Header Ads
Showing 75001 words to 78000 words out of 81184 words

Chapter 26 - Sirrin Daukaka Book Complete by Aisha JB .txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

1132

Ads at the middle of Article

zaman shi ƙarshe fita yayi a gidan, Girgiza kai kawai Jiddah tayi tare da sauke labulen window bayi ta nufa tayi Alwala tazo ta shimfiɗa sallaya nan ta fara jero nafiffilu tana masa Addu'ar shiriya bata runtsa ba saboda damuwa da baƙin cikin dake ƙunshe a zuciyarta kuka take sosai tana tunanin Nabil nacan gurin wata mace, macen ma Karuwa, Sai bayan Asubahi ya shigo gidan lokacin ta gama ƴan aikace-aikacen data saba, Nuwairah ce ta fito tana kallon yanda ta kammala komai “Kai Jiddah wannan aiki haka, kinsan fa baki da lafiya ai da kin bari nayi komai” “Barka da Fitowa Aunty Nuwairah, ai ba komai wallahi” Hannunta Nuwairah ta kalla tana faɗin “To ya ƙarfin jikin naki? Ina fatan kin ji sauƙi?” Jiddah tace “Alhamdulillah da sauki sosai” Zama Nuwairah tayi tana faɗin “To Masha Allah jiya Yaya yake min maganar da ban gane kansa ba, na fara tunanin gwara a kaishi asibitin mahaukata a dubashi dan ga dukkan Alamu karen hauka ya cijeshi” Girgiza mata kai Jiddah tayi tana dariyan zancen ta. “Kai! Nuwaih yana cikin hankalin shi nafi ɗaukar maganar da wasa yake..” ajiye spoon ɗin tayi tana faɗin “Wasa fa kika ce? Allah da gaske yake kuma nasan zai kai maganar gaba” Kallonta nayi domin wlh na ɗauka barazana yake “Allah ya kyauta” nace sannan ya shiga ɗaki nayi shirin fita.
Jin motsin tura Get yasa ta gyara zama tana daɗe faɗaɗa fuskanta da yalwataccen murmushin a tunanin ta Nabil ne, Amma jin wani ƙamshi na daban yasa ta shiga kokonto waye haka? Jiddah kuwa tsayawa tayi tana ƙarema Gidan kallo sosai tana kallon ɓarnan da akayi da dukiya musamman ma kyawawan kujerun Alfarman dake falon ga danƙareren tv bango “Waye Anan?” Aaliyah dake fitowa ta faɗi haka tana mamakin ganin mace, Cikin nutsuwa Jiddah ta juyo tana tuna mai muryan ja da baya Aaliyah tayi tana nunata “Meya kawo ki gida na?” harɗe hannuwa Jiddah tayi a ƙirji tana matsowa tare da ƙare mata kallo “Aaliyah!! Ohh daman kece Karuwar tasa? Kece kikayi kane kane a rayuwar mijina? Kice kika ɗauke wa mijina hankali oh Na tuna a can baya kince zaki addabi rayuwata hakane Abun dama? To yau koni ko ke dan wallahi saina Kashe ki yanzun! kuma anan!! Saina lalata duk wani halitta na jikinki..” ja da baya Aaliyah ta shigayi tana faɗin “A'a Jiddah dakata nayi miki bayani wallahi Ina Son Nabil shima kuma yana ƙaunata yanzun haka muna shirin Aure ne dan mu mallaki junanmu...” ɗauke ta tayi da lafiyayyen marin da se da ta fitar da jini ta hancin ta, cakume wuyan riganta Jiddah tayi tana jijjigata cikin ɓacin rai “Mijin nawa kike shirin Aura ko? Zaki Aure shi amma a lahira dan baki da gurbin zama cikin matanshi na duniya” tana gama faɗin haka ta shiga kifa mata mari kukuwa kawai Aaliyah ta shigayi da Numfashi saboda riƙon da Jiddah tayi mata Numfashinta na barazanan ɗaukewa Dunƙule hannun Jiddah tayi da niyar kai mata naushi cikin tashin hankali Aaliyah ta tare cikinta da hannu tana faɗin “Dan Allah karki kashe rai, Ciki gareni na sati shida Please naci albarkacin sa...” ta ƙarasa maganar cikin kuka, cikin tashin hankali Jiddah tace “What! CIKI!!! Innalillahi wainna ilaihi rajiun” Jiddah ta faɗa tana ja da baya tare da fashewa da kuka “Ciki de na Haihuwa? Kina da ciki? No! Ƙariya ne!!” dawowa tayi da gudu takai mata wani mummunan naushi a ciki, ƙara me ƙarfi Aaliyah ta saka tare da zubewa a ƙasa ɗif Numfashinta ya ɗauke na wasu daƙiƙu, ruwa me sanyi Jiddah ta zuba mata a Fuska tare da ɗagota “Karki yarda ki sake raɓan mijina ke ko Sunan mijina kikaji Ina so ki toshe kunnuwanki dan wallahi naji Mijina yana tare dake kashe ki zanyi!!” Kaman mahaukaciya haka Jiddah ta shiga dukanta ba ji ba gani, kafin ta shiga janta har ƙofan gida ta watsar da ita dawowa tayi cikin Gidan tare da Zuba fetur ta cinnawa gidan wuta tana fitowa ta tarar da Nabil yana shirin ɗaga Aaliyah dake ƙwance cikin jini Cikin wani irin mawuyacin halin Aaliyah ta Riƙe hannunshi tana faɗin “Yau nake shirin sanar da kai amma matarka ta ɓata komai Nabil Baby Na ciki gareni shine tazo ta kashe ni da Abinda ke ciki na” A zabure ya sa ke ta tare da nufo Jiddah nan ya shiga zuba mata mari cikin ɓacin rai “Akan me? Me yasa kika zubar min da ciki...”
“Nabilllll” da gudu ya nufi gurin Aaliyah tare da ɗaukanta yasata a Mota suka nufi asibiti.
Gida ta nufo gbɗy bata cikin nutsuwarta “Jiddah Ina kika je?” Ina Jiddah bata ma san da ita ake magana ba, riƙe ta Nuwairah tayi tana faɗin “Jiddah menene haka? Ya naga fuskan ki a kunbure waya dake ki?” wani irin kuka ta fashe dashi tare da faɗin “Nuwairah Yarinyar da Nabil ya ajiye har ciki gareka wannan Karuwar tasa nake faɗa miki ciki gareta saboda naje na dake ta shine Nabil ya mayar min da fuska haka Akan karuwa Ya min haka!” Cikin tashin hankali Inna ta ƙaraso gurin har zaninta na shirin faɗuwa kasa “Me nake ji haka? Ke! Jiddah me kike faɗa ne?”
Girgiza kai Jiddah ta shigayi tana faɗin “Babu komai..” Rufe mata baki Nuwairah tayi itama cikin kuka tana faɗin “Ƙwarai Abinda kunnuwanki suka jiye miki haka ne, Nabil ne ya ajiye Karuwa a waje duk wannan rigingimun da muke duk akan maganar ne..." Rufe mata baki Jiddah tayi tana girgiza mata kai alamar karta faɗa “ƙyale ni Jiddah Halin Nabil ya isheni gwara na fayyace komai” tiriyan-tiriyan ta dinga faɗa musu komai Wani wawan burki Nabil yaja yana kallon Nuwairah dake bayani Juyowa mahaifiyarshi tayi nan ta shiga zuba mishi mari tana faɗin “Wannan ba tarbiyan dana baka bane, wannan ba Renon Asma'u bace, Nabil kaine da ajiye mace a waje har da ciki?” sunkuyar da kanshi yayi ƙasa yana sake jin wani ɓacin rai, duk abinda suke Mahaifinshi na kallonsu jinjina kai yayi yana mamakin Halayyar da Nabil ya ɗauko “Da Girman ka, da ilimin ka, kana da iyali kasan Hukuncin zina kuwa? Anya Nabil baka fara shaye-shaye ba kuwa? To wallahi ka buɗe kunninka kaji da kyau bazan ɗauki wannan ƙazantar a cikin gidana ba, ban taɓa Zina ba, dan haka...” da sauri Jiddah tace “Dan Allah Abba karka masa baki, dan girman Allah kuyi masa addu'a shine kawai abunda yake buƙata” gyaɗa kai Mahaifinshi yayi tare da nuna shi da yatsa ransa a ɓace ya bar gurin haka ma mahaifiyarsa Nuwairah kuwa hannun Jiddah ta kama suka dawo part ɗinsu.
yanke shawaran barin Gidan Jiddah tayi, nan da Nan ta shiga haɗa kayanta tare da buɗe wani ƙaramin jaka ta ɗauko hoton Mahaifiyarta, rumgume hoton tayi tana hawaye sosai cikin kuka take faɗin “Umma lna cikin Ahalinki yau nice matsayin matar ɗan da kikafi ƙauna yau gashi zan barshi bazan iya cigaba da zama dashi a irin wannan rayuwar ba, bazan iya zama baƙin ciki da damuwa su kashe ni ba, gwara na koma inda na fito gwara na tafi kuma tafiyar da bana jin zan sake dawowa”
Zoben Azurfa da awarwaronsa ta ɗora kan hoton tare da ɗan shot note ta ajiye, ATM ta ɗauka tare da Nufar part ɗin Mama-Sadin ganin tana barci ne yasa ta juyawa da niyar fita ɗan gyaran murya taji mama tayi a hankali ta juyo tana kallon yanda Mama ke motsawa da sauri ta fita a gidan kuɗi masu yawa ta cire kafin ta bar ƙasar direct Gidan Fadilah ta nufa dan bata so kowa yasan tazo Nigeria daga dangin Ummi bata samu Fadilah a gida ba, me musu gadi ne yake sanar da ita tafiyan da tayi tare da mijinta key ɗin cikin gidan ta karɓa daga gurinshi kasancewar ya santa da Fadilah shiyasa bai wani damu ba, Ɗakin Fadilah ta shiga nan ta adana kayanta tare da shiga bayi tayi wanka a gurguje tazo ta biya sallolin dake kanta kasancewan dare yayi sosai bazata iya yin girki bane yasa ta haɗa tea kawai tasha ta kwanta.


Chadi....


Bana ganin Comment


Maman Faruq
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: ♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*


® AYSHA JB


FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION

Alhamdulilah jiki ya yi sauƙi sosai ina matuƙar godiya da addu'o'inku🥰🤝


35 Riƙe hannuwanshi tayi da ɗan ƙarfi tana kiran sunan shi, a hankali ya buɗe idanunsa tare da faɗin. “Sannu Aaliyah ya kike jin jikin naki yanzun?” ya ƙarasa maganar tare da shafa fuskan ta. “Da sauƙi Lover ai na ɗauka ka tafi..” Girgiza mata kai yayi sannan ya taimaka ma ta ta zauna, shafa cikinta tayi tana kallon shi da murmushi. “Kana murna kuwa?” zama ya yi kusa da ita tare da kwantar da kan shi bisa kafaɗarta shima ya ɗora hannunshi saman nata tare da sa kin kyakkyawan murmushi yana lumshe ido, sun jima a haka na tsawon lokaci kafin ya janye jikinshi daga gareta tare da nufan ofishin likita tattaunawa sukayi akan yanayin jikin na ta kafin ya dawo ya samu har ta koma barci gyara tsayuwar sa ya yi yana ƙare ma ta kallo tare da ƙurawa cikin jikinta ido, sosai yake jin farinciki mara misaltuwa a ran shi kallon agogon da ke ɗakin ya yi yana tunanin zuwa gida gashi dare ya yi sosai banɗaki ya shiga ya kama ruwa tare da alwala ya dawo ya shimfiɗa sallaya ya fara nafila a saman sallayan ya kwana washe gari aka basu sallama ya dawo da ita gida bayan ya sa an gyara komai na gidan da ƙyar ta ƙyaleshi ya nufo gida.
Nuwairah ce kaɗai zaune a falon domin tun jiya suke niman Jiddah amma babu ita babu labarin ta hankalin su ya yi matuƙar tashi sosai dalilin haka yasa mahaifin Nabil ɗaukan zafi kasancewar ba irin kiran wayan da ba'ayi masa ba amma ya ƙi ɗagawa Mama-sadin ma da taji labari hankalin ta ya tashi sosai inda ta shiga faɗa tana faɗin basu kyauta mata ba me yasa basu faɗa mata tunda wuri tayiwa abun tufkar hanci ba, shiyasa kwanaki take ganin Jiddah cikin yanayin damuwa ashe da walakin goro a miya domin Jiddah yarinyace me sakewa da mutane duk da ita ba mace bace me yawan surutu da son hayaniya amma akwai ta da daɗi hira ga iya tausasa lafuza duk maganar da zai fito daga bakinta me kyau ne da kuma ma'ana. tana da haƙuri da kawaici, sau da dama tana tambayar ta yanayin zaman nasu ba ta taɓa gaya ma ta wani abu da ake mata mara daɗi ba yawancin lokuta ma idan ta tambaye ta sai dai tayi murmushi kawai daga haka zata shashantar da zancen ta wani siga yarinyar ta shiga ran ta sosai tana jin ta kamar yadda take jin sauran jikokinta sai dai ƙaunar da take mata daban ne dalilin da yasa ta ɗaga hankalinta kenan akan ɓatan nata.
“Lafiya kuwa Nuwaih naganki cikin wananan yanayin?” kallon shi tayi tana jin takaici da baƙin cikin kasancewar shi ɗan'uwan ta wanda kuma yake matsayin miji a gareta ɗakin Jiddah ta nuna mishi tare da ɗauke hawayen dake zubo mata kallon ta yayi zuciyar shi na dukan uku uku a tunanin shi wani mugum abune ya samu Jiddan hankali a tashe ya nufi ɗakin cikin hanzari nan yaga gabaɗaya ɗakin a hargitse ga dukkan alamu babu wanda ya kwana cikin ta kallon inda akwatunanta suke yay nan yaga babu wasu daga cikin akwatunan zama yay gefen gadon tare da dafe kanshi da hannuwanshi duka biyu yana jin wani irin tashin hankali tare da tunanin Ina taje? Ina ta kwana? a wani hali ta ke? duk ba shi da me bashi wannan amsar kallon gaban madubin ya yi nan yaga gabaɗaya babu kayan kwalliya da mayukan shafe shafenta miƙewa yay yana zagaye ɗakin zuciyarshi na bashi lallai tana Nigeria yanzun haka, naushin iska ya yi yana jin babu daɗi a ran shi, ta gefen gadonta yaga awarwaro da sarƙa ɗauka yay tare da bude hoton dake gurin da wasiƙar da ta rubuta. “a lokacin da zaku iske wannan saƙon nasan nayi nisa Ina so abar wata maganar dangantaka kayi gaggawan aikomin da takarda ta, domin bazan iya cigaba da zama da mutum mara adalci irin ka ba, a yanzun na haƙura da aure da duk wani abu daya shafi ɗa namiji nafi sha'awar zama ni kaɗai domin babu komai cikin rayuwar Aure daya wuce baƙin ciki da damuwa. duka halin maza haka yake, duk yadda ka kai ga son gane halin maza bazaka taɓa fahimta ba, domin kullum cikin canzawa suke baka gane gaban su balle bayan su, Ina sake jaddada maka ka sauke min wannan ƙadararren Auren nake damin bazan iya cigaba da zama da kai ba, karka ɓata lokaci gurin niman inda nake” wani irin gumi ne yake tsattsafo masa tun daga tsakiyar kan sa zuwa wiyansa kalman Innalillahi wainna ilaihi rajiun kawai yake maimaitawa kallon hoton yake hawaye na tarige rigen saukowa akan fuskansa, Kenan Jiddah ɗiyar Ammah Asma'u ce? ita ɗin ƴar'uwa tace ta jini tasan da haka tsawon wannan lokacin shine bata bani fuskan da zan fahimci hakan ba? Ya Salam me kenan na aikata ban kyauta mata ba, juyowa yay da niyar zuwa shashin Mama-sadin nan yayi arba da Nuwairah tsaye “Ashe akwai ran da zakayi kuka? tabbas nasan wacece ita shiyasa tun farko na watsar da makaman yaƙina muke zaman lafiya nasan Jiddah ƴar'uwa tace Ƙanwa tace shiyasa nayi haƙuri muke zaman lafiya..” dakatar da ita yay ta hanyar faɗin “Kinsan da waɗannan abubuwan shine baki faɗa min ita ɗin Jinin mu ɗaya ba? maiyasa kika rufe ni? taya kika gano hakan? ni kaina nayi mamakin yanda lokaci ɗaya kika watsar da wannan kishin naki kuke zaune lafiya taya haka ta kasance?”
“Hanisa ita ta sanar min da komai ita ta sanar min da Jiddah ƴar'uwar mu ce, amma sai na musanta daga ƙarshe se nasa aka bincika min har can Benue ɗin a nan ne na samu labarin komai shiyasa na watsar da komai amman nace bazan faɗa ba, har sai ita da kanta ta fallasa komai. Nabil baka kyauta ba, bai kamata ka taɓa Jiddah akan wata karuwa mara daraja ba, bai kamata ka ɗagawa matarka ta Sunnah murya akan wata banza mara ƙima ba, Jiddah tana da haƙuri ni shaida ce.
Jiddah macece me sauƙin kai da kwantar da kai dan a zauna lafiya macece da abin duniya bai rufe ma ta ido ba, duk da tana kasuwanci amma haka tayi haƙuri tabar komai duk saboda tana son zaman Aure amma sai kaƙi fahimtar haka, duk wani ƙoƙarin da muke maka da ƙoƙarin sauke duk wasu haƙƙin ka dake rataye akan mu amma duk bamu ishe ka ba, meye a jikin wancan yarinyar?” shuru yay yana sauraronta daga ƙarshe suka nufi part ɗin iyayensu nan suka suka mishi faɗa sosai tare da nuna ɓacin rai akan abinda ya aikata mata shuru sukayi suna sauraron bayanin da Nuwairah take koro musu game da Jiddah “Innalillahi kika ce Asma'u ta rasu? Lahaula walakuwwata illabillah Allah sarki ashe babu rabon mu sake ganawa da Auta ta! Allah ya gafarta muku Husnah Allah yaji ƙanku da rahama ashe Hauwa'u jikanya tace shiyasa wani lokaci nake mata kallo kamar Asma'u ashe jininta ce to ka buɗe kunnuwanka da kyau ka jini maza-maza ka tashi ka nimo min jikanya kai harda ɗanta dan baza'a bar shi can ba, bazai yuwu mu danginta muna raye ita tana can wata uwa duniya ɗanta na tsakiyar kishiyoyi marasa adalci ba. Karka yarda ka dawo batare da ka samo su ba” Mama saddika ta ƙarasa maganar tare da fashewa da matsanancin kukan rashin ƴarta, nan suka fara lallashinta tare da kwantar mata da hankali.
Miƙewa ya yi yana duba wayarshi da niyar kiran ummi nan ya tuna ya bar wayan a gidan Aaliyah dole ya fito ya nufo gidan, sai dai ganin wata mota yasa shi shiga cikin mamaki fitowa yay yana kallon motan tare da nufar ƙofan ɗakin ya kai hannu da niyar tura kofan Bedroom ɗin nan yaji maganan daya kusan sumar dashi “Shi fa duk a tunaninsa cikin nan nashi ne bai san ƙariya nake masa ba, wallahi ina baka labari susucewa yay yana faɗa min in kula mishi da Cikin saboda yana tsananin son Haihuwa be san bayan shi Ina tare da kai ba...” da ƙafa ya taka ƙofan a zabure ta ja zanin gadon tana rufe jikinta, wayarshi yaje ya ɗauka tare da tattara duk wasu abubuwan da yasan nashi ne sannan ya nufi ƙofan fita yana faɗin “ki tattara duk wasu tarkacen ki nan da minti talatin ki bar min gida idan kuma ba haka ba se nayi miki dukan da yafi wanda Jiddah tayi miki shashasha wallahi nayi dana sanin haɗa jikina dake ƙazama! kariya!! kiyi gaggawan barin Gidan nan!”
“Nabil! dan Allah ka tsaya nayi maka bayani Nabil wallahi ina matuƙar ƙaunarka wallahi bazan sake ba, dama ɗaya kawai..” wani mugun tsawan daya daka mata ne yasa ta kasa ƙarasa sauran zancen nata fita yayi yana jin zuciyarshi na zafi, lallai ya aikata kuskure a tunaninshi cikin nashi ne ashe ba haka bane bayan shi tana tarayya da wanin sa, yana dawowa gida ya fara shirin tafiya washe gari kuwa sammako ya buga sai Nigeria ummi tayi mamakin ganinsa da kuma abinda ya kawo shi ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba lokacin daya ce mata ya biyo sawun Jiddah ne “To ai rabo na da Jiddah tun ranan da mukayi magana ta wayan ka bayan nan ban sake jinta ba, daman ina tunanin kiran ka ganin kwana biyu shuru ba labari” miƙewa ya yi da sauri yana faɗin “Innalillahi wainna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati..”
“Amma bari na tuntuɓi Iyanmu in ji ko taje zaria” kiran Iyanmu tayi nan ma babu labari hankalinta ya tashi matuƙa nan ta shiga kiransu Halimatu da Hanisa suma cikin tashin hankali suke sanar ma ta lallai bata zo ba, babu ɓata lokaci suka iso gidan duk hankalinsu a tashi.
Ummi tace “To

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads