Showing 3001 words to 6000 words out of 46909 words
Chapter 2 - BAKAR IZAYA Complete Book by Ansholy .txt
muka bari dare yayi kana muka tafi
domin masu sa ido cikin ikon Allah da mukaje ba asamu wata matsalaba yasaya yabamu kudinmu
nawane ma alhaji hamza yace milyan 40 yauwa damuka amso munyi niyar mudawo gida aranar amma alhaji hamza yace saimun kwana to da daddare nida mlm sule mukai shawar gwara asai wani abu da kudin
A aje zaifi da ace kudin xamu taho dasu kana in ansaya saimuba alhaji hamza ajiya to da haka muka kwanta
Da safe muka samu alhaji hamza da maganar shima ya amince da hakan amma yace bazai amshi ajiyar ba
daqel muka shawo kanshi yayadda zai amsa amma saida yakira mai dakinshi yafada mata da yaranshi dan shekara goma
mai dakinshice tabamu shawarar gwara musai diamond haka mukaje muka sayo diamond din milyan 39 akabarman milyan 1 ahannuna
shine damuka dawo mukace zamu taho yace saiya biyomu dan asamu sheda muma awurinmu
yana zuwa nan yai shiru saida najima shiru domin ina ganin wannan kasace
Hakanan daganin mutum saika yadda dashi harka bashi ajiyar milyan 39
*Ansholly*😘
[3/8, 1:05 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ðŸ˜BAQAR IZAYAðŸ˜9
😘Ansholly😘
Wannan gangancine amma saina bar abin azuciyata nafara mgn to mlm amadu
Miyasa kasaida raqumanka nibaka fadaman ba saida yayi jim kamar bazai fada manba kana yafara mgn
abinda yasa nasai dasu shine kasan ni yata daya dije kana yanxu ta Allah takasance
kaina nasan yan uwana bazasu ba dije gadoba koda sunbata ba wani mai yawa zasu bataba
shiyasa nayanke shawar tunkamin ta Allah takasance agareni gwara nayi kyauta da dukiyar
saida sarkin yaqara gyara xama kana yace to dijar kaima kyauta da dukiyar taka indai har ita kaba
to kaima kasan kayi rarguwar dubara dan kana mutuwa yan uwanka saisun amsa
a,a ba ita nababa dan daxata haifa naba ko yarda zata haifa nabasu halak malak
to shikenan Allah yara basu da abinda ke cikinta lfy aka amsa da Amin mlm sule ne yace ya kamata akira dangin mlm amadu asanar dasu
haka aka aika kiransu amma saida mukacema alhaji hamza yatafi domin inhar sukazo suka iskeshi to zasu iya bigeshi su amshi diamond din
Kana mlm amadu yace kadda yasake ya qara zuwa rugarnan sai bayan shekara shabiyar lokacin komine ne dija tahaifa ya girma yana tafiya bada jima waba saiga yan uwan mlm amadu
koda nagama fada masu abinda yafaru karkiso kiga yadda suka rikice tamkar dukiyarsuce aka saida kanan baffanshi harda daukeshi da mari danjin haushin abinda yai
harda cewa indai harbaije yadawo da wannan dukiyarba to babasu bashi
shidai shiru yai yaqalesu baice uffanba har suka gama zage zagensu saka tafi da amshe raquminshi daya dayarage
Allah yaso basuji cewa yanada milyan daya ahannunshi ba dan bankai ga fada masuba suka fars zage zage
nasan da har ita saisun amshe nandai nabashi haquri da abinda yan uwanshi sukaimai
yace bakomi ai abinda yasa yasaida raquman bawai dan dije na diyar shi daya ba jiyai suna shawarar xasu kasheshi inya fita kiwo
shiyasa yai maza yaje yasayar naji tausayinshi sosai sukatashi suka tafi suma hakadai
rayuwa taita tafiya yayinda cikin dije yakai wata tara haihuwa yau ko gobe
[3/8, 1:05 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ðŸ˜BAQAR IZAYA😠10
😘Ansholly😘
ranar asabar da asuba dije tasauka ta haifi kyaikyauwar yarta wace hatta unguwar xoman data wanketa saida yarinyarnan tabata tsoro
dan kyan yarinyar yayi yawa amma datai wani tunani taga daga uwar har uban kyawawane shiyasa yarinyar tazama maikyau haka
da akaba iro karkiso kiga murnar dayayi yana godiya ga Allah dan kyan yarinyar firgitashi yayi
To aqa idar garinnan inhar matar mutum tahaihu dole yaje masallaci yafada haka yai alwalla yatafi masallaci cikin farin ciki
bayan angama sallah yace matarshi ta haihu tahaifi diya mace kamin yagama rife baki
Wani yace kace annoba tafito duniya wadda in akace uwarta nada ciki mutum yanayin asara ina ace anhaifeta
shima kamin yarife baki wani yaro yashigo massalacin dagudu yace adamu babanka ya mutu kamin yaran ya ida magnar nan adamu ya fece daga
Masallacin da gudu kamin mi wani yinquri wasu yaran suka kaqara zowa suka fadamana mutuwar mutum ukku hadda kakanki
mlm amadu
da gananfa mutane suka fara tsanar dije da iro haka akakai matattu har hudu gidansu na gaskiya yayinda mahaifiyarki dije har suma tai
hakadai akaita zaman gaisuwa yayinda mutane ko kallanki basuyi daga dije sai iro saikuma kakaninki matake daukarki wani abin mamaki tunda
aka haifeki baki taba koda rintse idankiba koda cikin dare idanki abude suke ranar da su mlm amadu suka cika sati guda aranar
tun cikin dare kike bacci kema aranar satinki guda aduniya abin yayima dije dadi dataga kina bacci danda duk atuna nunsu kobaki lfy
har anfara neman maki magani shiyasa duk yan rugarnan suka sani tunda aka haifeki kwana shidda baki taba bacci ba
wanda ansan jariri da bacci
to aqa idar rugarnan inhar mutum ya mutu to ranar daya cika kwana bakwai aranar zakiga
anata abin ciccika kamar anayin biki kuma har yanxu
ba adaina ba haka mata dayawa suketa kai abincin gidan mlm amadu
wani fura wani tuwo wani nono hakadai mutane keta shiga da qwarya an aje da anyi sallah la asar za ai addu,a lokacin bai ida karasawa ba
mukaji wuta takama agidan mlm amadu ga mata dayawa aciki dan aqalla matan dake ciki zasukai ashirin
muka tashi dankai dauki amma da mutum yatin kari wutar zakaga kamar ta biyushi haka munaji muna gani wutarnan tacinye mutanan ciki kaf ciki harda mahaifiyarki da matar mlm sule da matar marigayi mlm amadu da matar liman
saida mangariba tai kana wutarnan tatsaya batare da ankasheta ba gurin yayi sanyi qalau kamar bawurin akai gobara ba
haka mutane sukaita shiga cikin gidan amma inba tukaba ba abinda kake gani
Kakanki mlm sule sumewa yayi dan tashin hankali daman ga mutuwar amininshi bata sake shiba yanzu gashi matarshi
ta mutu wani abun mamaki ke kina kwance ba abinda yasa meki dan wasanki kawai kike da hannu wanki
*Ansholly*
[3/8, 1:06 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ðŸ˜BAQAR IZAYA😠11
😘Ansholly😘
sadaukarwa g limsy🌺 ina godiya da addu,arki
haka mutane sukaita magan ganu akanki wasu suna cewa keba mutum bace qilan diyar aljannuce domin kuta kyanki aka duba ansanke ba diyar mutane bane
haka dai mutane suketa magan ganunsu wani mai zafin zuciya abbashe dan gidan jamo shiya daukeki ya samu karmami ya kunna wuta
yaje zai sakaki ciki alokacin muna chan wajan qokarin ibu tokar mutanan da suka qune ihun mutum kawai mukaji muduka da sauri muka fito daga inda muke
Abbashe ne muka gani cikin wutar yanata ihu wuta tana cinshi muduka kamar anriqe mana qafa muka kasa zuwa inda yake harsai da yacinye wutar tamutu
kana muka iya zuwa wurin yadda muka ganki acikin gida kina gefe haka yanzuma muka sameki sai wasa kike da hannunki
tan bayar mutane mukai cewa miya kawoki anan kida keki cikin gida nansuka fara bamu lbr abbashe ne yadauko ki zai sakaki awuta yazo dai dai wutar
sai yayi kamar anjefashi ciki muza musama harda yarinyar taqone hakadai muka sallaci tuka muka tai muka rife aka dawo da wata saban xaman
ke kuma babanki iro yadauke ki yatafi dake gida domin duk dacewa mutum ukku ya mutu agurinsu to ba wanda yakoma qofar gidan anadawo wa
daga maqabartar kowa yakama hanyar gidanshi dan atunanin mutane yanxu kuma maza xa akashe tunda bida bine abun andauki maza sai kuma aka dauki mata to
Insuka qara zama suza aqara dauka shiyasa da aka dawo maqabarta mlm sule yagaba wanda yabiyo su saiyaja iro cikin gida
yafaramai nasiha domin yaga yafara yadda da abinda mutane kecewa akanki shin iro ka yarda diyarka yar aljannuce kamar yadda mutane ke fada
iro saida yaqara sinkuyar da kai domin jiyake shima kamarya hadi zuciya ya mutu dan rasa matarshi dayayi da mahaifiyarshi
kana yafara magana to baffa zata iya kasan cewa haka domin daga yadda mutane sukace ba ataba
haifar mai kyantaba duk rugarnan ni kaina yanzu tsoranta nake
dan kyanta kanshi abin tsorone ballantana yadda kuma taxa mamma mutane annoba ciki hardani dan nima nayarda annobace aka haifa man kawai yasa kuka
*Ansholly*
*08136195038*
[3/8, 1:06 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ðŸ˜BAQAR IZAYA😠12
😘Ansholly😘
Mlm sule zubama iro ido kawai yayi yana kallanshi saida yayi mai isarshi kana yaishiru
kana mlm sule yafara mgn iro kaban mamaki dahar dakai ake cema diyar daka haifa annoba kuma wai yar aljannu to inajin jinina ajikin yarka kuma nasan wannan
yarinya yarkace domin jini baya qarya da yarka bace da baxanji jininta ajikina ba kawai dai nasan da abinda Allah yabuye akan wannan yarinya
hakadai mlm sule yaitaima iro nasiha ta dai dai iliminshi cikin ikon Allah iro yasa duda yayda dake yarshice danda
da gaske kallan yar aljannu yake maki nan suka samaki suna hainan dan ba asa maki sunaba kuma yasan yanxu inyace atara mutane asa maki suna ba wanda zai iya
zuwa mlm sule ne yace iro ya dauko shanuwa guda cikin shanunshi ukku yanka maki na sunanki dan alqawari yai indai dija ta haihu saniya zai yanka mata dan haka kuda bata da rai bazai fasa wannan al qawarin daya dauka ba saida aka gama yankan shanuwar
kana suka kama tunanin waye xai soya mlm sule ne yace iro yaje gida zai bada akawo mashi shi yasamu wadda zaya turo tasuya
yana tafiya ahanya yagamu da uwale ita uwale ba yar rugarmu bace rugarsu nagaba datamu
uwartace ke aure anan shine tatahu da ita agolanci to uwale tunda taga iro taji tana sanshi amma shi alokacin baya takanta domin
dijen shice abun sanshi gaisawa sukai kana taimai gaisuwa yaji dadin gaisuwar da taimai domin tunda akaimai mutuwar ba
wanda yaimai gaisuwa
wasuma harararshi kawai suke yai mata godiya harzata wuce yatsaida ta
dan Allah uwale wani tai mako nakesan kiman
to Allah yasa zan iya dama baffane ya yankama hainan shanuwa to narasa wanda
zai suya man yancikin koxaki iya taima kaman ki suya man kamin gobe nasamu mai suyaman gangar jikin
saida tara zana dataji ance saniya aka yanka maki domin koni aka haihu gidana tumakai nake yankawa dan kinsan fullatani da shaninshi gwara
yaga tafadi ta mutu da ace anyankata uwale cikin saurin murya tace ta amince amma saitaje ta gayama innarta
bakomi saikin dawo dannasan lokacin har ankawo naman
kuda taje tagayama mahaifiyarta bata hanata ba itama dauko gyaletai tabiyo yar tata domin sunada san banza sosai
koda yaran da mlm sule ya aiko kawo naman yazo sai iro yace yafa dama mlm sule yasamu mai mashi soyen
haka uwale da mahaifiyarta sukaxo suka kama soye bayan angama sallah magarib iro yafadi
ansa maki suna hainan ba wanda yace mashi ko uffan
hakasu uwale suka gama soyansu suka tafi da alqarin gobema zasu dawo su ida sauran
haka kowa yake jininshi bisa akaifa har kika kai sati daya lokacin satin mahaifiyarki daya bata raye
kekuma satinki biyu aduniya amma tun bayan baccin dakikai kina sati daya aduniya baki kuma wni baccin ba
😘Ansholly😘
[3/8, 1:06 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ðŸ˜BAQAR IZAYA😠13
😘Ansholly😘
To abinda yasa mutane suka saki jiki shine da sukaga harkinyi wata ukku ba abinda yaqara faruwa
yayinda uwale tashi gema iro sosai tunyana shareta har yake yafara kulata domin yadda take kula dake
yanxu kuma yafara jin saukin yan rugar dan sun fara rage tsanar da suke mashi shida yarshi
haka baffanshi yaje ya neman mashi auran uwale ba asa bikin da nisaba domin uwale ta jima gida dan xata kai shekara 20
dan duk rugarnan ba tsaranta danmu yarinya nada shekara 13 muke aurar da ita
ansha biki lfy ankawo uwale gidan mijinta
ya yinda kike da wata tara kina tafiyarki ko ina
alokacin uwale tadaina kula dake saiki kashinki harya bushe ajikinki bata wanke ba har sai iro yadawo shi zaya wanke maki
ranar dazaki ciki shekara daya aranar kikai bacci
hankalin iro yatashi dan gani yake kamar abinda yafaru abaya zai kuma faruwa da assuba yatashi yai alwalla yatafi masallaci
dan sadda yaje ko liman bai samuba haka yatsaya har liman yazo iro lfy naganka haka cikin tashin hankali
bai iya boyewa limanba yafada mashi abinda ke faruwa
wanda yaci ace ya boye wannan abun acikin xuciyarshi danda bai fadaba ba wanda xaice
dan kincika shekara daya wani bala,i yafada mashi hakadai aka kira sallah
bayan angama sallah liman yatashi yafara gayama mutane abinda iro yafada mai
kana yace nafada makune dan kusan da zanchan dan kar abar mutane cikin duhu
nan akaita surutu kamar ba masallaci akeba wani cayake wallahi inhar tasake tataba mani wani nawa aradun Allah saina bajeta
hakadai iro yatashi yatafi gida jikinshi duk ba dadi domin saiyanxu yake dana sanin fadar dayai
yana zuwa gida bai daddara ba yaqara fadama uwale kamin tace wani abu taji sallama kobata fadaba tasan qananta ne tafito da sauri Audi
lfy nangaka tunda asuba gashi sai kuka kake
saida yaqarasa wani kukan
kana cikin kuka yace uwale inna ta mutu ihu tasaki wanda
saida yasa iro yaji tsoro yafito daki da sauri lfy uwale ita bata masan
miyake cewaba dan hanyar dakinshi kawai tai saidai kanantane kefada mai abinda yafaru ihun
hainan sukaji amma ko motsawa iro baiyiba dan yana ganin haka uwale kadai zatai tahuce abinda takeji
dan shima jiyake kamar yaje yai mata dan banxan duka saida uwale taga kinsuma kana taqyaleki domin duka tai maki bana wasaba
kamar tasamu wata abiyarta hakata dakeki ko tausayinki batajiba
alokacin data fito lokacin kuma wani yaro yashigo yafa dama iro mutuwar baffanshi
dagudu iro yafito daga gidan yai gidan baffanshi ita kuma uwale komawa tai dakin iro tadaukoki
suka tafi itada kananta saida sukazo dai dai wannan rafin da kuke ibar ruwa kana tasakeki ciki suka juya suka tafi
suka barki sbd tasan dole ki mutu koba kumi ke yarinyace baki iya ruwaba kuma tasan ba mai taimakonki
iro yaji mutuwar mahaifinsa wannan lokacin mutum biyar ne yamutu ciki harda dan liman hakadai muka kaisu makwancinsu
nikaina abin yafara bani tsoro hakadai nabar abin azuciyata
iro yaje yima uwale gaisuwa nan yake gaya mata yayanke shawarar kaiki bakin ruwa yadda aljanun zasu dauki abinsu
nan uwale ke fadamai aitun da akai mutuwar taje tasaki arafi bai wani damuba domin shi harga Allah
yadauka ke diyar aljannuce haka yai mata sallama yatafi zuciyarshi sawai dan jiyake yarabu dake dagashi har uwalan basu koma gida ba
sai bayan da akai sarakar bakwai kana iro yabi yama uwale suka tafi gida
uwale natura qofar dakinta tai arba dake kwance kina mata dariya
*Ansholly*
*08136195038*
[3/8, 1:06 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ðŸ˜BAQAR IZAYA😠14
😘Ansholly😘
Da gudu uwale tafito daga dakin tare da fasa wata irin qara nabani mlm wallahi aljana adakina
tanata kerma wanda har fitsari tasaki batare da tasani ba
Iro da sauri yafito daga cikin dakinshi lfy uwale kijifa yadda kika saki fitsari daga tsaye
bata masan miyake cewaba dakinta kawai take nunamai tanace wa wallahi mlm
aljanace cikin dakinnan da dai yaga bata cikin hankalinta sai yashige dakinta
dasauri yajawo qofar dakin yace uwale kikace kin yadda hainan rafi amma miyasa naganta ada kinki
cikin rawar murya uwale tace wallahi mlm nakaita rafi har saida nagata nutse kana nabaru rafin
shi kanshi qafafuwanshi karma suke dan ya tsora yana tunanin ko uwale bata kaiki rafiba yaci ace kin mutu
Koda baki mutuba kinji gata domin ko babbane aka bari da yunwa natsayin sati daya dole yajigata ballantana yarinya
yajuyo yakalli uwale yace uwale aradun Allah hainan ba diyata bace aradu diyar aljannuce
kamin uwale tai wata magana kika bude kofa kika fito ai daga iron har uwalan waje sukai da gudu
suna naiman taimako karo sukaci da yalwa qawar uwale tace lfy mlm iro daga kai har uwalan naganku haka
kedai bari yalwa lokacin da kikazo man gaisuwa bana fada maki najefa hainan rafiba to wai yanxu muna dawo wa
na isketa ada kina itama tadan razana amma dayake yar duniyace saita nuna bata tsorata ba dan ita har burni tana shiga
haba mlm iro karkaban kunya mana kamarba namiji ba yanxu dai mushiga ciki
haka suka bita suka koma ciki amma atsorace suke
haryanxu tsaye take inda suka barta yalwa taje ta daukeki kana tajuyo takallesu
tace uwale nasan da gaske kinsa hainan arafi amma baki tunanin ko wani yaje yacireta
Sadda zaki sata ke dawa kikaje nida audi kanena kuma nasanshi da tausayi
shima ne yaje yacirota dan shika daine yaga lokacin dana sata
mlm iro shiru kawai yai dominshi bai yadda ba in ance audine yaci rota to wake kawo mata abincin daza taci waya budema audi dakin uwale
maganar dayaji yalwa nayi ita tadawo dashi daga tunanin daya tafi
Mizai hana mudau hainan mukaita chan kusa da rigar innarki uwale kinga acan ba wanda
ya sanmu bare mu ajeta wani ya biyomu da ita saida uwale tai jim kana tafara magana
tace yalwa shawarki tayi amma karki mantafa chan aka haifeni taya xakice basu sanni ba
aibacane mutafi tare dakeba tare da mlm iro zamu tafi
to hakanma yayi yanxu kuimaxa kutafi kamin ai magriba tunda ankusa
haka suka fito suka tafi saida suka kusan xuwa rugarsu uwale kana suka ajeki amma saida sukaga ba kowa kana
sai ana sallah isha,e kana suka dawo duk wanda yagansu ya tambayesu daga ina suke sai yalwa tafada masu dan dama surutu gareta
Aikin santa ko kai kawai tadaga domin kuka kawai take
kana yaci gaba haka suka dawo ma da uwale albishir taji dadi sosai
dan tana ganin sunrabu dake kenan iro tashiyai yatafi yaje yai sallah su kuma
Suka aza zancen duniya dan daga yalwar har uwalan sallah bata damesu ba
yalwa batabar gidanba saida dare yayi sosai kana tai masu salama tatafi
domin mijinta yajima da mutuwa gashi batada ya
tunda asussuba mlm iro yaji bugun qofar gida da sauri shida uwale suka fito dan bugun bana wasa bane
suna budewa sukaga yalwa tsaye duk jikinta shatin bulala
da sauri uwale tace lfy yalwa naga jikinki duk shatin bulala saida yalwa ta qara fashewa da kuka tace wallahi mlm iro
Aljanaka haifa
kuyi haquri fans am busy wallahi amma next insha Allah xanyi mai yawa
*Ansholly*
[3/8, 1:06 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ðŸ˜BAQAR IZAYA😠18