Showing 39001 words to 42000 words out of 84785 words
Chapter 14 - Farar Wuta Book 1 Complete Hausa By Aisha Aliyu Garkuwa .txt
da kowa ke gani tare da fararen idanunta, fatar fuskarta har maiƙo take saboda yadda take tas babu ko ɗigon ƙananun ƙurajen da ta saba fama dasu.
"Fatee, ina gurasar? Jiranki fa muke yi!"
Wata Shukra ɗaya daga cikin kawayenta a islamiyya ta kwallawa Fatiman dake can cikin hayaniyar tsakar gida kira, a cikin ɗakin nasu ƴanmata me fal da suka haɗa da kusan duka ƙawayen su na islamiyya da kuma na makarantar boko wanda duk a ƙoƙarin Fatima ne ta tattaro su, sannan ga su Ummi ma da tasu tawagar ƙawayen, don haka ɗakin ya cika taf sai faman hayaniya suke wadda ke sajewa cikin tarin ta gidan gaba ɗaya.
Don ko'ina a cike yake taf da mutane sai faman rabon abinci kawai ake, babu wanda yayi tunanin za'ayi wannan taron, Amma bata taba lissafa cewa yawan waɗannan mutanen zasu taru ba, amma ance wai biki dama ba'a masa gayya da kansa yake fallasa kansa, musamman ga su ɗin da kusan duk wanda suka mu'amalanta yana jin daɗin zama dasu.
A lokacin Maryam ta shigo ɗakin riƙe da wani faranti da aka cika da ƙullin zobo. Ummi da tasha kwalliya cikin ankon atamfar nan tace.
"Yawwa Mary, matso ta nan, tun dazu dama Aunty Safiyya ke cewa mu jira a kawo."
"Taɓ! Wallahi na wannan ƙawaye na ne suna can a dakin Aminu, plate nazo nema idan kun gama zan zuba gurasa."
"Au ba zaki bamu ba?"
"Waashi can fa ana ta ɗiba a ɗakin Amma, kuje ku ɗebo naku kafin ya ƙare don wallahi har yaje rabi."
Ummi ta miƙe da sauri tace.
"Mu nawa ne a dakin?"
"Ai kawai je ki ɗebo ashirin, in ma da saura ma kara." Cewar wata a cikin ƙawayen Aminan suna ƙyalƙyalewa da dariya gabaɗayansu.
Ummi ta fita daidai lokacin da Fatima ta shigo rike da plate guda biyu na banɗashen gurasar, Maryam kuma ta juya ganin ba zata samu abinda tazo nema ba.
"Wallahi kowa ya ɗauke hannunsa kafin in ajiye." Cewar Fatiman ganin yadda kowannensu yayi shiri da hannunsa.
"Dalla malama ki ajiye kawai meye haka wai?" Cewar Shukra.
"Wallahi sai kowa ya ɗauke hannunsa, salon ina ajiyewa in rasa."
Ta faɗa tana dariya, yayin da hayaniyarsu ta ƙaru kowa na fadin ta ajiye, ai kuwa tana dire farantin kafin ta mika nata hannun ta nemi gurasar ta rasa, sun wawushe ta tsaf suna ƙyalƙyala dariya, kuma yanayin fuskar Fatiman yasa Amina dake daga gefensu yin dariyar itama, lebbenta yayi talewar da har haƙoranta suka fito, don abu ne da ba yau suka saba ba, tun a makaranta sun saba irin wannan abin da an kawo abinci kawai wanda ya samu ya samu.
Kuma dariyar taji tana tafiya har ciki ƙirjinta, tana taɓo wani abu da ya kamata dama ace yana nan, wannan farin cikin da mace ke ji a lokacin aurenta.
A cikin hayaniyar da ɗakin ya ƙara ruɗewa dashi Aunty Ma'u tazo ta kira ta, tana fita taga Aminu ne yazo da mai hoto, aka shiga ɗaukar hoton kowa da ƙungiyarsa, Aminu na tsaye shine mai bada umarnin dake sa kowa yin dariya, don haka kusan duk a hotunan an ɗauka ne Amina na dariya, tayi kyau a cikin kayan da suka zauna a jikinta sosai ga kuma skirt ɗin kayan daya buɗe ta ƙasa, ita kanta ta yarda cewa telan nasu Ummi ya iya ɗinki ba'a banza suke ta yabonsa ba, kuma a kowanne hoto ita idonka zai fara gani saboda shigar kayan nata farare tas da kuma baƙin gashinta daya fito ya haɗu da baƙin ƙunshin hannaye ta yana ƙara haska farin.
Hatta Amma tayi kyau cikin shigar wani lace da ya dace da maman Amarya, itama tana ta dariyar da har ta mantar da ita haushin da zuciyarta ke ciki game da kayan jere da suka kai aka ƙi karba.
Ranar da su Tanti suka tafi za'a fara jeren nan, ranar zuciyarta ta sake yin baƙi game da al'amarin auren, don a waya Hajiya Kilishi ta kira tana gaya mata cewar ai su basu ce su kawo kaya ba, wai mahaifin yaron daya bada kudi ayi gyaran gida ya bayar har dana komai don haka su sun riga sun gama jeran su amarya kawai suke jira.
Sai da ƙyar bayan Tanti ta dage cewar baza su kawo ƴarsu haka ba sai da abinda zata kalla itama ta san cewar iyayenta ne suka yi mata kamar kowacce ƴa, sannan Hajiya Kilishin tasa aka fitar da kayan gado guda daga wani ɗaki suka jera nasu, kayan Kitchen kuwa suka zube mata gabaɗaya don shi dama abubuwan da aka ajiye basu da yawa, sai a sannan ne zuciyar Amman ta ɗanyi sanyi, amma har a wayewar garin yau bata dawo dai-dai ba sai a yanzu da Aminu ya saka ta yin dariyar dole.
Kuma duk yadda bikin ya kai ga zuwa a gaɓar da kowa ke ganin ba'a shirya ba, yayi mutuƙar yin daɗin da wataƙila ko da sun shekara ne suna tanadi haka komai zai kasance, banbancin kawai na farin cikin da za'a samu a zuciyoyinsu ne.
Wajen yamma, Adam ya kawowa Amina saƙon wata sallaya mai kyau da kuma alƙur'ani daga Abdallah, a hannayenta Amina ta rungume ledar ba tare da tace komai ba, idanunsa kawai take hangowa a ranar da ta gaya masa aure zata yi, yana kallonta da yanayin da bata iya fassara shi ba.
"Dama na gaya miki, ba wani son ki yake yi har cikin zuciyarsa ba."
Haka Fatima tace lokacin da ta gaya mata yadda suka yi, amma sai ta girgiza kanta ta bata amsa.
"Cewa yayi dama ya sani ba lallai ya iya aurena bane Fati, yace ya san ba lallai ni ko iyayena mu iya jurewa tazarar dake tsakani na dashi ba."
Da yamma Fatima dasu Ummi suka sa ta canja zuwa wani material kalar ruwan madara, a lokacin kuma kusan duka ƙawayen nasu na nesa sun tafi sai mutum uku kawai da kuma wasu daga cikin ƙawayen su Ummi, kalar kayan ta ƙara fito da hasken fararen idanunta, suka saje sosai cikin wani ɗauri mai kyau da Momi ta sake yi mata.
"Kece amarya ta farko a wannan lokacin da naga anyi bikinta bata yi make-up ba Amina, Allah ya shirya miki halinki."
Cewar Momin sanda take ɗaura mata ɗankwalin, sai kawai tayi wani murmushi tana kallon ƙunshin hannunta yayin da wata ƙawarsu ta ke cewa.
"Amma kuma tayi kyan da wasu amaren ma da yawa basu yi ba, kin san natural look ƙarshe ne."
Da haka sai hirar ɗakin ta koma kan kwalliya, kowa na faɗin ko a kwalliya simple make-up tafi kyau, wasu kuma na lissafo masu kwalliyar da ko heavy make-up ɗin suka yi tana yin kyau. Ta sani itama da aurenta bai zo a karkace ba zata yi kwalliyar, amma babu kalar tanadin data shiryawa wannan, ƙunshin ma don su Momi sun takura ne kuma ta san shine abinda kowa zai fara lura dashi akanta.
"Dama da kika haɗa kayanki baki ɗebi waɗancan litattafan ba?"
Fatima ta tambaya daga gefenta sanda idonta ya kai kan wani kwali a can saman durowarsu na litattafan makarantar ta, litattafan da ta san ba zata taba rabo dasu ba, don kullum cikin bitarsu take yi.
"Maryam ce ma ta haɗa kayan ai, ni ban san me da me ta haɗaba, kawai dai tace min ta hada su ne tare da sauran kayan akwatunan."
"Allah yasa dai bata haɗa miki da kayan sawa da yawa ba, don yawa zasu yi miki idan aka hada da sababbin, gwara ita a ta ɗan ƙara akan nata. Ina ledar su sallayar da aka kawo, bari na haɗa na kaisu kusa da akwatunan, kar a manta."
Fatiman ta faɗa tana ƙokarin miƙewa, sai dai kafin ta kai ga miƙewar Amina ta jawo hannunta da sauri, ta juyo ta kalle ta, idanunta sun kaɗa daga farinsu ta girgiza mata kai.
"Ki zauna kawai Fatee, ki bari ko anjima sai ki ɗauko su."
Muryarta da kaɗan tafi kuka, kukan dake kwance a ƙirjinta tun bayan ɗaurin auren da su Kawu Mallam suka kirata soro bayan dawowarsu, Kawu mallam ɗin ya danƙa mata sadakinta dubu ɗari a hannunta, da kuma bayan tafiyarsu da ƴanuwansu na Niger suka ƙaraso suna faɗin angon bai je ba... Kalaman da suka sata tambayar me yasa take yaudarar kanta ne? da kansa yazo har nan ya gargaɗe ta tun kafin komai yayi nisa don haka don ya fara nuna mata bala'in da ta kawo kanta cikinsa hakan ba komai bane.
Har bayan sallar magariba gidan nasu a cike yake, koina yayi kaca-kaca da ruwa da kuma abincin da aka zuzzubar, sannan ga tarin wanke-wanke fal a gefe, don haka ana idar da sallar magaribar ƴanuwansu na Niger suka fara aiki kotaina, Allah ya taimaka da wutar Nepa don haka akwai haske koina.
A lokacin ne kuma motocin ɗaukar amarya suka hallara!
***
A cikin motar dake tafiya kan titin Lamido cresent, ɗan karamin mayafin da Ruƙayya ta yafa akan doguwar rigarta ya zame ya sauka kan kafaɗunta, gashin kanta baƙi sidik da ya haɗu dana ƙarin data nannaɗe cikin bun ya fito ta cikin hasken street lights da kuma na fitilar motar ƴan sandan dake jiniya a bayansu, amma bata damu ba, hannayenta na rawa ne yayin da take kokarin sake kiran layin mahaifiyarta daya katse saboda rashin service yanzu da suke magana.
Ta samu kiran ya shiga a lokacin da muryar Ashraf dake tuƙa motar da kuma ta abokinsa Bilal da suke kira da B-man ta shiga kunnenta. Ashraf ɗin ne ke tambayar abokin nasa idan har lambar wayar da suke jira an turo masa, amma a gajarce kawai ya bashi amsa yana girgiza kai.
"Ina jin ki Ruƙayya kuna ina?" Muryar mahaifiyar tata ta shiga kunnenta daga cikin wayar.
Sai a lokacin ta jawo mayafin ta sake rufe kanta sannan tace.
"Maamah muna hanya, mun ɗauko Bilal ɗin yanzu zamu tafi can sabon garin, su Ibrahim ma sun je sun taho da police ɗin suna bin mu a baya, muna jira ne yanzu a turo masa da number wanda ya sani a gidan don a tabbatar idan tana nan."
Daga cikin wayar Hajiya Nafisa tace.
"Ko bata nan ku ƙarasa ku sami iyayenta ko kuma duk wani wanda zai iya baku bayani akanta, duk abinda ake ciki da kun isa you let me know, yanzu zan kira Daddy in gaya masa."
Ta gyaɗa kanta kafin kiran ya katse, idanunta na tafiya kan abokin Ashraf ɗin dake danna wayarsa hankali a kwance, tsawon kwanaki kenan suna nemansa amma ba'a same shi ko a waya ba sai a yau da da wanin abokin Ashraf ɗin ya kira cewar gashi nan ya dawo daga Ondo, don haka ba shiri suka taho har wajen da aka kwatanta musu yana nan, kuma cikin sa'a suka same shi. Amma don rashin mutunci irin nasa bai fito ya same su ba sai da suka yi kusan awa guda suna jiransa, har su Ibrahim da Ahmad da suka je suka taho da police ɗin da aka kai report wajensu, sannan ne ya fito da uzurin cewar wasu abubuwan yake kammalawa da baza su iya jira ba.
