Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 58708 words

Chapter 12 - NARJEESAH Book Complete Document By Nana Khadijatu .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

a gurin Umma akan maganar da ta shafi Anty Narjeesah? "


Dariya Nusaiba tayi tace, "kaima yau Anty kake cewa Anty Narjeesah? to ai kuwa zaka sha labarin Anty Narjeesah ko Umma? ".




Tashi Umma tayi tabar gurin, Nusaiba tasa dariya ta ce, "Umma ki zauna mana muyi labarin harda ke".




Umma ta ce, "Auta kema kinyi koyi da halin Amrah ko? Allah idan kika dameni sai na fasa maki baki"Umma na gama maganar tayi tafiyar ta.


Dariya sukeyi banda Salman da yayi murmushi yana kallon Nusaiba.


Nusaiba ta nisa, ta ce, "am yauwa Anty Narjeesah da Amrah basa nan yau kwanan su biyu da tafiya".


Da sauri Salman ya ce, "what...! Kina nufin cewar da Auren nawa ta je wani gurin kuma harda su kwana ba tare da neman izini na ba? ".




Sakin baki duk sukayi suna kallon Salman cike da mamaki, shi kuwa masifa yaci gaba dayi, Nusaiba ta ce, "ikon Allah to yan zun dan mutum yayi tafiya kawai sai a kama masifa, kamar yana gurin ashe dai nikam zan ga irin hakan da ido na biyu, to kai inda a gaban Umma ne hakan zakayi ta masifa mai laifin daban wanda akeyi wa masifar daban? Nikam gaskiya ba zan iya zuwa gidan ka ba".




Dariyar ƙurciyar Nusaiba sukeyi harda Salman ɗin Nusaiba ta bala'in bashi dariya amman kuma haushin Narjeesah yake ji taya zatayi masa wasa da Aure bayan ta zauna har a gano inda Shuraim yake, ya ɗauke su ya tafi dasu gidan Mai martaba, amman wallahi idan ta dawo sai ta raina kanta.




Muhseen ya ce, "harda wannan Yayar taki a kayi tafiyar kuma yaushe ne zasu dawo? "




Nusaiba ta ce, "nima ban sani ba amman idan sun dawo zan sanar daku, dan inda suka tafi babu service ".




Dafe kai Salman ya yi yace, "ok yan zun ko kin san garin da suka tafi da gidan? ".




Nusaiba ta ce, "nifa daman ban fiye zuwa wani gurin ba, ina zama ne tare da Umma na, shi yasa ake cewa na cika shagwaba, dan bana son nayi nesa da Umma na, a toh".




Dariya sukayi Salma kuwa ta ce, "Amman zaki zo bikin Aure na, dan har anfara shagalin biki, maganar ganin Shuraim da Maman sane da ɓatan Shuraim ne ya saka na dai na zama, yau saura kwana biyu ɗaurin Auren kin ga kuwa, ya kamata a ce matar Yaya Salman tana kusa, yanda zata ga kowa kuma tasan kowa kuma kowa yasan ta, amman tunda bata nan ita da Amrah ke kizo ayi dake sai ki wakilce ta".




Shiru Nusaiba tayi, Muhseen ya ce, "bafa sace ki zamuyi ba, kin ga da Antyn mu tana nan ai nasan da zaki zo ko? ".




Dariya sukayi Salma kuwa ta ce, "ki kirawo muna Umma mana".




Nusaiba tare da Umma suka fito Umma ta zauna, Salman ya ce, "Umma dan Allah ana bikin Salma ne shine nake son ki bar Auta taje dasu Humaira wannan bikin dan Allah ".




Murmushi Umma tayi tace, "babu damuwa ai Nusaiba ƙanwar kuce, zata je, amman ta cika laƙuwa da yawa, sai kunji ta bakin ta, ta yarda da kanta, dan gudun kada sai an shirya tafiya ta ce, ita ta fasa zuwa".




Dariya sukayi Nusaiba ta ce, "Umma zanje ai".




Sunyi farin ciki suka tashi sukayi masu sallama suka tafi suna fita Nusaiba ta ce, "Umma ba zani ba wayau ne nayi masu, gudun su dameni da magiya".




Dariya Umma tayi tace, "ai kuwa dai sai kinje kije kiyi shiri dan ina ga gobe ne tafiyar ".


Zum ɓuro baki Nusaiba tayi tana shura ƙafa, Umma kuma ta share ta.




A ranar su Salman suka dawo fada inda fadar take cike da mutane 'yan biki direct cikin gidan suka shiga sharp_sharp suka shirya aka soma hidimar dasu harda iyayen su duk suna a gurin da sauran yan uwa na gurin mahaifiyar su na can ƙasar London wato dan gin Mom ke nan.






Amrah ce ta gama shirin ta na zuwa royal hotel da shigar ta ta kece raini, tana fito wa, na soma yi mata iya shege, "wow kaga Hajiya Amrah ikon Allah Hajiya Amrah babbar mace, kai Allah dai yaja da kwana, matar babban mutum".




Na ƙarasa maganar ina dariya, kwaɓe fuska Amrah tayi ta zauna tace, "Anty Narjeesh wallahi zaki daina ko na fasa zuwa ma ".




Ummey ce ta fito tana dariya ta zo ta dafa kafaɗar Amrah tace, "ke kyaleta kinji Amrah na, indai dan wannan abun ne da takeyi maki sha kurumin ki, ai Daddy Shuraim ne zai shigar maki wannan rigimar ".




Ai kuwa a take na haɗe rai na ɓata fuska, suna kallon fuska ta suka soma dariya Amrah harda dafe ciki, ta ce, "yauwa Ummy kin kuwa bani satar amsa, Anty Narjeesh ta Yaya Salman ".




Da gudu nayo kanta, ai kuwa ta fita gidan da gudu sai gurin mota, ina dariya suka fita ni kuma na shiga gurin wankan ina fitowa nayi kwalliya na saka shadda ta ash color na fito, turare na feshe jikina dashi na fito da mayafi na, a hannu, makulin mota Ummey ta bani ta ce, "ke kiyi amfani da wannan kuma ga Ashiru nan yana jiran ki tun ɗazun".




Ansa nayi ina godiya na fito da sauri Ashiru ya tar yeni da fari ar sa, muka gaisa muka shiga ya jamu sai royal hotel, inda mukayi parking anan ne naga motocin wannan matan da masu basu kariya wato masu tsaron su, murmushi nayi, na Ashiru ne ya buɗe mani motar na sauko na fara taku, duk inda nabi na wuce, idon mutane, akaina jin nakeyi kamar na ɗora hannu na akai na fasa ihu Amman na dake na shiga gurin waya na kira Amrah ta ɗaga, ta ce, na ƙaraso.




Gurin Amrah na nufa, su kuwa da ido suka bini duk da kuwa ko wace, idon ta na a wayar ta amman hankalin su yana a kai na, murmushi nayi kujera Amrah ta ja mani na zauna da bisimillah, lemo ta bani na ansa na ce, "na gode" na ajiye na kalle ta a goggo hannun ta, ta kalla nayi murmushi na ce, "kinyi ta jira na kuma kinyi ta kiran waya ta, am sorry wani abun ne ya taso mani shi yasa ban samu lokacin ɗauka ba, ko na kira ki, to ya labari ina fatan kin nemo mani tarihin ko wace yarinyar ce? ".




Murmushi Amrah tayi, ta bani wani envelope na ansa da sauri zan buɗe Amrah tace, "kiyi a sannu mana, kibi komai a hankali zaki fi fahim ta ".




Kallon Amrah nayi, nayi mata murmushi nace, "da ace kin san yan da zuciya ta takeyi a halin yan zun da baki ɓata bakin ki ba, akai".




Buɗewa nayi ina duba bayanin komai sai da na kai ƙarshe nace, da sauri "ƙarfe nawa ne yan zun pleace ".




Ta ce, "shidda da kwata"


Cikin zafin nama na tashi harda gudu nake haɗawa nafi ta sai gurin Ashiru da sauri na ce, kayi sauri muje, da sauri na sanar dashi titin da zai kaini ai kuwa da mugun gudu yaja motar muka fita, tafe muke da gudu ina duba a gogon hannu na, wani irin burki ne Ashiru ya taka, da sauri ya fito ya buɗe motar nima na fito ina duba agogon hannu na, a take na soma masifa, "haba wannan wane irin hauka ne kasan kuwa irin barnar da kayi mani yan zun, kasan mota nan bata da lafiya kabari na fito da ita, da ba sai na shiga wata, motar ba, gashi yan zun ka sakani cikin damuwa ba zan same suba, oh sheet! "






Na dafe goshi sai go and come nakeyi, wayar Amrah na kira, tana ɗaga wayar nace, sun bar ƙasar sai nan da sati biyu kuma zan sake ganin sa, dan haka zan koma gida ne, sai na sake shiri, zasu haɗu dani ne, kiyi mani bucking ɗin jirgi zan bar garin nan da daren nan kawai! ".




Kashe wayar nayi na dawo nayi jin gene jikin motar, ina dafe da goshi na, naji an doka mani uban horn, kallon gurin nayi bayan motar mune na ɗauke ido na, naci gaba da cizon yatsa.




Fitowa sukayi suka nufo ni, dafani ɗayar tayi na ɗaga ido cike da mamaki ina kallon su ɗaya bayan ɗaya, murmushi suka sakar mani, ɗayar kuma ta kawo ruwan swan ta bani, masu sanyi kamar ba zan ansa ba, amman kuma sai naga sun kafeni da ido na ansa na buɗe robar nasha, ina ajiyewa na fara sauke ajiyar zuciya.




Murmushi suka sakar mani a tare, sai ɗayar ta bani hannu tace, "Sarah ko kuma kice, Mrs Naseer".


Ɗayar ma ta ce, "Nafisah ko kuma kice Mrs Nazeer".




Ɗayar ta ce, "Zeenat ko kuma Mrs Yaseer".




Ta ƙarshen ta ce, "Mrs brr or haulman nice duk faɗin ƙasar nan mai wannan Sunan, couse suna ne dana mijina, am naga kamar mijin kine yayi maki halin nasu na maza rashin gaskiya, amman nikam miyasa kikayi masa wannan saken da yawa har haka? ".




Kallon ta, nayi da kyau ban ce dasu uffan ba.




Dai_dai isowar Amrah, daket nace dace, "Nice meet your's sorry fa kunga ina cikin damuwa amman idan na rage damuwar sai mu haɗu daku yan zun zan koma gidan miji na ne ".




Murmushi suka yi, Mrs barr, tace, "idan ba zaki damu ba zan so muje dake gida na, duk da ni bana barin ko wace, karya tazo mani gida ke harda, wannan da kike ganin mu a tare dasu kasan cewar tare mukayi karatu dasu, kuma mazajen da suke Aure fitattu ne, a ƙasar nan shi yasa ƙawan cemu yakai har wannan lokacin gashi duk halin mu ɗaya illah wannan da kikaji ta sanar dake sunan ta Mrs Yaseer amman duk da hakan bata shiga hurumin da banata ba, so ke naji ina son kije gida na ki futa kafin na baki wata mafitar wadda zakiyi mani godiya ina fatan zaki karɓi wannan buƙatar tawa".




Ban ce da ita uffan ba, har sai da suka haɗa baki gurin roƙo na, nace dasu, haba, taya zan biki gidan ki, wata kila ma mijin ki yana, gida, idan dai har dan shi kika hana kowa zuwa gidan ki to ya zakiyi da ni nida baki san inda na fito ba? ".




Kallon_kallo suka shiga yi, sai sukayi dariya, Nafeesa tace, "a yanda kika mutu da kishin mijin ki, har kika biyo bayan sa, kika kashe kuɗi gurin neman labarin sa, to duk wani namijin baya a gaban ki, kin ga kuwa koni ce zan iya yarda kibi ni har gida na, bani da shakku a kan ki".




Dariya nayi na ce, "ok to ku dai yi mani wannan hakurin idan nadawo zuwa jibi zan sauka a gidan naki, koshi dan naji zaki bani mafita ne kawai, kin san akan mijina babu abunda ba zan iya ba".




Cikin farin ciki muka rabu dasu tare da musayar number, motar Amrah nabi, muka tafi airport koda mukaje muka shiga daga ciki, muka bi ta wata ƙofar Ashiru muka gani, ya ɗauke mu a mota sai gida.




A can gidan Umma kuwa sai da Umma tayi da gaske san nan Nusaiba ta yarda tabi Jafar da Aliyu Humaira da Hindu suka nufi gurin bikin Salma suna tafe, suna yiwa Auta tsiya su Jafar na tare mata, ita kuwa ta kyalesu ta turo baki gaba, ita ala dole fushi takeyi dasu.






Zaune nake ina, yiwa Ummey yan kan farce, Amrah nayin game a waya ta, kira ya shigo da sauri Amrah tace, "Anty Narjeesh Mrs Nazeer na kiran ki ".




Dariya nayi na ce, "kyale ta soma kira" kiran ne ya ƙara shigowa sai da ya kusa tsinke wa na ɗauki wayar na kara a kunne na, ta ce, "sai Mrs Nazeer uwar gida kuma Amarya daga ke ba ƙari".






Cike da wani irin farin ciki ta ce, "ramki ya daɗe ya kike ina fatan dai komai ya zama dai_dai, ina nufin kin rage jin haushin kowa ".




Dariya nayi na ce, "da sauƙi dai kam amman har yan zun ina jin haushin wasu".




Ta ce, "to share kawai madam gobe ne zaki zo ko? To ki zo da yam ma, saboda Mrs barr taje unguwa amman zata dawo gobe kasan cewar a hotel ta sauka kuma jirgi zata, biyo ko kuma kizo gida na kawai idan ta iso sai na saka direba ya kai ki ko ya kika gani ne? ".




Murmushi nayi, na ce, "kodai na bari a ƙara kwana biyu saboda bani son na takura wa kowa gashi ita bata nan ke kuma na zo na ɗaura maki nauyi".




Dariya tayi tace, "ina ma zaki zo tun yau ai da naji daɗi, wallahi".


Dariya kawai nayi zuwa can na ce, "sai goben dai Mrs Nazeer idan na sauka a airport kizo ki ɗauke ni, amman fa tare da wannan yarinyar zan zo sai ki ware muna ɗakin da zamu sauka gudun haɗuwar ta, da mijin ki, kin san mace, komai ƙuruciyar ta namiji na iya ƙyasawa da ita, dan kin gan mi nan akwai zafin kishi ".






Ajiyar zuciya ta sauke tace, "to sai kin zo babu damuwa ni nasan gurin da zan ajiye ta, kuma zanyi wa Mrs barr magana nasan ba zaki samu wata matsalar ba indai akan wannan ne".




Sallama mukayi naci gaba da aiki na, haka kuwa tun da safe ita ce, ta tayar dani daga bacci, dole tasa na tashi muka fara shiri tare da parking ɗin kayan da zamuyi amfani dasu, zuwa tara da rabi Ashiru ya zo mukayi sallama da Ummey muka nufi airport, zuwa ƙarfe sha ɗaya na kira Mrs Nazeer ai kuwa da farin ciki ta zo ta ɗauke mu sai katafaren gidan ta, duk ma'akatan gidan nata maza ne sai "yam mata, masu ƙananun shekaru daga sha biyu sha ukku suke nan,






Wani haɗɗen falo, kafin kace wani abu har an cika muna gaban mu da abinci irin da ban_daban, sai da muka futa sannan muka ci abinci da abun sha, wata yarinya ce, ta kira tazo, ta durƙusa ƙasa idon ta a ƙasa tace, "gani ya shugaba ta".




Dariya naso nayi amman na dake, Mrs Nazeer ta ce, "jeki ki kai wannan baƙuwar can kusa da part ɗin ku kuma duk abunda take buƙata ki tabbar mata da kin yi mata shi, kada ki yarda ta nemi abu ta rasa".




Da sauri ta gyaɗa kai, tashi Amrah tayi taja trolley ɗin mu tabi bayan wannan yarinyar, mu kuma muka saka fira inda take tambaya ta, labari na da suna na, nayi dariya na ce, "to yan zun ya ke nan Mrs barr ta ce, kada na yarda ku rigata jin wannan ".




Dariya ta saka ta ce, "kai wato dai wannan Haulman ɗin ta riga mu a komai kuma tafi mu sa'a to mun yarda maji daga baya, amman kin san wani abu kuwa".




Gir_Giza mata kai nayi, ta ce, "kin ƙara burgeni fa, wallahi, saboda tun yanzun kin fara riƙon sirrin mu, tun da gashi Haulman bata kusa kin faɗi sharaɗin ta, ɗaya daman haka muke so, shiya sa, har yan zun muke tare da Mrs Yaseer saboda tasan komai namu sirrin mu babu wanda bata sani ba, amman har ila yau bata taɓa fitar da sirrin mu ɗaya ba, a gurin kowa, dan haka kici gaba da hakan ".






Dariya nayi muka ci gaba da fira, har sai da Mrs barr ta kira ta ce, mu ƙaraso gidan ta, ta dawo tun ɗazun tana fatan dai Mrs Nazeer bata san komai a kai na ba"




Dariya mukayi haka muka bi ta gurin ɗakin da aka kai Amrah gurin akwai nisa da inda muke, kanar ba gida ɗaya ba, muka kira ta muka fita da direba ta haɗamu tare da sha tara ta arziki, na ce ba zan amsa ba, Amrah ta matsawa ita ce ta amsa, mukayi sallama, direba ya ɗauki hanya sai gidan Mrs barr, him to ai sai naga gidan Mrs Nazeer ba wani gidan bane tun lokacin da muka iso bakin get ɗin gidan nake ji wani irin bugun zuciya sai da na rufe ido da addu'a ɗauke a baki na muka lula cikin gidan, get ukku a na huɗun ne muka tsaya, da sauri wasu ma'aikatan gidan suka zo suka buɗe muna.




Kallon Amrah nayi naga duk a tsorace take sai da na dafata nayi mata murmushin ƙarfin hali sannan ta, fita nima fita nayi baki na ɗauke da addu'a kayan mu aka amsa aka shiga dasu, muka ma muna biye da masu yi muna iso har cikin gidan, faɗar haɗuwar falon ɓata lokaci ne .






Muna isa tsakiyar falon kamar ance mu kalli gurin tv turus mukayi muka zaro ido waje cikin rawar murya na ce..........






*Comment and share*


*Ummu Ihsan ce*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹




💐💐 *NARJEESAH* 💐💐




*Rubutawa*
*NANA KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_




3️⃣6️⃣⏯️4️⃣0️⃣

➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Cikin rawar murya na ce, "Amrah kin ga wani irin surprise kuwa, wannan tar ba haka, kai am very happy fa, har naji na rage yawan damuwa ta".


Ba komai bane a burin photon mune nida Amrah a lokacin da muka haɗu a royal hotel haɗuwa ta biyu muna murmushi a jikin photon an rubuta, *your welcome pretty and friend* da zaiba, kula ga flowers masu masifar kyau a gurin.






Kallon gurin kawai mukeyi, mun shagala da kallo, takun takalmi ne, na jiyo a bayan mu, ana sauko wa daga step juyowa mukayi, da murmushi ɗauke a fuskar mu, itama da murmushi ta ke tafe, tayi shiga ta kece raini.




Ta ce, "ku ƙasa ku zauna mana kamar wasu baƙi?"


Bayan mun zauna ne a saman manyan kujerun gurin da suka kusa make falon duk kuwa da irin girman sa, bayan mun gaisa ne kukun tane ya fara kai komo a gurin, abinci dana sha kamar hauka, har sai da nace, ya isa hakan, muka ɗan taɓa kaɗan, bayan mun ƙarasa ne

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads