Header Ads
Showing 57001 words to 60000 words out of 97223 words

Chapter 20 - JUHUD BY OUM HAIRAN .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

969

Ads at the middle of Article

hada dake na tsince muku zarafi yaran nan daga ita har mijinta basu damu da lamarin kowa ba ku kun damu dasu to waima Ina ruwanku da abinda ta Haifa ne ince dai nasu ne su suka Samar da abinsu ke yanzu bakiji kunya ba gotai gotai dake kizo kina yada girma gaban jikarki"
Hayayyaqo mata Dada Hanne tayi tana cewa eh dama Mana dole kice haka Aisha ai kinci kin qoshi mun kaiki matsayin da baki takaba a baya to dake da Mahfuz da Rasheedu da duk wani Wanda yake yaruwa a gidannan a qarqashin darajata yake balle wannan yar galaulawar da kuka kwaso kuka manna Mana saboda haka wlh muddin Ina raye Kuma Rasheedu daga tsatson sarki Waziri ya fito to dole ne a bani dannan mu karya masa maita takanas nayi tattaki har Kankia na karbo wannan maganin don tseratar da ahllinmu daga gurbacewa irin maita ai bala'i ne bazamu sake a lalata Mana halwa da son zuciya ba" Hajiya Bilki ce ta cafe da cewa “yo Dada Hanne da kike wannan mgnr jinki zasuyi ne ko zaa barsu su gane me kike nufi da gatan da kikeson yi musu ne ai anriga an lashe kurwas basuda katabus hatta Mai Martaban bashi da fuss indai akan wannan tsintacciyar magen ala qaqai dince kina gani fah saboda a samu a ceto yaron nan nabawa Alh Aminu shawarar yafadawa Mai Martaba tunda yaqi Hidaya ga Dijenan babu makusa in batafi ba bazaa fita ba ya aurawa Rasheed Amma yaron nan ya debemin albarka ta sama data qasa har Yana cewa indai halwata ce to har abada bayaso......"








Fashewa tayi da kukan munafurci nandanan Mom ta zuciya Mom akwai hqr da kawaici Amma tanada mugun zafi idan aka kaita qarshe ta miqe tace “Hanne ku fice daga bangaren nan tunda baa ginashi da sunan dayanku ba da sunan Dana Abdulrasheed aka ginashi Kuma iyalinsa ne a ciki munji ko Meenah zata rinqa sakatarmu da daidai munasonta a haka tunda danmu yanaso munafiki ya ciji yatsa maqi gani ya rintse ido insha Allahu Meenah saita haifi sarkin gobe a gdannan muga shegen daya Isa ya Hana Allah ikonsa magani ne bamaso mun gode bazaa bawa yaron nan ba indai ta jikin dana ya fita muga Wanda ya isa ya gwada ikonsa a gidannan"
Tana fadin haka ta karbe yaron a hannun Meenah data hada kanta da center table taketa kuka wannan cin mutumci da take jawa uwar mijinta yayi yawa itakam da tana da dama data fita daga cikinsu ko da samu salama to tunanin halin da Rasheed zai shiga shine yake takanta burki ya dauki amanar kansa da komansa yabata sun jibanci lamarinta sun yarda da kowanne irin cin mutumci indai akanta ne idan tace zata gudu tabbas batayi musu adalci ba domin ta kwaranye musu baya magautansu zasu samu damar yi musu dariya.






Kumbo Hami ce ta matsa jikinta ta riqe kafadunta tana jinjina girman halin da yarinyar take a ciki bata taba tunanin abun yayi qamarin haka ba dole yarinyar ta kasa sukuni cikin wannan ahli lamarin rashin kararsu azumin ne basa da mutumci ko kadan sosai kalamin Dada Hanne sun girgiza Kumbo Hami ta dago Juhud jikinta ta shige jikinta cikin kuka tace “don....don Allah Kumbo ki taimakeni kice da Rasheed ya hqr da zama dani tunda danginsa basa qaunata wlh zuciyata zata buga idan naci gaba da zama a cikinsu ya sukeso nayi ne da wanne zanji? Yaushe zanyi farin cikine yaushe zan samu salamar rayuwa nima kamar kowa, Allah inason mijina Amma lkc yayi da zan barsa na nemawa kaina yanci ina zangansu??"
Bubbuga bayanta Kumbo Hami takeyi cikin jimami tace “ki daina tuhumar ubangiji akan abinda bai kawo qarshensa ba Meenah meye laifin mijinki ne da zaki zabi jefashi cikin garari yanasonki baitaba kallonki da abinda wadannan debabbun ke kallonki dashi ba surukarki ta karbeki ta yarda da komai daya jibanceki kada ki bata rawarki da tsalle koda bazakiyi hqr domin Allah ba kiyi don wadannan ahlin mijinki mahaifiyarsa yan'uwansa da suka fito daki daya nasan Allah zai baki ladan saka Alkhairi da Alkhairi kada ki zama butulu rayuwar butulu bata qarshe me kyau kinji?"
Kwantar dakai tayi cikin yanayi na nadamar kalami tace “yanzu shikenan ni tawa qaddarar kenan Kumbo haka zanta rayuwa cikin tsangwama a cikin ahlin da ba nawa ba haka zan qare rayuwata ni a qunci halwata a qunci?" Murmushi tayi tace “kada ki cire tsammani daga rahamar ubangiji insha Allahu komai zaizo qarshe" da hikima irin tasu ta dattijan da sukaga jiya sukaga yau suke sa ran ganin gobe ta kwantar mata da hankali ta kwanta kanta na ciwo Aunty Hamida ta dauko Sarki junior ta kawo musu Kumbo Hami ta karbeshi ta zubawa yaron ido dan kyakkyawa dashi kamanninsa na ubansa hasken fatarsa na uwarsa.








Miqa mata shi tayi tasa masa nono ya kama Yana zuqa tana cije lebe zafi takeji sosai idan yanashan nonon hakanan take daurewa take shayar dashi bata jima da kwanciya ba bacci barawo ya dauketa cikin baccin taji ana shafa fuskarta tayi miqa tare da tallafe kan yaron ta zare masa nonon a bakinsa ta daga kai ta sauke idanunta da suka kumbura sukayi luhu² a kansa shima ita yake kallo yakai hannu ya dauki Mahfuz ya zubawa yaron ido yanajin qaunarsa data mahaifiyarsa na nunkuwa a ransa ya sake shafa fuskarta yace.
Kin biya Aminatuh Allah yayi miki albarka ya rayani tare dake" ajiyar zuciya taja me qarfi ya sake zubanta ido yace “naji labarin komai daya faru don Allah ki taimakeni kiyi hqr ki dainasa damuwar wadannan mutanen a ranki kinji" lumshe idonta tayi tare da lasar lips dinta daya bushe yace “talk me Mana" kallonsa tayi idanunta na tsiyayar hawaye tace “idan ya kasance nice matsalarka a duniyar nan Abdulrasheed meye yasa bazaka datseni cikin tarihinka ba ko ka samu record me kyau?" Sakin baki yayi yana kallonta ta zame daga gadon tace “don girman Allah mu hqr da zaman nan tunda mun kasa samun farin ciki a cikinsa Abdulrasheed bantaba zama silar farin cikinka ba saidai na akasinsa tunda ka janyoni ka hadani da rayuwarka taka ta gurbata ta ahlinka ta gurbace inda kai kadai ne da sauqi tunda kaine kaji ka gani Amma meye yasa saboda son ranmu da son zuciyarmu mu zamo silar yankewar farin cikin wasu Baffa'am Munjefa Mom cikin tsaka me wuya mun jefa Mai Martaba mun jefa kanmu mun jefa duk wasu masoyanmu. Please don Allah don girman Allah mu hqr kabarni na rayu da yanci kaima ka rayu da salama kaji"......








Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank






Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...






Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....






