Showing 9001 words to 12000 words out of 84785 words
Chapter 4 - Farar Wuta Book 1 Complete Hausa By Aisha Aliyu Garkuwa .txt
take fitarwa a lokacin da kuma yadda hawaye ke zuba daga idanunta yayin da take kallon ƴarsu da bata fi watanni shida a sannan ba... Babyn da ya karɓe daga hannunta ya wancakalar da ita a cikin falon, kanta ya bugu da kujerar gefe ta shiga ƙwallara kukan daya karaɗe gidan gabaɗaya, wannan sautin kukan da a kowanne daren duniya, dashi yake kwana a kunnuwan sa!
***
Me ya faru shekaru goma da suka wuce?
Wane bincike Ma'aruf ke yi da har ya kai ga tashin ciwonsa?
Wacece Rukayya? Me ya faru da ita da kuma ƴar ta?
Sannan wacece amarya ta huɗu a bikin iyalan gidan Alhaji Mansour Bakori?
#Aysha Shafi'ee.
#FikraWriters
#FararWuta.
BABI NA UKU.
****
A wannan daren...
NO. 38 Ramie Street, Nassarawa GRA, Kano.
.
A cikin ƙawataccen ɗakin, wata yarinya ta buɗe ƙofar ta shigo, ba zata fi shekaru uku da kaɗan ba, tana sanye da irin kayan yara kamarta, wani ɗan gajeran skirt kalar lemon greeen, (lemon tsami) sai farar rigar da itama akayi mata da ado da irin kalar, gashinta da ba wani yawa ne dashi haka zalika tsawo ba an tufke shi cikin kalba guda biyu da ribbon masu kalar kayan.
Ta karaso cikin ɗakin daya gauraye da sanyin A.cn da aka kai maƙurarta, akwai wani tebur irin na ado dake gaban hadadden gadon dakin, ta kansa ta taka ta isa kan gadon, ta hau tana bi ta kan ƙafafun wadda ke kwance har ta isa daidai fuskarta da ta rufe da bargon data lulliba gaba ɗaya.
"Mammy Mammy Mammy...."
Ta kira ta na bubbuga daidai kanta da ƴan hannayen nata, a lokaci guda mahaifiyar tata ta yaye bargon daga fuskarta ta buɗe idanunta da kyar tana kallonta.
"Menene Hameeda? Me ya kawo ki?"
Ta tambaya ranta a ɓace.
"Mammy I'm hungry. (Yunwa nake ji.)"
Taja tsaki a hankali.
"Ina Nannynki?"
Sai kawai ta miko mata takardar hannunta, kamar ba zata karba ba sai kuma ta yatsunta biyu ta sakala ta cikinsu sannan ta buɗe ta.
'Ajiya I'm sorry Oo, dey don call me now say my mother dey hospital. I'll return tomorrow by God grace.'
Ta sake jan wani tsakin mai tsayi, bata san sau nawa take gayawa Mary cewar ta daina yi mata pidgin a gida ba, amma don rashin mutunci shine har rubuto mata take yi a takarda.
Ta juya ta sake kallon yarinyar data tsura mata idanu, dogwayen gashin idanunta sun kusa haɗewa da juna, yadda take lumshe su ya tuna mata da fuskarsa a lokaci guda.
...idanunka kake gani ko Ma'aruf? Irin naka ne sak!
Muryar Mami ta haska a cikin kanta ranar farko na zuwan Hameedan duniya, ta tuno fuskarsa, yadda ya kalmashe ta cikin hannunsa, lumsassun idanunsa na haskawa da tarin ƙaunar da kamar wani abu ba zai taɓa giftawa a cikinta ba.
Ruƙayya ta sake yin wani tsakin da ya riga ya shiga cikin dabi'arta kafin ta ture bargon gadon ta miƙe, wata lallausar doguwar rigar bacci ce a jikinta da idan ka kalle ta zaka ga kamar tana zamewa ne tsabar santsi da kuma kyallin da take yi.
Ta kalli agogo wajen karfe bakwai na dare.
"Baki ci abinci bane da rana?"
Ta tambaya tana daure gashin kanta da za'a kwana a yini ana musu da wani akan cewar nata ne, don human hair ne (gashin mutum) da aka dinka mata shi cikin nata ya saje tsaf!
"Mami tun da na sha tea, Mary bata bani komai ba. Waya take ta yi."
Gwarancin yarinyar mai daɗi ya fito tana kallonta. Wani tsakin ta sake ja kafin ta dauki wayarta sannan tace.
"Oya, taho muje to."
Da sauri yarinyar kuwa ta sauko tabi bayanta, suka fita daga ɗakin zuwa wani dogon korido daya hada fuskokin ɗakuna, suka isa wani rantsatstsen falon da komai na cikinsa kalar ruwan gwal ne da kuma makuba, a gefensa akwai matattakalar bene, suka sauka har kasa zuwani falon da yafi wannan girma, ta jikin dining area suka shiga wata kofar da take ta kitchen ce, wani katon kitchen da yake a gyare tas.
Babu ko tukunya guda daya akan gas don haka ta san babu wanda ya dawo a cikin kannen nata uku maza, suma can yawonsu waye ma zai gansu yanzu da magaribar nan? Dama Ashraf mai bi mata ne idan ya dawo daga aiki sau da yawa zai shigo ya dafa abincinsa tun bayan da suka rasa Josh (mai yi musu girki) yanzu kuma yayi aure sati uku da suka wuce don haka babu mai shigowa kitchen din.
Hameeda ta ɗane kan ɗaya daga cikin kujerun da suka zagaye worktable din kitchen din sannan ta zuba mata idanun tana jiran taga me zata yi, Allah ya sani ita bata son wani girki yanzu, da safen nan fa dawowarta kenan Nigeria daga ƙasar Paris inda suka tafi ita da mahaifiyarta, shi yasa ta kwanta take ta sharɓar baccin ta kuma yanzu ta tashi ta kama girki?... sai kawai ta dago da wayarta ta shiga nemo nambar Mariya, babbar ma'aikaciyar gidan.
"Hajiya barkanmu da safiya. Ina kwana." Muryar dattijuwar ta cika kunnenta, bata ko amsa ba tace.
"Mariya, abinci zaki kawowa Hameeda yanzu, a dafa mata duk abinda zata iya ci kawai."
Daga cikin wayar Mariyan tace.
"Hajiya ai bana gidan, yau kwana na uku a madobi, mahaifina ne ya rasu wallahi, amma su Jamila da Aisha suna nan."
Ta ɓata rai a lokaci guda don ta manta lokacin da suna can taji mahaifiyarta ta na fada, sai kawai tace.
"Allah ya jiƙansa." sannan ta kashe wayar.
Ba zata yarda ƴarta taci abincin waɗannan kazaman yaran ba su tsaya a iya gyaran gidan da suke yi kawai, don ko Mama Mariyan ma da suka saba da ita tun yarintarsu ba kowanne girkinta suke ci ba, tunda Josh ya mutu shikenan kowa ya ta'allaƙa akan siyan abinci a waje tunda dama gidan ƴan maza ne ita kadai ce mace.
"Hameeda me zaki ci?"
"Mammy banda indomie." Ta fadi hakan alamun da gaske ta gaji da cin indomien, haka yasa ta gane cewar Indomie kawai Maryn ke ɗura mata da basa nan don haka ta gyaɗa kai kawai.
Ta ajiye wayar akan table din sannan ta juya ta shiga store, ta fito da kwai guda uku a hannunta, ta kunna ruwa a kettle sannan ta fasa kwan ta soya shi cikin ƴan mintuna, ta haɗa mata tea da ruwan zafin da yayi sannan ta ɗauko biredi a fridge ta saka mata kwan a tsakiyar, ta zauna a kusa da ita tana kallon murnar dake kan fuskarta sanda ta fara cin ƙwan, har yanzu bata kai shekara hudu ba amma tsaf ta iya cin abinci da kanta, sai kawai tayi murmushi sannan ta janyo wayarta.
Ta shiga whatapp tana fara ganin yadda messages ke tururuwa har da sababbin nambobi, sai da suka gama tsaf sannan ta danna kan sako guda ɗaya mai sunan Jawad da mintuna biyu kawai akayi da turo shi.
"Baby kin dawo ko? I'm badly missing u here... Zanzo anjima kinji." (Ina mutukar kewar ki anan.)
"Mammy nayi missing dinki."
Muryar Hameeda ta katse ta daga amsar da take shirin rubutawa. Ta juyo ta kalle ta, tana ta cin biredin da sauri alamar da gaske yunwa take ji. Itama tayi kewarta da gaske shi yasa ma ta kasa jiran Maamah ta taho. Bayan bikin Ashraf ne suka tafi Paris ɗin ita da mahaifiyarta don medical check-up kasancewar hidimar bikin ta wajiga su da yawa, kuma satinsu ɗaya acan ta gaji ta taho don ranar da suka tafi ma Hameedan na bacci a hannun Mary ko sallama basu yi ba.
Allah ya sani ta fara gajiya da wannan rayuwar, ba haka take hango ta ba sam, ba haka ta dinga hango abubuwa ba lokacin da mahaifiyarta dama kawayenta suka bata goyon bayan kashe aurenta ba, Maamah cewa tayi...
"Idan baki fito daga gidan nan ba kin kusa kashe kanki ki tsufa a banza Ruƙayya, ta yaya zaki zauna babu wani isasshen hutu sannan kuma ki fara tara ƴaƴa bi da bi? Yanzu kika fara rayuwar ki fa, kina da dama mai yawa a gabanki Rukayya."
Haka take gaya mata kullum, shi yasa ta rufe idanunta a wancan lokacin ta danne zuciyarta tayi abinda ya fito da ita ɗin, kuma har bayan aurenta da Alhaji Ahmad, tafiya take akan wadannan kalaman na mahaifiyar tata, takunsu take bi har ya kai ga mutuwar aurenta da Alhaji Ahmad ɗin shima, kuma ko a yanzu ma bata fasa gaya mata cewar komai kaddara ce ta cigaba da cin ganiyarta ba, amma ita ta sani cewar bayan wannan ƙaddarar har da ƙaddarar zuciyarta akansa shi ma.
Ta san duk irin halayen da zuciyarta ta shiga a gidan Alhaji Ahmad, ta san duk irin wahalhalun data fuskanta a kowanne lokaci na zamanta a gidan yadda ta dinga kwatanta abubuwa a gidanta na farko da kuma nasa tana ganin bambanci su a baiyane har suka kai ga matakin ƙarshe na mutuwar auren, don Maamah bata taɓa sani bane, amma MA'ARUF shine sanadiyar mutuwar aurenta da Alhaji Ahmad.
Kuma ko a yanzu da kowa ke kwaɗaita mata auren Jawad, ita ta sani cewar abinda ya faru shi zai sake faruwa, babu wanda zai taɓa iya cike gurbin Ma'aruf a ranta, ta so shi tun bata ma san kanta a duniya ba balle ta san menene son, ta so shi da dukkan kowanne bangare na ruhinta, don rayuwarta ma gabadaya tare dashi ta gina ta.
Iyayensu maza abokan juna ne tun da dadewa, saboda haka ba zata taba iya cewa ga ranar data san Ma'aruf ba, tayi wayo ne kawai a duniya tana iya lissafo shi a cikin abubuwan da ta sani na rayuwa, don haka kowa ya sani cewar tsananin kulawar da take yi masa shi ya janyo hankalinsa akanta shima har ya kai ga soyayyar su.
Sai dai a lokacin da ta aure shi, ta auri wani Ma'aruf din ne daban saɓanin wanda ta sani, ta san hakan don yasha gaya mata cewa Ma'aruf din data sani ya mutu babu ko da digonsa a cikin zuciyarsa, amma ta rufe idonta daga komai tace taji ta gani har aurensu ya tabbata.
Auren da tun a darenta na farko a gidan abubuwa suka yi juyin waina daga yadda take hasko su. Ta rufe idanunta a hankali tana tuna dukkan abubuwan da suka faru a waɗannan shekarun, irin wahala da barazanar da rayuwarta ta fuskanta, sai dai ashe bata san gwara su sau dubu akan abinda zata je ta tarar a gaba ba, don a yanzu ta gane abinda taso ta manta a baya, cewar duk duniya Ma'aruf ne kadai namijin daya tattara duk wasu halayen da take so a wajen namiji. Shi yasa bata son sake maimaita kuskure na uku a yanzu, bayan guda biyun da tayi a baya na fitowa daga gidansa har kuma da auren Alhaji Ahmad.
Ta riga yankewa kanta shawarar cewa ba zata sake biyewa kowa ba, ra'ayin zuciyarta kawai zata bi, zata samo yadda zata koma cikin rayuwar Ma'aruf kotawacce hanya kuwa, kuma bata ma tunanin cewa hakan zaiyi mata wuya tunda tana da abinda daga shi har iyayensa zai kassara su. Hameeda...
Tayi murmushi tana sake kallon yarinyar, lokaci yayi da a yanzu zata san waye mahaifinta!
***
A wannan daren....
Na baki amanar rai na, daiman
Yau zaki ceton raina, abadan
Kin ƙulle mini kwaɗon raina, da'iman
Ki taho, raina yana sururi numfashina kece abadan dai'man!
"Maryam dan Allah ki kashe waƙar nan, dan Allah."
Amina ta faɗa tana hararar rediyon da Maryam din ta kunna, ta jingina ta da langa-langar langar kitchen ɗinsu yayin da ita take ciki tana girki.
"Haba mana Yaya, kin san yadda nake son irin waƙoƙin nan fa, kuma yanzu zasu cire ma don wani shirin zasu fara."
Maryam ɗin ta faɗa daga cikin kitchen ɗin, kuma jin tayi shiru yasa ta kara da...
"Idan ana yi wallahi ji nake kamar in tashi sama don dadi, da wayarki android ce ai da har sai kin gaji da jin su ma."
Amina ta girgiza kanta daga kan tabarmar da take zaune Hafsa a kwance akan cinyar ta tana tsefe mata kalbar da ta baɗe ta tsaf da wani sabon yashi da aka zube a layin nasu inda yara kamarta ke tururuwar wasa.
"Ni basu dame ni ba sam, kawai a yanzu ne ban ga amfanin jin waƙar ba tunda kin san abinda yake faruwa."
Jin haka yasa Maryam ɗin tayi shiru tana cigaba da yanka cabbage ɗin dake hannunta, kuma a daidai lokacin ma suka cire waƙar, muryar wani ma'aikaci daga gidan rediyon ta fara gabatar da shiri na gaba a jerin shirye-shiryen su, amma tuno abinda ke faruwar kamar yadda Amina tace, yasa Maryam ta ajiye wuƙar hannunta ta taso ta kashe rediyon gabaɗaya.
A jiya da Baba ya fita zuwa kiran Hajiya Kilishin da yace, bai dawo ba sai wajen sha ɗaya saura na dare har su Hafsa da Adam sunyi bacci a sannan, wanda hakan wani abu ne sabo a wajensu, wani abu daban, saboda ba don sun kira shi a waya har ya ɗauka ba ma, Amina ta san tsaf Amma zata iya saka hijabinta a daren ita da Aminu su fara tafiya nemansa.
Shi ba mutum ne mai dadewa a waje ba musamman idan dare yayi, abubuwa da yawa komai muhimmancin su in har dare ya raba to zai ajiye su ne sai zuwa gobe, ko hirar maza irin ta daren nan Baba baya taɓa zaman yinta, tun suna yara sun taso da sanin cewa lokacinsa da daddare nasu ne, a cikin iyalansa zai zauna ayi wasa da dariyar da a cikinta zai fahimci dukkan matsalolinsu.
Don haka a jiyan da ya kai goma sha ɗayan dare dole zuciyoyinsu suka kasa nutsuwa sai lokacin da suka ji ƙarar shigowarsa da kuma rufe kofar gidan da yayi, babu wuta a lokacin, sannan Aminu ya fara tararwa jingine da bango yana danna wayarsa.
Kuma ta cikin ɗan hasken fitilar tsakar gidan da batiranta suka gama yin sanyi, Amina ta hangi fuskarsa tattare da dukkan wani nau'i na damuwar dake fitowa har a cikin sautin muryarsa sanda yake amsa gaisuwarsu, gaisuwar da daga ita bai sake cewa komai ba, ya nufi hanyar ɗakin sa kawai ya shige.
Amma ta ɗebi kwanukan abincinsa ta bishi dasu yayin da suma kowa ya kama hanyar makwancinsa, Aminu yayi hanyar soro inda ƙofar ɗakinsu shi da Adam take, su kuma suka dauki Hafsa suka shige nasu dakin, kuma ba sai ta tambaya ba, Amina ta sani daga ita har Maryam da Aminun babu wanda yayi baccin kirki a ranar. Kuma babban abinda ya ƙara tsurar dasu shine na yadda har a yau basu ji komai ba, ko daga bakin Amman kuwa.
Baban bai ko je aiki ba a yau, tun safe ya fita zuwa gidan wansa da suke kira da Kawu mallam kuma bai dawo ba har yanzu, Amman ma kusan a daki ta yini tun bayan fitarsa, ita kadai tayi ta kai kawo a gidan bayan sun tafi makaranta, tace mata wai gyaran durowarta take yi, amma tsaf Amina ta sani cewa kayan nata data barbaza akan katifar ɗakinta ba don ninki ta fito da su ba saboda yanayin dake fuskarta kusan iri daya ne da wanda ke kan fuskar Baba tun a jiya da daddare, kuma wajen la'asar sai ga kiran Baba a wayar Aminan cewa Amman taje ta same shi a gidan Kawu mallam ɗin, wanda hakan shine abinda ya ƙara ɗaga hankalinta, da ƙyar Aminu ya shawo kanta bayan sun dawo daga makaranta kafin ya tafi wajen aikinsa shima.
Sai dai kafin ta bawa Maryam amsa, Adam yayi sallama yana shigowa.
"Salamu alaikum, wallahi Yaya yarinyar nan ƙarya take, babu wanda ya ture ta, wasan banzan su kawai suke yi, ga sauran ƙawayen nata can ma har yanzu a kusa da yashin."
Ya zayyano dukkan wannan bayanin daga tsaye kasancewar shi yaje ya zaƙulo ta tsakiyar masu wasan yashin. Da jin haka kuwa Hafsa tayi narai-narai da muryarta ta shiga rantsuwa tana faɗin da gaske ture ta akayi ta faɗa kan yashin, wanda kowa ya san ƙarya ne wasanta tayi daga yadda baƙin gashin kan nata ya burɗine tsaf da ƙasa.
"Ko baki ɓata kanki ba meye amfanin zuwa wajen yashi da magriba Hafsa?"
Amina ta faɗa a hankali tana kama wata jelar, don ita ko kaɗan ba ta fadan nasu take yi ba, jikinta ne kawai zaune a gidan amma hankalinta ruhinta zarya kawai suke a hanyar gidan Kawu mallam kamar tururuwa, shi yasa ko girkin daren ma tace Maryam tayi.
Allah ya sani abu na ƙarshe da zata so a yanzu shine wata matsala ta sake gifta musu, rayuwarsu ta haska da kaloli mabanbanta a shekarun baya, sun fuskanci abubuwan da ko a labari basa son tunawa, kuma har yanzu ƙoƙarin tashi suke, ƙoƙari Baba yake don ganin rayuwarsu ta daidaita ko da ba kamar a baya ba, don haka ta yaya zasu taɓa son ace sai sun sako daga farko idan wani abu ya sake gifta musu ya a yanzu...
Har sai da ta gama wankewa Hafsa gashin nata da karkashi sannan Amma ta dawo, Baba kuma bai shigo ba sai bayan sallar isha, wanda kafin ayi hakan har Aminu ya riga su dawowa, a tsakar gidan ya tarar dasu tana sake yiwa Hafsa wata kalbar bayan ta wanke matta kan, yayi wanka yazo ya zauna a cikinsu shima yana ta mita da tsokana akan girkin da Maryam ɗin tayi, jollof din shinkafa da taliya ce da ko a ido tayi kyau, amma tunda ya zauna yake sukar abincin yana kuma kai loma.
"Wallahi akayi miki aure kika je kina irin wannan abincin sati daya zaki yi ya koro ki, ace jollof amma ba mai sa faman kora ruwa nake kamar dambu nake ci."
An kawo wuta a lokacin don haka tsakar gidan yayi tar da wasu sababbin ƙwan fitilar da ya haɗa da kansa ya saka musu. Maryam da a lokacin take wanke uniform dinta daga can bakin famfo tace.
"A haka babu man kake ƙoƙarin tayar da plate din ai."
"To idan ina jin yunwa ya zanyi? rufa miki asiri kawai nake ma wallahi, don yanzu ina tafiya wajen Isah (mai shayin layinsu) kowa sai ya gane cewar a gidanmu ba'a iya girki ba kenan, kinga masu kokarin zuwa nan gaba ma sai su fasa. Kuma Amina ita ta riga ta samu kece a ruwa."
Maryam ta juya bayanta amma yana ganin adadin yadda gefen fuskarta ke juyawa wajen murguɗa baki tana faɗar wasu abubuwa da ba jin su yake ba. Yayi murmushi yana sake faɗin.
"Hotonki zan nemo a