Showing 45001 words to 48000 words out of 81184 words
Chapter 16 - Sirrin Daukaka Book Complete by Aisha JB .txt
zan nutsu Yarona na cikin mawiyacin Hali? Ki fad'a min Ummi taya zan samu kwanciyar Hankali yarona na gurin matar da tayi ikirarin saita kashe shi! wayasan me ta masa Yanzun, yaron da magana ma bai iya ba, Wallahi gwara da cikin Ya fita, wannan ai masifa ce Wallahi ki fad'awa lbrahim ya bani Yarona in ba Haka ba, Kotuce zata rabumu, Ya dawo min da Yarona, Har mari na yayi dan zan d'auki Aakif. ki kalli yadda ya shimfid'amin hannunshi jikina, Wallahi Bazan bar musu d'ana ba ki fad'a mishi Ya bani Yarona kafin Hukuma ta shigo ciki.." magana take tana jijjiga kai tare da cije baki tana son ƙwacewa.
"Naji kiyi shuru Zai baki d'anki Meya had'aku?"
"Saki uku yamin"
Zaman dirshan ummi tayi a K'asa "innalillahi saki d'add'ai har uku?" Hannu Halimatu ta d'ora akai tare da buga salati Hanisa dake baya tace. "Amma Uncle yayi asara!"
Halimatu tace. "Babbama kuwa" daƙuwa ummi ta musu "Zanci Gidanku" shuru sukayi Ganin doctor ta shigo dubata tayi sannan tace "Ki daina motsi me karfi jikin ki, ba ƙwari fa"
Kallon baki San mai nakeji bane Jiddah ta mata sannan ta d'auke k'anta "Zansha ruwa" nace inna sakin numfashi me d'auke da Hawaye ni kad'ai nasan Abinda nake ji, a zuciyata Doctor tace. "Ruwan d'umi zaku bata" Hanisa ta d'iba a cofin fulask ta bani, Karb'a nayi nasha kad'an Ajiye nayi sannan na sauka a hankali na nufi Band'aki.
Sai Yamma Nafisa ta dawo Gidan nan ta Ga Aakif shi d'aya a falo hawaye ya bushe mishi a fiska "a a Aakif mamma fa" kuka yaro yasa daga Zaune Yana Mika mata hannu domin Yunwa ta cishi sosai babu wadda ya bashi abinci d'aukar shi tayi zata nufi d'akin Jiddah taga fitowar Sa'irah Kofar ta gani Kulle cikin mamaki tace "Ke inna Maman Aakif?" Nan yarinyar ta fad'a mata yadda Akayi i'do ta zaro tana kallon Yarinyar kafin tayi magana wayarta yayi Kara, "Iyah" tace sannan ta d'auki Kiran "Assalamu alaikum Nafisa" cikin Girmama Nafisa ta amsa Mata Iyanmu tace. "Meke faruwa Ummi ta kirani wai Hauwa'u ta nufi Kaduna!" Cikin sanyi jiki Nafisa ta sanar mata komai salati Iyanmu tayi sannan tace. "Yayi kyau zai Gamu dani i'ta Kuma Zainab zata ga karshenta Sakamakon Yanzun tun anan Duniya Allah ke nunawa insha Allahu sai rabbi ya saka mata."
'Dakinta ta nufa da yaron shayi ta had'a mishi me Kauri ta d'aurashi saman cinyata kafin ta bashi ya fara Kokarin Karb'a, tana sanya mishi Kofi a baki da sauri Ya Karb'a Yana Sha yana sauke Ajiyan zuciya, wani i'rin kuka tasa ganin yadda yaron yake karb'an tia din a Yinwace. "Allah saiya saka maka" wani i'rin kuka ta fashe dashi kallon yadda yaron yake rik'e da Kofin tayi "Wannan wani i'rin son zuciyane yaro karamin za'a rabashi da uwarshi!" Aakif na gama sha ya sake kofin tare da qwala ihu Yana Kiran "Mamma.." mikewa tayi dashi tana jijjigashi Jumana ce ta shigo "Momy lafiya naganki da Aakif Aunti Amariya fa kofarta ƙulle?" Kallon yarinyar tayi sannan tace. "Kisa ruwan zafi ki masa wanka" ajiyeshi tayi domin ya fara barci ta nufi Band'aki tayi wanka.
Zaina ce ta fito bataga Yaron ba rik'e Qugu tayi tare da K'unduma ashar. "wani d'an shege da shegiyace ya d'aga yaro anan? Akan mutum yake da za'a d'auka?"
Nafisa ce ta fito daga d'akinta hannuwanta hard'e a baya, ta rik'e igiyan caji. "Nina d'aukeshi ko zaki dakeni ne, kaman yadda kika sa ya daki Yar mutane.." Hannun Zaina ta d'aga da niyar marinta da sauri Nafisat ta rik'e Hannun. "Ki nada tsaurin i'do ga shegen saurin Hannun Yanzun ke ki kalli tsaban idona Kice zaki mareni? Sa'arkice ni Zainaba?.." Zaina tace. "Ked'in Banza ked'in wofi wacece ke da baran dake ki, ba..." Kafa tasa mata ta fad'i K'asa "Kina cikamin ciki Zainaba Yau zanci ubanki harda uwarki zanga uban da ya d'aure miki tsuliya kike zuba mulk'an Gidana dan inna Miki shuru inna K'yale ki.." zuba mata wayar ta shigayi sosai Zaina ke ihu tana Kare K'anta, Mikewa tayi da sauri tana rik'e zaninta Fure dake tsaye tasa dariya. "Yar Banza Wallahi Nafisa baki burgeni ba, dakin fasa jikin shegiya.."
Zaburowa tayi tare da Rik'e wiyar rigan Fure "Ni ni kike fad'awa haka zaki gani zan miki abinda harki bar duniya bazaki manta ba, na barki na Yau!" Tureta tayi ta fad'i kallon Nafisat tayi. "Kin burge tunda har kika iya dukana Amma zakiga ladar dukan domin zan miki Babban Kyauta..." Wani i'rin dariya tasa harda hawaye tana mata kallon Tsana "Kaman yadda kika Zane jikina sena addabi rayuwarki, kaman yadda kika sani kuka, saina saki, zan Kashe ki da ranki, zan miki abinda kina jin kukan Amma zaki kasa Yinsa! Nice fa! Zainabu-Abu HahhhHahhh!!" Ta karasa maganar tana dariya kaman zautacciya.
"Bakince ke shed'aniya ba, insha Allahu babu abinda zan gani Wallahi Kaman yadda kike tak'ama da shed'an, Haka nake tak'ama da Allah Yanzun aka fara!" Kad'a kai Zaina tayi tare da shigewa d'akinta.
Yana dawowa ya shigo d'akinta. Yana kallonta ta saka kwalli a idanunta "Muazzan ni Nafisa ta duka dan nace ta bani Aakif harda zagin iyayena ni ta Zane har tana ikirarin saita Kashe ni akan ka saki Hauwa'u-Jiddah, Taci min mutumci ni Wallahi ka sake ta, daman nace zan Bata ladar abinda tamin ko ka, saketa Kona bar maka Gidanka..." Jikina rawa yace. "Dan Allah Zaina kiyi hakuri wallahi zanyi yadda kike so" takarda ta wurga mishi "Zana mata d'aya Kuma ka karb'o Aakif ka kawo min!" Dauka yayi da sauri zama tayi tana murmushi Yana Gamawa ta Sashi gaba, Zaune tayi akan Kujeran falo shi Kuma Yana K'asa Fure ya fara Kira, a waya sannan ya Kira Nafisat.
Suna karasowa ya Mika mata takarda "Meye wannan?" Cikin masifa yace "ki Karb'a in kin bud'e Kya gani! Sannan Aakif ba d'anki bane da zaki d'ukesa nasan dake na zab'eta dan haka ki ajiye min d'ana!!" Ya kasara maganas kicin tsawa.
Murmushi Nafisat tayi. "Qwarai ba d'ana bane, naka ne Amma ka sani Allah yana sane Yana ji Yana Kuma Gani, Zakaga sakamako"
Bud'e takardan tayi a razane ta kalleshi tare da kallon Zaina.
"Kyautace! Na baki sannu a hankali zan baki ladar dukana da kikayi Ba'a tab'a ni a tashi Babu kyauta me tsoka, Na, baki wannan".
Mikewa Nafisat tayi tare da sauke yaron kasa jiki. "inkin manta zan tuna Miki Ayi a Kare yafi abari gobe a karasa". a sanyaye ta nufi d'akinta Fure ma jikinta yayi bala'in sanyi "Kinsa ya sake ni ko? insha Allahu zai mike fiye da abinda kika min namiji ne fa? Ance miki namiji D'an Amana ne wallahi ko kad'an ba'a bawa namiji Amana , ba'a d'aukan yarda abawa namiji , Namiji bad'an goyo da zani bane, insha Allahu Zaina Zaki ga sakamako karki manta aci a sha a rage don gobe, Amma Kuma aci yau aci Gobe , shine Ci! Gida kuwa inna Zaune daram domin zuwa kikayi kika same ni" shigewa tayi d'akinta
Kallon Banza ta watsawa Fure "Malama tashi ki bar Nan!"
"Abinda Dama ta jure, hagu. Bazata Jure ba, ko Nima sawa zakiyi ya sake ni?"
Girgiza kai Zaina tayi. "Ai abun fad'a namai Baki ne." Tace tana murmushi
Kallon shi Fure tayi, "Kayi shuru ai baka ga komai ba, bade ka zauna Gindin Zaina ba, se kayi kuka Mara iyaka shashasha kawai.."
d'akinta ta shige mikewa Zaina tayi zata shiga d'akinta yace. "Kinbar yaron Kuma?"
"Kai a banzar tunaninka zan rik'e d'an kishiya ne, Allah sauwake, ai ya Zama na tsakar Gida, Kuma Wallahi naji ka d'auki yaron Nan ka kai, mata saika gamu dani" ta karasa maganar da jan,tsaki sannan ta shige abinda.
Kallon Yaron da ya zauna shuru yayi wadda da tukan alamu ya fara maraicin uwarsa "Aakif" yace Yana mikawa Yaron hannun "Affa.." yaron yace Yana Mika mishi hannu d'aukar shi yayi tare da Rumgumeshi hawayen da baisan na menene ba ya sauko mishi. d'akin sa ya nufa da yaron,
Kwana na Goma aka sallamoni Gida. Koda muka dawo kurma nazame musu bana magana damuwa tamin yawa Yarona nake son gani kusa dani inna kewar d'ana sosai Yau da abin ya isheni Fitowa nayi na tsaya mata bakin Kofa. "Wallahi kewa K'anin ki ya dawo min da d'ana.. Ummi" Murmushi tayi sannan tace "Yi hakuri shalele" kuka na saka mata tare da zama a kasa Hanisa dake Zaune tace. "lah ji shashasha Yanzun kuka kike Ai wiya Bata kisa, Babu abinda zai samu d'anki Kinga Anwar na Miki dariya Zamu lalub'o Sir Nabil, yayi Wuf dake Kinga saiya Baki wasu 'Ya'yan ba d'aya ba Biyu ba.."
Hannu bibbiyu na auna mata zagi. "Ba uwar da zanyi dashi ki barni Kinga tashi ki bar Gidan Nan Wallahi kafin na b'ata ranki!" Na fad'a inna niman abinda zan bigeta dashi kallon Hanisa ummi tayi sannan tace. "Tashi! ki tashi Nagode tunda kinzo ki b'ata mata rai ne, a dai-dai wannan lokacin da take cikin damuwa Bai kamata kizo da wannan batun ba" Cikin sanyi jiki Hanisa tace. "Kiyi Hakuri in-law" Cikin zafin maganganunta Jiddah tace. "Bakisan zafin da nake ji, bane Shiyasa kika Fad'i Haka Amma ba komai, ki tafi kawai banson Ganinki" fita Hanisa tayi.
"Kiyi hakuri na kirashi Yana zuwa" da sauri nace. "D'ana nake bukatar gani ba shi ba uwar me zan mishi"
Murmushi ummi tayi domin tana mata uziri sosai tunda abin nan ya faru ta zama mai zafi Rai, bata da hakuri kana fad'a mata zata baka amsa , can tace. "Ummina dan Allah kiyi hakuri inna miki rashin Kunya, ba laifi na bane, na kasa Jurewane. na kasa Yin hakuri, ni nasan rad'ad'in da nake ji na rashin Aakif"
Sati biyu tsakani ummi na Zaune falo.
Sallama yayi tare da shigowa Kujeran dake fuskantar ta ya zauna. "inna yaron?" Ummi tace mishi " 'Da nawane inna da iko dashi na Riga na sallameta tayi rayuwarta Nima nayi tawa rayuwar, bazai Yuwu na barmata d'ana ta b'ata min tarbiyanshi ba Kamilar mace ake barwa Yara ba watsattsiya ba.."
Dai-dai fitowarta. Nuna kanta tayi tana dariya tare da Zama "Me acikin ido banda tarin ruwa, ka sake ni shine zai hanani rayuwa, Ance maka sonka nake dazai dameni! So uku kana jifana da K'azamar kalma nice Karuwa mazinaciya Ko? Yau Kuma kace min watsattsiya! Bazan maka Gorin abinda na maka a baya ba, Amma kaje nabarka da fitowar rana da fad'uwarsa insha Allahu Kalman da kake jifana dashi zai tsaya a kanka.." mikewa tayi tana hawaye tabar Gurin
Kuka ummi ta fashe dashi tana kallonshi "A gabana kake wannan maganar zarginta kake daman Arab yaushe ka zama Haka! Yaushe ka zama Mara adalci da son zuciya Naji Nagode tashi ka tafi...!"
Azuciye ya mike "Akan yar iska kike Korata shi kenan na tafi.."
Fita yayi mikewa Ummi tayi da sauri ta nufin d'akin da Jiddah take tab'a kofar tayi taji a kulle. "Zoki bud'e min Kofa" murya cike da kuka tace "Me zan miki Ummi kina ji ai Kinji abinda ya fad'a, Yace bazai bani Yarona ba, kin kasa yin komai, ya rabani da d'ana ya baiwa Muguwar matar Sa ba matsala yaje Allah na Nan"
"Ki bud'e min Kofa Hauwa!" K'ememe taki bud'e Mata kofar Haka har ummi ta gaji ta koma falon ta zauna.
Wayarta ta d'auka tare da Kiran Nafisat tana d'auka tasa mata kuka. "Lafiya?" Nafisat tace mata
"Maman Jamil wani nauyi zan d'aura miki Ga amanar Aakif dan girman Allah banida wadda zai masa Kyakkyawan rik'o sai ke, Ki kula min da Yaro na dan Allah" kashe wayar tayi tare da fashewa da sabon kuka. "Allah kana gani Allah in wani laifi na maka wadda kake Hukuntani Ubangiji na tuba, Allah ka yafe min.."
Maman Faruq
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: ♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*
Farin Jini Writer's Association
Page23.
♡
Haka ta wuni a d'aki tana kuka ko lek'owa waje batayi ba, rayuwar daki tacigaba dayi, Bata jin dad'in komai ko abinci ummi ta kawo mata sai tayi da gaske take cin kad'an , kukan d'anta take yawanji yana cika kunnuwanta Ga zaurawa ta ko'ina zuwa sukeyi , bata san ya'akayi jama'a suka san bazaurace i'ta ba, Yau da abin ya i'sheta ne ta fito d'akin ummi ta shiga tana sallan walaha , zama tayi kusa da i'ta tana sallamewa ta kwanta jikinta tare da sakin kuka, addu'a ummi tayi ta tofa a ruwa d'agota tayi tare da Sanya kofin a bakinta Bisimillah tayi tare Da shanyen ruwan tana sauke ajiyan numfashi. “Ummi.." kasa karasawa tayi sakamakon hawayen dake zariya saman fiskanta share mata fuska ummi tayi “Allah ya sanya Dangana a zuciyarki Ubangiji ya sassauta wannan zafin ran da kike fama dashi kiyi hakuri kiyi hakuri, ki fauwala Allah lamuranki ki cire damuwar Aakif wiya bata kisa..." Hannuwan ummi ta rik'e
“Wallahi bazan i'ya ba, 'Dana na cikin wani hali Yana bukatar kulawata Dan Allah ki rok'eshi ummi ya bani Yarona! 'Dan uwanki ne ,Bakiji yadda kunnuwa suke jiyo kukansa ba, Kullun mafarki nake dashi yana kuka Yana mik'omin hannu ummi.."
“A Gabanki so nawa inna kiransa ba ya d'aukan kirana so nawa inna tura masa saƙo baya bani amsa laifi na kike ganin ko? Zakice nafiya son Kaina da ƙanina ko Hauwa'u?.." zataci gaba da magana Jiddah tace. “Kiyi hakuri ummi" daga Haka ta mike ta fita, d'akinta ta koma.
Bayan sati biyu.
Fitowarta kenan daga wanka taji yaro yayi Sallama Himar ta saka tare da Fitowa “wa kake Nima?" Yaron yace. “wai ana Sallama da Jiddah.."
"Koma kace bata Nan" har zai fita ummi dake Fitowa tace “Je kace tana zuwa"
"Amma ummi.." katseta tayi “Kimanin wata takwas kenan duk wadda yazo sai ki Kore shi me yayi zafi Jiddah?" Sunkuyar da kai tayi K'asa .
“Babu Aure cikin tsarina a Yanzun d'ana kawai nake bukata, ummi duk wadda ya aureni Yanzun gangan jikina ya Aura zuciyata da tunani na yana ga Yarona, ki barni ummi bana bukatar wani Namiji cikin Rayuwata!" Ummi tace. “Laifi wani baya shafan wani shalele Nah, in har na i'sa jeki shirya ki fito.." ‘Daki ta koma tare da saka doguwar rigan atamfa shigowa ummi tayi tare da kallonta sama da K'asa “wani i'rin shigace wannan? Haka zaki fita Baki shafa mai bare Hoda, Yanzun wannan katon Himar d'in zaki saka? Haba Jiddah ban hanaki suturta Jikinki ba, amma ki cire wannan Himar d'in ki saka mayafi yaushen rabon da kiyi kwalliya ya kamata ki sanyawa zuciyar ki nutsuwa"
“kwalliyar me Ummi? A Yanzun ban bukatar wani Namiji yaga kyawuna bare har na rud'ashi, zamana a Haka yafi min wallahi in har kika ce na sake shiga na fasa fitan!" Murmushi ummi tayi “Allah ya sauke wannan shed'anin dake kanki"
"Ameen" tace sannan ta fita.
Batayi Sallama ba ta bud'e gaban motar da yake “Kaine wadda ke niman iso dani ko ? da alama an fara bud'e babinka na Karshe To bara na fad'a maka ban shirya Aure ba, Bak'in aljani gareni abinda yasa Mijina ya sake ni kenan Wallahi kana Aurena Zaka mutu in kashirya ma yaranka su zama marayu to.." da sauri Mutumin yace “a a Wallahi" murmushin jin dad'i tayi sannan tace “Shi kenan zaka i'ya tafiya"
Tana tsaye Gurin ya tada motarshi sai da taga fitarshi sannan ta shigo Gida, Haka ta ringa Koran duk wadda yazo Gurinta da Sunan Baƙin Aljani gareta. Wasa wasa aka shafe shekara da watanni Abin na Bata mamaki ganin yadda take Wahal dasu Amma har yanzun Banzaye wawaiyu basa ganewa Matsorata ne, ta kanyi dariya in ta tuna yadda suke rikicewa da zaran tace Bak'in Aljani gareta. i'do kawai ummi ta zuba mata, randa abin ya i'sheta ta isketa d'aki lokacin tana duba sakonin ta Email d'inta “Hauwa'u" ummi ta kira sunanta. Kallo d'aya Tama ummi sannan ta d'auke Kanta domin tasan abinda ya kawota “Na'am Ummina" janye laptop d'in tayi daga Gareta. “Hankalin ki zaki bani magana zamuyi" tagumi tayi tare da zuba mata i'do “Maiyasa duk wadda yazo niman Aurenki kike koransa? Ki fad'amin Auren ne baki so ko me?"
Hannunta ta matse har sai da yai Ƙara. “Ummi bawai Auren bane bana so ban shiryawa Auren bane, sabida har Yau, ban samu wadda zuciyata tayi na'am dashi bane, Nifa ba Budurwa bace ya kamata in samu nutsattse wadda yasan mutumci da Kuma kimar d'iya mace , Namijin da zai iya kula dani nake bukata inna son Namijin da ko yau na mutu zai ringa tunawa dani Ummina inna son Namiji Kamili mai Addini inna son Namijin da yasan wacece mace , abin Nufi Namijin da zaiyi Hakuri da Halayyar ta Akwai Mazan da Basu da Hakuri da zaran mace ta b'ata musu zasu hauta da fad'a ta inda suke shiga ba ta Nan suke fita ba, inna son Nagartacce wadda zai na min Uziri wadda da zaran nayi masa kuskure Zai rarrashi zuciyarsa wadda da zaran na ɓata masa in na bashi Hakuri zai karb'i Uzirina Ya Hakura inna Son Namijin da zai tarairaye ni inna son Namijin da zai shagwaɓa ni inna son namijin da zai mai dani tamkar yarinya inna son Kimtsattse tunda Kinga ni watsattsiya ce ko Ummi? Banida Nutsuwa! Mazinaciya, inna son Salihi wadda zai karb'e ni a ko ya-ya nake, inna son Namijin da zai Mutumta ahalina Ya girmama min Ummina ,Yah Allah Babu wani sarki Bayan Kai, Allah Kai mai Kyauta ne, Ubangiji kamin Kyautar Bazata! Allah kai mai azurtawa ne, Yah Rahimu ka azurtani da Kimtsattsen Miji. Allah kai meji Ne, Ubangiji ka amshi rok'ona Albarkan Wannan rana ta Juma'a..."
Wani i'rin kuka take mai tab'a Zuciya, tana magana. i'ta kanta ummi jikinta yayi masifar sanyi a duniya, Babu kalma mafi Muni da za'a jefeka dashi kaman ace maka mazinaci abun da ciwo shiyasa har yau take jinshi a ranta i'ta a iya sanin da tayiwa Jiddah yarinyar Akwai yafiya Amma da wuya ta manta abinda aka mata duk da tariga da ta yafe mishi tasha jin tana addu'ar Allah yabi Mata Hakk'inta Akan K'azafin da aka mata, abin da ciwo sosai Amma ya za'ayi sai Hakuri.
“Ummi kina ganin kaman ban kyautawa ko? To kiyi hakuri tunda Aure kike so nayi zan tsayar da Mutum nayi Amma nasan bani da nagartan da za'a Soni ko Ummi?" Ta karasa maganar tana tsare Ummi da idanuwanta masu Kama da mage, mayar da kukan