Kuma duk da irin tashin hankalin da yaji suna ciki da kuma ma babban labari na ɓatan ɗan mutum guda, bai nuna ko a jikinsa ba bayan Allah ya sawwake guda din da ya furta. Ta sani cewa shi kansa Ashraf ɗin yaji haushi amma bai nuna bane saboda abu suke nema daga wajensa dole sune a ƙasa, amma duk da haka ta fahimci cewa akwai wani abu ne da ya faru da babu wannan kalmar ta abota a yanzu tsakaninsu.
Sai dai ba wannan ne a gabanta ba yanzu, a cikin kwanakin da suka gabata, zuciyarta ta mutu ta miƙe fiye da ƙirgan mai ƙirga, ƙarya ne ta iya kwatanta tashin hankalin da take ciki, tashi hankalin da sai da ya shafi kowa a gidan nasu gabaɗaya, ya zamana ba abinda ake yi banda fafutukar neman Mary ko ta wacce hanya amma basu same tan ba, hatta mahaifinta dake can ƙasar Romania yana aikinsa kullum sai yayi waya tsakaninsa dasu da kuma ƴansanda akan abinda ake ciki.
Idanunta kaɗai idan ka kalla sune shaidar rashin baccin da kuma na abincin da take ciki. Ta rantse a ranta fiye da sau shurin masaki cewar Mary zata gwammace bata zo duniya ba idan har suka kama ta, tunaninta baya iya lissafa abinda ya kamata tasa ayi mata.
Sun isa cikin unguwar ta sabon gari a lokacin da duhu ya riga yayi sosai, a lokacin kuma gabanta ya shiga faɗuwa cike da tsananin tsoro ganin irin cakuɗaɗɗun layikan da suke wucewa da kuma mutanen cikinsu, zata yi rantsuwa ba adadi cewa Mary ba zata taɓa rabarsu ba inda ta san daga waje irin wannan take fitowa, amma a haka ta zauna tana kula da ƴarta tsawon watanni bakwai.
Kwatancen Bilal ya kai su har wai takurarren gidan da mutane ke ta fitowa daga ciki kamar gidan tururuwa, bata san lokacin da ta dunƙule ƙarshen mayafinta akan bakinta ba yayin da kwalla ta shiga fitowa daga idanunta da suka riga suka kaɗa, zuciyarta bata iya kwatanta mata cewa Hamida tana wannan wurin ko kaɗan.
Ibrahim da Ahmad da suka fito daga motarsu bayan sun tsaya suka bada shawarar cewa ta tsaya su suka shiga ciki, amma jikinta na rawa ta girgiza musu kai, ruhinta zai bisu ciki ne ko da ta tsaya ɗin.
Ashraf da Ahmad ne suka fara shigewa gaba sai Bilal da kuma Ahmad, ita tana daga bayansu sai kuma ƴansanda biyar dake rufa musu baya, warin iskar gidan ta fara shaƙa kafin ta fahimci girman da yake dashi daga ciki, ga tarin ƙofofi birjik daga kowanne gefe inda hayaniya ke fitowa kamar zata fasa kunne.
Kuma ganin ƴan sandan yasa hayaniyar gidan ta ƙaru har da masu ihu suna shigewa ɗakunansu, a tsakar gidan su Ashraf da kuma ƴansandan suka shiga tambayar cewa Mary suke nema, kuma wasu ƙattin inyamurai da su kaɗai suka tsaya suka shaida musu cewar Maryn dake gidan sun fi mutum ashirin.
Koina a jikin Rukayya kawai rawa yake yayin da take kallon ƙofofin ɗakunan da dukkan fatanta na duniya, da ƙyar da kwatance aka samu wani a cikinsu ya gane wadda suke nema, kuma kai tsaye suka shaida musu cewa kwana biyu da suka wuce Maryn tare da iyayenta suka kwashe kayansu tsaf! suka tafi garin su.
Sai da ƙyar ƴan sandan nan suka samu mutanen nan suka fito musu da wani tsoho da akace ɗanuwansu ne. Kuma shima ganin ƴan sandan ya ruɗa shi, ya dinga rantsuwa bai san komai ba sai da yaga da gaske ana shirin tafiya dashi sannan yayi bayani cewar ya san yarinyar da ake neman, kuma har da ita a dalilin barin su Mary garin bayan ciwon mahaifiyarsu.
Ruƙayya gabansa taje ta tsugunna a lokacin yayin da yake bayani da gurɓataciyar hausarsa.
"Wani mutum ne anan yazo ya dauki yarinyar ya tafi dashi, kuma Mary yace ya bawa yarinya maganin bacci mutumin zai kamata, kuma the madam she's serving zai ce ta ɓatar da yarinya, ita bata san yadda zata yi ba, don haka sun kwashe kaya nasu sun tafi."
"Shi mutumin da yazo ya tafi da yarinyar waye shi?" Wani daga cikin ɗansandan ya tambaya tsaye akansa.
"Mary yace shine oga na inda babanshi Mr. Okafor yake aiki."
"Ka san wajen aikin nasa?"
Ya ɗago cike da tsoro yana kallon ɗan sandan.
"Ka san wajen da baban nata yake aiki?"
Wannan karon Ruƙayya ce ta tambaya, muryarta na rawa da dukkan fatan na cewar amsar da zai bayar ta kasance abinda take son ji, kuma cikin abinda zata iya kira da sa'a, sai ya daga kansa yace.
"Eh ya sani, wajen inda ana..."
Bai karasa ba ɗan sandan ya bashi umarnin tashi su tafi, jikinsa na rawa ya miƙe tsaye ya shige gaba, aka sanya shi a motar ƴan sandan bayan sun fita, suka fara yin gaba sannan su kuma suka shiga nasu motocin suka bi su.
Wannan karon Ibrahim ya shigo motarsu ya zauna a wajen Bilal da shi ya koma motar Ahmad, tana ji kowannensu na waya, Ashraf da matarsa yana gaya mata inda suke, Ibrahim ɗin kuma da Daddy yana yi masa bayanin abinda ya faru.
Fuskarta ta juya waje idanunta na bin fitulun kan titi ke haskawa akan gilashin da kuma fuskarta, hawaye take sharewa da gefen mayafinta yayin da hannyenta ke rawa kamar zuciyarta, bata iya hango yadda zata kasance idan har bata sami Hamida a wajen nan ba.
Sun iso daidai gaban wani dogon gini mai ɗauke da gilasaivda kuma fitulu kamar rana, akwai manya-manyan rubutu a sama wanda bata iya karantawa ba saboda halin da take ciki da kuma ƙwallar da ta taru a idanunta. Ashraf da ya tsayar da motar ya juyo ya kalle ta, kuma ganin yadda take share hawaye yasa ya girgiza kansa yace.
"Stay inside, bari muje mu gani."
Da haka ya buɗe ƙofar motar ya fita, Ibrahim na bin bayansa.
Sai kawai ta kifa kanta akan cinyoyinta ta shiga rera kukan da take kasancewa a cikinsa duk dare, gani take idan har ta rasa Hamida rayuwarta ta gama rushewa gaba ɗaya, ba lallai ne ta samu fatan da dashi take ganin zai sake gina rayuwarta ba.
Don samun Ma'aruf shine ƙarshen fatanta yanzu a duniya, bata hango komai a gabanta sama dashi, wani gefe na zuciyarta na jin cewa zata iya hakura da Hamidar ma idan har rayuwa zata iya dawo mata da Ma'aruf ta wata hanyar, amma ta san daga shi har iyayenta babu mai sake kallonta idan babu yarinyar, don haka ba zata taɓa rasa ta ba.
Wayarta tayi ƙara a lokacin daga gefenta, ta kalli screen ɗin tana karanta sunan Jawad da ya fito tar! akai, tun da ta barshi a hotel ɗin nan bata ƙara bi ta kansa ba, ya kira wayarta sau da yawa bata ɗaga ba, a jiya da yamma har gidansu yazo amma ta aika masa da saƙon ba zata iya fitowa ba, tana kallonsa ta tagar ɗakinta ya juya da motarsa ya fita.
"Babe I'm really sorry, ki manta maganar da na gaya miki dan Allah, just talk to me!"
Sakƙon message ɗinsa bayan katsewar kiran ya nuna akan wayar, sai kawai ta ɗauke kanta tana kallon waje, bata lissafa Jawad a cikin matsalolinta na rayuwa ko kaɗan.
Ta kalli wajen daidai lokacin da idonta ya kai kan su Ashraf da ƴan sandan nan, magana suke da wasu mutane a ƙofar wajen basu