*Oum Hairan*
[8/3, 9:13 PM] Oum Hairan: *0027* Tunda Juhud ta durqushe gabansa ta riqe qafafunsa tana kuka tanayi masa magiyar jikinsa ke rawa ya kafeta da manyan lumsassun idanunsa ya kasa furta mata ko kalma daya da zata zama salama ga ruhinta saboda gani yake duk furucin da zauyi yayi kadan wajen goge mata radadin ciwon dake cin zuciyarta wanda harya sanyata zabar rabuwa dashi fiye da rayuwa dashi. Kwantar da kanta tayi a cinyarsa ta dora hannunta a fuskar Sarki junior ta sake rushewa da kuka tace “idan ya kasance kalaminka sun qare ni Kuma Ina kakeso nawa suje Baffa'am kaine duniyata kaima kana neman zamewa daga gareni tabbas rayuwata babu kai akwai rudani a cikinta Amma zan zabi na rayu da quncin rashinka fiye da rayuwa da haqqin wasu nikam banajin dadin yanda zamana dakai ya zamo silar rarrabuwar kawunan ahlinka Baffa'am meyesa Allah bai qadarta zamowata Alkhairi gareku ba?"
Lumshe idonsa yayi ya bude ya saukesu akanta ya miqe hannunsa dauke da dannasu yana sake shigar dashi jikinsa yace “abune da bazai taba yuwuwa ba kike furtawa Meenah shiyasa nake ganin asarar bata lkcna wajen baki amsa" yana fadin haka ya fice daga dakin ya nufi nasa ya zauna a gefen gado ya yaye fuskar Mahfuz yayi masa addu'ar da baisamu yayi masa ba ya kwantar dashi tare da miqewa yasawa dakin key ya cire kayansa ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya dawo yana shiryawa yana kallon yanda yaron keta wutsil²n dinsa na jarirai yayi murmushi a fili yace “girman rabo Ina Mai Martaba da yakeson yakaimin wannan Soldier da zai fita daga jikina ya shiga na Meenah ta qinqishemin shi? Da a Ina yakeso na saka wannan kyakkyawan qwan da bai cancanci qinqisar kowa ba saita rayuwata?" Bayan ya gama shiryawa yayi sallar Isha da baisamu yayi ba yayi shafa'i da wuturi ya haye gadon ya kwanta tare da daukan yaron ya dora a qirjinsa yanajin qaunar gudar tsokar tasa har cikin bargonsa, zubawa p.o.p idanu yayi yana nazarin kalaman Meenah tabbas lamarin yau me girma ne Meenah da bakinta ta furta masa gara rabuwa dashi akan rayuwa dashi wannan abu yanayi masa ciwo duk wata matsala ta gidansa bata zuwan musu a kankin kansu saida wasu su qirqireta idan yace zai dauki mataki a hanasa wannan wacce irin rayuwa ce ne?"








Miqewa yayi ya dauki Mahfuz daya farka a bacci yake neman uwarsa ya fita ya nufi dakinta ya bude ya shiga ga mamakinsa ya isketa zaune can qarshen gadon ta zuba uban tagumi ya zubanta ido tausayinta da qaunarsa na qara nunkuwa a zuciyarsa ya haura gadon ya kwantar da Mahfuz ya sanya hannunsa ya janye mata tagumin ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sunsunar sumarta yanajin wata natsuwa na kwararo masa yace “idan na rasa gatan kowa a duniya baikamata na rasa naki ba Meenah bai kamata na zamo mara galihun nunawa duniya a gurinki ba bayan kin kasance mace daya tal dake mulkin zuciyata please na roqeki ki daina jin a ranki akwai abinda zai rabamu qaddarar mutum Babu me tayashi dakonta ni kece qaddarata nima nine qaddararki bazan hanaki kuka ba akan abubuwan da suke faruwa Amma dai ki rinqaji a ranki iyakar rintsin rayuwar duniya ni nakine ke kadai Babu wani tsanani da zaisa na rabu dake saidai qaddarar mutuwa idan ta gifta saboda haka banson sakejin wadannan kalaman naki don Allah kinji?" Zamewa tayi a jikinsa ta miqa hannu ta dauki Mahfuz tayi Bismillah ta Sanya masa nonon ya kama yanasha shikuma yana aikin kallonsu.








Kwanciya tayi badon tayi bacci ba saidon tabawa zuciyarta hutu shima kwanciya yayi a bayanta ya maqaleta da haka sukayi bacci washegari da wuri ya fice daga gdan duk cika ta gidan sarautar idan ka shiga barayin Rasheed bazaka taba cewa sabuwar haihuwa akayi ba saboda yanda gdan yake a yashe daga ita sai Kumbo Hami suketa harkokinsu Rasheed bai dawo ba sai bayan Isha lkcn har sun kwanta ya shigo ya kirata ta miqe ta nufi dakin nasa yana safa da marwa ta samu guri ta zauna shima ya zauna a gabanta ya dubeta sosai yace “nasa anzo an kama Hajiya Bilki da Dada Hanne....." Dafe qirji tayi da sauri tace “na shiga uku Baffa'am me sukayi maka?" Share zufa yayi ya miqe yace “saboda a koya musu hankali su fita daga harkata da iyalina" yana mgnr yana hada kayansa ta miqe ta Isa gabansa jikinta na rawa ta durqushe tace “wlh wannan abin baikai ka dauki wannan matakin ba Abban Sarki ana barin halal ko don kunya please kada kayimin haka wani bala'in zaka qara jefani a ciki kasa a sakosu wlh ni na yafe musu...."
Rufe mata baki yayi yace “ke zaki iya yafewa saboda bakisan ciwon kanki ba nikam ban yafe ba Yana fadin haka ya shige bathroom yabarta sake da baki wannan mutumin kwai dan neman jarfa anason kashe wata yana neman zunguro sama da kara








Tananan zaune ya fito daga wankan Yana tsane ruwa ta sake dubansa zatayi mgn ya nuna mata hanya yace “jeki ma hadu da safe inason zanyi yan nazarce nazarce" miqewa tayi jikinta a mace ta koma dakinta ta ishe Kumbo Hami tana sallar Isha ta zauna bayan ta idar ne take tambayarta meye yake faruwa ta kuwa zayyane mata komai tayi shiru na dan lkc sanna ta dago tace “banji dadin kaisu qara da yayi ba shima hakan qarin wata fitinar ce daya qyalesu watarana sai lbr"
Miqewa tayi ta Sanya Sarki junior a gadonsa tana cewa “nima abinda naso ya fahimta kenan yaqi bani hadin kai koroni ma yayi Kuma tunda yayi niyya Babu me hanashi" da wannan tayi addu'a ta kwanta sukayi baccinsu itadai da zullimi ta kwana aikam abinda take gudun ne ya faru da safe Yana fita Hidaya da Khadija sukayiwa gdan tsinke suka rinqa zaginta sunacin mutumcinta Meenah babu baki sai hawaye kawai da takeyi suna tsaka da wannan tujarar ne Kareem yazo musu barka don shi sai ranar ma yakejin lbrn haihuwar gurin Fadila aikuwa ranar Khadija da Hidaya sunji a jikinsu domin dukan mutuwa yayi musu kamar shine sojan daqyar Mai Martaba ya qwacesu barkar da baiyi ba kenan ya fice daga gdan rashin mutuncin gdan ya fara girmewa tunaninsa ace Babu Wanda ya isa ya fada aji anbi an tsangwami yarinya akan abinda bashida tushe balle makama aikam ranar hatta Addah Abulle Saida taji kunyar irin rashin albarkar da Kareem yazo ya zazzage mata a gdan akan rashin zuwa taga Dan da aka haifawa Rasheed yan uwansa kuwa gda gda ya rinqa binsu yana ci musu mutumci Yana fada musu ai ba Meenah suke qi ba Rasheed suke qi tunda shine ya dauko Meenah Kuma yakeson kayarsa sannan ba Meenah kadai ta haifi Mahfuz ba Rasheed shine silar zuwansa duniya saboda haka shine basaso"








Basu wani dauki mgnr da muhimmaci ba ba Kuma su risuna ba sukaci gaba da dabdalarsu rikici yaqi qarewa cikin wannan family har ranar suna akayi sunan babu wani armashi kamar abin arziqi dangi suka hadu ranar Meenah Saida ta gwammace ita dama mutuwa tayi da wannan baqin cikin data riska wannan Rana a qarshe baa gama sunan da ita lfy ba sai a gadon asibiti ta qarashe sunan jininta yayi mugun hawa hawan da Rasheed bai taba tsammani ba ya shiga tashin hankali matuqa da yanayin da yaga matar tasa a ciki, da dare aka sallamesu suka dawo gda kanta na ciwo sosai da Rasheed da Mom da Kumbo Hami sunata rarrashinta da kalami na kwantar da hankali bacci ya dauketa washegari badon yaso ba ya shirya yabar garin ya koma wajen aiki yabarsu cike da kewar juna................








_Kuyi hqr da wannan_










Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank






Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...






Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....






*Oum Hairan*
[8/4, 8:56 PM] Oum Hairan: *0028* Kwananta sittin da haihuwa Kumbo Hami ta koma Mali inda ita Kuma taci gaba da rainon danta cikin kulawa da tattali a hankali lkc yaketa tafiya qaunarta da Rasheed tanata qara gaba inda aiki ya riqeshi kusan watanni biyar sannan ya waiwayosu ranar anyi qara'in rayuwa kamar bazaakai gobe ba yayi musu sati biyu ya shirya domin tafiya wani aikin hadin gwiwar qasa da qasa zuwa Togo yaso tafiya da ita Mom tace gara yaje yaga yanayin gurin tukunna inyaso sai yazo ko ya aiko tabisa.
Hakanan suka rabu bason ransu ba wani abin almara tunda ya tafi wayarsa bata shiga da farko sun dauka yanayin aiki ne tafi tafi da tafiyarsa ya dauki wata biyu babu waya babu aike, sosai hankalin Juhud yaqi kwanciya hakanan wata faduwar gaba ta aureta Mom ma tana cikin damuwar rashin jin labarin dannata hakanan take daurewa tana kwantarwa da Meenah hankali, tafiya na qara tsayi har aka tafi wata shidda Babu waya Babu amo Babu labari. Qa'idar aikin nasu yace watanni shiddan ne gashi sun wucce nan fa Mai Martaba ya tashi takanas yaje barikinsu inda ya dawo cikin matsanancin tashin hankali suna ganinshi Meenah dake zaune ta dora kanta saman cinyar Mom tana aikin kuka ta miqe tana cewa “Mai Martaba kaganoshi Yana cikin qoshin lfy?"








Sunkuyar dakai Mai Martaba yayi yana kwance rawaninsa yace “lamarin akwai daure kai fah naje barikinsu duk sojojin da aka tura Togo sun dawo tsiraru ne suka mutu Amma shi bai dawo ba dana matsa da bincike ma a data na aikinsa tun sunada wata biyu da tafiya wani mugun ciwon kai ya sarqeshi shine dalilin da yasa aka bashi hutu da zummar zai dawo gda tsayin watannin nan bai dawo ba....." Yanke jiki Meenah tayi ta fadi qasa sumammiya gabadaya sukayi kanta Mom ta dauko ruwa ta fara yayyafa mata daqyar ta dawo hayyacinta ta miqe zaune ta dubi Mai Martaba cikin gushewar hayyaci tace.
“Me kakeso kacemin Mai Martaba mijina ya taho gda daga filin daga Kuma baizo gidaba to Ina ya tsaya Kuma wayoyinsa basa shiga tun satin daya tafi?" Gumi Mai Martaba ya sharce yace “shine abinda nima nake tambaya kada ki tashi hankalinki na sanar da duk Wanda ya kamata na sanarwa wannan isue din Kuma sun fara bincike daga yau insha Allahu komai zaizo da sauqi...." Cikin kuka tace “ta yaya zan kwantar da hankalina bayan rayuwata tana cikin garari nikam don Allah ku fitomin da mijina wlh inason kayana" daqyar suka samu suka lallasheta shima ba shiru tayi da kukan ba kawai surutan ta daina hakanan aka duqufa babu ji Babu gani nemansa ta kafofin sadarwa na Internet da duk wasu hanyoyi da zaa samu bayaninsa Amma shiru Babu amo Babu labarinsa.








Gabadaya hankalin gdan sarautar Babu na kwance wannan baqon alkaba'i daya fado musu Babu zato ya girgiza zuciyar kowa a gdan daga yara har manya hatta wadanda ke nuna adawarsu irinsu Hajiya Bilki a zahiri suna nuna alhininsu tare da jefar da maganganu na zargi a fakaice suna alaqanta batan nasa da Juhud da take kwance cikin halin jinya bata kwana uku da lfy

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads