Header Ads
Showing 78001 words to 81000 words out of 81184 words

Chapter 27 - Sirrin Daukaka Book Complete by Aisha JB .txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

1134

Ads at the middle of Article

wai nikan meya haɗa ku da har tabar Chadi? anya Nabil ba wani mugun abu ka aikata ba kuwa? domin nasan halin Jiddah nasan irin tarbiyan dana bata faɗa min abinda ya haɗa ku”
Sunkuyar da kai ya yi yana jin girman maganan a ranshi “Bari na kira Fadilah ko Gurinta taje” cewan Halimatu kiran Fadilah tayi tare da sanar mata halin da ake ciki , nan ita ma take sanar mata cewan sunyi tafiya amma yanzun haka suna kan hanyar komawa gida in ta huta zata zo, daga haka ta ajiye wayan jiki a sanyaye fita yayi a gidan yana tunanin Ina zaije nimanta yanzun.
Kiran Arab Ummi tayi tana tare da sanar dashi halin da ake ciki sannan ta buƙaci ya kawo mata Aakif shuru kawai yayi yana kallon wayar domin bata jira taji abinda zai faɗa ba ta kashe wayar Kallon Nafisa ya yi kasancewar a ɗakinta yake nan ya sanar mata Halin da ake ciki “Masha Allah kaga yanzun babu wata damuwa inaga ka basu yaron kawai Ita kuma duk inda take Allah yasa tana hannu na gari” Jinjina kai kawai ya yi tare da miƙewa ya fita a ɗakin a falo ya samu Aakif ɗin Yana karatu “Aakif dare fa yayi sosai kaje ka kwanta haka mana” ɗagowa yayi tare da faɗin “To Abba” yana cikin tattara takardunshi hoton Jiddah ya faɗo kallon yaron yayi tare da ɗaukan hoton kana yace mishi “Kana son ganin Jiddah?” da wani irin mugum sauri Zaina dake fitowa daga ɗakinta ta ƙaraso gurin “Ji nayi kamar kace zaka kaishi gurin Jiddah Hahahaha! Nace maka Jiddah bazata taɓa zama da wannan yaron ba, nice tayi asiri na rabaku nice nasa aka tunzura zuciyarka har ka koreta sannan nice na hanaka Bata ɗanta duk wasu abubuwan da suke faruwa nice na aikata Hahahaha! Nice silar mutuwar Mazkhura nice nayi karan tsaye a rayuwar Jumana nice! Nice!!” miƙewa yayi ya shiga kifa mata mari ba gaggautawa da sauri Aakif ya riƙe shi yana faɗin “Abba kayi hakuri ka dena dukanta bata cikin hayyacinta mu kaita asibiti..” Nafisa dake fitowa tace “Babu wani asibiti Ishara ce Allah ya nuna mata, ai dama duk wanda ya ɗebo da zafi bakinsa” dariya kawai Zaina take ba ƙaƙƙautawa duk tayi wani iri nan ta shiga fisge kayan jikinta tare da watsar dasu, gashin kanta ta shiga fisgewa tana ihu da surutai da wani irin gudu tayi waje wani irin sanyi jikinsu yayi nan take tsoron Allah ya sake ɗarsuwa a zukatan su Fure'atu dake tsaye wani irin kakkarwa jikinta yake hankalin ta tashe, hakama Nafisa da Arab jikinsu yayi matuƙar sanyi fita yayi domin duba yanayin da take ciki sai dai duk yadda ya kai ga hanata fita Ina tafi ƙarfin sa Tafi take tana faɗin “Huhuhuuuu zan je gani nan zuwa Jiddah zan zo bazaki taɓa ganin daidai ba tunda kika ɗauke hankalin mijina Ihuhhuuuu ja muje ina tafe” a zabure tayi waje shi da mai gadi tare da me musu wanki suka mara mata baya, gudu take akan titi tana ihu da surutai wani Babban gwangwaro ne yazo a guje tare da take ta, gabaɗaya yanayin babu kyan gani baka iya ganin komai banda Ƙwaƙwaluwan kanta tare da kayan cikinta wadda suke waje duk tayi daga daga, motan na wucewa suka nimi gawar suka rasa zaman dirsham yayi yana faɗin “Innalillahi wainna ilaihi rajiun” kalman da yake ta nanatawa kenan gabaɗaya ya tsorata ya firgice ya fita cikin hayyacinsa haka aka rirriƙoshi zuwa gida wani irin mugun zazzaɓi ne ya rufe shi gabaɗaya jama'ar dake anguwar jikinsu ya mutu tabbas mutuwa babban wa'azice Nan kowa ya dinga faɗan halayyar ta da irin abubuwan da take aikatawa duk yadda Nafisa taso dubashi a gida kasawa tayi domin ita kanta tana buƙatar me dubata haka duka ɗunguma asibiti har Fure'atu Jumana ce kawai aka bari a gida tare da sauran yaran wadda suka rikita gida da koke koke.
** ** **
Buɗe ido nayi ina kallon Fadilah data zuba min marin a cinyata “Kai Amma Jiddah ke ba ƙaraman ƴar iska bace daman nan kika zo kika maƙale gabaɗaya kin ɗagawa mutane hankali kinga yanda ummi dasu Hanisa suka ɗaga hankali kuwa? yanzun fa daga can nake nace bari nazo na ɗanyi gyare-gyare se na koma kawai ina shigowa me gadi yace nayi baƙuwa wallahi take zuciyata ya bani kece Haba komai yayi zafi fa maganinsa Allah komai na duniya fa sai da haƙuri domin itace jagaba kuma jagoran dake tafiyar da komai, wallahi yadda naga Nabil ya bani tausayi sosai koma menene yayi miki tunda ɗan'uwan ki ne ya kamata ki ƙara Haƙuri akan na baya wallahi baki kyauta min ba domin lokacin da Ummi ta take magana hawaye take..” da sauri na tashi zaune ina faɗin “Ummin tawa ce ke hawaye wayyo Allah sarki Sorry ummi...”
“Allah ya shirye ki wallahi nayi tunanin zakice mu tafi ne yanda kika wani zaburo kika tashi zaune” yatsina fuska nayi tare da nufan Toilet da niyar wanka kiran Ummi Fadilah tayi tare da sanar mata Jiddah na gidanta jin haka yasa Nabil nufo gidan cikin gaggawa fitowa nayi ɗaure da zani yayinda nake goge gashi na da towel kasancewar na wanke shi ganin mutum kawai nayi a gabana take nasa ihu ina shirin zubewa saboda tsananin tsoron daya kamani da sauri ya taryo ta cikin jikinsa yana shafa fuskanta domin da gaske de sumewa tayi ruwa ya shafa mata a fuska tare da zubama kyakkyawan fuskanta ido yana kallon yadda take buɗe idanunta a Hankali tureshi nayi ina niman zani na wani irin Kyakkyawan Murmushi yayi tare da danneta yana faɗin “Im so sorry Jiddah nasan na aikata abubuwa da yawa Amma dan Allah kiyi Haƙuri komai ya wuce wallahi nayi nadama kaina bisa wuyana ina mai bada haƙuri kodan albarkacin Ammah da Ummi ayi haƙuri a yafe mini Please Sweetheart” ya faɗa cikin kashe murya tare da zuba mata narkakkun idanunsa shuru kawai nayi domin bana jin zan sauko lokaci ɗaya a bazata naji bakinshi cikin nawa da wani irin masifan na fara ƙoƙarin tureshi ina faɗin “Kawai kace min kazo kaji daɗi dani ne, kazo na Buɗe maka ƙafa bayan irin cin mutuncin da kamin akan wata karuwa..” haɗe bakinsu yayi tare da girgiza mata kai.
Wani irin lafiyayyen kissing ɗinta yake tare da shafo na shanunta laƙwas tayi tana jinshi domin gabaɗaya yayi nasaran kashe mata gaɓoɓin jikinta kifa kanshi yayi yana wasa ƙirjinta sosai tare da faɗa mata wasu irin kalamai masu wiyar ɗauka kuka ta saka tare da ƙanƙameshi tana faɗin “Me yasa ka kasa fahimtar irin soyayyar da nake maka Sir Nabil! mai yasa! Wallahi ina ƙaunar ka sosai, Yayana ina sonka soyayya mara iyaka amma ka kasa fahimtata duk wani kawaici da kunyata na ajiyesu gefe na fito fili na fayyace maka Sirrin zuciyata kaine muradina tun lokacin dana fara arba da kai, sai dai nayi ƙoƙarin nesanta kaina da kai ne saboda sanin matsayi da kuma son kare mutunci da martaban Aure na..” shafa fuskanta yayi yana faɗin “Na sani nasan kina sona nasan kuma kinyi haƙuri da halin ƙuncin rayuwa kinyi haƙuri akan komai lallai ke macece da kowa zaiso ki zamo mallakinsa Ina miki nikin ba nikin ƙaunar da kike min. Ina so kiyi Haƙuri kizo mu ƙarasa rayuwarmu kina da farinciki da jinin daɗi domin Ahalinki suna can suna tsumayin zuwanki Kowa nason sake ganinki kowa na murna dajin cewa ke ɗin ɗiyar Asma'ulhusnah ce ke ɗin fa Autar Ummanta ce shalelen Ummi Ƙanwar Nuwairah da Nabil matar Nabil farinciki a gidana..” (tsakani da Allah wanga soyayyar ta tsumani..)
rufe mishi baki tayi da nata daga haka suka lula duniyar ma'aurata can ƙololuwan sararin samaniya Cike shauƙin So da Ƙauna suke faranta ran junansu.
Bayan komai ya lafa ne ya kalleta tare da jan karan hancinta yana faɗin “Ki shirya sai mu wuce gidan ummi tare ko?” Ajiyan zuciya ta sauke tare da gyaɗa mishi kai, tare sukayi wanka sannan ya tayata shiryawa wanda gabaɗaya cikin shiririta aka gama shirin fita yayi yana jiranta a waje, shigowa Fadilah tayi tana kallon Jiddah ta fashe da dariya “Taɓ lallai har an kammala soyewan Allah yasa de ba'a ƙone ba..” da ɗankwalin hannunta ta jefi Fadilah tana dariya “Kinga bana son sa ido fa” Fadilah tace “Babu wanin nan munafuka ana so ana kaiwa kasuwa, sai a cigaba da haƙuri kisan lamarin rijalu sai ana haɗawa da batun haƙurin nan” rumgumeta Jiddah tayi tana faɗin “Na gode sosai Bestie sai kin shigo kenan” daga haka sukayi sallama gidan Ummi ya kawota sannan ya nufi hotel ɗin daya sauka domin yaƙi zama cikin gidan nan ummi ta shiga faɗa kaman zata ari baki domin ranta yayi matuƙar ɓaci, “Kiyi haƙuri Ummin mu tunda tana cikin ƙoshin lafiya ai Alhamdulilah koma dai menene ya wuce kema Jiddah baki kyauta ba domin kin ɗaga mana hankali sosai” cewan Hanisa “I'm so sorry nasan ban kyauta ba amma in sha Allahu hakan bazai sake faruwa ba ayi haƙuri Ummi na Please kiyi mun ɗan Murmushi mana haba uwata kin san de bani da tamkar ki a yanzun dan Allah kiyi Haƙuri kinji haba ummi Shalelen ki ce fa..” rumgumeta Ummi tayi tana jin hawaye na cika mata ido “I'm so happy too you Shalele naji daɗi ƙwarai kasancewar kina cikin danginki sai dai ina jin babu daɗi ganin kinyi nesa dani nasan ba lallai kuma su sake bari ki zo...”
“A'a ummi karki ce haka ina nan tare dake zaki dinga gani na akai akai Ummi bazan taɓa mantawa da uwa kamarki ba, Ummi kinyi min komai wadda uwa take yiwa ƴarta shiyasa a kullum nake miki addu'a da fatan dacewa anan duniya da kuma lahira a duk lokacin da kike Son ganin Shalelen ki zata zo miki batare da kawo wani uzuri ba..” cikin burgewa Halimatu da Hanisa suke kallonsu daga ƙarshe suka saka dariya har Ummi ɗin, haka suka ci gaba da hira har dare kafin mazajensu suka zo ɗaukan su. Gida ya saura daga Ummi se yaran Halimatu tare Anwar Dan nan suke karatu suna taya Ummi hira kasancewar gidan babu kowa shiyasa suka dawo dan ɗebe mata kewa.
Hira sosai mukayi da ummi inda ta dinga min nasiha tare da bani addu'o'in, sai da akayi kwana shida ana gobe bakwai tukun muka ji labarin mutuwar Zainab wanda seda na gigice domin yadda Nafisa take faɗawa Ummi lamarin ya ɗaga hankalin mu, a ranan Ummi ta nufi Abuja gida ya saura daga ni se yara sai kuma Nabil daya tare min duk ya hanani saƙat kwana goma Ummi tayi kafin ta dawo nan ta same ni kwance ina fama da zazzaɓi “Ummi sannu da zuwa ya ƙarin haƙuri kuma? Ubangiji ya gafarta mata Allah ya mata rahama”
“Allahumma Amin Jiddah sannu ya jikin naki? Nabil yake sanar dani rashin lafiyan ki meyasa bakuje asibiti ba?” lumshe ido kawai nayi ina jin yanda cikina ke juyawa “Kinga bari na kira Nabil ɗin yazo muje asibiti..” dakatar da ita nayi ta hanyar faɗin “A'a Ummi ki bari har ki huta mana” dakatar da ita Ummi tayi tare da kiran Nabil nan suka nufi asibiti gwaje gwaje da Aune aune suka shiga mata ƙarshe de gado aka basu dan yanayin jikin nata sai a hankali sai washe gari, sakamako ya fito da wani irin murna Nabil ya rumgumeta yana faɗin “Alhamdulillah Allah na gode maka ashe ina da rabo nima Thank you for the last night Thank you Fadilah Dan nasan a gidan ki muka samu Baby...” Ai fita sukayi gabaɗaya har Ummi domin Nabil kan ya zama mara Kunya sosai sukayi farinciki ganin tana da ciki gashi yana ɗan bata wahala sai da ta kwana uku aka sallamesu bayan kwana biyu suka fara shirin tafiya saboda mutanen Chadi sun matsa sosai akan su koma badon taso ba haka ta fara shirya kayanta sauran kwana ɗaya tafiyarsu Arab ya zo tare da Aakif da wani irin murna ta rumgume ɗanta harda hawayen farinciki cikin tsananin jin daɗi shima yace “Umma na! Shine kika barni bakya zuwa gurina da Abba na!” shuru kawai tayi tana shafa kan yaron tare da kissing fuskanshi “Kayi haƙuri Aakif amma yanzun in sha Allahu komai ya wuce ina tare da kai zamu kasance tare har abada”
“To umma meyasa ba zaki zo mu zauna tare da Abba na ba?” miƙewa Nabil yayi dan basu damar ganawa da juna sosai, da kallo ta raka shi se take ga kamar maganar Aakif ɗin ne ya ɓata mishi rai Nan ta shiga mishi faɗa tare da faɗa mishi babu wani sauran zama tsaninta da baban shi hasalima tare zasu koma Chadi yaje yaga family ɗinta sannan zai zauna gurinta “Wallahi bani zuwa ko'ina batare da Abba na ba...” buge mishi baki tayi tare da faɗin “wani irin tarbiya ce wannan? Ina ilimin da ake yabon ka dashi? Ni mahaifiyarka ina faɗa kana faɗa Abokiyar wasan ka ce ni? to ka buɗe kunnuwanka da kyau gobe tare zamu tafi” shigowa Ummi tayi tana faɗin “Ya ya meya faru nake jin tashin muryan ki?” cike da jin haushin abinda Aakif yayi mata ta sanar da Ummi kallon Aakif Ummi tayi kafin tayi wani magana ya rigata “Ni wallahi babu inda zanje batare da Abba na ba..” Ummi tace “A kul! karka sake kuskuren ɓata mata rai kasan damuwa da ƙuncin data shiga duk saboda kai? Kasan irin wahalan data sha kafin ta saba rayuwa batare da kai ba? Haba Aakif ban sanka da wannan halin ba..” “Ummi ai bata sona inda tana sona to meyasa tayi wani Aure? taje tana jin daɗi ni kuma ta barni har wani baby aka ce zata haifa ni gaskiya bazan je ko'ina ba tayi tafiyarta kawai tunda tana da wani Mijin” Kuka Jiddah tasa tana kallon yadda yake magana yana cika yana batsewa tare da tamke fuska kaman bashi yayi maganar ba “Ummi kina ji ko? wai dan Allah meyasa rayuwa take juya min baya? tsawon shekaru ban saka shi idanuna ba, duk kewarsa da nayi da irin kalaman da zai tare ni kenan wallahi nima yayi zaman shi bani zuwa dashi ko'ina bare yaje yana rena min miji..” Ummi tace “Kaci gidanku ka duka kaba mahaifiyarka haƙuri ina ruwanka da Auren ta! laifi ne dan ta rabu da mahaifinka kai baka san ƙaddara bane? Kayi gaggawan bata haƙuri kafun na saɓa maka shashashan banza, shi uban naka yasan da haka ya sake ta”
Kuka ya saka yana jin Haushin abinda Jiddah tayi domin shi duk a tunaninsa batayi wani Aure ba. “Kiyi hakuri amma gaskiya babu inda zanje bazan iya zama inda babu mahaifina bare ayi mini Kallon agola...” “Innalillahi ummi kina jin abinda yake faɗa ko? irin abunda nayi gudu kenan tun farko gashi an ɓata min yaro babu tarbiyan arziki nasan da tun farko yana tare dani da hakan bata kasance ba Dan Allah Aakif karka ƙara min damuwa kayi hakuri Nabil ɗan'uwa nane ina Son mijina shima Abban ka ne tunda Yayana ne...” “Ni ba Abba na bane kuma na faɗa bani zuwa ko'ina kawai kiyi Haƙuri in da rabo wata rana zanzo amma banda yanzun Kina son mijinki Nima Ina son Abba na” duk yanda taso ya fahimce ta yaƙi sauraronta tayi lallashi ita da Ummi amma ina ya kafe akan babu inda zaije karshe haka zuciya ya ɗibeta seda ta kikkifa mishi mari Amma ko a jikinsa ranan tayi kuka sosai a dalilin haka ta ɗaga tafiyan tana tunanin ko zai sauko ya saurareta da safe ne suka gaisa da Arab inda take mishi ta'aziya kallonta yayi tare da murmushi yana amsawa zuciyarshi a sake domin yanzun baya jin wani rigima ko tashin hankali “Amma gaskiya Yallɓai banji daɗin tarbiyan da aka yiwa yaron nan ba, ya za'ayi ina magana yana magana sam banji daɗi ba”
“Kiyi haƙuri insha Allahu zai zo tunda yanzun yaƙi ki ƙyaleshi zan lallaɓa shi” cikin tsananin fushi Jiddah tace “Bana son a sangarta min yaro bana son goyon sangarci a bashi tarbiyan data dace bayan haka ina maka fatan alkhairi Allah kuma ya sada mu da Alkhairinsa bana jin zamu sake haɗuwa ban sani ba ko Bikin Jumana idan me gidana ya yarda to, dan Allah ina sake jaddada maka a kula a san irin tarbiyan da za'a dinga bawa yara” daga haka sukayi sallama har ta juya tana tafiya sai kuma ta juyo tana kallonshi tare da ɗan sake fuska “Na gode Jiddah ina miki fatan samun farinciki me ɗorewa a rayuwarki Allah ya sani ina Ƙaunar ki babu yadda na iya ne”
Ɗauke kanta tayi sakamakon ganin Nabil dake tsaye nesa dasu yana jiranta ba tare da tace mishi komai ba ta nufi gurin mijinta.
Kwana biyu tsakani suka tafi ita da Nabil Aakif kan ya kafe babu inda zashi.
*** ** ***
Sun isa lafiya inda kowa ya shiga nuna mata soyayya tare da kulawa na musamman lokacin da suka samu labarin Juna biyun da take ɗauke dashi sunyi murna sosai haka ma Nuwairah tayi matuƙar murna tare da Addu'a Allah ya bata in tana da rabon Haihuwa Mama-sadin ma tayi murna sosai sai dai taji babu daɗi na rashin zuwan Aakif a hoto kawai ta ganshi amma duk da haka bata cire rai da zuwan nashi ba, tattali soyayya ƴan'uwa da soyayyar miji tare da Ƴar'uwa ta Abokiyar zama su suka sake kwantar min da hankali yanzun bani da wata damuwa wadda ya wuce Allah ya sauke ni lafiya kullum muna magana da Ummina ta video call su Halimatu ma haka, Hanisa yaranta Biyar yayinda halimatu take da huɗu, wata tara da kwanaki Allah ya sauke ni lafiya inda na samu Asma'ulhusnah rayuwata a Chadi cikin dagina abun farinciki ne, muna zaman mu lafiya babu me jin kanmu ban samu zuwa bikin Jumana ba amma na yiwa Nafisa aike daga ɓangaren dangin Mahaifina ma muna waya sosai kuma ina tura musu da duk abubuwan bukata ban manta da mutanen da suka tallafi rayuwata ba kamar matar me anguwa da mijinta ina musu alkhairi daidai gwargwado a baki Nuwairah nake jin labarin Aaliyah ta

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads