai inda yaga dama.
Minti goma kawai ya ɗauke shi gama shiryawa cikin wasu kayan bayan yayi wanka, ya dawo falon daidai lokacin da wayarsa ke ƙara a inda ya ajiye ta, lambar mutumin da yasa ya nemo masa bayani akan Mr. Okafor ne, ya tsaya kawai yana kallon kiran ba tare da ya dauka ba har ya katse sannan ya tura masa dan guntun saƙo cewar suyi magana zuwa gobe.
A yanzu ya sani cewar tarawa kansa abubuwa yana ɗaya daga cikin abinda ke saka shi damuwa har ciwonsa ya tashi don Allah ya sani a yanzu yana tsoron ciwonsa fiye da kowa, ya sani cewa idan abubuwa suka lalace masa a yanzu bai san me ya cimma a rayuwarsa ba. Shi yasa bai ɗauki kiran mutumin ba, don a yau kaɗai abubuwan da ya fuskanta suna da yawa.
Takardar sammacin da ya samu ɗazu a Office ta girgiza shi ba kaɗan ba, ya kasa hango inda Rukayya da iyayenta suka samu karfin gwiwar kaishi kotu akan zancen Hamida, kalaman Baffa su suka bashi damar ƙin saurararsu amma bai taba tunanin hakan daga garesu ba. Ya kira Ishaq sunyi maganar amma duk tsawon tattaunawar su ya gaya masa cewa chance din da suke dashi kaɗan ne don a matsayin Hamida na mace dole ne a wajen mahaifiyarta ya kamata ta zauna har girmanta kuma ƴan bayanan da suke dashi game da dalilin su na dawowarta wajensa basu da karfi sosai.
Sannan bayan yayi haka ya san yayi aiki a Office din amma ya tabbata idan ya koma gobe zai samu kura-kurai da yawa, don a cikin aikin ya gama yanke dukkan abinda ya riga ya tsara game da zancen kotun da kuma Hamida.
Kuma baya buƙatar yin zancen da kowa shi yasa ko cikin gida bai shiga ba tunda Baffa baya nan yayi tafiya Abuja, yaga kiran Mami amma shima bai bi bayansa ba kuma itama bata sake kiran ba har yanzu.
Ƙafafunsa suka sake komawa kitchen ɗin bayan ya kunna fitila yana nazarin komai, akan table ɗin kitchen ɗin, jerin kayan abincinsa ne kamar yadda take tsara su kullum, yaji wani abu ya zarce cikin makogwaronsa, a cikin ƴan kwanakin nan ya sani cewar yarinyar nan ta taimakawa ƙwaƙwalwar sa wajen samun hutu ta wani ɓangaren, don akwai nutsuwa sosai ace idan aiki ya zuƙe shi da rana akwai inda zai iya zuwa ya huta ba wannan hargitsatsen gidan nasu shi da Ishaq ba. Kamar ya zauna yaci abincin sai kuma kawai yaji ba zai iya hakan ba alhallin bai ganta ba.
Sai kawai ya zaro wayarsa ya kira lambar Samirah, bugu ɗaya biyu kuwa ta dauko, muryarta a ciki ta fara cewa 'To Mami.' kafin tayi sallama.
"Yaya barka da dare."
"Kun yini lafiya?"
"Lafiya ƙalau."
Ta amsa sannan tayi shiru tana jiran abinda zai faɗa a gaba, kuma hakan kaɗai ya bashi amsar da yake nema cewa Aminan bata ciki don haka kai tsaye yace.
"Sai da safe."
Ya kashe wayar ya zura ta a aljihunsa sannan ya koma cikin gidan, ɗakinta da bai shiga ba a yanzu shi ya nufa kuma bai jira komai ba ya buɗe shi, fitilar a kashe take kamar yadda ya gani sai dai babu duhu a ciki don hasken fitilar waje na shigowa ta windon ciki, kuma a lokaci guda idonsa ya hango masa ita, tana zaune daga gefen gadon ɗakin ta ɗora kanta akan gadon yayin da jikinta yake a dunƙule, kamar dai ranar daya fara ganinta, ranar da ya fara ganinta a matsayin matarsa.
Wannan shine karonsa na biyu shigowa ɗakin kuma ya sake tarad da ita a irin wannan yanayin da ya san cewa tabbas akwai abinda ya faru. Hannyensa duka biyun suna cikin aljihu, sai ya fito da ɗaya daga aljihunsa ya sosa kan hancinsa yana kallon idanunta da suke a rufe.
"Assalamu alaikum." Muryarsa ta ratsa ɗakin cikin amonta.
Kamar wancan karon ta dago kanta da sauri ta kalle shi amma bata mike ba, kallonsa take yi cikin hasken ɗakin wucewar sakanni biyu kafin bakinta ya amsa sallamar tana ƙoƙarin dagowa daga kishingiden da take.
Sai kawai ya juya ya koma ya kunna fitilar dakin, haske ya gauraye koina, yana nuna masa kumburarrun idanunta da tabbas kuka tasha dasu.
"Me ya faru? Me ya same ki?"
Tambayar ta fito sak kamar ranar da ya ganta cikin daren nan, amma wannan karon sai yaji abinda yake son tambayar yafi hakan, zai iya jero kusan guda goma don ya samu gamsashshiyar amsa.
"Babu komai."
Ta fada tana ƙoƙarin juya kanta gefe don naɗe sallayar da take kai, yana iya ganin dogon hancinta wanda da alama ta murza shi fiye da kima.
"Kayi hakuri, ban ji lokacin da ka shigo ba, barka da dawowa..."
Muryarta ta faɗa sanda ta gama ninke sallayar ta miƙe tsaye tazo zata wuce shi, amma sai kawai ya riko hannunta na hagu ta baya ya tsayar da ƙafafunta.
Ba shiri Amina ta cije lebbenta tana kallon tiles ɗin dake ƙasan dakin, gayawa zuciyarta take yi cewa ta daurewa wani kukan dake shirin tasowa a ƙirjinta amma sakon baya tafiya sam, don lokacin da ya jawo ta baya ta dawo gabansa ƙwalla ta sake cika idanunta taf.
A yau ɗaya rayuwarta ta canja, ta shiga tashin hankalin da bata san da me zata kwatanta shi ba, a cire mamakin halayen Hajiya Kilishi daya nade zuciyarta a gefe, tsoro da taraddadin hatsarin da ta kawo kanta cikinsa ya hargitsa kowanne abu mai kyau na tunaninta, tana tuna kalamanta, tana tuna ranar da ta yanke hukuncin karɓar auren nan, da wani zai gaya mata da wani abu ko da makamancin haka ne... da tabbas labarin zai canja daga yadda yake yanzu.
Ita bata san ma me take ji ba, bata san yadda zata fassara halin da take ciki ba, kawai dai ta sa zuciyarta ta karye da kowanne abinda kalaman Hajiya Kilishin ke nufi, kuma shi kansa Ma'aruf ɗin ma a yanzu bata yarda dashi ba, don bata san me Hajiya Kilishi ke nufi da 'matakan da take ɗora shi akai don tsarinta ya tafi daidai ba.'
Zuciyarta tayi rauni da yawa ta yadda fuskar Aminu ce kawai ke yawo a kanta da tunanin halin da yake ciki, shi yasa a karo na farko tun bayan ranar da aka kawota gidan, hawaye ya kasa tsayawa a idanunta, don a wannan lokacin tana jin cewa kukan shine kawai sauƙin abinda take ji a kirjinta.
"Ki gaya min abinda ya faru da kuma dalili da yasa kike kuka."
Ma'aruf dake riƙe da hannunta ya fada da muryarsa cike da ikon dake nuna mata cewa da gaske yake yi, sai tayi ƙokarin maida kukanta ta hanyar share idanunta da ɗaya bayan hannunta sannan ta shiga gyara tsayuwarta don ji take kamar zata fadi.
"Me ya same ki Amina?"
Bai gaji ba ya sake tambaya a lokacin da take jin kamar ƙamshin turarenta na kassara kasusuwanta ne, bata da wani zaɓi da ya wuce ta lalubo wani sauti daga can ƙasa maƙoshinta idanunta har yanzu suna ƙasa tace.
"Aminu ne ya gamu da hatsari, yana asibiti tun jiya."
"Ya salam, Ya salam, wane asibiti ne?" Bai san waye Aminun ba, amma ya fahimci ɗanuwanta ne.
Ta girgiza kanta wani kukan na shirin ƙwace mata.
"Ban sani ba, muna waya da Amma sai... Sai wayar ta ɗauke."
Zancen ya fito daga can ƙasan maƙoshinta ba tare da ta tsara shi ba.
Sai kawai yasa ɗaya hannunsa da baya rike da ita ya zaro wayarsa daga aljihu, santsinta ya biyo hannyensa yayin da ya kunna password ɗin da yatsansa sannan ya shiga wajen dial log kafin ya miƙo mata.
"Ki kira ta sai muji wane asibiti ne?"
Sai a yanzu ta ɗago ta kalle shi kuma kafin tayi saurin sake maida idanunta ƙasa, ya gani cewa har yanzu kwalla ce taf a cikinsu, a hankali nata hannun suka karbi wayar don babban abinda take bukata a lokacin kenan, kuma ga mamakinsa bata matsa ba ta shiga danna nambar wayar Amman.
"Assalamu alaikum."
Sautin muryar mahaifiyarta da ya fito ta ciki yasa a yanzu ƙwallar idanunta ta gangaro... Karo na farko a duniya taji so take ta ganta a gabanta wannan lokacin ta rungume ta, so take ta cusa kanta a jikinta ta rera kukan da har yanzu take jin nauyi ta a ƙirjinsa, ta gaya mata cewa tayi nadamar ƙin gasgata maganganunta, don abinda ya shigo cikin rayuwar tasu yanzu wani abu ne da duk ƙarfin hangensu basu gano ko rabinsa ba, wani tashin hankali ne da ya tsallake dukkan tunaninsu.
A yau ta ƙara yarda da zancen Amma na cewar babu wani auren gaske tsakanin mai kuɗi da talaka a wannan zamanin, indai ya faru to tabbas akwai wani boyayyen abu dake ƙasa, Amma tace rayuwarki zaki sadaukar musu Amina, ashe su duka basu sani ba cewar bayan tata rayuwar suma tasu ta shigo ciki wataƙila har da sunan duk wani da ya rabe su ma.
"Amma, Amina ce."
Muryarta ta fito tana kakkarwa kamar yadda hannunta keyi acikin nasa.
"Amina... Amina." yadda muryar Amman ta kira ta a jere da wani irin sautin ajiyar zuciya yasa lebbenta talewa cikin kokarin wani kukan.
"Me ya faru ɗazu wayar ta dauke? Mun gwada yafi sau hamsin kuma bata shiga ba. Har Hajiya Kilishi na kira ita kuma ba'a dauka ba?"
Sai da ta hadiye wani abu a ƙirjinta jin sunan Hajiya Kilishin sannan ta iya cewa.
"Amma wayar mutuwa tayi kawai, kuna ina yanzu? Ya jikin Aminun?"
"Gamu nan mun dawo gida don Baba yace bai yarda yayi zaman asibitin ba, yanzu dai sunyi masa abinda zasu yi masa mun dawo gida, gobe kuma zamu tafi jigawa gidan wannan ɗanuwansu Fatiman mai gyaran karaya, saboda duka ƙafafun nasa biyu sun karye Amina."
Sautin kukan da ya fito daga bakinta shi yasa Amman cewa.
"Ba kuka zaki yi masa ba Amina, addu'a zamu yi Insha Allahu zai samu sauƙi don ance shi mutumin ya iya aikinsa, ba za'a haɗa dana asibiti ba."
Muryar Amman dake lallashinta itama a karye take kawai, ta sani suna da kuma matsayinta na Uwa shine abinda ke rike ta daga nata kukan.
"Ku duka zaku tafi Amma?" Tayi ƙokarin tambaya ta cikin kukan muryarta a rarrabe.
"A'a, dani da Baba da kuma Fatiman da zata kaimu gidan zamu tafi, su Maryam suna nan saboda makaranta, ita kuma Hajiyan Fatiman saboda jinyar Inna (kakar Fatiman) ne ba zata samu zuwa ba."
Sai da tayi wata ajiyar zuciya mai nauyi sannan tace.
"Ina Aminun?"
"Bacci yake Amina, tun jiya sai yanzu bayan magaribar nan sannan ya samu baccin, idan ya tashi na kira ki, wannan nambar waye?"
Bata amsa ba don bata san me zata ce ba, kuma shirunta ya bawa Amma amsarta don haka sai tace.
"Addu'a zaki yi tayi masa Amina, kowanne ɗan adam baya wuce ƙaddararsa, komai zai zo da sauki insha Allah."
Kalaman kaɗai sun isa su kara tsoratar da Amina, don ta san idan har Amma zata faɗi haka to al'amarin ba ƙaramin abu bane, don komai tsananin rashin lafiyar mutum Amma bata zuzuta shi haka, balle ma akan Aminu da yake namiji, don haka bata san lokacin da bakinta ya ƙara talewa da ƙoƙarin yin kukan da har yanzu take dannewa ba.
"Zan saka Maryam ta kira ki da safen kafin mu tafi, su can gidan Kawu Malam zasu koma kafin mu dawo."
Ɗaga kai kawai take kamar Amman na kallonta yayin da sautin kukan ke shaƙewa a ƙirjinta yana fitowa a kakkatse, Allah ya sani rabonta da irin wannan kukan tun Maryam bata da lafiya, lokacin da aka nemi kuɗin maganinta aka rasa, tana kallonta a kullum tana tunanin mutuwa zata yi.
Ma'aruf yasa hannu ya karɓi wayar daga wajenta bayan sunyi sallama, ya maida ita aljihunsa, bata kalle shi ba har yanzu tasa bayan ɗaya hannunta tana ƙoƙarin share hawayenta, da hannun da ya mayar da wayar ya sake riko ɗaya hannun nata ya tsayar da ita daga goge hawayen, sannan a lokaci guda ba tare da ta ankara ya jawo ta jikinsa, karo na farko ya rungume ta, hannunsa ɗaya ya zagayo wajen ƙugunta yayin da kanta ya samu mazauninsa a kusa da wuyanta.
"Kar ki maida shi zai cutar dake... Just let it out."
Muryarsa ta faɗa a cikin kunnenta da wani sauti daya shiga dagargaza dukkan wata jijiya ta dauriya a jikinta.
Kuma a karo na farko Amina ta manta komai akan Ma'aruf ta sunkuyar da kanta a jikinsa don babban abinda take buƙata kenan, kukan da sautinsa kaɗan ne ya suɓuce daga bakinta yayin da jikinta ke girgizawa a cikin hannunsa.
***
Bayan kwana biyu.
"Kin shirya?"
Ma'aruf ya tambaya yana kallon Amina data fito riƙe da wata ƴar ƙaramar jaka a hannunta da kuma wani madaidaicin basket, doguwar riga ce a jikinta ta baƙar abaya, ta yafa baƙin mayafin kawai akanta ba tare da ta saka ɗankwali ba, tana tsaye daga hanyar koridon dakunan tana cakuɗa yatsunta cikin junansu, har yanzu ta kasa yarda da abinda yazo dadaddare ya gaya mata jiya cewa ta shirya zasu je jigawa a yau.
Jiya da safe a wayar tasa suka yi waya da Amma ta shaida mata lokacin tafiyarsu wanda bayan hakan tayi ta binsa da kallo tana so taji yace wani abu amma bai faɗa ɗin ba har ya fita, ya barta a zagayen halin da take ciki, kuma Allah kaɗai ya san yawan abubuwan data saka ta kwance a cikin kanta a jiyan wanda duk iya tunanin nata yana ƙarewa ne a gaɓar da bata san yadda zata yi ba.
Haka ta yini har a jiyan tana share hawaye duk lokacin da ta tuno cewa duk irin halin ciwon da Aminu ke ciki saboda ita ne, saboda itan da bata san yadda zata budi baki ta gayawa wani ba, ko da Ma'aruf ɗin ne kuwa tunda shi kansa babu alamun yana da wata masaniya irin wadda ita ta sani yanzu akan Mamin, duk da cewa bata gama sanin ainihin abinda take nufi game dashi ba ko kuma shi nasa ra'ayin akanta.
Sai da daddare bayan ya dawo ne kawai yace ta sako mayafinta zasu shiga cikin gida, wajen Mami suka fara zuwa kamar yadda suka zata, kuma gaishe ta kawai suka yi kafin ya furta abinda yasa kowannensu mamski daga ita har Hajiya Kilishin.
"Gobe zamu wuce Jigawa Mami, na san kin samu labari, brothern ta ne ya gamu da hatsari zan kaita ta dubo shi."
Har yanzu tana jin nauyin yadda idanun Hajiya kilishi suka dinga kallon fuskarta, tana jin tafiyarsu a ko'ina na fuskar tata, yadda ta dinga kallonta da wani irin yanayi da yake nuna mata cewa itama a lokacin taji zancen, da kuma yadda tata zuciyar ta dinga bugawa har sai da taji kamar ta tsugunna ƙasa ta ɗauko ta lokacin da suka miƙe tsaye, don tsabar tsoro ƙirjinta fayau ta dinga jinsa