Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 81184 words

Chapter 2 - Sirrin Daukaka Book Complete by Aisha JB .txt

Ads the beginning of article before Image

30 May 2024

1111

Ads at the middle of Article

alaman i'tama kuƙan take son yi Larai ne ta shiga mana nasiha kafin tace "Asma'u sede kiyi hakuri Usama ya rigamu gidan gaskiya" tun lokacin da Larai ke magana mama tayi shuru tana kallonta cak kuƙanta ya ɗauke wani i'rin abune ya tokare mata makoshi da kyar ta i'ya faɗin "Allahu akbar.. Allah kaji ƙan usama. mijina me kaunata! mijina meson dariya da farin cikina.
"Allah ka saukarwa Ado masifa da bala'in dayafi karfinsa Allah ka haɗashi da ajalinsa kaman yadda ya zamo ajalin mijina Allah ka tozartashi kaman yadda ya tozartamu Ya Allah na roƙeka kabani hakuri da jurinyan rashin mijina uban 'Ya'yana Allah kakai haske da rahama kabarin Usama Allah..." kasa, karasa maganan tayi sakamakon kuka da yakwace mata wanda bata san da zuwansa ba. tana kuka nima inna kuka Larai nata bamu hakuri dakyar na tsayar da nawa kuƙan na kara matsawa jikinta na ɗaura kaina a cinyarta fuskana na kallon nata hawayen idanunta na ɗiga a fiskana.
Hannu nakai fuskanta tare da share mata hawayenta "Ya zamuyi da Ƙaddararmu Haka Allah ya tsara mana Hakuri shine kalman da kullun Baba yake faɗa komai ya fito bakinsa seya haɗa da hakuri se yace muyi hakuri watarana zamuga riban haƙan, sannan duk wanda ya nufemu da sharri mu, mubisa da alkhairi, Mama kiyi hakuri kidena kuka bana son ganin zuban hawayenki hankalina tashi yake.." shuru Asma'u tayi "shi kenan Jiddan Baba nayi shuru Allah ya kara mana juriya da, dangana"
"Ameen mamana"
Kallon larai Asma'u tayi kafin tace "Dan Allah kimin magana da liman" miƙewa Larai tayi kafin tace "Toh" ciƙe da tausayawa Abinci larai ta aiko musu dashi Kallon mama nayi tare da buɗe kwanon samiran tuwon masarane da miyan kuka "Mama kici abinci" girgiza mata kai tayi " a a Hauwa bana bukatar abinci a yanzun... "Dan Allah mama karkice haka yaushe rabonki da abinci ai ko dan ƙani ko ƙanwata ya kamata kici" lumshe ido mama tayi "Bazaki gane ba, Hauwa ki bar maganan abincin nan kawai.." kuka nasa mata da sauri tace "Ya isa haka zanci" ɗan murmushi nayi kafin nace "yauwa mamana buɗe baki na baki" buɗe bakinta tayi nan na shiga bata tana haɗiya kawai take tana kallona hawaye nabin fisƙanta loma biyar na bata ana shiga ta dakatar dani.
"Ya isa haka kema kici" Girgiza mata kai nayi "Base naci ba burina na cigaba da baki har ki koshi.."a a Hauwa kici abinci" rufewa nayi kafin nace "Anjima zanci" Liman da larai suna tsaye suna kallonsu abin sha'awa ya basu ganin yanda yarinya karama take nunawa mahaifiyarta kulawa abinda ya kara birgesu yanda Jiddah ki magana cikin kwantar da murya tare da rarrashi yarinyar da i'ta ya kamata abaiwa wannan kulawar kai! gaskiya Rayuwa ba abakin komai take ba, ta ko'ina Allah yaga dama seya jarrabi bawansa kuma baka isa ka tsallakewa wannan kaddarar ba, Bar ganin Kanada dukiya ka samu duniya kana cinsa yanda kake so kaci me kyau kasha me kyau, ka sanya me kyau kana tafiya cikin isa da izza masu baka kariya nabiye dakai a baya in mota zaka shiga za'a buɗe maka kana zama za'a rufe maka matuƙinka na gefenka duk inda kake so nan za'a kaika mutane na bauta maka sabida dukiya kai kuma a lokacin jin kanƙa kake kafi kowa babu wanda ya kaika zaka taka kowa son ranka! Sufa wanda kake nuna musu isa da izza kake takasu yanda kaso ba finsu kayi ba! domin suma Bani Adam ne kaman yanda kake banbanci shine kai Kanada dukiya, suma in Allah yaso lokaci ɗaya seya kwace naka ya basu nikin ba ninkin naka, Allah yasa mudace Allah ya rabamu da kwaɗayi da ruɗin DUNIYA sallama Liman yayi a hankali Asma'u ta amsa mishi miƙewa nayi naje na kwanko hannuna na dawo "Hauwa in sauran kayan mu na kusa ki duba zaki sami takarda ki ɗauko" hakan kuwa tayi karɓan takardan Mama tayi sannan ta miƙawa malam "Wannan takardan yana ɗauke da sunan Mu'azzan da numbobin wayarsa da adireshinsa mu'azzan nabin usama dubu talatin shekara guda ke nan da watanni babushi babu labarin sa ganin halin matsin da muke cikine yasa usama yanke huƙuncin biyan bashi da Hauwa kafin ya rasu sede ya faɗamin kuma jadda damin nan ta kwashe komai ta faɗa musu sunkuyar dakai kawai nayi inna hawaye "Dan Allah liman ka dubi halin da muke ciki da wanda muke shirin shiga ka samo mutumin nan Hauwa ke kuma kiyi hakuri bamu da yanda zamuyi bamuda shi bamu bawa wani ajiyan sa ba dolence tasa mahaifinki yanke huƙuncin haka" liman yace "insha Allahu zanyi i'ya kokari na gurin ganin na samoshi Allah yaji ƙan usama" da dare ina zaune saman sallaya mama na kwance saman katifan larai duk munyi shuru ga abincin da larai ta kawo mana na dare miƙewa nayi na ninke sallayan tare da cire himar ɗin dana saka "mama abinci" Buɗe idonta da sukayi ja tayi "kici Hauwa inna sane ɗazun bakici ba.. "a a mama ki faraci kafin naci" miƙewa tayi "To shi ƙenan" yanzun ma kaman ɗazun a baki na bata shinkafa da mai da yaji bataci sosai ba ta juyar da kai ruwa na bata ina shirin rufe kwanon ta buɗe nan ta shiga bani dolece tasa nakeci haka ta bani seda ta turamin abincin sosai kafin ta barni. ruwa nasha nazo na kwanta kusa da i'ta Larai na ɗakin liman a haka har barci ya ɗauki mama niƙan idona biyu domin tunda Baba ya rasu na kasa barci tunanin halin da zamu shiga nan gaba nida mahaifiyata da abinde ke cikinta nakeyi domin nasan zaman mu a gidan liman bame ɗorewa bane tun ina kuƙan zuci har ya fito fili ban saniba Hannun mama kawai naji tana share min hawaye na "Ki dena kuka Jiddan baba, Allah yana sane damu be manta damu ba , Hakuri kawai zamuyi mu rumgumi kaddararmu" a daren nan mama tamin nasiha sosai kuka nake wiwi na kasa tsayar da hawayena ashe na bankwana takemin ashe i'tama tafiya zatayi ta barni ta samin albarka tamin addu'a sosai tana shafa kaina tana magana har barci ya ɗaukeni ban sani ba kallona kawai take i'tama barci ya ɗauketa da sanyin asuba ne ya farkar dani har yanzun hannun mama na ɗaure a kaina juyowa nayi na kalli fiskanta tayi fayau se wani haske da tayi zare hannunta nayi nafita naje nayi ɗahara kafin nayi alwala na dawo ɗakin ana kiran sallan asuba naje inna tashin ta "mama lokacin Sallah yayi" a hankali nake magana amma shuru bata amsa min ba ganin haka yasa na taɓata "mama ki tashi haka lokacin sallah yayi" shima shuru kafin na sake magana sega larai "Har kun tashi" a hankali nace "na tashi mama ne take barci ina tashinta taki tashi ma" hannunta larai ta kama nan taji ya sake da sauri ta ɗaura kanta a setin zuciyarta amma ina rai ya riga da yayi halinsa domin kominta baya motsi "innalillahi wainna ilaihi rajiun Allah ya miki rahama Asma'u" bansan lokacin da nayi zaman ƴan bori a kasa ba ɗif nadena jin komai....






Maman Faruq
12/26/23, 8:58 AM - UMMI JB: *SIRRIN ƊAUKAKA..*

_Wattpad@ayshajb_


Free Book


*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*





Page3 .
..........Salati kawai Larai takeyi kafin tayi kaina "Hauwa! Hauwa!!" Amma shuru da sauri tayi waje Liman da shigowarsa Kenan ya dawo daga masallaci yace "Lafiya naganki haka?" Larai tace "malam lna fa Lafiya! Asma'u ta rasu.... " Be gama jin maganarta ba ya nufi d'akin Nan ya tadda Jiddah kwance Larai na shigowa yace ta kawo masa ruwa da sauri ta d'ibo ruwan ta kawo masa shafamin yayi a fiska ajiyan zuciya na sauke ban bud'e idanuwa ba , kuka na fashe dashi shi Kenan banida uwa bani da Uba , babu dangi Na rage ni kad'ai dagani se Allah se Kuma halina wayyo haka tawa K'addarar take yanzun babu Wanda zan kalla inji Dad'i ..
"Kiyi Hakuri Hauwa.." Da sauri na katse shi "To ya zanyi inba hakurin ba! Banida kowa fa! Babu ! ni ce fa ni D'aya! Kai!!." Wani irin kuka na sake fashewa dashi Bani da Gata fa yanzun , Larai da wasu mata makotanta ne sukayiwa Mama wanka malam yaje ya siyo likkafani ina kwance inna kuka har aka gama had'a mama Akayi mata sallah koda akace inje in mata addu'a kasawa nayi rik'e mankaran nayi inna kuka harda majina na kasa furta komai ganin na jima ne yasa Larai zuwa inda nake wai zata d'agani Amma tayi tayi naki tashi karshe de maza ne suka d'agani a gaban mankaran inna ihu da shurewa haka suka d'agani fad'i kawai nake "ku barmin mamana ku wasu i'rin azzalumai ne me yasa bazaku tausayamin ba , mamanace fa zaku tafi min da i'ta so kuke rayuwata ta tagayyara? banida uwa bani da uba ya zanyi kuji tausayi na mana haba! Bayin Allah..Wayyo Allah jama'a kuna gani zasu tafi min da UWA" mutanen dake gurin seda suka kokamin na zama wata iri bani da aiki se kuka abinci bana ci magana ma banayi Sallah kad'ai shike d'agani satin mama D'aya Liman ya shiga niman mu'azzan Balarabe Numbobin wayarsa baya shiga kullun aka Kira a kashe zuwa lokaci na fara saka juriya wa zuciyata sabida kullun Liman da matarsa hard'a 'ya'yansa haka zasu tasani gaba suna tausar zuciyata da kalamai masu kwantar da hankali hakade nake daurewa ina cin abinci badon inna jin dad'insa ba, bana son gwalesu ne kawai suna kokari dani banida abinda zance musu sede Allah ya saka musu da alkhairi Wata D'aya da kwana biyar aka samu wayar Balarabe bansan abinda Liman suka tattaunaba nede yace min sunyi waya da mu'azzan hakan ya faru da kwana biyar se gashi sunzo su biyu .
Dangin mahaifina babu Wanda yazo Kuma an aika musu haka lokacin da Liman ya aika a kirasu ko da Wanda ze wakilci auren Amma babu Wanda yazo karshe shiya tsayamin wanda sukazo da mu'azzan ya zama waliyinsa A masallaci bayan sallan azahar aka d'auramin Aure da mutumin da bansan waye shi ba.
Kai! ranan nayi kuk'an da yafi na ko yaushe Larai tasani a gaba nayi wanka i'ta ta bani sabon kayan yarinyarta D'aya na saka Wai Ashe a ranan zamu tafi ban sani ba se da Akayi la'asar tace in had'a abinda ya dace na d'auka "Inna nifa ban gane in had'a abinda ya dace ba" Larai tace "Hauwa tafiya zakuyi.." da sauri na Mike har inna dafe Qirji "Ni dawa zamu tafi Kuma inna ne?" Murmushi Larai tayi kafin tace "Keda mijinki Kinga shi ba d'an garin nan bane..."
"Nashiga uku da Allah kimin rai mutumin da bansan wanene shiba zan bishi wayyo Allah kumin rai" kamoni tayi tare da zaunar dani "Hakuri zakiyi Aure babu inda baya Kai mutum.." nasiha ta shiga min Liman ma ya shigo ya d'ora da nashi nasihar Inna kuka suka karkatoni gurin jibgegiyar motarsa Mu'azzan dake zaune a mota shida abokinsa suna Hira cikin hiran abokinsa yace "Kai kaga yarinyar Kuwa Arab daga ganinta akwai nutsuwa kalli yanda take zuwa k'anta a kasa" mu'azzan yace "Wallahi inna tausaya mata yanda Zata shiga cikin iyayenta" Dariya Abokinsa yayi sannan yace "Gidanka Gobara ne zasu iya sata zuba mata fetur su k'yatta mata ashana" runtsa ido yayi yana tuna Gobaran dake gidanshi.
"Dan Allah kalleta fa , karaman yarinya 'yar sha uku" fitowa sukayi Abokinsa ne ya karb'i bakon kayana yasa a bayan motar Baya ya bud'e Inna kuka na shiga k'ankame jikina nayi tare da cusa kaina a gwiwa na kuka nake wiwi haka naji tashin motar Kara sautin kuka na nayi suna tafiya ba Wanda yace min ci k'anki tafiya yayi nisa min munfita Obudu har mukazo Gboko har muka bar jihar benue inna kuka daga Nan muka d'auki hanyar abuja barci barawo ne ya d'aukeni Inna sauke a jiyan zuciya Jin shuru na Dena kuka ne ya sashi lik'awa Nan yaga wiyanta ya karkace "Adam tsayar da motar na gyara yarinyar Nan" ba musu ya tsayar fita yayi tare da bud'e baya kwantar dani yayi sannan ya dawo gaba yana zama yayi shuru Adam yace "wayaga mijin mata hud'u ta hud'un ma yarinya yar Sha uku.. Allah sarki yarinya har na hango yanda za'ayi wasan qwallo dake" dukan wasa Arab ya Kai mishi "banson Shakiyanci mubar wannan maganar Wallahi fargaba na bansan yanda zamu kwashe dasu ba" tsaki Adam yaja "inna jin takaici haba se kace ba namiji ba! Ka tsawatar musu ma ya gagareka Wai ace kana da mata har uku ba kwanciyar hankali fitinar yau daban na gobe daban wallahi idan ka Kai musu wannan mareniyar suka cutar da i'ta kai da Allah domin bawai biyan bashi kad'ai aka baka ba, wallahi amanace iyayenta suka baka inka barta matanka suka nakasata Kai da Allah" Arab yace "naji Kai gwara na kaita Zaria ko na mikata Gurin Hajiya kawai , mahaifiyarshi Kenan" Adam yace " wallahi kanada aiki gwara de ka Kai musu Susan matsayinta a gurinka" Arab yace "shike Nan" a haka suna hirarsu har suka karaso abuja.
Nik'an innata ramuwar barcin da banyishi kwanakin baya ba Gidan shi nacan gaba da babangida market , Gidane babba Wanda fad'ar had'uwa da tsaruwanshi bata lokacine hon adam yayi megadi ya bud'e mishi kofa yana gama fakin suka fito hannu Adam ya Mika mishi sukayi musaba daga Nan ya Mika mishi makullin motarsa "To abokina fatan alkahairi zan d'auki motana nima naje naga tawa Matar a kula da 'yar mutane Dan Allah" Arab yace "nagode a gaida Maryama" Adam yace "insha Allahu" bud'e bayan motar yayi tare da Kiran sunana jiddah bud'e ido nayi "fito Arab na jiranki"
"Waye Arab?" Adam yace "To mijinki" take idona ya kawo ruwan hawaye haka na fito kai seda na tsorata wallahi na d'auka ba mutum bane farinshi yayi yawa kaman ka tab'a jikinshi jini a fito kasancewar d'azun ko kallonsu ma banyi ba bare nasan yanda yake babban mutumne Amma kud'inshi ya b'oye girman nashi.
Gaba yayi nabi bayanshi muna doso kofan gabana ya buga ras tsayawa shima yayi kafin ya juyo ya kalleni girzgiza k'anshi yayi tare da tura kofan kwan..! Se sauk'an kofin glass a goshin sa har hulanshi ya fad'i dafe goshin yayi tare da fad'in "waiku wasu i'rin dabbobi ne! Kullun se kuci ku hau ihu kaman karnuka ! jubi Gidan Nan kullun a hargitse ni Kenan inna da mata uku bani da kwanciyar hankali haba! Haba!! Wannan wacce i'rin masiface" nide kasa nayi na d'auko hullanshi ji kawai nayi an fisge Juyowa nayi Dan inga wacece wata farar mata ce fiska a d'aure ta kalleshi sannan tace "Ibrahim Nafisa ce masifar ko Zainab dan ni Fure wallahi baka isa ka kirani da masifa ba Ga karnuka nan..." tana nuna Nafisat da Zainab "Kutuman uban Amma ke Fure'atu anyi yar..." Faf Fure ta make mata baki Nafisat ta kamo wiyan rigan Fure "ke yanzun Dan Kinga kinyi Kiban rashin zuciya shine zakice min kariya kazama dake shegiya me warin hammata..." Wallahi bansan lokacin da na k'yalky'ale da dariya ba kalli tib'a tib'a dasu Wai suna fad'a da junansu.. juyowa sukayi shi kuwa ya jani bayansa Dan yasan halinsu zasu i'ya makeni a gabanshi ba damuwarsu bane "Ke Kuma daga l'na aka rarumoki kasan de bama bukatar 'Yar aiki ko?" Arab yace "Kai! Kai!! Ya isheni haka haba!! Duk kunbi kun cikawa mutum kunni..." ZAINAB tace "Heee Tsaya nima kana cikamin kunni Bayani zaka Mana wacece wannan?" Ta karasa maganar tana jawoni "ku zauna na muku bayani to" Zama sukayi a kasa dukkansu domin kujerun ma an turasu gefe tsaban fitina da bak'in kishi i'rin nasu.
Seda ya jawo D'aya ya zauna domin be i'sa yace a kawo mishi abin Zama ba yana Zama ko sauke numfashi beyi ba Nafisat tace "munajin ka" Arab yace "yanzun ko arzikin ruwa da abinci bazan samu ba..." Fure tace "Kai kai dakata lbrahim babu baiwarka anan ka Mana bayani wannan" nunani tayi Arab yace "Matatace.." wayarshi ne yayi kara mikewa yayi tare da fad'in "Ku bata abinci da masauki inna zuwa" fita yayi da sauri yana Kara wayan a kunninsa.. a sukwane Fure ta tashi hannuna ta kama "ke fad'amin Gaskiya Wai da gaske Auro ki yaje yayi ko sadakarki aka bashi domin nasan halin mijina seya wanke hannu kafin yake zab'o mace kalle ni da kyau ki kalli sauran kin gammu da muni?" Girgiza mata Kai nayi Nafisat tace "fad'amin da gaske ke matar shi ce?" Shuru nayi Zainab ta zaburo tare da daka min tsawa "Ke ba magana ake Miki ba!" Da sauri nace "Eh Eh matar sa ce ni..." Ai ban rufe baki ba naji ta d'aukeni da mari fau.. har seda gefen bakina ya fashe da sauri Nafisat tayi kichin galan d'in karanzir ta d'auko tashiga zazzaga min a jiki Zainab ta cire min himar ihu nasa Fure taje ta d'auko a shana Tsayawa tayi tana karemin kallo "in banda maza ma da shegen jaraba uban me zeci a jikin wannan yarinyar Qirji a shafe ba cinya ba sharab'a Yau zakije lahira in aka tambayeki ya'akayi kikazo a haka kice *Matan Mu'azzan Balarabe* ne suka jefoki baki shirya ba tana shirin k'yatta ashana ya shigo a guje dan tun a waje ya fara jin hayaniyan su yana doson kofan yaji ihu na abinda yasa ya shigo a guje ke Nan ture fure yayi ta fad'i ragwajan kafin suyi wani Yunkuri ya d'aukeni kaman yar Baby da sauri ya fita Zainab da Nafisat ne sukabi bayanmu "Bud'e min Get da sauri" makuli yasa ya bud'e motan domin gudun ma be karb'esu ba Sabida Kiba Ta gurin Direva ya turani a kujeran gefe motan ya shiga yaja kofan a guje yaja de de lokacin da suke karasowa da gudu suka rufa mishi suna nishi "Zainab tace zaka dawo ka same mu wallahi" juyowa sukayi kowa na zuba masifa a bak'in kofa suka samu Fure'atu "Ina suke?"

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads