Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 58708 words

Chapter 2 - NARJEESAH Book Complete Document By Nana Khadijatu .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

magagganu take saki wanda babu wanda yasan manufar ta, shi yasa kowa ya fita iskan ta.






Da yamma zuwa ƙarfe biyar bayan anyo wankan marece ni kuwa ina gyara wa, Su Yayan mune duk suka shigo cikin ɗakin Inno su takwas duk maza mata ukku masu Aure da sauran wanda basu da Auren da ƙanen mahaifin mu da matan sa harda yaran sa duka, duk sukayi tsaye suka zuba mani ido.




Ni kuwa na saka kayan da Yaya ta fito mani dasu harda hijab na ɗauko mai zan shafa ke nan, sai na saki man domin na shiga tashin tsananin tashi hankalin wanda ba'a sa masa rana, gashi mutanen duk fuskar su a haɗe take, Goggon muce ta shigo cikin ɗakin a har gitse ganin yaron a hannun Inno kawai cikin fushi tace.....








*Comment And share*






_*Yin comment din kune zai bani amsar karɓuwar littafin*_


*Ummu Ihsan ce* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹


💐💐 *NARJEESAH* 💐💐


*RUBUTAWA, DAGA ALƘALAMIN:-*
*NANA KHADEEJATU* *_UMMU IHSAN_*




*YA ALLAH KAJIƘAN IYAYE NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SADA SU DA RAHMAR KA ALLAH KA SANYA SU DAGA CIKIN DAUSAYIN ALJANNA ALLAH DASU DA DUK KANNIN YAN UWA MUSULMI BAKI ƊAYA AMIN YA ALLAH*




*_BISMILLAHIR RAHMANIN*


*3&4*


➿➿➿➿➿➿➿➿


Tace, "wannan wace irin masifa ce? A gidan ɗan uwana akan "yar da yafi ƙauna a rayuwar sa, wannan shine ake kira da baya ta haihu ke nan! An maida gidan Yaya na gidan tara shegu, Narjeesah sai da kika ɓata sunan gidan nan, to wallahi ba zamu ɗauka ba, yan zun nan zamu ɗauki mata ki akan abun da kika aikata, kuma duk wanda yake da niyar aikata makaman cin irin abunda kika aikata, idan yaga hukunci da ya hau kanki sai ya gyara idan yaso yin hakan! "


Kawu Bala yace cikin masifa, "ai dama na daɗe da yanke hukunci shiru kawai nayi tagama haife abunda ke cikin ta, to bari kuji hukunci da na yake ku a gurin ku ya yi kuwa ko kuna da ja acikin sa? Yau ɗin nan za'a raba maku gado kowa ya kama kansa wanda suke da yawa kuma suke da abun siyen gidan nan ko kuma sukaci gidan nan su zasu zaune shi, saura kuma kowa ya kama gaban sa! "


Ai kuwa da sauri Mama tace, "nida yara na mun yarda ku tambayi sauran yaran da kanku kada kubi ta iyayen su dan zasu hana su ƙwatar "yan cin su".


Zuciya ta nake jin kamar zata fito daga cikin ƙirjina, sai dafewa nayi ina karanta duk abunda yazo baki na.


Su Yaya Auwal suka ce duk abunda kuka yanke bamuda ja, da a bata muna sunan gida, gara kowa ya kama kansa"


Su Basira murna kamar su zuba ruwa ƙasa su sha, Inno dai kallon kowa takeyi yaran ɗakin ta sam sun nuna basu son ayi hakan, Amman ɗakin Yaya idan ka cire Yayar da yaron ta Mudarsir sune kawai basu yarda ba, sauran kuwa duk sun yarda mu kuwa muda ba'a bakin komai muke ba ba a bi ta kan muba kawai suka fita aka kira dillalai akayiwa gidan kuɗi akaje aka duba gonar Baban mu, suka je gurin malamai akayi rabon, muda muke zaune a gidan su goggo da Mama da sauran su Anty Asma dasu duk suna kasa sun tsare sunƙi fito cikin ɗakin, har su kawun suka shigo gidan.


Kiran Umma na akayi da ƙanne na a take kawu ya fara magana wadda ban san ranar da zan iya man tawa da ita ba, yace, "to an raba maku gado daman nasan shi su Narjeesah suke jira ita da Umman ta, dan hakane suka tsiri ɓatawa gidan nan suna, to Allah ya fiku, ga abunda kuka samu dubu ɗari biyu da saba'in ku dukan ku, yan zun sai kuzo ku bar gidan nan ku kwashe kayan ku, yau_yau ɗin nan nake buƙatar kubar gidan nan! "




Inno tace, "wannan wane irin rabon gado ne haka da rana tsaka, kuma kuce ga abunda suka samu bayan baku sanar da abunda kowa ya samu ba? Wallahi wannan ba adalci a cikin sa, indai ba zalunci kuka tsaro ba".


Cike da masifa akayo kan Inno wadda su Yaya jafar suka dakatar tare da faɗa, "sufa bazasu ɗauka ba kuma gaskiya Inno ta faɗa"


Rigima ce aka sanya kowa ya faɗi albarkacin bakin sa, Yaya tace, "kowa a sanar dashi abunda ya samu dan gaskiya nima ban yarda ba".


nan dai aka ce, Mama mai "ya"ya maza su shidda mata ukku sune sukaci rabin gidan duk girman sa, Inno da take da "ya"ya maza biyar mata hudu, taci kusan rabin gidan kaɗan aka rage ɗaki ɗaya da zaure, sai aka baiwa yaron Yaya ɗaya wannan ɗakin da Zauren, sai aka koma gona, inda muda sauran su Yaya aka rabawa gonar.


Umman muce ta shigo cikin ɗakin ba tare da tayi magana ba, kawai ta bashi hannun ta, a take duk suka zuba mata ido shi uban gayyar kuɗin ne ya watsa mata, wanda duk muka zaro ido waje muna kallon wannan wulakancin.




Umma tace, "nagode sosai fa" Sannan ta dubi tace "Inno mun gama shirya wa ga su Amrah can suna fitar da kayan mu ina ga ma sun kusa kwashe wa dan basu ɗaya bane harda yaran, unguwa zamu tafi duk wanda muka yiwa laifi to yayi hakuri".


Babu wanda yayi magana daga cikin su, Umma ta dubeni tace, "Ke! kuma ki tashi ki baiwa masu gida gidan su ki fito ga mota can tana jiran mu".


Kafeni da ido Umma tayi wanda a tarihin rayuwa ta shine na farko haka zalika a tarihin rayuwa ta wannan shine maganar da Umma ta taɓa yi mani a cikin mutane jikina sai rawa yakeyi, ashe bani ɗaya ba, duk wanda yake gurin yasan Umma yau anyi mugun cika ta, dan ita sam bakajin bakin ta koda kuwa kashe ni za ayi a gidan mu kuma bata taɓa yi mani magana ba, koda a cikin ɗakin mune ballema acikin mutane.


Tsaye tayi, har sai da ƙanwata Amrah tazo a gaban Inno ta tace, "Inno bani ɗan albarka na nan gurin abun sona farin cikin rayuwar mu wannan yaron da kike gani ya shige a cikin zuciya ta, yaron nan daga gani mujaheed ne dan zaiyi taimakon addinin Allah da taimakon mutane, shi daga ganin sa ba zaiyi aiki da jahilci ba kuma, bazaiyi aiki irin na jallai ba".




Dariya Inno da Yaya sukayi dan kowa yasan Amrah ta sakar wasu kawu Bala magane, Inno tace, "amman kuwa kin zaba masa sunan da ya dace dashi dan Allah ki riƙa kawo mani shi ina son shi wallahi har cikin raina, Allah sarki Allah ya rasa rayuwar musullunci" amin aka faɗa.


Yaya tace, "kice dai a riƙa kawo muna shi duk da muma cikin satin nan zamu bar gidan nan amman ni kun san gidan da nake dashi wanda na bada haya a can zan koma, dan Allah ku riƙa kawo muna shi Allah ya rayasa Allah yayiwa rayuwar sa albarka Allah yasa ya zamo farin ciki a garemu baki ɗaya amin ".




Amrah ta ansa ta goya shi,Nusaiba na shigowa ta raɓa kowa tazo ta kwashe kayana da suke ɗakin Inno ta rufe jakar ta riƙa hannu na tabi ta gaban Umma dani muka fita, Inno ta share hawayen idon ta, tazo ta anshi kuɗin wanda kowa ya kasa ɗauka ya bata, ita ta ɗauka ta baiwa Umma, Umma ta ce, "to mu yafi juna Allah yasada mu da alkawarin sa"




Fita Umma tayi ta duba ɗakin taga babu komai tayi murmushi ta juya zata fita Inno da yaran ta, da Yaya da yaron ta suka rako Umma har gurin mota, Inno ta dam ƙawa Umma kuɗin wanda ta ɗaure da leda, Umma ta amsa, ta shiga cikin motar, mu kuwa a lokacin muna ciki, ga mutane ƙofar gidan kamar rana duk kuwa da cewar magriba ce, sai da motar ta tashi muka ɓacewa ganin su .




Umma ce ta kalli Amrah tace, "Amrah kin sheda masa inda zai kai mu ko? "


Amrah ta goge hawayen da takeyi tace, Umma na sanar dashi amman Umma kina ganin su kawu Habu zasu yarda mu zauna a gurin su kuwa? Kin fa san halin sa da zafin zuciya ga rashin fahimta Umma ni wallahi tsoro nake ji".




Umma dai kallon su kawai tayi ba tare da tace dasu uffan ba.


Sai ƙarfe tara na dare muka ƙarasa unguwar su kawu Habu sai gaban mu ke faɗuwa, dan kowa a tsorace yake, sauka mukayi aka fara sauke muna kayan mu harda mai motar, Umma ta bashi kuɗin sa, muka shiga cikin gidan a tsakiyar gidan muka sami kowa da kowa, Kawu yace, "ina fatan dai ba cikin nan ne aka haife ba, kuma kuka dawo mani dashi gidan nan ku raine shi a gidana ba".




Shiru Umma tayi kafin ta ce, "kayi hakuri kawu, ka barmu mu kwana anan da safe zamuje mu nemo gidan haya sai mu koma a can kaga dare ne yan zun ".




Matar shi tace, "haka kawai zaku kwaso ƙafar ku harda kayan ku da shege ku zo muna gida cikin dare ai dai kwana ɗaya kika roƙa kuma shi zakuyi ehe! ".




Umma dai batayi magana ba, ɗakin aka bamu ɗaya har kayan mu, nidai ban samu na rimtsa ba dan nasan nice duk silar faruwar hakan, Umma ce naga ta tashi tayo alwala ta fara nafila, da addu'a yaron ne ya motsa wanda yake kwance a jikin Amrah da sauri ta tashi ta kawo mani shi tace, "dan Allah bashi yasha kin ga yaron akwai hakuri".


Ansar shi nayi na fara gir_giza shi amman kukan yakeyi fitila Umma ta hasko mani, tun da naga hakan nasan mi take nufi, gyara shi nayi na soma bashi, kawai muka jiyo masifar kawu Habu da matar sa, suna faɗar "wannan wace irin jaraba ce haba ya zaku sakawa mutane hawan jini ku hanasu kwana? Nifa wallahi idan naga kun cika damuwar mu muda moƙwota sai dai muce kubar gidan nan ".




Shikuwa bawan Allah harma ya koma bacci, suka gaji da masifar su sukayi koma ɗakin su.


Tun da aka fito sallar Asubahi, muka gaisa da mutanen gidan muka fita ko karya wa bamuyi ba, muka fara neman gidan haya, har ƙarfe tara na safe bamu samu ba kuma bamu ci abinci ba, gashi ina jego, ganin hakan ne yasa Umma ta sai muna ƙosai da koko muka zauna Zauren wani gidan muka ƙarya muka tashi muka shiga yawon neman gidan haya, ga baki ɗaya sai da muka bar unguwar sosai zuwa sha biyu na rana Allah yasa muka dace kuma gidan babu kowa cikin sa ɗaki biyu ne da kichin da bayi, shekara ɗaya dubu, talatin haka muka biya anan aka barni nida yaron suka tafi gurin kwaso kayan.


Zaune nake na buga uban tagumi ina kallon yaron wanda nake jin yan zun ina kaunar sa, to amman ya ya rayuwar mu zata kasan ce ne nida yaro na, zuwa gaba, har yaushe ne zan saka Umma na da yan uwana farin ciki?.




Jin ana shigo da kaya yasaka ni dawowa hayyaci na, kawai na tashi na baiwa Nusaiba yaron ta ansa ta goya sa, ni kuma na taya saka kayan Umma ɗaki ɗaya muka saka mata gadon ƙarfen ta da da wadurof din ta da mu kuwa a ɗaya ɗakin muka saka gado ƙarami da katifa ɗaya, waje kuma aka saka durom naruwa da tukunyar ƙasa.




Kichin Umma ta shiga ta gyara komai da komai, kayan miya ta fito dasu zata fara jajjage da sauri Amrah ta ansa ta ce, "haba Umma kibar shi muyi mana ai ke ya kama ta ace kin futa kawai".




Umma ta ce, "naga kun gaji da yawa kibar shi kije ku futa, taliya ce kawai zan dafa muna".




Dariya Nusaiba tayi tace, "Umma Allah ya raba mu da fu kina aiki muna zaune muna kallon ki da ran mu da lafiyar mu".




Dole Umma tayi dariya wadda rabon da muga dariyar ta tun kafin cikin jiki na ya bayyana sai yau dan haka kowa sakin baki da hanci ya yi yana kallon Umma, itama sai ta daina dariya ta zo ta wuce ni ta shiga cikin ɗakin ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa ta zauna, tashi nayi na shiga cikin kichin ɗin da kaina na fara gyara itace zan fura wutar Nusaiba tazo ta ansa tana faɗar kai Anty su waye suka taɓa barin mai jego na aiki, ai mai jego sarauniya ce ko ya ki ka ce, Anty ƙarama? ".




Dariya Amrah tayi tace, "wato dai ba zaki sauya mani suna ba ko? "




Haka dai suke ta bidirin su abun su, suna gama dafa taliyar suka ɗora mani ruwan wanka, suka zuba wa Umma nata mu kuwa suka zobo muna guri ɗaya abincin muka ci sai da muka ƙoshi Amrah da Nusaiba suka fita suka nemo ganyen bedi suka kawo mani suka kwashe mani ruwan wanka naje nayo kamar yanda su Inno suka fara yi mani, cikin zuciya ta nace Allah sarki ashe dai su Inno gata ne suke yi mani da suke yi mani wankan nan yan zun gashi nice nake yi da kaina.




Koda na fito Amrah ce na sama tana yiwa yaron wanka Nusaiba na ce mata, kiyi masa a hankali mana kada kije kisa sabulu ya shigar masa, ni wallahi inda nice nafi ki iyawa dan nataɓa yiwa Anty Basira wankan saifullah so da yawa".




ai kuwa nikam dariya na zauna ina yi masu bayan sun gama yi masa wankan aka zo gashin chibi, Umma najin ihun yaron da sauri tasa hannu ta anshe sa ta fara faɗa, "kashe ɗan mutane zakuyi ne waye yace maku da zafi sosai akeyi, dallah ku tashi ku bani guri nayi masa ni bana son hauka! ".




Ba niba hatta Amrah da Nusaiba sakin baki sukayi suna kallon Umma ni kuwa harda murza ido na keyi, fita iskan mu Umma tayi, kamar ba san mun tsare ta da ido ba, gashin tayi masa har sai da yayi bacci Amrah tace, "Anty kayan da zamu sakawa yaron nan fa? Dan naga kamar kala biyu gare shi "yan gobe suna".




Shiru nayi ban ce da ita komai ba, Umma ce ta tashi ta buɗe akwatin ta, ta ɗauko kayan jarirai har kala biyar kuma masu kyau da zanen goyo na saƙa da kayan sanyi saiti.






Cikin farin ciki Amrah ta kwaso kayan tana tsalle, ita kuwa Nusaiba sai rawar jiki takeyi zata saka mashi kayan da sauri Amrah tace, "nifa zan shirya masa bara na ɗauko masa pampas din sa wanda na ajiye masa".




Itama cikin kayan ta ta ɗauko pampas da wando na jarirai masu yawa da swafa da fula harda takalmi, itama Nusaiba tace ni dai bari ku gani, cikin kayan ta taje ta kwashe su, ta fara ɗauko mayukan shafawa da powder dasu turare ta kawo ta ajiye a gurin Amrah tace, "nima ga nawa kayan Baby boy a gyara muna abun mu mukam muna son shi".




Ni kam cike nake da mamaki ba kamar Umma da zan iya cewa wannan shine karo na farkon da ta taɓa yin abun da faran ta mani rai sabo duk wani abun da yake da dan gata da farin ciki na Umma bata taɓa yin saba, ni ada nama ɗauka Inno ce ta haifeni sai da Inno tayi da gaske san nan na yarda da cewar Umma ce ta haife ni dan ko ɗin kin sallah bata yi mani amman Amrah da Nusaiba da Mariya 'yar ɗakin Inno dan kala biyar_biyar sai tayi masu harda takalmi kala ukku, ni kuwa Inno tayi mani ɗaya sai kuma idan Allah yasa mutanen arziki sun yi mani dan haka duk kowa ya fini yawan kayan ado, wata rana kuma idan antashi yin ankon biki idan ta kai ayiwa su Amrah ɗinkin biki, nike zuwa na anshe turmin zane ɗaya, idan taji sai ta kaiwa Inno ƙarata Inno kuwa tace, tayi mani magana da kanta mana, to anan ne nake samu nasara akan ta.






Umma ce ta gyara masa tayi masa shiri mai kyau wanda abun ya yi ta bani mamaki, Umma kuwa basu yaron ta yi suka ɗauka suka fita, nima ina gama gyara wa, na fita cikin "yan uwa na ina kallon su na ce "Amrah Nusaiba " kun kam mala jarabawar ne ko kuwa?.




Amrah tace, Anty nifa na ajiye 'kara tun bokon nan kamar yanda kika ajiye jss 2 kallon ta nayi cikin jin haushin maganar ta nace amman kuwa bakiyi mani adalci ba, ai ni kinga tawa ƙaddarar ke nan, dan haka dan Allah kuyi karatun nan kada ku manta burina bai wuce nayi karatu mai zurfin gaske ba boko da Arabi amman ku dubi yanda na kasan ce, to dan Allah kuyi hakuri kuyi karatun nan kunji!?.




Shiru duk sukayi cikin tausayin halin da na tsinci kaina, sukayi mani alkawarin yin karatu.




Haka dai mukaci gaba da rayuwar mu, a can makaranta su Amrah suka jiyo maganar Auren da za'ayi nasu Yaya Auwal dasu Surajo dasu Shamsiyya da Zuwaira dasu Balkisu wanda duk suna gaba na wasu shekaru biyar suka bani wasu shekaru ukku, bikin wanda aka ce a sanar dani kada na yarda naje gidan naɓata masu biki, 'yan gidan mu suka faɗawa mutanen gari kuma da Mariya da kanta tazo har gidan mu ita da wasu ƙannen mu, suka sanar damu wannan maganar.




Ita dai Umma ta yarda taje gidan ita dasu Amrah inda suka dawo gidan kamar wanda aka koro.




Hawaye na gani a idon su Amrah cikin tashin hankali na buɗe baki zan tambaye su, kawai naga Umma itama kukan takeyi, da sauri naje ina tambayar Umma hawaye na zubar mani amman Umma bata ce dani komai ba, tabbas nasan babban abune ko miye, daket Umma ta buɗe baki tace........

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads