Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 58708 words

Chapter 7 - NARJEESAH Book Complete Document By Nana Khadijatu .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

dai nan zaku kawo wani can ba? ".




Dariya tayi, na ce, "nikam zan gudu kuwa dai_dai lokacin suka shigo cikin ɗakin, ƙirji na ne naji kamar zai fashe, ko kallon inda nake baiyi ba, na koma na kwanta na rufe ido na Aliyu naji yana faɗar badai ciwon kan bane, Narjeesah? ".




Kallon sa nayi kawai na tashi zan bar ɗakin na ɗauki gyalen nawa, na riƙe a hannu na bar masu ɗakin su Amrah na yiwa nace, ku tashi muje gida sunyi baƙo kuma ni bani son ganin sa, ban san dalilin hakan ba".




Tashi sukayi Aliyu ya ce, "baƙon mu zai rage maku hanya" da sauri na juya na kallesa nace, bana so ya tafiyar sa".


Dariya sukeyi, Amrah tace, "Yaya Aliyu mun yarda zamu je tare da baƙon mu dan har naji baƙon ya kwanta mani tunda har zai kai mu gida ".


Tsaki nayi na ce, "ai sai kuje tunda mayun mota kuka dawo".


Dariya sukayi suka dawo suka zauna nayi_nayi dasu mu tafi amman suka ƙi tafiya har sai da Jafar yazo ya ce, "ku fito yana jiran ku, zai kai ku gida, amman fa tare yake da masu bashi kariya, dan kada kuje ku ji tsoro " da dariya yake maganar ya kallon fuska ta Humaira ma dariyar takeyi Aliyu ya saka ni gaba yana dariya har muka fita ƙofar gidan da gaske kuwa mutanen yau sun fi wanda na gani ranar dinier din nan, muna zuwa suka buɗe muna mota ɗaya.




Tsaye nake su Amrah duk sun shiga sai da Aliyu da Jafar sukayi da gaske nazo shiga suka rufe ƙofar suka buɗe mani gidan gaba, kamar nayi kuka na shiga cikin motar kawai naji ƙamshin da bazan taɓa manta irin sa ba, a take hankali na yayi mugun tashi, muka ɗauki hanya muna tafiya wanda yake tuƙin motar ne ya dubi su Amrah ta madubi ya buɗe bakin sa ya ce, "mike damun wannan yarinyar da ai ban san lokacin da na wani irin juyowa gabaki ɗaya nace,...




Sauke ni a nan malam kaji ko? Shima da sauri ya ɗaga ido sa ya waro su waje ya kafe ni da ido ya ce, "what!! Wani wawan burki ya taka ji kake ƙiiiiiiii ya ce, "kina nufin cewar wannan yaron ɗan ciki nane!!?.




Cike da zafin zuciya na ce, "baka da ɗa kuma ka daina alakan ta ɗana da sunan ɗan kane, yaro na bai da uban kuma kai ba kowa bane a gurin sa!!! "




Tsawa ya daka mani ya ce, " rufe mani baki anan malama! Kuma kada ki yarda ki sake dan gata yaro na da wani ban za can!! ".




Cike da masifa da rashin tsoro nace, "an cevShuraim ba ɗan ka bane, Shuraim bai da uba!! "




Yace, "ƙarya kikeyi Shuraim ɗana ne baida wani uban bayan ni!! ".


Su Amrah duk sun shiga cikin ruɗani, da sauri ta buɗe motar ta kira yaron sa saboda yadawo a kujerar da ake ɗora yara ya baro gurin tuƙin, saboda masifa, bamu ma san wani ya shigo motar ba, jan motar yayi Amrah nayi masa kwatan ce, har ƙofar gidan ya yi parking ya fita ya rufo motar mu kuwa masifar mukeyi ba bu ji ba bu ga,




Da gudu Nusaiba taje ta kira Umma sai ga Umma ta fito nima fita nayi shima fitowa yayi nasha ɗamara da gyale na, nace wallahi baka da ɗa a tare dani, kuma sai nayi ƙarar ka kotu sai an bi mani haƙƙina! ".




Shi kuma ya ce, "idan kika sake alaƙan ta yaro na da wani ban za can sai kin bin ciko mani shi, munyi shari'a dashi koda duk dukiyar dana tara zata ƙare!! ".




Umma ce, ta daka muna tsawa tace, "ya Isah! haka dan Allah kuke shirin tara wa kan ku mutane! koda ya ke ai ma na fahim ci komai, wannan shine Baban Shuraim dan ga kamar su nan dash! Ku shigo daga ciki muyi magana ".




Da sauri nace Allah ya raba Shuraim yayi kaman ce ceniya da wannan mugun! ".


Shima ya ce, wallahi ɗa nawa ne, ehe! ".


Hannun mu Umma nawa dana shi wannan shine lokacin na farko a ta rihin rayuwa ta da Umma ta taɓa riƙa hannu na mukayi tafiya muna shiga a falon gidan muka zazzauna Umma ta ce, " *NARJEESAH!!* yau ina son sanin sirrin da kike ɓoyewa yau nake son sanin taya kika sami cikin Shuraim har zuwa yau ɗin nan, yau nice da kai na na kira Sunan ki karon farko da nake son jin damuwar ki dan haka gareki".




Cikin farin ciki da baƙin ciki na ce "Alhamdulillah Umma yau ne karon farko da zan fara faɗar abunda ya faru, sirrin da ban taɓa sanar wa kowa dashi ba, saboda a ayi sani da duk abunda ya sami ɗa uwar sace ta farkon da zata fara sani, to ni kuma tawa uwar tayi ban za dani tayi kamar babu ita a duniyar nan shine nima na ɗauki alkawarin sai uwata ce kawai zata san sirri na to yan zun tun da uwata ta damu da damuwa ta, zan sanar daku komai".






"Umma a yau zan sanar dake gaskiya abunda ya faru a shekarar da nake zana hara bawar shiga j ss 3,............ "




*Allah kajiƙan iyaye na kayi masu rahma ka saka su cikin aljannar ka ta firdausi dasu da duk kannin yan uwa musulmi baki ɗaya amin*




*Comment And share*




*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹




💐💐 *NARJEESAH* 💐💐






*Rubutawa*
*NANA KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*




*ELEGANT ONLINE WRITERS*




_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_




1⃣6⃣⏮2⃣0⃣






➿➿➿➿


Amrah ta ce, "amman kafin ki fara Anty Narjeesah taya ya akayi kuka haɗu da wannan mutanen amman abun mamaki ke baki san shiba kuma kun haɗu dashi tun ranar da akayi dinier kuma a guri ɗaya kuke dashi amman duk baku nuna kun san junan ku ba, sai yau ko yau ɗin sai da yayi magana kika nuna kin san shi shima hakan ce a a gurin sa a gaskiya kun saka mu a cikin duhu miyasa hakan?


Murmushin takaici nayi nace, "ban san shi ba kuma ban taɓa ganin sa ba"




Amrah ta maida duban ta a gareshe ta ce, "bawan Allah kai kuma fa taya kake cewa Shuraim ɗan kane bayan ita bata san ka ba? "
Ya ce, nima ban taɓa ganin taba, amman kuma Shuraim ɗana ne wannan shine gaskiyar magana! ".




Su Umma duk sun shiga cikin duhu, tashi tsaye ya yi ya ce, "Umma ni zan tafi ina da uzuri ne, amman gaskiya zan sanar maki, ita ɗin mata tace, akwai Aure a tsakanin mu, kuma Shuraim ɗan mu, ɗan halak ne shi ba shegeba dan nine mahaifin sa, kiyi hakuri Umma na barku lafiya kuma a kila da igiyar Aure na duk da bata san ni nima nima ban san taba, amman muna da Aure nida ita".




Kawai ya fita, da sauri na ce, "Allah ya raba ni da Auren mugu irin ka azzalumi! ".




Aliyu da Jafar da matan su su Humaira da Hindu suka shigo, suna kallon mu, Umma ta ce, gara da kuka shigo, ina fatan kun ga mutumen da ya fita? ".




Gyaɗa mata kai sukayi anan Amrah ta labar ta masu komai bata boye, masu ba, kowa tambayar yakeyi taya ya hakan ta faru kuna da Aure a tsakanin ku harda ɗa ɗaya amman baku san junan ku ba, sai a murya gashi kun haɗu ya kai sau nawa?.


Umma tace, "ke muke saurare"?


Kallon su nayi na ce, Zakuji labarina yanzun kuwa".




Sunana Narjeesah Isah Musa, mahaifina malam Isah Musa mutume ne ɗan kasuwa Allah yayi sa da zafin nema, matan sa huɗu Maryam itace uwar gidan sa amman muna kiran ta da Inno sai Larai itace ta biyu muna kiran ta da Mama sai Atika ta ukku muna kiran da Yaya, sai Aysha wato Umma itace cikon ta huɗun".




Zama akeyi na haɗin kai dan basa faɗa ko kaɗan idan ka cire Mama wadda take da zafin kishi da son abun ta da nuna nata_nata ne, ga shegiyar rowar tsiya, gashi itace da manyan "yaya a gidan, sam sauran halin su ya ban banta dana sauran mutanen gidan, haka yaran ta duk halin ta sukayo dan duk ta ɓata su.


Yaya ma cikin yaran ta Mama ta ɓata mutum biyu saboda suna zama a ɗakin ta ne, Yaya kullum cikin nasiha take da nuna masu halin da suka tsira bai da kyau, mata ne su gidan wasu zasu amman inaa.. Duk wanda yayi nisa baya jin kira"






Nice ta fari a gurin Umma dan haka ban samu kulawar ta ba ko kaɗan dan ni sai da na yi wayo nake yarda da cewar Umma ce ta haifeni amman sam ni bana yarda a tunani na Inno ce ta haifeni dan ma Inno tana yi mani yaƙi a gurin Umma tana amsar mani abu koda rabo ne na cikin gidan idan Umma tayi rabo, to nawa sai dai Yaya ta ɗaukar mani ko Inno amman ita bata cewa ga nawa, Umma bafulatana ce, kunya ne da ita ba ta wasa ba, kasan cewar bana samun kulawar ta ne Baban mu, ya maida ni ɗakin Inno.




A cikin gidan mu nice, wadda Allah ya ɗora soyayya ta a cikin zuciyar mahaifin mu, komai ya samu Narjeesah baya son gani na a ciki damuwa koda kuwa kaɗan ne, bawai yana fifita ni bane aa dai duk abunda ya samu nice zai kira na kaiwa duk wadda take aiki, gashi na taso da masifa ga faɗa sam bana yarda acuce ni, idan aka kaiwa Umma ƙarata, bata kula mutum sai dai mutum ya gaji da tsayin sa yayi gaba, sai da mutane suka fahimci cewar Inno ce, inna ta, kawai sai suka daina kaiwa kashe dina, idan Baban mu yana nan sai dai ya bada haƙuri ya ce, na daina ba kyau.


Baban mu ya Auradda da manyan mu, su Anty Basira su ukku har sun haifu daga mai biyu sai mai ukku, sai maganar Auradda su Anty Shamsiyya da Zuwairah da Hanan wanda suka bani shekaru biyar, wato shekarar su ashin ni kuwa sha huɗu ke gareni ke nan.


Wata ranar laraba ce, Baban mu zai tafi kasuwan cin sa, a ranar na tashi bani da lafiya, duk bana jin daɗi kuma ban san abunda yake damuna ba, yau rakiyar Baban mu naji ina son yi haka nabi sa harda su yaya Auwal wato babban Yayan mu na ɗakin Inno.




Tun da muka isa tasha Baban ne yaja hannu na gefe yake tambayar mike damu na nace, masa babu komai kawai dai ban san abunda yake yi mani ciwo ba, kuma ni jin nakeyi bani da lafiya.




Ya ce, "Allah sarki Narjeesha ki yi hakuri halin Umman ki nata ne, ba aro tayi ba, ki rage damuwa da abunda takeyi maki na rashin kulawa wata rana zata sauya, kuma ki sani sirrin ki naki ne kada ki yarda ki sanar da wani abunda yake damun ki ko ya sameki, ko waye kada yasani, indai ba wadda ta haifeki ba, taso jin damuwar ki, kada ki faɗa kiyi ƙoƙarin ganin mahaifin ki ta janyo ki a jikin ta, kuma ina son ko miye ta fara sanin sa kafin kowa ya sani, dan uwa itace Babbar masoyiyar mutum ta nan duniya, saboda haka kije kiyi ƙoƙarin ganin ta saurari kukan ki, ko ba a yan zan ba".






Ni kam saboda ƙuruciya ta, sam ban wani fahimci komai ba, daga cikin maganar sa, addu'a kawai nakeyi masa ta Allah ya kai shi lafiya ya dawo dashi lafiya, haka su Yaya Auwal addu'a ce, sukayi masa, muna tsaye har motar su ta tashi ta tafi, sannan muka dawo gida, zuwa marece, su Yaya Auwal suka dawo, cikin tashin hankalin ni kuwa dama ina kwance bani da lafiya jikina rawa, yakeyi har sai da Inno tayi marufa, Yaya ce ta kira ta ta fito kowa yana tambayar lafiya, kawu Bala ne ya shigo shima cikin tashin hankali, ya ce, "sai haƙuri Malam Isah sun sami hatsarin mota, motar da suke ciki babu wanda ya fita, sun ƙone ƙurumus! ".




Faduwa wasu daga cikin mu sukayi atake gidan ya kacame da kuka, ni kam fito wa nayi ana biyar layi ɗaya bayan ɗaya, na ce, sam wannan maganar ba gaskiya bane, ni ban yarda ba, ruɗewa nayi kamar wata mahaukaciya, somewa nayi, ban sake sanin kaina inda yake ba sai da safe.






Tunda na tabbatar da cewar gaskiya ne, Baban mu ya mutu shike nan nadawo kurma bana magana bana cin abinci kullum cikin kuka sai da aka haɗani da addu'a aka samu nadawo dai_dai tun daga wannan ranar ne Mama ta fara rigimar gado itada su kawu dasu goggo, amman saboda babu wanda ya goyi bayan hakan sai aka bar maganar.








Tunda muka koma makaranta daman burina bai wuce nayi karatu mai zurfi ba, boko da islamiyya har na ce sai nayi aiki saboda karatu, shi yasa bana fashin zuwa makaranta, gidan mu da unguwar mu sai suyi ta dariya wai sai sun ga yanda zan yi karatun mai zurfin tukun, ni kuwa sai nayi ta masifa, amman makarantar islamiyya idan ban haddace karatuna ba, malam Nura ne ke zuwa ya saka ni gaba, sai naje makarantar, idan ba haka ba bana zuwa.




A lokacin da nake shirin shiga jss 3 ne na haɗu da wannan iftala'in tare muka tafi makaranta nida su Hanan wanda suke ss2 a lokacin shikerata sha biyar ne, sai da muka gama jarabawar mu, muka fito misalin ƙarfe biyu da rabi na rana, bani mance wa munyi jarabawar Maths ne duk mun gala baita, ajin mu shine na ƙarshe da fitowa, na fito ina tafiya ni ɗaya a bakin titi duk nagaji yunwa nakeji kawai na zo zan raɓa wasu motoci da suke a gefen titin saboda idan nabi ta gaban motocin zan hau titin ne kuma mashin zai iya bigeni ko mota ko keke, gashi yau sam hankali na ba kwance yake ba.




Na wuce mota biyu lafiya lau nazo a mota ta, ukku, kawai aka kamani aka jefani cikin mota baƙa itace ta ukkun, rufewa kawai akayi a kaja motor da ƙarfin gaske, ihu na zun duma, kafin na rufe baki har an watsa mani wata, powder a take naji garin na juya mani, zuwa can sai bacci ya ɗauke ni.


Ban tashi falkawa ba sai a wani gurin, tare da wasu mutane manya_manya,




Wasu kuma malamai ne dan naga littafai ne a gaban su suna karatu, da sauri na tashi zaune ina dube_dube,


Nidai ganin nakeyi ba'a gidan mu nake ba, wasu matane suka zo inda nake, da sauri naja da baya sai ji nayi antaro ni ta baya, da sauri na juya na ɗaga kaina wata matar ce, zata kai sa'an Inno, da sauri na dun ƙule jiki na guri ɗaya, wannan matan ne suka riƙoni sai cikin wani ɗakin a gaban wasu limamai ina jin sun fara magana,




Sai naji sam wannan ba hausa irin tamu bace, dan hausar su bata fita kamar Umma na.




Mutumen yace, "yarinya kiyi hakuri ki anshi jarabawar ki, idan kina son ki tsira da mutumcin ki to ki yarda a ɗaura maki Aure a yanzun idan kuma bakya son wannan Auren anshrya maida ke karuwa, to ni kuma mutumen daya turo nu yace, kiyi hakuri ki anshi wannan Auren dan kuwa mukam mu sai da mukayi istahara akan Auren kuma munga babu wata illa idan kin yarda da ƙaddarar Allah to ki ashi Auren nan da hannu biyu ".


Kallon sa nayi na ce, "bawan Allah kadubi girma Allah ka tausaya mani ni marainiya ce kuna ƙaramar yarinya ce!"




Murmushi mutanen ya yi yace, "shekarun ki nawa ne yan zun? ".




Da sauri nace, "sha biyar".
Ya ce, "shin kin mance, cewar NANA Aisha yardar Allah ta tabbata a gareta, shekara nawa akayi mata Aure? Shin ke nan ke a yanzun uwa ce ko? To kiyi hakuri ki ɗauki Auren nan kada ki bari ayi zina dake".






Kalamai masu shiga jiki akayi mani, dole na yarda na amshi sadakin dubu sittin aka ɗaura Auren wanda nake jin kamar wuta aka ɗaura mani a jiki tashi sukayi bayan sun gama saka mani albarka da adduar kariyar Allah da wasu ruwan addu'a da suka bani, nasha ina kuka, suka fita, wasu matan ne suka kawo mani wani abun kamar zuma da kuka na nake sha saboda muguwar yunwar da nakeji ga tsoro ta ko ina, bacci ne ta ɗauke ni ban sake sanin inda kaina yake ba.



A cikin wani ɗaki mai duhun gaske na tsinci kaina, hannuwa na a ɗaure haka ido na da baki na, na rasa ya ya numfashi na zai iya fita a sauƙaƙe.




Jin motsi nayi a kusa dani, a take nayi yun ƙurin guduwa, kawai naji an janye mani ƙafa, na faɗi ƙasa Ashe akan katifa ne, ƙafa ta aka raba biyu, aka ɗaure a wani gurin da ban san miye ba, sai kawai naji saukar mutum a jiki na, Ashe ma ko kayan jiki na an cire, hannu na duk suna a ɗaure haka nayi ta dukan mutumen amman ina koda ba a ɗaure nake ba ƙarfin mace dana namiji ba ɗaya ba, kawai ya afka mani.






Tabbas wannan itace baƙar rana a gareni yau nice akayi wa fyde tabbas babu wani bam banci wannan fyde ne! .






Sai da na kusa sumewa aka ƙyaleni, zuciya ta naji tana batun bugawa, naji duniyar ta isheni naji na tsani kaina da kowa ma na cikin duniyar nan!.




Bayan wani lokacin haka aka sake afka mani, haka dai nayi ta kukan zuci wanda yafi wuta zafi, da ƙuna, bayan kamar wani lokacin sai naji an fita, kuma an dawo, sautin murya naji, kamar haka:-






"Yarinya badan mace ɗaya bace, tsari na ba dana, ajiye ki koda a wani guri ne, kodan wannan abun da nayi maki, amman yanzun ga kuɗi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads