Showing 15001 words to 18000 words out of 58708 words
Chapter 6 - NARJEESAH Book Complete Document By Nana Khadijatu .txt
shiga cikin wannan yanayin".
Hindu ta ce, "to ina Halima zata tafi bayan itace ta, taramu a gurin nan ".
Angon ya ce, "wallahi na ɗauka tana can gurin da aka kira mani ku, to amman ina ta tafi ne? ".
Wayar Humaira ce tayi ƙara tana duba ta sauke ajiyar zuciya ta ce, video coll Halima Allah dai ya shirya muna ke, ɗaukar wayar tayi, kawai sai ga Halima muna gani ba'a cikin holl din ba.
Halima tayi dariya ta ce, Humaira ki saurare ni da kyau kiji, da hankali na nake komai, ina fatan kin san da sanin cewar Yazeed abokin Jafar wanda zan Aura ko? Wanda yake mutum makusan cin Jafar ko nace aminin sa, wanda yake zuwa guri na yace Jafar ne ya aiko sa guri na, har ka kace kin tsane sa, yana son ya ɓata Aure na da Jafar ne, to ki sani soyaya mukeyi dashi kuma shi nake so ba Jafar ba, yan zun haka ma nabishi mun tafi a ɗaura muna Aure dashi, shi kuma Jafar yayi hakuri Allah ya bashi wadda ta fini".
Da sauri na anshi wayar nace, "Halima baki da hankali ne wai, taya zaki yanke wannan ɗanyen hukuncin kada ki biye ruɗin zuciyar ki mana? "
Halima ta ce, "ki baiwa Humaira shawara, nasan zata ɗauka, ki sani na baiwa Humaira miji ta Aura kece aminiyar ta dan haka kiyiwa Humaira adalci tayi Aure ga farin masoyi nan wanda take son na Aura wanda take fushi da nurul ƙalbina Yazeed a kan sa, lallai Humaira mutum ce kuma adilah".
Hindu ta ansa tace, "Halima ki dawo hayyacin ki dan Allah ".
Halima ta ce, "Hindu nayi nisa bana jin kira, ku baiwa Jafar dasu Mama hakuri kuma kuyi recordin ɗin abun da nake faɗa yan zun ".
Jafar ne ya anshi wayar ya ce, "saboda miye zaku yau dare ni keda yazeed miye laina dan nace ina sonki kuma baku tashi yau dara ta ba sai ranar dinier? ".
Halima ta ce, "Jafar yan zun ni matar abokin ka ce, dan haka bara na bashi shine dai_dai da kai".
Yazeed yace, "Kayi hakuri amini na haka Allah yaso Halima ba matar ka bace mata ta, ce".
Halima ta ce, "nasan kuna recording ɗin komai Baba da Mama ku yafeni abunda nayi maku bana son Jafar a yanzun dan haka ku maida masa da kayan sa, na barku lafiya".
Kashe wayar tayi, kowa ya shiga cikin damuwa Humaira kuka kawai takeyi, ta ce, "Hindu ban faɗa maki ba, ban yarda da alaƙar Halima da wannan wawan ba? "
Hindu ta ce, yan zun fa kawai musan abunyi kawai kowa ya rasa mafita, kawai wayar Jafar tayi ƙara yana dubawa, ya baiwa Aliyu sai Aliyu ya ce, "muje gurin Mutanen nasan shi yanada mafita".
Haka mukaje gurin tun kafin mu ƙarasa naji zuciya ta kamar zata faso ƙirji na ta fito sai dukan ukku ukku takeyi da sauri da sauri rufe ido na nayi muka ci gaba da tafiya muna zuwa naja nayi tsaye batare da na kalli mutanen gurin ba, Aliyu ne ya bashi labarin akasin da aka samu da duk yanda akayi kallon mutanen kawai yake.
Dafe zuciyar sa yayi da sauri, ya tashi tsaye duk suka zuba masa ido, cike da mamakin sa, kallon inda ya kafe da ido sukayi ga mamakin su nice yake kallo gashi nima nayi tsaye na juya baya, ina dafe da ƙirji na.
Shuraim ne ya gudu yaje ya rungume sa, ya ce, "na kamaka wallayi".
Cike da mamaki aka maida ido a kan Shuraim da wannan mutanen, kawai ya saka hannu wansa ya ɗauke sa ya rungume sa a ƙirjin sa, suna sauke ajiyar zuciya sun ɗauki wasu lokuta a haka kafi ya ƙara duba fuskar Shuraim ɗin ya yi masa murmushi.
Ni kuwa jin shirun ya yi yawa sai na maida ido na akan, su Humaira sai naga tana kallon wani gurin nima sai na ɗaga ido na abunda nagani ne ya fir gitani Shuraim ajikin wani mutum kuma sun kafe juna da idon sai murmushi sukeyi iri ɗaya.
Aliyu ne da Jafar suka ce, "man ya zamuyi da mutane zauna wa yayi da Shuraim a jikin sa, ya riƙe dashi, yana kallon sa, kawai naje kusa dashi nasa hannu na ɗauke Shuraim na juya zan wuce, naji an riƙe Shuraim a fusace na juya zanyi masifa kawai naga ashe.......
*Comment And share*
*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
💐💐 *NARJEESAH* 💐💐
*Rubutawa*
*NANA KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*
*ELEGANT ONLINE WRITERS*
_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_
1⃣1⃣⏮1⃣5⃣
➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Kai sai naga Ashe Shuraim ne ya riƙe masa hannu cikin jin haushin sa kawai na doke hannun sa, ya saki mutumen, ya fashe da kuka, sukam kallon mu kawai sukeyi, da sauri naja hannun Humaira da Hindu muka bar gurin, muna fita na sauke ajiyar zuciya na maida hankali na a gurin Hindu nace, "Hindu ya kamata Humaira tayi kamar ita ce Halimar saboda kada mu kunya ta wannan bikin musam ma abokan Angon nan da yan uwan kamar Halima ko ya kuka gani? Tunda kaya iri ɗaya ne kuka saka kwalliya kaɗan ce ta ban banta, sai na baki wannan gyalen nawa yafi naki girma yanda babu wanda zaga fuskar ki bare yasan wace ce a gurin ki duba yanda ake ta cigiyar Amarya kuma dare kayi fa".
Da sauri Hindu tayi na'am da shawara ta, mukayi wa Humaira kamar Amaryar mukaje muka zaunar da ita akan kujerar Amaryar, tafi kawai akeyi, Hindu ce taje ra sanar dasu abunda muka tsara suma daket Jafar ya yarda suka rakoshi ya zauna a gefen Humaira, kiɗa aka sanya aka fara yin dinier cake aka ce a zo a yanka, Humaira taƙi tashi sai da na roƙeta da ket ta tashi a hankali take tafiya gurin yanka cake ɗin sai da Aliyu da wannan baƙon nasu sukayi tsaye wa Jafar ya riƙe wukar muka, taku rawa Humaira itama ta riƙe wukar suka yanka, Dj yace, sai su ciyar da junan su, hakan duk ka ƙiya ni kaina banyi tunanin hakan ba, da ket muka samu ya saka wa Humaira abaki itama ta saka mashi, tafi akayi suka koma suka zauna haka dai akayi ta dinier har aka gama komai, motoci ne suka zo suka fara kwashe mutane Humaira na can tana kuka bayan ta gama gaisa wa da mutane da abokan Angon.
Mota zan shiga na juya banga Shuraim ba inada na barshi a kusa da Humaira da sauri kira Amrah da Nusaiba da suke jira na cikin kuka nace dasu banga Shuraim ba.
Hindu ta ce, "Narjeesah wane irin baki ga Shuraim ba, bayan a hannun ki na gansa".
Nace wallahi a nan yake zaune kusa da Humaira, na barshi zan samar muna mota, cikin kuka nake magana.
Ai kuwa atake kowa ta shiga neman Shuraim babu shi babu labarin shi, kuka kawai mukeyi nida su Amrah harda Humaira gashi dare yayi har kusan ƙarfe ɗaya, Jafar ya kira duk motocin da suka fita sunce basu ga yaro ba, su kam".
Neman duniya an yiwa Shuraim amman ba'a samesa ba, dole sukayi ta bani hakuri suka ce nemo mani shi, gida muka koma a ƙofar gidan mu suka sauke muka shiga gidan, Umma tana ta duba inda zata ga Shuraim amman bata gansa ba gashi duk idon mu yayi jawur dashi.
Da gudu na shige cikin ɗaki na, nayi kwance ina kuka, Umma kuwa cewa tayi, "kun baro sa a can ko? To kuwa kun kyauta, taya ma zakuje ku saki ƙaramin yaro a can cikin taron mutane kuma cikin dare gashi ba yarda yakeyi da mutane ba, wallahi badan kada ayi biyu ba, da sai ku. Koma cikin daren nan kun nemo sa, yo wannan ai sakarcin banza ne! ".
Faɗa kawai Umma keyi ta inda ta shiga ba tanan take fita ba, ganin yanda Umma tayi fushi ne take ta faɗa kowa ya gudu cikin ɗakin sa, kuma kowa kuka yakeyi, alwala na ɗauro a ranar ban rintsa ba, kaina kuwa saboda ciwo kamar zai watse, da safe abun karin kumallo ne aka kawo mani bana iya saka komai a bakina Humaira ce ta shigo itama idon ya kumbura, ta gaida Umma, Umma ta amsa ta kafe ta, da ido har ta tashi ta shiga guri na, Umma ta dakatar da ita, ta dawo ta zauna abinci Umma ta zuba mata ta tsare ta, tace, "ki cinye sa ki bani kwanon nan shi nake jira".
Humaira juya cokalin takeyi ta kasa saka loma ɗaya a bakin ta, Umma na ganin abunda takeyi tace da Nusaiba jeki ki ce ta fito ina kiran ta"
A tare muka fito da Nusaiba ina fito wa na kafe Humaira da ido, a kusa da Humaira na zauna cokali Umma ta bani tace, " kwanon kawai nake buƙata".
Duk kan mu juya cokalin kawai mukeyi, har abincin ya fuce, Maman su Humaira ce ta aiko kiran mu tare muka tashi su Amrah suka raka mu, Maman Humaira ce ta ce, "kuzo muje gidan su Halima ana can ana neman ku".
Tare muka tafi gidan yan biki cike da gidan ɗakin Mommy muka shiga Maman Halima, ita ma tace kuzo muje inda ake neman ku"
Muna shiga cikin ɗakin mutane muka samu a gurin harda su Jafar mahaifin Halima ne ya buɗe taron da addu'a sannan yace, "naga saƙon Halima kuma muna godiya sosai da abunda ta aikata muna, zata kuwa gani ga kwaryar shanta".
Sannan ya dubi mahaifin Jafar ya ce, "malam dan Allah kuyi hakuri laifin ɗan yau ne ba namu ba, mu bamu ƙi mu haɗa zuriya da ku ba, amman haka Allah ya so ga kayan ku da kuka kawo sai ayi lissafin abunda taci wanda babu shi anan ciki! ".
Mahaifin Jafar ne ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "tabbas bamu ji daɗin abunda ya faru ba, amman babu komai ƙuruciya ce kuma ni kam ba zani anji komai ba daga hannun ka tunda daga kan sadaki har komai, kai mahaifin Jafar ne, zaka iya nema masa mata aduk inda kake so kuma nasan zaka zaɓa masa ta kwarai dan haka wuƙa da nama duk suna hannun ka".
Mahaifin Halima ya ce, "ina godiya da wannan karamcin amman ku baiwa Jafar hakuri kuma ku bashi damar fitar da wadda yake so ni nan zan masa waliccin Auren nata".
Jafar yace, "bani da wani zaɓi duk zaɓin da kukayi mani yayi "
Mahaifin Halima ne ya kalli mahaifin Humaira ya ce, "to malama Abdullahi gani nazo da ƙoƙon bara na, ina son ka baiwa ɗana Jafar Auren "yarka, Humaira".
Da sauri muka haɗa ido da Humaira wadda tuni ta soma zubar da hawaye, kuka ta fashe dashi ta kwanta a jiki na.
Baban Humaira ya ce, "da Humaira da Halima duk naka ne kamar yanda zakayi hukunci akan Halima haka zakayi sa akan Humaira dan haka wuƙa da nama suna hannun ka".
Murmushi mahaifin Halima yayi ya ce, "Humaira zan tambaye ki ki sanar dani tsakanin ki da Allah, shin kina da wanda kike so ko babu, ina son ki sanar dani gaskiya bana son ki ɓoye mani komai ".
Kasa magana Humaira tayi sai kuka takeyi, kowa ya zuba mata ido, mahaifiyar Humaira ce tace, "Narjeesah ke nasan kin san sirrin zuciyar Humaira kada ki ɓoye muna komai shin Humaira nada wanda take so ko babu? ".
Shiru nima nayi har sai da mahaifin Halima ya ce, "ki bada amsa dan duk gurin nan mun yarda dake".
Kallon Hindu nayi ta matso kusa dani ta kafeni da ido alamar nayi magana, da ket na buɗe baki kasan cewar murya ta bata fita naci kuka tun jiya har yau, nace, Humaira bata kula kowa ma, ita a tsarin rayuwar ta bata son samari barkatai".
Shiru duk sukayi zuwa can Baban Halima ya ce, to Alhamdulillah, shin Humaira zaki iya yarda ki Auri Jafar a matsayin zaɓi na? "
Kallon Humaira akeyi har yanzun dai kukan takeyi, sai aka dawo da tambayar a kaina, Hindu ta gyada mani, kai.
Nace, "ku iyayen mune zaɓin da zakuyi muna shine mafi can_canta mubi dan haka mun yarda da zaɓin ku".
Hamdala sukayi dukan su, anan aka maida sadakin Jafar akan Humaira suka ga addu'a akace yau za'a ɗaura Auren duk sai da muka zaro ido har Hindu, sai kuma aka koma zan cen neman Shuraim da aketi har gidan redio an bada ciya da gidan tv, da unguwar ni.
Baro ɗakin mukayi muka dawo gidan su Hindu Maman Hindu tayi ta bamu baki, kowa faɗar yakeyi duk sune silar ɓatan yaron nan, hankalin kowa a tashe yake, haka aka ɗaura Auren Humaira da Jafar, Humaira har yanzun kukan takeyi.
Nima kukan ɓatan Shuraim na keyi a ranar ne aka kai Humaira ɗakin ta, muna kaita na baro gidan muka dawo gida, yau ma da kukan na kwana, zazzaɓi mai zafi ne ya kamani, gashi idan ina ciwo komai bana iya ci, duk nabi na rame na susuce.
Har cikin sati biyu babu Shuraim babu labarin sa, nikuma har yanzun banyi lafiya ba kullum cikin ciwo, Humaira ce ta aiko kira kashe na tara, Umma ce yau ta ce, "ke ni gaji da wannan aiken ki tashi kije kiji kukan ta".
Tashi nayi, na shirya cikin riga da siket na shadda lemon green na ɗora gyalen a kafaɗa ta yau ban yafa har a kaina ba, Amrah ma shadda ce marun Nusaiba ma shadda ce pink, fitowa mukayi zamu tafi Aliyu ne ya gan mu yazo gaida su Mommy daman ya saba yin hakan, tsayawa yayi yace, muje ya kai mu yasan dai gidan su Humaira zani yasan ba gidan sa zani ba".
Kaina na dafe da yake yi mani ciwo sosai nace, "wallahi ko ita Humaira wannan shine aike na tara tun ranar da muka kai ta ban koma ba, sai yau gashi har yanzun bani da lafiya ".
Tausayi na bashi ya ce, "wallahi har yanzun bamu daina neman Shuraim ba, dan yaron nan idan muka daina neman sa ba muyi maku adalci ba, saboda ata dalilin mune aka ɗauke sa, to taya zamuje muyi farin ciki ku kuyi kuka kin kuwa ba zai yuyu ba, har gidan Humaira ya kai mu nace masa wani satin insha Allah zamu je gidan sa.
Muna shiga cikin gidan da farin cikin Humaira ta, tarye mu kallon ta kawai nake duk tabi ta rame ta sauya kamar ba Humaira 'yar gayun nan ba, zama mukayi ta kawo muna abun sha su Amrah suka sha, kallon Humaira kawai nakeyi, tayi murmushi ta ce, "kada kice dani komai malama aike yafi nawa sai yau kika ga damar zuwa? ".
Murmushi nayi na ce, "Humaira kema kin san abun da yake damu na".
Humaira ta ce, "nima shine damuwata wallahi kullum da shi nake kwana nake tashi, na rasa ma wace hanyar ce zamu bi mu nemo sa? ".
Amrah ce ta ce, "Anty zamu ɗan fita mu dawo "Humaira ta ce, babu inda zaku bari mu baku guri kunna masu kayan kallo tayi, ta basu remote tace, kuyi kallon ku, kichin ta shiga ta kawo masu kayan motsa baki muka basu guri sai dariya sukeyi wai mun gano manufar su.
Cikin wani ɗakin muka shiga, muka yada zango, bayan mun zauna ne nace , "Humaira ya gidan ya mai gidan da fatan dai kun sasanta kanku "
Humaira ta nisa tace, "wane sasanta kai kuma Narjeesah kin fa san ba son junan mu muke yi ba, zuciyar sa tana akan Halima kuma ni har yanzun ganin nakeyi dawowa zatayi ga masoyin ta to sakin jiki na miye? Inje in saki jiki a kaini a baro sai na faɗa son sa Halima na dawowa ya koma mata ni ya sako ni ko ya kike nufi? ".
Dariya nayi harda dafe ciki na ce, "haba da ranki ya daɗe har sai da kika sa nayi dariya wadda rabon da nayi ta tun ranar da mukayi abinci yan zuwa dinier, sai yau, to ke kice hauka ce kike zaune kikeyi a gidan mijin ki, haba Humaira kefa ce, kike son miji wanda zai baki kulawa, kuma mai hankali gashi Allah ya baki amman kike wasa da damar ki dan Allah kiso mijin ki, ki dawo da hankalin sa a gareki ki cire masa tsoron mara da yashe sa, wallahi Humaira kina da abunda ba kowa ce mace bace ta tara suba, koda a gurin tsatar ki da ilimin ki kawai aka tsaya uwa uba natsuwa, Humaira ki yiwa kanki faɗa mana".
Shiru Humaira tayi Jafar dake tsaye a bakin ƙofar tun ɗazun, yayi murmushi ya ƙaraso da sallamar sa yana dariya ya ce, "madam yau ke ce a gidan namu to munyi farin cikin zuwan ki, duk da muna fushi dake, a ce sai yau kika dawo gidan nan ".
Dariya nayi na ce, "ranka ya daɗe ba wata lafiya ce dani ba wallahi ko yan zun haka kaina ciwo yakeyi ".
Ya ce, "wallahi kina da gaskiya ɓatan yaro ai babban abune wallahi tunda mutum bai san irin halin da yaron yake ciki ba".
Ya dubi Humaira ya ce, "Madam baƙona ya iso yana ƙofar gidan nan yan zun ya kira ni, Allah yasa akwai abunda za'a tarye sa dashi dan wallahi nima bai sanar dani zuwan nasa ba, sai da yazo ƙofar gidan nan ".
Humaira ta ce, "ok babu damuwa bari mu haɗo masa abunda akwai idan baya cin sa, sai a sama masa wani abun da ban ".
Tashi tayi tace, "muje ki taya ni" kwanciya ta nayi na ce "wallahi ba zanyi ba, nima ta kaina nake da nakejin yana ƙara mani ciwo ga bugun zuciya ta ya ƙaru".
Ido suka haɗa da Jafar da sauri tabar gurin shi kuma yace, naje na shigo da baƙo na".
Da sauri na ce, badai a nan cikin ɗakin ba".
Dariya ya yi ya fita ni kuma nayi kwanciya ta, abinci ta ajiye a cikin ɗakin na ɗaga ido na na ce, "ba