Showing 30001 words to 33000 words out of 97223 words
Chapter 11 - JUHUD BY OUM HAIRAN .txt
sun kashemin jiki Baffa'am Amma ban fahimci komai ba" iska ya furzar yace “bakisan soba ko Meenah?" Daga masa kai tayi ya zuba mata ido Yana lasar lips dinsa yace “nikuma Yana wahalar dani sosai Meenah son wata yarinya Yana neman tarwatsamin zuciya abin takaicin ni jarumi ne a filin daga na iya riqe kunamar bindaga da sakin ruwan harsashe Amma a gabanta matsoraci nake zama na kasa fada mata Meenah"
Cikin yanayin tausayi ta dago tace “Allah sarki Baffa'am meye yasa bazaka fada mata ba to babu wani abin tsoro a lamarin soyayya Kuma ma fah zai iya yuwuwa itama tanasonka bazata iya fada maka bane" tunda ta fara mgnr yake kallon bakinta har tayi shiru yaja zuciya ya dafe kuncinsa yace “idan tanasona me yasa bazata fadamin ba ita tunda ni nakasa?" Murmushi tayi daya qara bayyanar da sihirtaccen kyaunta tace “kaima dai Baffa'am to kaima namiji da aka sanka da jarumta akan muradinsa ka kasa tararta ka fada mata sai ita da take mace da aka sani da yakana da kunya kaima kasan bame yuwuwa bane ai"
Sake sanya hankali yayi akanta yace “ta yaya zan gane idan tanasona Meenah ita yarinyar ta kasance tana matuqar ganin girmana fiye da kowa tana mutumtani batason bacin raina batason damuwata har tana kirana da babanta........ Dagowa tayi da sauri yayi murmushi yace “haka nake nufi sunan babanta ne dani babana haka take kirana a gaban kowa Meenah wlh inason Aminatuh fiye da son da nakewa kaina banjin zan iya rayuwar aure da wata mace ba Aminatuh ba na Raina kaina ranar dana fahimci ba shaquwa ce tasa nake tsananin kishinta ba sone, nayi qoqarin mayar da lamarin mafarki Amma ya faskara har takai zuwa yanzun duk wani fitar numfashi nawa da tunaninta yake fita please ki bani shawara ya zanyi na fahimtar da Aminatuh inasonta?".........
*Oum Hairan*
[7/21, 6:31 PM] Oum Hairan: *JH015- littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki*
*Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*
*Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde*
Wani gwauron numfashi Meenah ta saki tace “idan har kace saika Bari ta gane da kanta to kuwa da jan aiki a gabanka Baffa'am idan Irina ce me qarancin fasaha wajen gane abubuwa hannunka Mai sanda bazai wadatar wajen fallasa mata sirrin zuciyarka ba misali kamar ni duk da har yanzun ban karbi tayin qaunar Ya Kareem ba, Ganin nidin bame ganewa bace yasa ya fito ya sanar dani abinda ke ransa ko banza nasan zai samu sauqi game da ciwon dake cin zuciya balle ma ni......"
Dagowa tayi ta dubesa tsoro ya kamata ganin yanda lkc daya ya hargitse yanayinsa ya canza daga na walwala zuwa matsananciyar damuwa, da sauri ta miqe tace “kayi hqr don Allah Baffa'am kaine kace duk wani abu dake damuna na rinqa sanar dakai kafin na sanar da kowa......" “Shut-up Meenah!" Abinda ya fada da qaraji kenan ya miqe jikinsa na rawa zuciyarsa na motsawa da qarfin gaske maqwallatonsa kamar zai faso maqogwaransa tsabar bala'in dake cinsa suka fara zagaya dakin cikin tashin hankali ganin guri ya qure matane ta zame a qasa kawai ta saki kuka me sauti tace.
“Na shiga uku ni Aminatuh Baffa'am meye laifina ne don naso Ya Kareem wlh ko zaka kasheni saina fada maka inasonsa saboda yanada cikar Kamala da nagartar da tayi qarancin a samarin zamanin nan inasonsa saboda zuciyata tana fadamin shine ya dace da maraici na Baffa'am Ya Kareem baitaba sani dole ba baitaba hanani dole ba saidai akan aya da hadisin ma'aiki (S.A.W) baitaba takuramin akan nasoshi ba saidai ya roqi alfarmata duk da kasancewar banida alfarmar shine yake da ita domin a cikin da'irar arziqinsu nake rayuwa, Ya Kareem baitaba nuna yanason jikina ba hasali ma yaqi yakeyi da duk abinda zai tarwatsa mutumcina Kuma, Ya Kareem ya fadamin cewa Allah Yana maraba da bayinsa da sukayi soyayya dominsa wannan dalilin yasa naji inasonsa domin Allah Kuma zan rayu das......"
Bata iya qarasa kalamin nata ba saboda wani gigitaccen mari daya sanyata kifawa ya nunata da yatsa zuciyarsa na tuquqi yanason yayi mgn Amma harshensa ya sarqe a hankali ya janye ya koma ya zauna yana furta “Innanillahi wa innah ilaihir raji'un" ya maimata ta takai sau goma kafin yaji nutsuwa ta fara saukar masa ya dago idanunsa da suka kada sukayi jawur kamar garwashi bakinsa da jikinsa har yanzu rawa yakeyi yace “kina sonsa ko Meenah?" Dagowa tayi idanunta shabe² da hawaye yace “bakiyi qarya ba duk gdannan babu wanda ya tara wadannan suffofin da kika lissafa sai Kareem nima shaida ne saboda haka ya cancanci kisoshi tabbas Amma Kuma yanzu ya zakiyi da wanda ya daukoki tun baki cika mutum ba yajaki jikinsa ya mayar dake mutum ya bata darensa da ranarsa dominki ya Hana kansa farin ciki sai yaganki cikin farin ciki yake shiga damuwa da damuwarki koda kuwa bakwa tare motsinki ya zama nasa lfyrki tasa ciwonki nasa Aminah ya zakiyi dashi wanne halacci zakiyi masa da zaiji a ransa kin saka masa da kwatankwacin tausayinsa da qaunarsa gareki?"
Tunda ya fara mgnr ta kafesa da idanunta da yake tsiyayar da hawayen tashin hankali tasowa yayi ya matso gabanta ya miqar da ita yace “idan ya kasance kin kasa saka wancan Alkhairin da abu mafi daraja wato qaunar da wannan mutumin yake nema a gurinki to tabbas ke ba yar halak bace domin dan halak shine yake jiran gabar saka Alkhairi da komansa koda kuwa gurin bai cancanci sakayya ba shidai burinsa yaji a ransa babu bashi tsakaninsa da wannan mutumin"
Sakinta yayi ya juya zai shiga bathroom har ya bude ya juyo yayi mata murmushi yace “kije kiyi tunani akan kalamai na" a mugum kasalce ta bude qofar ta fito ta nufi cikin gdan zuciyarta na kai kawo akan kalamansa tana shiga dakinsu ta zube a bakin qofar tana mayar da numfashi Amrah dake fitowa daga bathroom taja ta tsaya sake da baki ganin yanda ta cure jikinta tanata rera kuka takaici yasa Ya'isha miqewa tace “dallah malama ke baki rabo da kukane meye Kuma akayi miki" dagowa tayi ta kwantar da kanta jikin Amrah tace “nikam Ina ganin rayuwa Amrah don Allah meye wadannan kalaman suke nufi......"
Zayyane musu komai tayi ta qarashe da cewa “bansan meye yasa qwaqwalwata bata gane abubuwa ba" numfashi Amrah da Ya'isha suka saki tare Amrah tace “kan ubancan lallai akwai qura a gdannan Juhud bafa wani abu Big Cele yake nufi ba kece yakeso kece Aminan da yake baki lbr ke kadai ce me wannan siffar daya suffanta" Ya'isha ce tayi murmushi tace “ke saiyau kika fahimta ai dake da Aminah dukkanku kallonku nakeyi Amma wlh batun yanzu ba na fahimci Big Cele son Juhud yakeyi tsabar miskilanci ne da girman kai ya hanashi bayyanawa yake wani bada fadi da hura hanci kamar kyankyaso aikin banza na dade da gano damuwarsa kekam ta bakin naki kina ganin rayuwa ga Mai Martaba yayima Ya Kareem alqawarin aurenki" cikin mutuwar jiki ta dago tace “nikam ya zanyi wlh da gaske bantaba daukar wannan gundumemen lamarin zai fadomin ba banyi masa muhalli a bangarena ba bantabajin Baffa'am zaice yanasona ba kai bama abinda yake nufi ba kenan babu abinda zaiyi dani"
Dariya sukayi dukkansu ta zubansu idanu Amrah tace “waima to shi ya gani wlh yarinya tun wuri ki takansa birki inba hakaba zakisha wahala Big Cele bashida mutumci gashi da ganinsa zaiyi wuta babban tashin hankalin ma mgnr aurensa da Zulaihat tayi mugun nisa harma fah ankai kudin tambaya sa rana kawai zaayi anasa rana Kuma raqashewa zamuyi Kinga kenan bakida gurbi kawai batankin gomanki zaiyi dayanki bata gyaru ba"
Tagaji dajin wadannan kalaman hakanne yasata miqewa ta shiga bathroom ta sakarwa kanta ruwa ta fito taji ana kiran magrib ta dauki dabino ta tauna ta fita ta dauko ruwa tana dawowa Amrah ta miqa mata waya ta Amsa ganin number Kareem ta Kara a kunnenta tace “nasha ruwa lfy Habiby kaifa?" Murmushi yayi yace “yanda kikasha Luv ya exams?" Kwanciya tayi tana lumshe ido tace “inajin dadin exams din da taimakonka" hirarsu sukaci gaba dayi tama manta da batun Shan ruwa saida yace “kije kisha ruwanki zan kiraki anjima" ta aje wayar ta tayar da sallah tayi buda bakin.
Tun daga wannan ranar salon rayuwar gdan ta canza musamman tsakanin Juhud da Rasheed duk inda tasan zasu hadu gujewa gurin takeyi saboda ita har cikin zuciyarta bataji a ranta zata iya soyayya dashi ba bayan haka ma sannu a hankali Kareem ya gama siye zuciyarta da salon qaunarsa me tsayawa a rai da wuyar gogewa kullum idan sunyi waya kalmarsa daya itace don Allah Aminah ki kulamin da kanki nayi miki tanadin kaina na tsare kaina tsayin shekaru burina ya kasance a halali na na fara shuka inason gonata tayi kyakkyawan yadon da yabanyarta zata burge kowa idan amfanin ya nuna ya isa moro ya morawa duniya baki daya Aminah samawa yayana uwa ta qwarai shine abinda na dade Ina addu'a nasani bazan taba danasani ba idan kin kasance mata a gurina zaki bani farin cikin da zanyi alfahari dake a duniyata da lahirata"
Idan ya fada mata haka Yana kashenta jiki matuqa takanji kamar ya daureta da jijiyarta ne duk saitaji wani shauqin qaunarsa Yana qara mamaye ruhinta wannan dalilin yasa ta qara qaimi wajen tsare kanta tunda me bata kariyar bayanan gashi ya Daura mata nauyi Mai girma na amanarkai.
Kwanci tashi lkc ya rinqa tafiya cike da matsaltsalu Rasheed mugun miskili da baa gane matsalarsa Amma yanzu kusan kowa ya fahimci yanada damuwa gashi da baqin zurfin ciki ya kasa furtawa kowa damuwarsa saidai yaje Garden yayi tagumi ko ya tusa waya a gaba yayita kallo. Ranar da sukayi Candy suka hada qwarya²r party a gidan sarautar Juhud batada qawaye su Ya'isha ne suka gayyato samarinsu da qawayensu Mai Martaba shine ya daure gindin partyn harda dauko musu Dan Hausa yazo don qarawa abin armashi qarfe hudu suka fara caskalewa samarinsu duk sunzo itace kadai saurayinta baizo ba baya qasar ma Amma yayi mata fatan Alkhairi sun dauki wanka na tashin hankali sunyi kyau na bam mamaki dama dukkansu ba baya ba wajen kyau Amma sukansu Saida suka sallamawa Juhud tayi kyau kamar wata amarya suka fito daga gdan ana take musu baya suka fara hotuna anyi mata hoto yafi kati dari da shiga daban² ta karbi wayar Ya'isha ta zagaya baya ta Kira layin Ya Kareem bugu daya ya daga tayi ajiyar zuciya tace “rayuwata tana cike da kewar masoyi banajin komai yana tafiyar min daidai" dariya yayi yace “kinajin abinda nakeji kuwa Aminah nifa inajin kamar zanyiwa Mai Martaba mgn ne zanzo hutun azumi kawai a hada bikinmu dana Big Cele ayi a bani ke mu taho nan"
Juyowar da zatayi suka hada ido da Rasheed dake tsaye jikin swimming pool kallon da yake mata ne yasata kama in...inar qarfi da yaji tace “am...in...." Ji tayi ya warce wayar ya duba yaga number qanin nasa yana mgn Yana cewa “hello..... Luv....." Qit ya kashe wayar ya jefa a aljihunsa ya juya yabar gurin daga Ya'isha dake qarasowa ta dafata tace “wai me kikeyi ne anata nemanki" juyowa tayi idanunta ya ciko da qwallah tace “ya qwace wayar Amrah...." Binsa sukayi da kallo Ya'isha tace “hmmm wannan mutumin dan rainin hankalin mutumin wlh bashi da mutumci yanzu duk hotunan da mukayi sun tashi a banza kenan?"
Qwafa Amrah tayi tace “kuma duk baqin cikinsa bazamu fass shagalinmu ba Allah yasa ba layina bane akai daya cuceni" janta sukayi suka shiga filin itadai yaqe kawai takeyiwa mutane har takwas taron ya tashi suka shiga gda ta shige daki ta kwanta tana mayar da numfashi.
Da wayar Ya'isha Kareem ya sake kiranta yake tambayarta Ina wayarta ne yanata Kira a kashe taja fasali tace “Baffa'am ya qwace tawa ta Amrah ce nakesa layin itanma dazun ya qwaceta" wata iska ya furzar yace “ina Gsky abin nasa ya fara yawa fah banason shigarmin hanci da qudundunen nan da yakeyi Ina ganin girmansa kada azo ayi babu dadi zan fadawa Mai Martaba ya dakatar dashi gsky na gaji duk yabi ya takuraki to ko hsihuwarki yayi kikakai yanzu ai ya qyaleki balle a sama yaganki" itadai batace komai ba saboda itanma duk kawaicinta da kararta Baffa'am din nata ya fara duba juriyarta.
*************
Satinsu biyu da Candy samarin Ya'isha da Amrah suka aiko neman aurensu da farko Mai Martaba yaqi amsar batun a cewarsa karatu zasuyi Alh Ibrahim wani amininsa shine ya sameshi ya bashi shawarar tunda sun nuna auren sukeso yayi musu ba lallai sai mace a gdan iyaye zatayi karatu ba a gdan mijinta ma zata iya karatunta da farko bai dauki mgnr ba saida Addah Abulle ta sake samunsa da mgnr Kareem fah ya matsa akan mgnr aure da Momy da ita da Ya Arman sune suka sameshi suka rinqa nuna masa abin hakan suna nuna masa Kareem namiji ne Kuma yanada kawaici tunda har ya fito da maitarsa ayi masa kada azo a samu matsala.
Badon yaso ba ya amshi shawarar tasu dake dama an gama shirya komai na baikon Rasheed da Zulaihat hakanan ya Kuma bada maqudan kudade aka shiga kasuwa aka sake yo siyayyar baikon Kareem da Meenah Meenah batasan meye akeyi ba ranar baikon korasu akayi Katsina gdansu Addah Abulle acan suka yini suna tantalbadedensu akatsai da ranar aure Rasheed da Zulaihat wata biyu masu zuwa ya kama bayan azumi da sati uku dake azumin ya rage saura kwanaki bakwai ne sukuna akasa wata shidda saboda an qiyasta abinne da yanda zaizo daidai da hutun shekarar Kareem din ayi bikin ysnana ya dauki matarsa su tafi.
Ranar farin ciki gurin Juhud da Kareem kamar su hadiye juna ta waya inda Rasheed yayi yinin qunci da baqin ciki a qarshe ma daki ya shiga ya kulle kansa yini sur har dare har safiya bai fito ba Mom ce ta kirata tace taje ta duba Baffa'am dinta tun jiya bai fito ba, bataso ba batason haduwa dashi tsoronsa takeji batasan da wacce irin fuska zai kalleta ba, hijjab dinta ta dauka ta Sanya ta fita ta nufi part din nasa tun daga falo ta fahimci akwai matsala kaca² ta tarar dashi gabanta ya fadi ganin kwalaben wine da wasu qananun kwalabe ta matsa ta dauki daya ta duba tare da dafe qirji da sauri tace “A'uzubillahi Baffa'am Alcohol kakesha?" Tsorone ya sarqeta takai hannunta qofar tana bugawa kusan 20 minutes bataji motsi ba murdawa tayi tajita a kulle ta rinqa bugawa da dukkan qarfinta Amma shiru dube dube ta farayi a falon can ta hango mukullaye a hade ta dauka da sauri ta fara gwadawa cikin saa na qarshen da tasa ya bude qofar ta tura da sauri, toshe hancinta tayi saboda warin daya daki hancinta takai dubanta inda ta hangeshi kwance a qasa cikin amai ta saki qara tana cewa “innanillahi meye hakan meye ya sameshi?" Matsawa tayi ta shiga jijjigashi Amma kamar tana jijjiga dutse daidai lkcn Momy da taji shirun tayi yawa ta shigo ganinsa a wannan yanayin yasata sakin ihu tace “Abdulrasheed meye hakan bakada lfy ka kulle kanka a daki zaka kashe kanka....."
*Oum Hairan*
[7/22, 6:51 PM] Oum Hairan: *JH016 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki*
*Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*
*Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba 94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde*
Gabadaya gidan ya rude Big Cele babu lfy Mai Martaba dakansa yazo suka daukeshi da likitan gdan suks nufi asibiti dashi suka fara bashi kulawa sosai likitan ya kadu dayin hoton zuciyarsa da yaga ta kumbura jininsa ya hau fiye da misali tashin hankalinsa ya nunku ya fito Yana sharce gumi iyakar saninsa Abdulrasheed ba mutum ne me shiga sabgar mutane ba balle su Dora masa damuwa to meye yaja asalin damuwar tasa?
Da wannan tunanin ya fito ya sami su Mom a zaune suna ganinsa suka miqe ya sake share gumi ya dubi Mom yace “dama Rasheed yanada heart issue ne?" Da sauri suka kalleshi Mai Martaba yace “aa bashida ita" iska likitan ya furzar yace “to mgn ta gsky akwai abinda yasa a ransa da yakecin zuciyarsa har yayi mata Ramin da ciwo ya shigeta hoton da nayi masa ya nuna cewa zuciyarsa ce ta kumbura jininsa yayi mugun hawa fiye da misali nikam lamarin ya firgitani meye damuwarsa meye yasa a ransa da yake neman salwantar da rayuwarsa akansa?"
Goge gumi Mai Martaba yayi ya dubi likitan yace damuwa Kuma a Rasheed din to wacce irin damuwa ce wannan nikam bansan irin yaron nan ba zurfin cikinsa yayi yawa" Mom ce tace “kuma ba akan yarinyar nan bane da yace bayaso kasanshi fah da baqar gaba idan yaqi abu zai iya komai akansa Mai Martaba ka duba lamarin Rasheed fah da Zulai......" Daganta hannu yayi yace “dakata Ayshatu indai akan wannan ne to zan tanadi likkafanin suturarsa don wlh bazan watsawa zuminci baqar toka ba ko zai mutu saina daura aurensa da Zulaihat......."
Kwanansa goma a asibitin duk sanda zasuje dubashi daya ganta saiya lumshe idonsa bazai bude ba harsai ta fita a dakin maganar duniya bazai kulata ba tun abin na damunta har ya daina damunta da zugar qannensa da suketa famfata akan kada ta kuskura ta bashi qofar da zai gane tanajin tausayinsa zai kaita ya baro ne qila ma ba aurenta zaiyi ba Kuma ma yaushe zata saki saurayi ta kama tuzuru tuzurun ma me Shirin auren wata a fari ba