Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 58708 words

Chapter 10 - NARJEESAH Book Complete Document By Nana Khadijatu .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

tsaya masu, cikin kwana ki ƙan ƙani sunan su ya baza gari kowa zuwa yakeyi da buƙatar taimakon su, suna taimawa, amman mai gaskiya kawai suke yiwa wannan idan kazo da rashin gaskiya yi sukeyi kamar basan da zuwan kaba, idan ka gaji dole ka tashi ka tafi, sai aka maida su garkuwar talakawa, Sunan su ya zaga ta ko ina, duk Nigeria an san dasu, anan ne mutane keyi ta kawo masu, gari mata da maza, yan mata kuwa kowa, Salman yake son Aure dan dai kawai babu damar ganin sane, samari da manyan mutane kuwa Salma suke son Aure amman sam basa kila kowa.




Watan su Salman biyar basu koma london ba, iyayen su sunji kewar su, har gaji kawai suka shirya zowa Nigeria, barare da sun kira sun sanar da zuwan nasu ba.




Yau su Salman ne zaune a cikin "yan uwan su, dan yan zun sun saba da su, Salma kuma ta fara saka doguwar riga amman har yan zun bata wani saba, dan zafi takeji idan ta saka, sallamar su, Dad da Mom ɗin sune suka shigo cikin falon aikuwa kowa da farin ciki ya tashi suke tarbon su, su kuwa farin ciki sukeyi suna rungume jinin nasu, kallon su Salman sukayi da suketa harkar gaban su, Salman yana danne_dannen laptop Salma ma laptop ɗin ce a hannun tana aiki, shi kuwa Muhseen waya ce a hannun sa ya saka earpiece akunne sa, cike da mamaki kowa yake kallon su, fulani kuwa cewa tayi, "Salman Salma Muhseen bakuga iyayen ku bane? ".




A tare suka ɗaga kai suka dubi fulani, suka maida idon su akan aikin su, cikin sanyi jiki Mom ta ce, "my ɗear baku san da zuwan mu bane a nan way kuka share mu?.




Ɗaga idon sukayi suka ɗaga masu hannun "hi Mom hi Dad" suka tashi bar gurin iyayen bin su sukayi da ido suna shiga cikin ɗakin su, su Dad suka zauna daɓas cikin damuwa.




Fulani ta dubesu ta ce, da alama kunyi wa yaran ku, laifi amman zasu sauko ne, tunda gashi sun sauko yan zun sun saba da kowa".




Uncle ɗin sune yake ƙara sheda masu aikin da sukeyi anan shine ya hana su koma gurin su ba, Mai martaba ba, Dad ya ce, eh duk abunda akeyi ina sane saboda ina magana da Mai martaba a kullum, kuma tun lokacin nake sheda masa yaran nan sam ko mun kirasu a waya ba wani magana mukeyi dadu ba daga gai suwa basa ƙara cewa damu komai! ".




Tausayin su sukaji ya kama su, a ce kai da ɗan ka, amman babu wata magana daga gaisuwa har tsayin wata biyar , lallashin su akayi sai da suka haƙura aka cika masu gaban su da kayan ciye_ciye.




Salman da Muhseen da Salma kuma suna shiga cikin ɗakin suka fara dariya harda tafawa ajiye kayan sukayi suka, zauna Salma ta ce, "kagafa Dad wai har ya manta irin tsawar da ya daka muna wai mun zagi ƙasar sa, ai ga munan mun zauna ƙasar tasu, kuma ba zamu koma ba".




Dariya duk sukeyi, Muhseen ya ce, kuwa ma yan zun ma yawon zaga gari nake son yi, duk da ranar naji Dad da Mai martaba suna magana akan bikin ɗan gidan Mai girma governor ashe abokin Dad ne, shine naji yana faɗar ba zai samu damar zuwa ba, sai dai mu muje mu wakilce sa".




Salman ya ce, "sai dai ku kuje ni kun san babu inda zani, saboda ni ban cika son yawan damuwa ba, ba kowa nake son hulɗa dashi ba, gaskiya kuma kun fi kowa sanin haka, kune ƙanne na wanda nasa daku, duk da a gida ma, ba wani cika shiga lamarku nayi ba, kasan cewar bana son haya niya kwata_kwata".




Dariya duk suka sanya masa, sukaci gaba da aikin su, da sukeyi a computar su.




Tun lokacin da Mai martaba yaga gudan jinin sa ya dawo, shike nan farin cikin sa yakasa ɓoyuwa, sanar dashi damuwar su sukayi, murmushi ya yi yace, ai tunda kun dawo sai ku jawo abun ku a jikin ku, ku tashi ku shiga cikin ɗakin su"





cikin sanyin jiki suka shiga cikin ɗakin gurin Salman suka fara dosa domin shine babba sauran kuma biyayya sukeyi masa a tsakiyar su suka saka Salman, shi kuma yana ganin hakan ya shagwabe fusa ya kwanta, jikin Mom ya saki laptop ɗin sa ajiki sa, Mom tace, "son fushi dai fushi dai abu yakai some 6moth ya kama ta kuyi hakuri haka nan, duk irin son da muke yi maku, ku a tunanin ku, shike nan Mai martaba zai nemi alfarma muƙi yimasa ne? Haba son kudu ba fa, munyi kewar ku, sosai ko a waya baka sakar muna jiki duk kun bi kun hanamu kwanciyar hankali, iye? Nifa na haifeku ni mayi haƙuri nabi umarnin kakan ku amman ku sai kusa na kasa yi masa biyayya bayan tamkar mahaifi yake a guri na? ".




Dad ne ya ce, "ni kuma fa baiwa nayi maku tsawa bane dan kuji haushi bafa dan kawai kuyi saurin fahim tane nayi maku hakan amman shine kuka ɗauki fushi damu".




Tsakanin ɗa da iyaye sai Allah atake suka shawo kan su, sukaci gaba da farin ciki tare dasu.




Bikin da su Dad sukace ba zasu zoba, sai gashi dasu za ayi Dad ɗin sune yaje dasu gidan governor, anan suka haɗa kan iyalen su, inda anan muka haɗu da Salman kasan cewar Khalid ɗan gidan governor abokin mune tare muka tashi dashi munyi karatu dashi tub daga secoundary har i zuwa university couse ɗaya mukeyi dashi har muka dawo gida nigeria, muka fara aikin likitanci, sai dai ba garin mu ɗaya ba, muma bikin sa ne muka zoyi, kasan cewar Salman sa'an mune, sam bamu wani sha wahalar zama abokai ba, kasan cewar mu bama da hatsaniya dan duk abunda abokan ango sukeyi, badamu ba, zuwa gurin Amarya da ƙawayen ta, sai da ma za'a gurin dinier ne, angon ya nuna fushin sa, akan dole nida Aliyu da Salman sai munje gurin dan yasan halin iri ɗaya ne, ganin yanda ya kafe dole muka shirya mukaje, koda mukaje gurin bamu shiga ba muna cikin motar, waya yayi ta kira saboda anfara shagali bai saka mu a idon saba.




Dole muka ɗauki wayar sa kasan cewar yayi kiran wayar mu har ransa ya fara ɓaci mu muna kallon sa, dole muka fito uban yan naci ya kira mu.




Bamu wani jima a gurin ba, saboda yanda "yamta ke ta zuwa gurin gurin amsar number waya dole muka dawo cikin motar, har aka tashi muka koma gida, tunda aka kai Amarya muka anshi number wayar Salman, muka baro kaduna muka dawo nan yola, tun daga wannan lokacin ne abota mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanin mu, ko ince aminta har muka san junan mu da aikin juna da sirrin juna, kowa idan wani abun ya shige masa yakan kira ɗan uwan sane, kwata_kwata bama yin abu ko miye dan muna mu biyu sai mun saka Salman aciki shima haka, a dangin sa duk ansan mu haka ma dangin mu kowa yasan Salman.




Numfa sawa Jafar ya yi ya ce, "babbar damuwar da Salman ya fara fuskata a rayuwa wadda ta zame masa ƙalubalen rayuwa take ci masa tuwo a ƙwarya har yanzun wadda wannan ya shafeki Narjeesah shine zaki sani a yanzun kasan cewar, har yan zun baki san waye Salman ba shine.... ".






*Comment and share*




*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹




💐💐 *NARJEESAH* 💐💐




*Rubutawa*
*NANA KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_


*Ya Allah kajiƙan iyaye na kayi masu rahma ka sada su da rahmar ka dasu da duk kannin yan uwa musulmi baki ɗaya amin*




2⃣6⃣⏮3⃣0⃣


➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Narjeesah Salman sai da ya zamo fittacen lauyan da ƙasa take alfahiri dashi ya kasan ce mutum mai gaskiya wanda akeji dashi ta ko ina a faɗin ƙasar nan ".




Rayuwar Salman ta fara sauyawa ne saka makon haɗuwar sa da yar mataimakin shugaban ƙasa, Haulart, Haulart ta shiga rayuwar Salman ne da ƙarfin gaske, wanda muka rasa taya hakan ta faru kasan cewar bamu sani ba, dan bai sanar damu ba sai ranar ɗaurin Auren sa, wanda ta kasan ce iyayen Salman da "yan uwan sa sai ranar suma suka san da zan cen, dan haka Auren bai wani samu shagalin biki ko ɗaya ba, dan yace wa su Mai martaba kada ayi taron komai dan shima Auren zuwar masa yayi da rana tsaka.






Tunda aka ɗaura Auren Salman da Haulart suka bar ƙasar sai da suka shafe shekara biyu suka dawo garin Abuja suka sauka, Salman ya sauya, baya neman kowa nasa, daga shi sai matar sa kawai suke bidirin su.




Matsalar farko da ta fara fuskar tar Salman rashin haihuwa wanda alokacin kowa yasan Salman baya cikin hayyacin sa, dole Mai martaba da kanshi ya nemi Salman kuma yayi masa nasiha da ya dawo hayyacin sa, ya waiwayi iyayen sa, da suke fushi dashi, cikin ikon Allah kuwa Salman yayi abunda Mai martaba ya umurce sa, dashi kowa yaji daɗin sauyawar Salman, kuma fa duk wannan halin da Salman ya shiga, yana nan yana aikin sa akan gaskiya da sanya marasa gata a cikin lamarin sa, ƙungiyoyi ya kafa sosai na kula da gajiyayyu da marasa ƙarfi, da marayu, da malamai hidima sosai yakeyi masu, wannan shine ya ƙara wa Salman daraja a idon mutane,




Ganin har shekara ukku Salman da matar ta basu haifu ba, suka fara shiga damuwa kasan cewar Salman shine ya shiga damuwar da yawa sai suka fara zuwa ganin likitoci amman abun mamaki duk ƙasar da sukaje result ɗin Salman yakan nuna cewar Salman kwata_kwata baya haihuwa matar sa ita kuma lafiyar ta, ƙalau, wannan abun ya ɗaga hankalin kowa ba kamar Salman wanda ya shedawa iyayen sa, zai rabu da matar sa, dan gudun kada ya cutar da ita, sunji tausayin Salman sosai kuma sunji daɗin Salman zai rabu da wannan "yar isakar matar wadda tunda sukayi Aure da Salman sau ɗaya suka taɓa ganin ta har su Mai martaba.






Tunda Salman ya shedawa Haulart hukunci da ya yanke tace, sai Salman yayi nadamar rayuwar sa, shida iyayen sa, duk sai sun zubar da hawayen su, ai kuwa tun daga wannan ranar Salman bai sake fita koda ƙofar gidan sune sai da jami'an tsaro wanda mahaifin matar sa, ya haɗasa dasu, ga baki ɗaya Salman ya manta kowa nasa, baya tuna koda sunan iyayen sa, haka iyayen suka tsani ace sun haifi ɗa mai suna Salman.






Abu kamar da wasa ƙaramar magana ta zama babba daga baya ma baya iya kallon ko wace mace, saboda duk maccen da zatayi wa Salman magana zai ganta a gaban sane kamar suffar alade, Haulart ce kawai yake ganin ta a matsayin mace kuma cikkakkiyar mace, wannan abun har iyayen sa, sun shiga daga cikin abun ƙin sa, akwai ranar da Salmah ta haɗu da Salman a wunin wani aikin da ya haɗasu a tare, kasan cewar sun san Salman yan zun baya ko tuna sunan su, ta matsa a kusa dashi ta ce, "bros nasan baka son ganin fuska ta, nima haka, amman kasani muna kewar ka muda iyayen mu, bro duk wanda ya aikata hakan a gare mu ba zamu taɓa yafe masa ba, na barka lafiya ".




Tunda Salma ta ambaci sunan sa, kansa yake a ƙasa bai ɗago ba, har tabar gurin, a ranar da ciwon kai ya kwana mai tsananin gaske, sai da ya kwana, biyar yana jinya sannan ya samu sauƙi, tun daga wannan ranar ne yake yi muna sallama a WhatsApp wanda rabon da yayi muna hakan har mun manta dukan mu, to anan ne yake sheda muna yana barar addu'ar mu, kuma muje ga iyayen sa, mu sheda masu halin da yake ciki da yanda yake jin kowa a garesa inba Haulart ba, to anan ne kowa yasan mike faruwa, shine muke bashi shawarar duk lokacin da muka gama magana dashi ya goge farar da yake yi damu, cikin ikon Allah kuma babu abunda ya sake faruwa muna yawan magana dashi kuma yakan turo muna da kuɗi muci gaba, da kulawa da har kokin sa, na yau da kullum, tare da sadaka da neman addu'a a bakin mutane da dama da malamai.








A wata ranar laraba ne yake sheda muna, yana cikin tsananin tashin hankalin, domin yana jin a jikin sa cewar akwai akwai macen da yakejin zata iya shiga rayuwar sa, kuma Haulart ta tada masa hankali akan cewar, ko wace mace ce sai ta ne mota, shi bai san a ina tasan da wannan zancen ba, dariya mukayi dan mun ɗauki abun kamar almara fa shirme, amman sai ya matsa muna akan muje mu sanar da Mai martaba dan abun bana wasa bane, jin hakane mukaje har gurin mai martaba muka bashi wannan labarin, a take mukaga hankalin sa yayi mugun tashi, a gaban mu ne ya saka aka kira masa malamin masarauta, ya labar ta masa kuma cikin ikon Allah ya ce, a bashi kwana biyu zai je ya dawo masu da amsa, mai matarba, ya hanamu komawa, dole muka zauna har zuwa kwana biyu.




Anan ne Malamin yasa aka kira mu, bayan mun zauna ne, yace, "tabbas wannan yarinyar itace haske a cikin rayuwar Salman kuma akwai rabo mai tarin yawa a tsanin su, kuma yan zun haka akwai rabon da yake a kusa_kusa dan haka duk yan da za'ayi a ɗaura Auren Salman da yarinyar nan saboda akwai igiyar Aure a tsanin su kuma igiya ko ɗaya ba zata tsinke ba, duk da kasan cewar su nesa da juna.




Yana gama bayanin ne duk mun kasa gane wannan bayanin kawai ya ce, kada ku sanar da kowa gaskiyar wannan lamarin har Salman ɗin a take ya sanar da mai matarba cewar, a riƙa bibiyar rayuwar Salman da matar sa daga ɓoye, haka kuwa akayi mai gadin gidan Salman shi aka baiwa wannan aikin har da wayar da zai riƙa kira yana sanar da abunda yake faruwa, da yake mutumen yana da hali mai kyau shine yayi ta sheda wa Mai martaba abunda ke faruwa.






Bayan wata biyu Mai martaba ya kira mu yake sheda muna cewar Salman zai zo gurin mu duk yanda akayi mu hanasa tafiya har sai idan shine ya kira mu ya bada umarnin barin sa ya tafi, ya tambaye mu cewar ko Salman yanada gurin sauka a garin mune, muka sheda masa cewar eh amman bamu san unguwar da zai sauka ba, dan yana da gidaje a garin mu harda motoci dan haka yanada masauki.




A gidan Salman kuwa wani irin ciwo ne ya taso masa, wanda yayi kamar zai mutu, sai shure_shure yakeyi ma aikatan gidan ne suka samesa a hakan da sauri suka kira wayar Haulart duk da kuwa irin tsoron ta da sukeyi, sukayi shahadar kiran ta, sai da taga damar ɗauka ta ɗauki wayar cikin masifa, take tambayar su miye?".




Cikin tsananin tashin hankali direba ya ce, "ranki ya daɗe wallahi yallaɓai ne bai da lafiya sai shure_shure yakeyi! "


Kashe wayar tayi cikin minti talatin ta iso gidan ita da guard ɗinta, da sauri ta shigo cikin falon turus tayi ta kafesa da ido tana ya tsinar fuska, wani uban ashariya ne tayi, cike da masifa ta kira waya, ana ɗaukar wayar tace, "abunda aka faɗa ya tabbata, kuma ance ko na barsa ya aikata ko ni na mutu, gashi ina da tsananin kishi, amman tunda ni rashin aikata abun zai shafa, to nayi ƙoƙarin samo yarinyar da aka ce, har ankai photon ta, a gurin bokon kuma ya sheda muna cewar ita ce, kuma nasa an sato yarinyar har ankawo ta wata hotel, kuma yan zun zan saka akaisa a ƙofar hotel ɗin a jiye sa a hakan kamar yanda aka ɓukata, nikuma zan koma na cika ɗayan aikin ".




Magana akayi mata, daga can ɓangaren, kawai ta kashe wayar da gudun ta ta fita, tare da body guard dinta ta shigo su huɗu suka ɗauki Salman suka fita dashi, maigadin ne ya kira Mai martaba ya sheda masa, ai kuwa aka bisa daman shima nashi ma aikatan suna biye da duk wani motsin Salman da matar sa.






Ban san ya akayi ba, nu dai Kawai mun ya ankawo Salman tare da jami'an tsaron sa, airport mukaje muka ɗauko su, a hotel suka sauka, sai da ya kwana biyu ya fara magana, kuma tun daga lokacin bamu sake zuwa inda yake ba saboda umarnin Mai martaba, sai dai ya kiramu yace, Salman zai koma mu kaisu airport, tun daga lokacin Salman bai sake zuwa nan garin ba sai wannan karon .






Amman fa matar sa wani sabon salon ta ɗauka duk wata macen da ta samu labarin cewar Salman ya kalla sai taga bayan ta, da sai an nemeta an rasa, kai abun ma harda abokan Salman bata bari ba, amman ban san miye yasaka mu bata rabamu da Salman ba, har tsayin wannan lokacin duk da tasan da cewar muna tare dashi, saboda duk inda Salman ya saka ƙafa tanada masaniya, akai abu kamar aljana".


kuma har yan zun sakamakon Salman baya haihuwa yake nunawa, amman kuma sai gashi Shuraim yazo a matsayin ɗan Salman, wanda kusan kullum matar Salman har a internet tana posting din Salman da result ɗin rashin haihuwar sa, anayi mata like, wannan abun ba ƙaramin ɓatawa Salman da "yan uwan sa yakeyi ba him! "




Nisawa jafar yayi ya ce, "NARJEESAH kinji tarihin Salman kuma har yan zun Salman tutar sa a gurin kowa tsaye take, koda kinyi ƙarar Salman ba zaki samu biyan buƙata ba, sai in da Matar sa zaki kai ƙarar sa"




Kowa shiru ya yi Amrah ce, ta ce, "Antyn Nargeesah dan Allah kada ki kai ƙarar Salman saboda idan har mutane suka kalli Shuraim duba na hankali zasu fuskaci cewar ɗan Salman ne, to masu kawo wa Salman hari kina ganin kamar yanda muka rasa sanin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads