Showing 75001 words to 78000 words out of 97223 words
Chapter 26 - JUHUD BY OUM HAIRAN .txt
fita sukayi sallama ya dawo dakin ya kwanta ta miqe ta nufi kitchen din bata samu komai ba sai ragowar Naman da sukaci jiya shi ta dumama ta sake hado masa tea ta dauko ta nufo dakin ta aje masa ta cire hijjab dinta ta zauna a qasa tace “kaci abinci saika samu qwarin jikinka"
Girgiza mata kai yayi tare da daga rigarsa ya sanya hannunsa cikin wandonsa ya bude bakinsa cikin muryarsa me sanyi yace “bana tare da yunwa kinsan matsala ta Meenah ita kadai nakeson kimin maganinta" sunkuyar da kanta tayi ya sauko ya dago kannata ta lumshe ido yayi kissing na lips dinta yace “kiyi hqr dani nasan na takura miki ko?" Girgiza masa kai tayi ya janyota ta kwanta a jikinsa ya matseta duk da firgicinta tayi masa rawar gani ya samu yanda yakeso.
Rayuwa sukeyi me armashi cike da kulawa da tattali wa junansu musamman Kareem da kacokan lissafin rayuwarsa yake akan Juhud itanma fahimtara irin tasa matsalar yasa kan dolen dole ta yakicewa kanta bayyananniyar damuwa, ko tunani ta daina yarda tayi a gabansa yanzun nan saiya rikice mata rayuwarsu a qasa mai tsarki ta zame mata wata rayuwa da take bata nishadi tanajin Kareem a ranta fiye da tunani Amma har gobe takasa canza gurbin Rasheed kullum shine cikin tunaninta mafarkinta da dukkan wani motsinta hatta addu'arta ya kwashe kaso mafi rinjaye shidin bashi da tamka cikin rayuwarta bazatayi masa madadi ba.
Watansu biyar a Saudi aka dauki azumin watan Ramadhan a lkcn Juhud lfy tayi mata qaranci ita ba ma'abociyar bacci bace Amma baccinta yayi yawa Kareem shine ya fara lura da yanayinta suna kwance da dare ya janyota jikinsa Yana shafa mararta ta riqe hannunsa ya daganta gira ta turo baki tace “nikam Allah ya Kareem zaka sani guduwa waikai baka gajiya da abinga ne?"
Murmushi yayi ya zubanta ido Yana lasar lips dinsa yace “kintaba ganin inda mutum ya gaji da dadi ai kullum qari kake nema kinma san me?" Girgiza masa kai tayi ya shafa cikinta yace “baki tunanin komai game da sauyin yanayinki?" Dariya tayi tace “yanzu fah sai kace ciki ne dani ko?" Hade rai yayi kama kunnenta ya murde ta saki qara yayi dariya yace “wato kin mayar dani abin tsokanarki ko naga Sarki junior shekara daya da aurenki kika haifesa nikuma kina neman kaini biyu duk qoqarina" murmushi tayi tace “to abinda bazaka yima kanka ba Ya Kareem meye na damuwa kafa taba aihuwar nan balle kace tsoro kakeji" numfashi ya sauke yace “kawai inason naga yayanmu ne Meenah zanji dadi zanyi farin ciki sosai inasonki shiyasa nakeson zuri'a ta wanzu tsakaninmu nasan ko bana raye bazan goge a mind dinki ba"
Shiru tayi masa ya kama kunkuminta yayi mata cakuli tayi dariya ta qanqameshi da haka bacci ya daukesu da asuba ya tashi taba jikinta kawai yayi yaji jikinta zafi zau ya tasheta tayi miqa yace “jikinki zafi" numfashi ta sauke tace “na kwana zazzabi Ya Kareem" wanka yayi itama tayi sukayi sallah suka fita asibiti suka shiga aka bata magunguna tare da yimata gwaje² labari me dadi ga Kareem abinda yake zargine itadai jikinta ya mutu batasan meye dalili ba babu farin ciki Babu baqi a ranta saima hawaye da batasan sanda ya zubo mata ba.
Tasbihi da taslimi yayima ubangiji Sarki daya me ikon zartar da komai a lkcn da yaso ya juya gareta ganin yanda take sharar hawaye duk sai ta Sanyaya masa jiki ya kama hannunta suka tafi suna zuwa gda ya dubeta idanunsa sun kada sunyi jawur yace “bakyaso ko?" Girgiza kai tayi da sauri tace “ba haka ban...." Katseta yayi da cewa to mene?" Kuka ta saka ta fada jikinsa tace “babu fah kawai Ina jinjina girma da buwayar ubangiji Ya Kareem meye kayimin da zanqi jininka" ajiyar zuciya ya sauke yajata suka zube ya share mata hawayen yace “ki daina kina sani a tunani kinji" dagansa kai tayi yace “me zakici?" Kallonsa tayi tace “azumin fah" kallon magungunan yayi yace “ok idan bazaki iyaba ki hqr Allah yayi muku uzuri fah
Dagansa kai tayi yini sukayi yanata tattalinta da riritata wannan ciki Yana ganin boni komai yagani ya rakito mata kayan baby kuwa abin har yazama hauka abinda ya bata mamaki Mom ce kadai tasan da cikin har yakai watanni biyar a lkcn ne Kuma wani baqon al'amari ya sakosu a gaba hakanan sai taga Kareem yayi tagumi ya tsunduma duniyar tunani idan ta tambayeshi dalili sai yace mata Babu komi Tasha zuwa ta tarar dashi Yana kuka a daki shi daya tambayar duniya sai yace mata Babu komi dole ta zubansa ido a dan ritsin ne Kuma ya kama rashin lfy sosai itadai Saida ta Kira Mai Martaba ta sanar dashi domin an bashi gado baisan waye akansa ba wani abin mamaki daya razana duniyarta ranar da Mai Martaba yazo tana tsaye jikin gadon da Kareem yake riqe da hannunsa tanayi masa addu'a taji sallamar Mai Martaba ta dago da sauri cak ta tsaya komanta ya tsaya hatta da numfashinta lkcn da tayi arba da wanda yake takewa Mai Martaba baya cikin bugawar zuciya tace “Baffa'am!" Kallonta yakeyi da alamun rashin fahimta ta nufesa da sauri tana cewa “Ya Allah Mai Martaba yaushe akaga Baffa'am dina Amma aka boyemin meye yasa akayimin haka ashe akwai abinda zaa iya boyemin game da Baffana....."
Tana mgnr tana nufarsa shikam ya saki baki ne Yana kallonta zuciyarsa na wani irin bugawa da mugun qarfi qara waro idanunsa yakeyi yanason ya ganeta ya kasa tana Shirin kai hannunta jikinsa taji yace da Mai Martaba “mai Martaba itan wacece?!" Ba itaba shi kansa Mai Martaba Saida tambayar ta dakeshi ya dubeta yaga tayi mutuwar tsaye hawaye nabin kuncinta bakinta yana rawa alama ta magana takeson yi ta kasa kama hannun Meenah Mai Martaba yayi yace “ki nutsu Meenah Rasheed fah ba qalau yakeba duk duniya Babu wanda yake ganewa" zubawa Mai Martaba ido tayi tace “meyesa aka boyemin bayyanarsa?" Murmushi Mai Martaba yayi yace “akwai hikima cikin hakan yanzun ma banso kikasan da bayyanarsa ba so dandai ya matsa ne saiya biyoni"
Zubewa tayi ta rushe da kuka tace “Allah na gde maka daka bayyanamin shi a raye Mai Martaba Amma ya gane Sarki junior ko?" Murmushi yayi yace “ni kaina da zan fita na dawo saiya tambayeki waye ni" zubawa Rasheed ido tayi da yake bin dakin da kallo yace “Mai Martaba shima wannan dakin bansanshi ba shikuma wannan da bashi da lfy waye?" Yana mgnr yanakai hannunsa ga Kareem dake kwance kamar gawa riqe hannunsa Mai Martaba yayi yace “bakasanshi ba?" Daga kai yayi yayi murmushi yace “wani qaninka ne Kareem ja tunasa?" Dafe kansa yayi kamar zai tuno ya dago yace “ok shine wannan wanda mukayi yaqin tare dashi aka sacemu tare aka kaimu Sudan kace sunan gurin ko?" Murmushi Mai Martaba yayi ya dubi Juhud data kwantar da kanta a jikin gadon tana kallon ikon Allah.
Likitan ne ya shigo suka gaisa da Mai Martaba suka fita suka barta ita da Rasheed abin yana tsuma jikinta da ruhinta wai gata ga Baffa'am dinta Amma baiko kallonta harkar gabansa kawai yakeyi ta miqe tanajan tsohon cikinta me watanni takwas ta matsa bayansa ta sassauta muryarta tace “Abdulrasheed" juyowa yayi ya zubanta ido tare da dibanta ya watsar hawaye ya sake tsiyayo mata tace “wai da gaske baka ganeni ba?" Daina latsa wayar yayi ya sunkuya ya ciro takalminsa duka biyun ya miqa mata yace “nasan sune sukayi miki kyau to gasunan na baki" noqewa tayi taqi karba tace “meyesa zaka mantani tsayin shekara shidda nakasa cireka a Raina na kasa karbar kowa bayan kai Rasheed ni ban cancanci ka mantani ba....."
Saurin ja baya tayi lkcn daya fara kwance tazugen wandonsa gabanta ya fadi tana kallonsa tanajin ninkin faduwar gaba gani tayi ya zare wandon ya kuma cire rigar ya rage dagashi sai singlet da boxes ya nufeta Yana murmushi yace “nifa kinganni banida rowa idan kinason wadannan dinma zan iya baki wlh Meenah ta tafimin duk abinda na mallaka a duniya Kuma kinsan Meenah ta mutu Ina zuwa kogin maliya zan fada ciki na tsunduma tsundum na mutu nima kowa ya huta yawwa ai kema kinsan zan hadu da Meenah acan ko?"
Tashin hankali Yana matsarta tana matsawa ya damqo hannunta ta rintse idonta ya damqa mata kayan yace “ki riqe nabaki sadaka idan kinason agogon ma da zoben duk na cire miki Ni dama na daina kwalliya takaba nakeyi Kuma bazan qarason wata mace ba a duniya tunda na rasa Meenah"
Girgiza masa kai takeyi tana kuka me gunji ya dora hannunsa a bakinsa yashe “dallah malama kiyi shiru Meenah batason kuka" gumtse bakinta tayi ya juya zai fita Mai Martaba ya budo qofar ya shigo yaja ya tsaya da sauri yace “ya subhanallah Rasheed meye hakan?" Murmushi yayi ya sosa sumarsa yace “ai harkai zan iya kyautarka indai akan Meenah ne" zaro ido Mai Martaba yayi yace “nidin Rasheed" dariya yayi harda riqe ciki yace “kaidin har wata daraja ce dakai ta musamman da zatasa naqi fansar dakai akan Meenah?"
Girgiza kai Mai Martaba yayi yace “naji banida ita Sanya kayan naka muje masauki" juyawa yayi ya kalli Juhud ya tsugunna yace “don Allah mamana kibani aro Allah niba barawo bane zan dawo miki dasu yau dinnan aidai bake kika sani ba nine nasa kaina nabaki kyautarsu ko?" Miqa masa tayi yace “aafah Hajiya in kinsan ba tsakani da Allah kika baniba bar kayanki"
Dauke qwallah Mai Martaba yayi yace “karbi tsakani da Allah tabaka" yasa hannu ya karba Yana sawa Yana waqarsa “Meenal Aso kin matar da zuciyata ta mace! ki tausaya karki sani bangare na yaudara!! Ina gudun duniya!!!"
Da wannan ya fice Mai Martaba ya dubeta yace “likitana ya tabbatar min da zai samu sauqi fah karki damu" ficewa sukayi suka barta da kallon Kareem dake kwance kamar gawa ta juya itama ta fice kamar mahaukaciya ta nufi block nasu ta fada gado domin tabawa zuciyarta hutu daga sabon tashin hankalin daya tunkarota ga Baffa'am dinta a gabanta Amma yakasa ganeta to waima meye asalin dalilin sukurkucewarsa ne haka Shiba Mai mgn ba Amma surutai rarrara kamar Wanda ya qone a qeya miqewa tayi tare da cewa “tabbas lkc yayi da zan sakawa Mafi cancanta Alkhairinsa....."
Tunaninta ne ya tsaya cak da tunawa da Kareem shikuma da yake cikin halin ni yasu dora hannu tayi akanta daidai lkcn da wayarta tayi ring ta wawurota Ya'isha tace “na dade inason tsegumta miki watanni biyu baya anga Big Cele a Tanzania to tsoron jagula wannan dofanannen auren naki da Ya Kareem yasa Mom ta Hanani fada miki wai Kuma yau sainaji me kankat ankawo mikishi har qasarku"
Cikin kuka tace “shine me gata ko rashin galihu yasa kukaki fadamin labari mafi soyuwa a duniyata Ya'isha ko ku fada ko karku fada Rana irin wannan zatazo gashi tazo Baffa'am ya dawo zamana da Kareem ya qare....." Da qaraji Ya'isha ta katseta da cewa bakida hankali ne karki soma wlh Kareem yafi kowa buqatar taimakonki kinaganin fa a halin da yake" jan zuciya tayi tace “meye ribata dama uwarsa ta rantse indai na haihu saiya sakeni to kafin ma na haihu zanbar mata gidan danta nima a dole nake zaune don halacci" magana Ya'isha keson yi mata ta kashe wayarta can Mom ta kirata tace “idan kin kwantar da hankalinki akwai labari me dadin dadi da nakeson baki"
Muryarta harta dashe tace “kun boyemin abinda na cancanci nasani Mom meyesa" murmushi tayi tace “saboda kada muyi mahaukata biyu a dangi shiyasa Meenah kifa nutsu motsi kadan zakiyi ki fada rami mijinki yafi kowa buqatarki to kibi sannu kada santsi ya debeki"haka Mom ta rinqa bata kalamai wai ita a dole saita kwantar mata da hankali batasan qara tashin hankalinta takeyi ba suna kashe wayar Dr Khazeem yazo ta dubeshi yace “ya naki jikin batason hayaniya hakan yasa tace “naji sauqi so ganin yanayinta yasashi ficewa ta koma ta kwanta kamar bazata koma asibitin ba saidai taji zucciyarta taqi natsuwa dole ta shirya ta nufi asibitin ga mamakinta saita isheshi a zaune shida Mai Martaba ta dubesu suka gaisa da Mai Martaba yace “kema kina buqatar hutu ya kamata ki koma gda ki haihu acan" jinjina kai Kareem yayi yace “dama inada burin hakan sai na kwanta jinyar nan" da wannan sukaci gaba da tattaunawarsu hankalin Kareem na kanta Mai Martaba yace “ki koma masaukinku ki huta zan kwana dashi muga abinda hali zaiyi".......
_Yau fah saidai hqr da qarancin page din_
Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...
Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....
*Oum Hairan*
[8/12, 8:08 PM] Oum Hairan: Duban juna Juhud da Kareem sukayi yayi mata qaramin murmushi ya shafa sajensa tare da nuna mata hanya yace kije ki huta heart kinyi qoqari fah na gde Allah yabada lada" sunkuyar da kanta tayi tare da daukar wayarta tayi musu Saida safe ta fice ta nufi masaukin nasu zuciyarta na kaikawo tsakanin qirjinta da duniyar Rasheed, tana zuwa wanka kawai tayi tayi sallah ta kwanta itakam wannan dare barawon ma kasa satarta yayi gabadaya ta rasa nutsuwarta batajin daidai saina tunanin Rasheed, da asuba tayi sallah ta zauna tanayima iyayenta da Rasheed addu'a tare da fatan sauqi da sassauci cikin wannan jarabawa da suka tsinci kansu a ciki ciwon tabuwar qwaqwalwa a Rasheed abin Babu kyau.
Data tashi da ciwon mara ta tashi hakan yasa bata koma asibitin da wuri ba Saida Tasha magani ta dan samu relief sannan ta fita ta nufi hospital din a qofar dakin da Kareem yake ta ishe Rasheed Yana tsaye yana danna waya kamar ance ya dago suka hada ido ya lumshe idanunsa qirjinsa Yana bugawa itama haka ta matsa gabansa tace “barka da sfy Baffa'am" ja tayi da baya lkcn daya kece da dariya yace “shegiya ashe kinsan sunana ai Meenah ce take kirana da wannan sunan" lumshe idonta tayi hawaye ya ciko ijiyarta ta bude akansa ta girgiza kai tare da cewa “ka manta kowa da komai ka manta kamannin Meenah a zahiri Amma baka manta sunanta ba Baffa'am ya akayi hakan?"
Yarfa hannu yayi yace “nima to nasani kawai dai kema kinsan idan na kama Wanda ya kashemin Meenah a gabana saina dirmeshi da alburushi ke barima kiji fah koda yake na daina kulaki Meenah kishine gareta batason a hadata da wata a mafarki Ina ganinta kullum Kuma fah tana dan kama dake kadan Amma bakikai kyaunta ba" Mai Martaba ne yajiyo mgnr ta Rasheed tayi yawa ya leqo yaga ashe shida Meenah ne tasashi a gaba sai hawaye takeyi ya qwala mata Kira tayi saurin goge hawayen tace “ok ganinan" ta juya zata tafi ya riqota yace “shifa Wannan mutumin dan raini ne ya rainani yama zaayi Ina mgn da mutum ka kirashi to kaima ka kiyayeni kafin na qundumeka" zaro ido sukayi dukkansu ya dora hannunsa a bakinsa yace “lalalah ashe fah sabo nakeyi kayyy ke haihuwa zakiyi me zaki Haifa?"
Ganin batada niyyar tahowa ne Mai Martaba ya fito yaja hannunta yace “idan kika biyewa wannan saiku raba Rana da dare yanayi miki soki burutsunsa" sosai sautin kukanta yake fita batare da tasan kalmar ta subuce ba tace “ta Ina zan fara taimakonsa?"
Dubanta Kareem yayi ya kawar dakai yanajin wani abu nayi masa yawo a qirji da sauri ta share zancen da cewa “Mai Martaba ya jikin nasa?" A gajarce yace da sauqi sosai dama lkcn hutunsa yayi zamu tafi gabadaya daku saboda dukkanku kuna buqatar kulawa" jinjina kai tayi tabbas tana buqatar kulawa sosai Kuma taji dadin hakan domin itace damarta ta fuzgo yancinta zuciyarta na raya mata dolene Kuma wajibi akanta ta qwaci kanta domin Baffa'am dinta.
Kwanaki biyu suka qara a asibitin aka sallamesu cikin kwanakin ta fahimci abubuwa da yawa game da Baffa'am dinta hakanan wani lkcn sai yayi shiru yaqi yima kowa mgn ya rinqa kallon kowa daidai idan Mai Martaba ya cika damunsa saiya tashi kawai yakoma jikin tagar dakin yana hango waje yana cewa “kawai don anga Aminatuh batada gata sai a takurawa mijinta nifa idan kunsan takurawa na Meenah nazakuyi to kubarni ko da qafa zan koma Tanzania harda Sudan naje naci gaba da gadin kabarin Meenah ta"
Zantukan nasa a sukurkutacce suke ba kowa ke fahimtarsa ba Amma ita tana gane wani abu cikin maganganunsa ta fahimci kamar akwai hoton abinda yake masa yawo a kwanya da yake bashi gizon mutuwarta tunda dukkan wata kalma tasa mutuwa yake cewa Meenansa tayi to ya akayi haka?" Abin da yafi komai bata al'ajabi ita daya yafi yiwa wannan soki burutsun zantukan nasa marasa kan gado inda ta fahimci Kareem ko kadan bayason yaga Rasheed ya fiye mata mgn shi kansa Mai martaba yana nuna alamun hakan wannan take sanyata cikin jimami domin da tazo asibitin kafin sallamarsu zai tareta da cewa yawwa qawata zo na baki lbrn Meenah a duk sanda ya fadi haka sai takanga fuskar Kareem tayi duhu inda ita Kuma takan shiga tunani da zullumin wannan lamari.
Kwana uku suka qara komansu ya kammala suka dauki hanyar 9ja ko a cikin jirgin da Rasheed ya fara mata mgn sai Mai Martaba ya katseshi da cewa kai wai meye yake damunka ne Rasheed shikuma gashi ko yayi shiru baa minti biyar zai sake zungurota yace mata “yawwa qawata akai kaza akai kaza" haka Mai martaba zai sake mata tsawa itadai ta kasa jurewa ganinta wannan ai takura dan adam ne Kuma ma meye don ya zabeta matsayin abokiyar hirarsa aikuwa tayi kicin kicin da fuska ta juya gabadaya gareshi ta kamo hannunsa tace “labarin me kakeso ka bani Baffa'am?" Dago kansa yayi da yasa cikin cinyarsa ya dubi Mai Martaba da Kareem yace “ai dama batun yanzu ba na fahimci wadannan Gayun basasona da qawance dake Kuma na daina kulasu"
Murmushi tayi tace “to Kuma meye na kukan aini Inasonka da qawancen...." Ihu