Showing 6001 words to 9000 words out of 81184 words
Chapter 3 - Sirrin Daukaka Book Complete by Aisha JB .txt
Cewar Fure Nafisat tace "Ya tafi" Fure tace "aikuwa ze dawo ya sameni" Zainab tace "i'rin ke kad'ai ce matarshi dole ya dawo ya sameki ai"
Maman Faruq
12/26/23, 8:58 AM - UMMI JB: *SIRRIN ƊAUKAKA*
_Wattpad@ayshajb_
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*
Page4 .
............Yana tuƙi yana shafa goshin shi‚ domin kofin Da aka jefo masa harya fasa mishi gurin Tausayi ya bani har bansan lokacin da na cire D'ankwalin kaina na mika mishi ba cikin masifa yayi magana "Ke dallah barni wannan kayan karanzir d'inne zansa a jikina Allah ya kiyaye duk ba ke kika jawomin wannan fitinan ba" Shuru nayi tare da mayar da d'ankwali na‚ kuka nasa inna mishi ihu harda dukan kujeran da nake kwance "Wallahi baka i'sa ka d'aukoni daga garinmu ka kawoni cikin wannan kattin banzan ba ance maka bani da gata ne! su sumin kaima ka fasamin kai da ihun ka wallahi kamayar dani inda kad'auko ni" gaangarar da motarshi yayi tare da tsayarwa "Ke! Da kike maganar kina da Gata uban waye gatan naki inba ni ba haba! wannan wacce i'rin masiface haka ! karna kuma ji kin kiramin matana da Katti inba haka ba wallahi zakiji a jikinki" wallahi bansan ina da masifa ba se yau "Allah ne gata na domin kai ba gatana bane , matanka kuma nace katti kayi duk abinda zaka min kai! nifa ba jakarsu bane da zasu fasamin baki wallahi sena rama kuma karka karacemin masifa domin ka barosu a baya kuma zaka koma ka taddasu domin na rantse da wanda raina ke hannunsa baka i'sa kamar dani wancan hargitsattsen gidan ba, Gidan jahilai wanda basu san kishi ba..." fauf ya bigemin baki "Allah ya isa kai kaci zalina matanka suci Zalina akwai Allah wallahi kuma seya saka min tunda ban muku komai ba" inna fad'ar haka naci gaba da kuka Na shikuwa shuru yayi ganin haka yasa nace “Nifa bansan amfanin tsayuwarnan da kayi ba in baka da inda zaka kaini ka bud'emin mota na fita.." Hannu ya d'agamin tare da d'aukan wayarshi dake kara tun d'azu “Adam wallahi akwai katon matsala kaina duk ya kulle bansan Ya zanyi dasu..." Nan ya kwashe komai ya fad'a mishi me Adam zeyi kuwa in banda dariya matarshi dake gefe ta rik'e baki tana kallon i'kon Allah Arab yace “Kaga malam banson hulak'anci ya zan fad'a maka abinda sukamin maimakon ka bani shawara se ka b'ige damin dariya mahaukaci ka mayar Dani?”
Adam yace “a a yi Hakuri yanzun kuzo Gidana Amma kafin nan ka siyo mata wasu kayan da Zata canza” Arab yace “Toh” duk inna jinsu kala bance mishi ba ya tada motar munyi nisa da tafiya kafin ya tsaya kusa da wani kantin kaya inna zaune a cikin mota ya fita ya siyo ya dawo tafiya kad'an mukayi se gamu a kofar wani madedecin Gida Adam d'inne ya Bud'e Mana Get yana gama faka mota ya fito Arab yace “Wai kai har yanzun bazaka sa megadi ba? Kafi so in kayi bak'i kazo ka bud'e musu get in Kuma ka fita Ruma ce zata bud'e Get yanzun Kuna jin dad'i rayuwa haka?” Adam yace “Taya zansa megadi ya ringa kalle min mata a a wallahi inna kishin matata rayuwarmu a haka yayi in nafita na dawo tazo ta bud’e min kofa ina dalili" nik'an da zaman motan ya isheni na shiga bubbuga glass da sauri Adam ya bud'e min na fito wani uwar harara na maka musu kafin naja gefe na tsaya gaba Adam yai yana dariya “Arab ka Tara mata kutt kowa da guntun nata rigiman muje ciki" Matarshi Ruma na zaune ta amsa sallamarmu da fara'arta Zama nayi a kasa tare da fasa ihu Arab yace “Kefa na lura mahaukaciya ce karki tasar musu yara suna barci...” birgima nashiga yi ina duk'an kasa “wallahi ni ba mahaukaciya bace sede matanka sune mahaukata nide dan Allah kuce ya mayar dani garina na fasa Auren zan biyashi kud'insa” Hannu ya d'aga ze mareni Adam ya rik'e shi “Haba Ya zaka huce akan karaman yarinya marainiyan Allah wannan ba yi bane Gaskiya koda wasa karka sake marmarin D'aga hannunka zuwa jikinta Su sauran matan naka kana duk'ansu ne?” zaune na tashi “Wallahi daka barshi ya dakeni tunda na Zama jakarsu kalleni fa jikanin sukayi da karanzir zasu k'onani bayan sun fasa min bak'i shima dan rashin imani ya sake bug'emin bakina Allah daka barshi inya dakeni zan rama ai ba jaka bace ni‚ in Kuma Kuna ganin banida Gata babu me tsayamin dan,ni talakace akwai Allah zan Kai mishi karar ku tunda ba zaku iya duba maraicina ba” tausayinta ne ya kamasu maganarta Kuma gaskiya ne Ruma ta Mike tare da kamo hannuna “Kiyi Hakuri Jiddah Allah ze saka miki zo muje kiyi wanka se kici abinci” Mikewa nayi nabita “Gaskiya abokina abinda kayi kaida matanka be kamata ba yarinya karama zakusa a gaba haba Mu'azzan bansan ka da duk'an mace ba” Zama Arab yayi tare da dafe kai “Ni wallahi Adam bansan mesu Nafisat sukeso dani ba, kullun burinsu suga hankalina a tashe sun mayarmin da Gida kaman filin dambe ban isa Kuma na hanasu su hanu ba ya zanyi ne wallahi nagaji kasar zan barmusu na huta da wannan fitinar‚ Mata Uku ko Gobara?” ..
“Wallahi ka i'sa ka Hana Kuma su hanu inhar kaci gaba da nuna musu kana tsoronsu abinda zasuyi maka Nan gaba seya fi haka‚ Ga abinci kaci kaima se kayi wanka” Band’aki ta kaini Tsayawa nayi inna bin gurin da kallo kwab'a baki nayi zanyi kuka tace “Ya salaam! Meye Kuma?” Seda na gama cire kayana kafin nace “toya zanyi nayi wankan?” bata ja da tsayi ba tamin wanka tsefe kitson da yafi wata uku tayi tare da wanke min kai mun dad'e a bayin domin Gaskiya ta wankeni sosai Kuma na wanku sede hasken fatata ta fito tana wankeni tace “Masha Allahu Tubar khallah Ibrahim ta zab'o mana kala me kyau wankan tarwad'a” babban tawul ta bani da sufe jikina yayinda take goge kaina da karami seda ta busar min da gashin da wani abu ko menen oho gurin Jane na ringa mafa ihu domin da zafi Nan da Nan gashina na sake ya kwanto har wiyana‚ ga shi baki sid’ik Mayuka masu khamshi ta shafani dasu “Jirani inna zuwa” Falo taje Amma babu kowa ledan dake gurin ta bud'e Nan taga kayane doguwan riga me ruwan zuma ta d'auko da d'ankwalinsa Duk ta duba kayan babu kanfe dole cikin kayan yaranta ta samo karamin wando nasa Himar ta bani nasa Nan nashiga yin sallolin da banyi ba inna idarwa ana Kiran isha‚ sallan isha'in nayi naso inyi shafa'i da hutiri sena tuna inna tashin dare Dalilin da yasa banyi ba Kenan Zama nayi inna lazumi se takwas da rabi‚ nabar saman Sallayan duk abinda nake Ruma tana kallona ji kawai tayi na birgeta barinma yanda nake abubuwana cikin nutsuwa “Zo muje kichi abinci” Bin ta nayi har falon d'azun zama nayi a kasa ta zubomin tuwon shinkafa da miyan taushe se farfesun kayan ciki.
inna cikin cin abinci Ruma ta fara min fad'a “Jiddah karki Kara d'agawa Arab murya in yana fad’arshi in bazaki iya ce masa yi Hakuri ba karki kuskura ki tanka masa Sannan ki Dena ce mishi kin barshi da Allah Kinga babu kyau yima babba rashin kunya matsayin miji yake a gareki tunda wa'yancan banzaye sun kasa rik'eshi inna so ke ki rik'eshi ki jawoshi a jikinki sosai ki zama me share mishi hawaye a duk lokacin da yake kuka da halayyarsu ki zama maganin damuwarshi karki Kara d'aga mishi murya domin babu kyau mace ta ringa d'agawa mijinta Murya sannan innaso in yazo kice ki tsuguna har kasa ki bashi Hakuri matan shi Kuma babu runki dasu ki Dena ce musu katti Kinga sun girme Miki tsakaninki dasu mutumtawa da girmamawa Kinji” tunda ta fara min nasihar Nan nayi shuru ji nake kaman mamana ne take min magana cikin sanyi murya nace Mata “To nagode Mama Amma dan Allah kice ya Dena dukana iyayena har suka rasu babu Wanda ya tab'a dukana Kuma kice mishi ya Dena cemin mahaukaciya bana so kalman yamin zafi” sharemin Hawaye Ruma tayi kafin tace “insha Allahu bazai Kara ce Miki mahaukaciya ba matukar kikayi abinda nace miki Kinga anan zaku kwana Kuma d'aki d'aya inna so idan kunje kwanciya kice mishi ya yafe miki bazaki sake ba, Kuma Gobe ze kaiki Zaria ki gaida mahaifiyarshi daga Nan ze kaiki Kaduna Gidan Yayarshi i'ta zata rik'eki zata zame Miki uwa da uba domin malamace zata koyar dake abubuwa kala kala Dan Allah banda rashin kunya ki Mata biyayya kinji” Gyad’a Mata Kai nayi kafi nace “Amma kince d’aki D'aya zamu kwana Kuma babu kyau fa...” katseni tayi “Ai mijinki ne da kaman ba mijinki bane shine za'ace babu kyau” ..
Kafin na Kuma cewa wani abu se gasu sun shigo kasa kasa na kalleshi Nan naga ya canza kaya da alama shima yayi wanka tab'ashi Adam yayi tare da yin magana kasa kasa “Kai Arab kaga Amariyarka kuwa Gaskiya ka samu mata Ashe haka take da kyau” Had'e Gira Arab yayi ba tare da yace komai ba sema satar kallonta da yakeyi batare da anlura dashi ba ‚ Zama sukayi Arab yace “Sannu da kokari Ummuh Rumana” murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba “Karfe Tara fa ya gota madam na fara jin idanuna na rufewa Arab asuba ta gari ga makullin d'akin” Karb'a Arab yayi Adam na shiga d'akin Ruma shima Arab ya Mike ya bud'e kofa “Tashi kije ku kwanta karki manta Kuma da abinda nace” wanke hannu nayi nace Mata “Seda safe Ummuh” Murmushi nima tamin kafin tace “Allah ya tashe mu lafiya” kwashe kanunk'an abincin tayi seda ta gyara Gurin kafin ta kashe kwan wutan ta nufi D'aki ‚ da Sallama na tura kofan yana zaune bak'in katifan dake shimfid’e a kasa ya amsa min Durkusawa nayi tare da fad'in “Allah kayi Hakuri da abinda na maka in Allah ya yarda bazan Karayin rashin kunyar ba” da sauri ya kalleni Mamaki ne ya cikashi shine yau mace take durkushe a gabanshi tana bashi Hakuri abinda be tab'a faruwa dashi ba lallai a gaida Ruma dan yasan i'tace tasa Jiddah “Kaji kayi Hakuri” maganarta ne ya Kara katse shi “Naji kema kiyi Hakuri da abinda matana suka miki” A hankali nace “Na Hakura Amma dan Allah karka sake kaini Gurinsu domin zasu kasheni ne tun kafin burina ya cika” ..
“Meye burin naki” Zama nayi sosai kafin na fara mishi lissafi “burina idan na girma nayi karatu na samu aiki zan Gina katon Rijiya Kuma inyi bohol zan Gina islamiya na marayu zan ringa tallafawa gajiyayyu...” cikin gajiyawa da maganarta yace “Naji Allah ya kaimu zoki kwanta kiyi barci nik'an barci nake ji” yana fad'in Haka ya shiga cikin Gadon tare da rufe kanshi da sauri Kuma ya bud'e bargon “na manta ga maganin a saman firizan can ki balle kisha seki kwanta”
Da nasha maganin memakon inhau Gadon sena koma na zauna tare da d'ora kaina saman Gadon shuru shuru beji tazo ta kwanta ba yasa shi mikewa “Ke a Haka zaki kwanta?” d'agowa nayi cikin turo baki nace “To ai ba kyau a kwanta gado D'aya da namiji” Dariyan Shakiyanci yasa sannan yace “Amma baki da hankali an fad'a Miki wani abu zan Miki? Me zanci a jikinki? Me zan shafa naji dad'i abu sur Kashi gani da cikak'ku had'add'un mata me zanyi da jikin yarinya! inma zaki zo ki kwanta gwara ki taso” murkud'a mishi baki nayi “oh koma menene nide nace bazan hau Gadon ba” saukowa yayi “To Ni na sauka jeki kwanta” Ai da sauri nace “Wa? Bade Ni Jiddan ba gwara ma kayi kwanciyar ka‚ ni hakan yamin” be ja da tsayi ba ya koma yayi kwanciyarshi nima a Haka na kwanta kayana.
Maman Faruq
12/26/23, 8:59 AM - UMMI JB: *♡SIRRIN ƊAUKAKA♡*
_Wattpad@ayshajb_
®️🌁
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..*
FREE BOOK
Page5
Barcin ma rabi da rabi nake yinsa domin tsoron ya taɓani nake ji can da barci ya fisgeni naji ya cicciɓeni ya dora saman gadon zabura nayi tare da kurma ihu jikina na ɓari dan ko gizau be yi ba, haka ya ajiye ni tsawa ya daka mata. "Ke mahaukaciyar lnace! in banda wawanci irin na ɗan kauye me zesa ki kwanta a kasa sanyi na shigarki, lna miki Gata kina kaucewa" na tsani tsawa ban sabaji ba, domin har iyayena sukabar Gidan duniya basu taɓa tsawata min ba, shiyasa na toshe bakina da hannuna kalmominsa sun ƙona min rai sosai ajiyan zuciya nake saukewa hawaye na wanke min fiska haka ya gama cimin mutumci ya kwanta abinsa takurewa nayi sosai lna ajiyan rai barci ɓarawone ya ɗauki "Bansan ki da wannan halin ba jiddah lokaci ɗaya kina kokarin fanɗarewa! raina na ɓaci in naji kina mayarwa mutumin daya amsheki batare da ya musa ba!, me akayi ko? hakuri zakiyi domin Guguwa na nan tana tunkaroki sekin tsunu ki sanyawa ranki hakuri... "amma Mama kina gani daga zuwana matanshi zasu kassarani shima zagina fa yake yi har cemin yai mahaukaciya yamin zafi! naji ciwo bazan iya ba!.." shafa kanta tayi kibar kuka kiyi hakuri da komai shi zaman duniya ɗan hakuri ne karna kuma ji kin ɗaga mishi murya.." Gyaɗa mata kai nayi cikin wani irin juriya nace "insha Allahu mama bazan sake ba" murmushi tayi tare da share min hawayen dake sauka kuka nasa sosai lna jin raina na zafi zan sake magana ta hanani lna kuka naji ya daka min tsawa ashe sosai nakeyi domin sautin muruyana na fita, "ke tunɗazu nake tashin ki kinyi banza dani kina kukan banza" miƙewa nayi jikina na rawa hawaye na zubamin ban taba tsintar kaina cikin quncin rayuwa irin na yau ba, hanyar banɗaki ya nunamin na shiga tsarki nayi da alwala lna fitowa naga ya shimfiɗamin sallaya ga himar ma , fita yayi nima na tada ikama sallanake inna kuka cikin sujadata lna kai karansu gurin Allah kaina nakasa har ya dawo ya zauna a gefen gado, ɗagowa nayi na sallame sallan ɗaga hannuna lna addu'a a bayyane "Allah kaji ƙan iyayena sanyi idaniyata abaɓen alfaharina allah yakai haske da rahama kabarinsu allah ya yafe musu zunubansu allah ya haɗasu da annabinka annabin rahama sallallahu alaihi wasallan, Allah na kawo karan wasu bayin ka, wanda sukayiwa rayuwata dirar bazata ba tare da na shiryawa haƙan ba, Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu Allah kamin katangar karfe dasu Allah duk wanda ya zalunceni kabimin haƙƙina Allah ka yafe kuskurena..."kukane yaci karfinta haka ta shafa addu'ar ta mike tare da ninke sallayar Tsungunawa nayi gabanshi "ina kwana?.." cikin masifa yace "daban kwana ba, zaki ganni? watou har karata kike kaiwa gurin Allah gani azzalumi ko?" ban kulashi ba na tashi haka ya ringa cin mutumcina ko cin kanka bance mishi ba, karshe ma fita nayi a ɗakin,
suna zaune a falo durkusawa nayi na gaida adam cikin sakin fuska ya amsa min "Ummuh lna kwana?" nace mata lna kara sunkuyar da kaina kasa "matso nan ƴata" domin a haife ta haifeta matsowa nayi na kwanta a jikinta kukan da naketa matsewa ne ya kwace min, kuka nake sosai shafa kaina tayi tare da faɗin "A duk lokacin daka tsinci kanka cikin Qunci rayuwa kace alhamdulillah base Allah ya jarrabeka da abin farin ciki zaka gode masa ba, ki zama me amsar kaddarar aduk yanda tazo miki.." gyaɗa mata kai nayi "inshaallahu nagode da tunatarwa" murmushi tayi sannan ta nuna min abinci kaɗan naci sabida raina a ɓace yake, miƙewa yayi bayan ya gama cin abinci "tafiyan kenan?" adam ya tambaye shi kallon agogon dake ɗaure Tsitsiyar hannunsa yayi tare da taɓe baki "lokaci na tafiya ki tashi" ya fad'i haka tare da tsare ni da ido rai a had'e danne kukan dake shirin kwacemin nayi tare da mikewa nayiwa ummuh sallama suna gaba lna biye dasu har gurin mota Ummuh ta rakomu tana mana fatan Alkhairi, hannun sukayiwa junansu kara rikeshi Adam yayi "Arab dan Allah ka sauko da zuciyarka kasa yarinyar nan a firgice take da kai.." "naji!" a takaice ya fad'a tare da bud'e motar ganin bana gaba yasashi tsayawa turus cikin bala'in yace "Ke fito ki dawo gaba!" lna zaune na jingina da jkin kurejar idona a rufe bamma san yana magana ba, domin nayi nisa a tunanin yaruwar data riskeni,
"Ke dan gidanku lna miki magana kin min shuru nine zan zama direvanki? "Kayi hakuri..." cikin kufula yace "fito ki dawo gaba" jiki a sanyaye na fito nan naga duk basa nan ajiyan zuciya na sauke domin na tsani cin mutumci a bainin naasi, haka na zauna na mayar da fuskana jikin glass lna kallon waje shigowa motar yayi tare da buga murfin yana jan tsaki nide ban kulashi ba, domin Allah kaɗai yasan abinda ke raina kiris nake jira na sauke nawa kwandon rashin mutumcin domin tunda ya shigo rayuwana hakurina yayi karanci,
***
Tafiya kurame shine tafiyar da mu kayi munyi tafiya sosai kafin ya tsaya a wani kauye fita yai yaje yin sallah ganin be cemin kala ba, nima na fita, ruwa na zuba a buta naje bayan gurin nayi tsarki sannan nayi alwala na rigashi dawowa cikin motar domin yaje siyan abinci koda ya dawo tekawey ya ajiye bemin magana ba nima kuma ban kulashi ba haka muka ci gaba da tafiya komai ya siya seya ajiye ni kuma banyi karanbanin tab'awa ba, ashe ranshi ya b'aci har barci ya fara fisgata ya taka wani wawan birki motar tayi gaba ta dawo baya kainane ya bugu na dafe hannunna a gurin lna cije baki domin naji zafi sosai ban zata ba , ya jawoni tare da had'a himar dina da wiyana ya shakeni sosai "Ni kika mayar asararre? in kashe kud'ina gurin siya miki abinci amma ki brshi ya lalace ga soko ko?" hawaye ne ya shiga zariya wani nabin wani da kyar nayi magana domin numfashi na ya fara barazanar barin ganagan jikina "Daka siya kace min Hauwa'u gashi? ko kace naci ne da zan d'auka ? an fad'a maka ni mayunwaciya ce , to ban bukata shi kenan! d'auki