Header Ads
Showing 12001 words to 15000 words out of 58708 words

Chapter 5 - NARJEESAH Book Complete Document By Nana Khadijatu .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

"Anty Narjeesah tun lokacin da muka tun karo garin nan kike ciki ƙunci da damuwa, kuka kuwa tun a cikin mota kike yin sa har zuwa lokacin da muka shigo cikin gidan nan, miye shi wannan damuwar da kukan kuma ta ya ya kika san garin nan kika san gidan nan batare da sanin muba".




Shiru nayi jin wannan tambayoyin masu kama da saukar kibau a ƙirjina na, kuka na saka suka ishe ni da tambayar da ƙarfi na rufe ido na cike da masifa nace masu, Gi... Da... Na... NE nan halak malak!.




Duk suka tashi tsaye suka gir giza kai suna faɗar, gidan kine kuma? ta ya ya zaki faɗi hakan ..?








*Comment And Share*




*Ummu Ihsan ce* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


💐💐 *NARJEESAH* 💐💐




*Rubutawa*
*NANA KHADEEJATU*
*_UMMU IHSAN_*


*ELEGANT ONLINE WRITERS*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_




9⃣⏮🔟
➿➿➿➿➿➿➿➿➿ Nace dasu babu ko shakka wannan gidan nawa ne, kuma Abu na biyu da zan sanar daku shine bazan ƙara amsa maku wata tambayar ba dan gane da wannan rikitaccen al'amarin, saboda dalilin masu yawa".




Amrah ta ce, "Anty Narjeesah ki sani mune 'yan uwan ki baki da kamar mu a nan duniyar Umma kuma itace ta haife ki baki da wata uwa a duniyar nan wadda ta dace da tasan sirrin ki bayan ita, kasan cewar babu wani bare a cikin mu, miya sa ba zaki iya sanar da mu sirrin kiba?".




Kallon Amrah nayi cikin matsanan cin kuka na ce, "Amrah" duk ku kun yarda da cewar Umma ce ta haifeni amman ni har yan zun ina da shakka akan hakan, miyasa kuka damu da damuwa ta bayan wadda ta can_can ci da tayi mani irin wannan tambayoyin ko fiye da hakan sam batayi ba! "




Umma bata sona, da Umma tana sona da tun kafin na san kaina ita na fara sani, saboda miye zan sanar da sirri na ga wanda bai son jin hakan!? "Amrah Nusaiba "ku jini da kyau wallahi kamar yanda tun farkon lamarin ban sanar da kowa ba, to yan zun ma, baya ga sanar daku cewar wannan gidan nawa ne ba zan ƙara cewa komai ba, akai har sai ranar da Umma ta buɗe bakin ta, ta tambaye ni da kanta, tana son sanin gaskiyar lamarin ni kuma nayi alkawarin a ranar ko ɗigon gaskiya bazan ɓoye mata ba! "




Duk sai suka maida idon su akan Umma wadda tayi kamar bata gurin kamar bata san mike faruwa ba, gyarawa Shuraim kwanciyar sa ma takeyi.


Gir _giza kaina nakeyi kawai na wuce su naje na kwanta akan kuje ɗaya na rufe ido na.




Nusaiba ta ce, " Umma dan Allah ki.. Kallon da Umma tayi mata ne ya sakata yin shiru, Amrah ma ganin yanda Umma tayi wa Nusaiba itama sai taje ta kwanta, haka muka kwana kowa babu daɗin zuciya.




Tun da mukayi sallar asuba bamu koma ba, da garin ya soma haske muka tashi muka soma gyara gidan, Amrah da Nusaiba ganin irin dukiyar da aka zube a gidan sai da suka tsorata kasan cewar mu a gidan talakawa muka tashi kuma ƙauye, Umma dai har yan zun bata ce damu komai ba, ko cikin dorowa da zamu saka kayan mu cike muke da mamaki har dani saboda kayan da muka gani, zanen gado ya kai bakwai, kuma shaddodi atamfofi les matiriyas iri daban_daban.


Rufewa mukayi mukaje muka ajiye kayan namu a inda suke sai dai muka gyara komai, bayi da muka shiga duk sai da na koyar dasu komai muka fito.




Nusaiba ce taje ta koyar da Umma komai akwai ɗakin da ban buɗe ba wanda bani da niyar buɗe sa, ko kaɗan bana son kallon ƙofar ɗakin.




Sai da muka gama, muka shiga cikin kicin ɗin muka gyara ko ina, store ne na buɗe gurin yayi uban datti sai yanar gizo_gizo, attishawa kawai mukeyi, windo muka buɗe gurin ya ɗauki haske ta ko ina kuma na kunna glub, buhu huwan shinkafa muka gani da kwalayen taliya da indomi da kus_kus da semo cike muke da mamaki wanda su kansu su Amrah sun tabbar da nima ina cike da mamaki.




Amrah ce ta ɗauki taliya ta ɗebi indomi ta fita, mu kuma muka gyara muka goge muka rufe, girki Amrah ta ɗora a rishon da muka zo dashi, ɗaki muka nufa kowa yayo wanka sai da muka fito Amrah taje tayo Nusaiba ce ta zubo muna taliyar mu ukku, Umma ita ɗaya, shuraim shi ɗaya ai kuwa yaƙi ci ya dawo jikin Nusaiba ya zauna yana ci, sai muka gama ne muka wanke kayan da muka ɓata muka fita yawon duba gari amman bada Umma ba.




Haka mukeyi kullum har muka saba da gidan da unguwar muka daina jin tsoron komai.




Watan mu ukku yau a garin nan duk mun ciko mun murje sam bamu da wata damuwar hankalin mu a kwance, shuraim ya cika shekara ukku cif sai shegen surutu kamar Aku.




Zaune muke a kujera muna labari mu ukku Shuraim yana jikin Umma yana yi mata kukan shagwaba, ita kuwa ta biye masa tana lallashin sa.


Dariya mukeyi Amman ƙasa_ƙasa gudun Umma ta san su muke yiwa dariyar,ƙwan_ƙwasa get ɗin ne aka soma yi, muka saurara muji nan ne ko kuwa, sai da muka tabbar da nan ɗin ne muka soma kallon_kallo, Umma ta ce, "a dubo mana kukayi Zaune".




Tashi mukayi muka shiga cikin ɗaki muka ɗauko mayafi, muka fita da gudu Shuraim ya kama hannu na, muka fita, a lokacin duk ana ƙwan_ƙwasa ƙofar buɗe wa mukayi, "yam matane su ukku a tsaye, da murmushi a fuskar su, hannu na basu nace, "Assalamu Alaikum" muka gaisa dasu, haka su Amrah sukayi masu.




Dariya sukayi, ɗaya tace, haba "yan uwa sai kubar mu a waje, ba zakuyi muna karramawa ba irin ta baƙin ku ba? ".




Murmushi nayi nace, na ɗauka tambaya kukeyi ne shi yasa Amman kuyi hakuri ku shigo daga ciki".




Tare muka shiga dasu har cikin falon suka gai sa da Umma, nace su zauna bayan sun zauna ne Amrah ta kawo masu ruwan sanyi suka sha.


Bayan sun shane ɗayar wadda tayi magana ɗazun tace, "Suna na Aysha Umar" da sauri muka kalli juna, duk suka bimu da ido suna kallon mu.




Tace, "sunan nawa babu daɗi ko? ".


Da sauri nace aa keko mai babba suna kiyi hakuri zamu kira ki da Humaira dafatan bamu ɓata maki suna ba".


Dariya sukayi dukan su, tace, "ashe babba suna ne to na yarda".


Ɗayar kuma tace, "ni kuma Hindu" ɗayar kuma tace, Halimatus Sadiya".


Humaira ta ce, "mu ba baƙi bane a unguwar nan ba, kuma yan zun haka ana cikin hidimar bikin Hindu ne, to da an gama da sati ukku sai bikin Halima, ina fatan daku za'ayi komai dan muna yawan ganin ku kuna zaga unguwar nan bakwa shiga gidan kowa".




Dariya mukayi nace insha Allah zamu halarta, ni ce Narjeesah wannan ƙanwata Amrah itace ke bina shekara biyu na bata, sai Auta Nusaiba gata nan ".




Suka ce wow, "wannan big boy din fa? .


Amrah ta ce, "yaron Anty Narjeesah ne".


Humaira ta ce, "my boy yaushe zaka zo gidan mu ne? ".


Dariya yayi kawai bai ce dasu uffan ba gurin Umma ya komawar sa.


Fira mukayi sosai sai da la'asar muka rakasu kowace har ƙofar gidan su, gida muka dawo mukaci da har kar gaban mu kwata_kwata mun manta da maganar bikin da aka gayya ce mu, sai ranar kamu, su Humaira suka zo gidan mu ni kuma ina sama a kwance kaina ke ciwo Umma suka gaisa da ita, suke tambayar ta, "Umma kodai kece kika hanasu su zuwa bikin nan" .




Umma kuwa ta ce, "aa rufani ku sayani yaran nan, ku shiga ciki ita tana nan amman Amrah da Nusaiba sun fita da Shuraim na aike su".




Da sallama suka shigo cikin ɗakin, zaune na tashi Hindu sai harata takeyi, dariya nayi na ce, "afuwa Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida".




Dariya sukayi Hindu ta ce, "idan na kashe ɗan masu gida ai ke ce zaki fara bada shawarar a kaini kotu a ɗaureni ko kuma ki fara yaɗani a duniya".




Dariya duk mukayi, na ce, "dan Allah kada kuce komai wallahi mantawa mukayi yau kuma kaina ke ciwo "




Hindu ta ce, "wallahi babu wani batun hakuri sai kin tashi mun tafi.




Dariya mukayi dole na tashi na ɗauki gyalena daman ban wani daɗe da fitowa wanka ba na saka kaya amman banyi kwalliya ba, ciwon kai kawai yafi damuwa na, fitowa mukayi Umma bata nan tana ɗakin ta, na shiga nace "Umma zan tafi bikin can idan sun dawo su sameni a can dan Allah ".




Ai kuwa Umma bata ce dani komai ba, har nagaji da tsayi, na juya zan wuce ke nan ta ce, "Adawo lafiya kuma a kula da kyau".


Jin tayi shiru da sauri na jiyo ina kallon Umma wadda taci gaba da aikin gaban ta kamar ba itace tayi magana ba.




Cike da farin ciki na fito gurin su nace muje, tafiya mukeyi amman zuciya ta sai mai_maita addu'ar Umma takeyi farin ciki kawai nakeji wannan shine karo na farkon da Umma ta taɓa yi mani abunda nake so, kuma nake mafalki.




A gidan su Humaira muka sauka gaskiya Maman Humaira da yan uwan ta, basu da matsala gasu dai masu kuɗin gaske amman basu da wulakanta mutane, a ɗakin Humaira muka yada zango hum Humaira kam badai gayu ba, budurwa ce "yar gayun gaske nikam akan gadon ta na faɗa nayi kwance, yan mata kuwa gayu kawai suke ɗauka, Halima ce ta dube ni ta ce, "Narjeesah ki tashi ki gyara zamu gurin saloon ne fa kuma ke kin wani kwata, dolene fa ki ajiye ciwon kan ki a gefe sai angama biki ehe".


Dariya mukayi nace, waye zai iya ajiye ciwo ke mu banda abinki? "


Tace, "to kisha magani kuwa" kallon ta nayi na ce, "ke kisha mani maganin mana idan kin sha mani zan warke".


Dariya ta saka mani tace, "malama ki fito fili kawai kice bakya shan magani nafi gane hakan".


Dariya mukayi dukan mu, duk kowa yana gama gyara wa, Angon ya kira waya yace, "a fito ga motoci nan.




Tashi mukayi zamu fita, Humaira ta janye ni ta maidani ɗakin ta, ta zaunar a kujerar madubi ta ɗauki kayan kwalliya ta soma yi mani dariya kawai na keyi nace, Humaira nifa bana kwalliya sam".




Tace, "haba malama ai kuwa tunda kina tare dani dole sai kin iya dan ni jinki nakeyi kamar uwa ɗaya uba ɗaya muke, to waima ni kam haka kike zama ba bu kwalliya kamar ba mace ba? "




Dariyar Hindu muka jiyo a bayan mu tana faɗar da kyau my Humy wallahi yi mata raɗau da kwalliya ".


Jefe ta nati da marfin foda ai kuwa da gudu ta fita tana dariya.


Sai da Humaira tayi mani kwalliya mai kyau bamai yawa ba, mai tarkace, muka fito Halima ce ta dube ni ta ce, "wow ko kefa malama Narjeesh, wallahi kin fi kowa kyau a gurin nan harda Amaryar, jakar hannun Hindu na amsa na jefe ta dashi da gudu ta fita tayi waje".


Maman Humaira ce ta ce, "Allah dai ya shirye ku, kuyi ku tafi dan Allah kun bar mutane nata jiran ku".


Amrah da Nusaiba ne suka shigo da sallamar su, da sauri ƙanwar Humaira ta kama hannun su, suka shiga cikin gidan Humaira kuma ta ɗauki Shuraim suka fita muka bisu a baya, gidan su Hindu muka nufa inda motocin ƙawayen Amarya duk sun shege motoci mu kuwa, wata haddiyar motar ce, muka nufa, Halima ce ta shiga gidan gaba mu kuma muna gidan baya harda Amaryar".




Tunda muka shiga cikin motar babu wanda ya ce uffan, Halima kuwa fira sukeyi da mutumen, har dasu dariya sukeyi, mu kuwa har muka ƙarasa ba muyi magana ba.




A bakin wani haɗaɗɗen guri suka ajiye mu, kawai muka shiga ciki gurin salon ne da gyaran jiki, wanke kai kawai da ƙafafun mu akayi muna muka fito suna ɗaukar mu sai holl muku nufa duk an ƙawata shi, ta ko ina yaji gyara sosai, shiga mukayi gurin na zauna a kujerar da aka tanadar wa manyan ƙawayen Amarya nida Humaira da Shuraim Halima kuma suke ƙara gyara wa Amarya, haka akayi komai da zamu koma Angon da kansa ya ɗauke mu muna tafe suna fafa tawa da Humaira, yana ce mata azzaluma ita kuwa tana ce masa zata saka a ƙara masa sati biyu, mukam dariya mukeyi.




Halima ta ce, "to kai idan ta saka aka ƙara sati biyu ka ce abokin ka ya ƙara wata biyu sai ayi bikin ".




Dariya mukeyi harda Angon da sauri Halima da Hindu suka ce "ƙarya kike yi ai kin mafi Angon zumuɗin bikin tunda yau saura kwana ishirin da biyu".


Shiru tayi, nidai suna burge saboda na lura suna ƙaunar junan su, Halima ta ce, "nifa wallahi banƙi jinin a ɗaga wannan Auren ba".


Humaira tace, "komai abun ki Aure kamar anyi sa an gama ne".




Muna isa gidan aka fara kiran sallah da sauri muka fita daman ƙofar gidan su Humaira muka sauka muna shiga cikin gidan naja su Amrah muka tafi gida, tun da safe sai gasu Humaira mukaje gurin kitso da lalle akayo muna, tunda muka dawo gida, hima dai akeyi tare damu, aka ɗaura Auren aka kai Amarya ɗakin ta.




Alhamdulillah anyi biki lafiya an gama lafiya, sai himar bikin Halima ta kunno kai bamu dai wani futa ba, rabon cimgam muka tafi, munsha yawo muka dawo munje gurin saloon mun dawo sai dai wannan bikin za'ayi dinier banyi niyar zuwa ba, amman ganin du sun ɓata ran su dole na yarda zanje harda ankon bikin akayi muna mu duka kuma bada ko naira namu ba.




Kallona Humaira tayi tace, "Nikam har yanzun banji kin sanar dani komai ba kina da Aure ko babu ina Baban Shuraim amman fa ban ce dole sai nasan komai a kan kiba, kada kiyi fushi idan har wannan abun sirrin kine dan Allah kada ki sanar dani kinji Narjeesh? ".




Dariya nayi ban ce da ita komai ba tace, "na fahim ta, amman nikam bari kiji, Narjesh kin ganni nan kwata_kwata bani da saurayin da nake saurare saboda na tsani yau dara, duk wanda yazo guri na sai na fara tambayar sa miye ya kawo sa guri ba da zarar ban gamsu da baya nin mutum ba nakan da katar dashi, shi yasa aka ce korar samari nakeyi ".




Dariya nayi nace "mutum sai Allah kinji Humaira Allah ya kawo maki miji na kwarai musha biki, ranar nice kan gaba ".


Firar mu mukeyi muna aikin gyara kayan miya tunda akayi abinci muka baiwa mutane tare da Hindu muke komai shirin zuwa gurin dinier mukayi sosai, nikam duk sai naji kamar kar naje, amman duk sun hana ni suna tsare dani, da nace zan je na dubo Shuraim sai Humaira ta ce, "Shuraim kam yana gurin mijin Hindu wato Aliyu".




Cike da mamaki na ce, "kuma ya yarda yaje gurin sa? ".


Hindu ta ce, "to da miye nufin ki malama? Ai Shuraim yaron mune ba naki ba".


Dariya kawai nayi na ce, "Allah yaron baida yarda ne kun dai san halin sa ni mamaki ne nakeyi".


Dariya sukayi, motoci aka kawo muka tafi, tafe muke ni dai ba zan ce ina jin daɗin wannan dinier ba ko akasin hakan.




A gurin dinier ma kujera na samu na zauna nesa dasu saboda yanda naga wasu yam matan nayi abun baiyi mani ba, Humaira ce ta zo inda nake tace, "Narjeesh wallahi kin bani wahala ina ta neman ki kizo ku gaisa da Angon dan ya iso shida manyan abokan sa harda wani babban baƙon sa naji ana faɗa".




Oh Humaira ke kinje kun gaisar ne nikam, tace, "ban jeba tare zamu je dake nima bada son raina nake son zuwa ba saboda ban wani saba da wannan angon ba, Aliyu munfi sabawa dashi, kuma shine ya aiko Hindu ta kira mu ".




Tashi nayi muka Jera muna tafiya sannu a hankali kamar wasu marasa lafiya Hindu ce ta taryemu tana dariya ta ce, "wai lafiyar ku kuwa twins sister na? Naga duk jikin ku yayi sanyi".




Bamu bata amsa ba, taja hannun mu sai gurin mijin ta, yana ganin mu ya taso yazo ina muke ya ce, "haba dan Allah kuje ku gaisa da Angon da abokan sa mana, kuma munada babban baƙo amman yana can gurin saboda yan mata ya koma can".


Ni kuwa nace, "hala ma mayen mata ne shi?"


Dariya sukayi ya ce, "kai wannan ai babu wata mace a gaban sa sai matar sa, muje kawai ".


Mere baki nayi hannu na Shuraim ya kama yana tsalle_tsalle gurin Angon da abokan sa mukaje muna ganin Angon muka gaisa, dashi ya amsa ba yabo ba fallasa abokan sane suka fara tsokanar mu, bamu biye masu ba, har mun juya zamu wuce Angon ya ce, "Humairah kuje ga babban aboki na can gurin ku gaisa dashi".


Ba Humaira ba ko ni da naji yanda ya kira sunan nata sai da muka jiyo da sauri muka kalli junan mu, kai tsaye nace, "ai ba sai mun jeba saboda mutane sunyi yawa ni zan ma koma can baya na ɓuya Humaira kuje ki gaisa dashi".


Kai tsaye ta ce ba zan je ba, Angon ne ya nuna rashin jin daɗin sa a fili yace, "ok nagode da karramawar da muka samu a gurin ku".


Hannu na dana Humaira Hindu taja tace, to honey muje ka raka mu naji kace jami'an tsaro ne dashi".


Harda Angon tare muka tafi muna tafe, Shuraim yana riƙe dani, 'yan mata muka gani sai iyayi sukeyi, wasu har gurin sa suka nufa amman an hanasu su ƙarasa gurin, mu kuwa muna tafe nace, "Hindu Humaira banga fa Halima ba wai tana ina ne? ".


Humaira ta ce, "wallahi tun ɗazun nake neman ta, harda wayar ta na kira bata zuwa, duk shi yasa na

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads