Showing 87001 words to 90000 words out of 97223 words
Chapter 30 - JUHUD BY OUM HAIRAN .txt
Huci ya furzar yace “Har matarsa aka kashe ko iya shi kadai ne?" Sake jan numfashi yayi yace “ok zan dawo gobe" daga haka ya kashe wayarsa.
Ya miqe ya nufi makwancinsa ya soma safa da marwa Yan fashi sun shiga gdan Kareem sun kasheshi shida matarsa? To akanme?" Tambayar da ya rinqa yima kansa kenan mara Amsa a hankali yaji wasu hawaye sun zubo masa ya nemi guri ya zauna Yana tuno haduwarsu ta qarshe da kalmar qarshe ta Kareem ya fada masa, “Kai dan uwana ne na jini Ya Rasheed a tunanina murna ya kamata kayi da ya kasance nine na kula maka da iyalanka a halin bakanan ba gaba yakamata kayi dani ba! Ya Kareem har gobe inason Meenah bazan taba daina sonta ba har fitar numfashina na qarshe na hqr da Meenah ne badon zuciyata ta hqr ba saidon bata damar kasancewa dakai domin kaine zabinta, dani qaddara ta rubutawa bacewa ka auri matata idan na dawo gdy zanyi maka badon bana kishinta ba aa saidon nasan ta cancanta ne shiyasa ta zama matar gado cikin ahlinmu"..........
A daren nan Rasheed bai rintsa ba kwana yayi Yana tuna abubuwa da dama da suka faru tsakaninsa da Kareem tun daga ranar farko da suka fara qullah soyayya da Meenah kawo lkcn daya aureta ta qarfi da irin wahalar da Kareem ya rinqa Sha ta ciwon zuciya duk akanta kawo yanzu yanayin da suke ciki da irin bibiyar da Kareem ya rinqa yi masa akan yayi hqr ya daina gaba dashi sosai yayi kuka da baitabayin irinsa ba a duniya tabbas ya tafka kurakurai masu wuyar gyarawa Kareem baya duniya labarinsa ya shude balle yaje ya nemi afuwarsa akan abinda yayita qoqarin ganar dashi yaqi bashi qofa.
Da asussuba kuwa ya dokawa Mom Kira itanma yanda ya kwana haka ta kwana saboda tun Daren itama aka fada mata abinda ke faruwa Meenah kam batasan meke faruwa ba Amma ranar ta kasance cikin wani yanayi domin a daren waya sukeyi da Kareem Yana mata wasu kalamai data kasa fahimtarsu can taji yace “Meenah kada ki manta wannan wlh tallahi duk duniya nafi kowa sonki ban barki don biyayya ga umarnin Addah ba nabarki ne don nasan kedin banine a zuciyarki ba Meenah in son samuna ne Muneefah ta rayu a qarqashin kulawarmu ni dake nasan hakan bazata samu ba wani abu yana gaf da faruwa dani, Ina kukan rabuwa da abubuwa biyu da nafi qauna ke Meenah da Kuma yarmu Muneefah Amma a wani sashin Ina farin cikin kasancewar zata rayu da cancanta madadina wato Rasheed Meenah ki komawa Rasheed don Allah don taimakon maraicin Aishatuna kinji......" Daga haka ya tsaya da mgnr taji wata qara can taji yace “ina zuwa zan kiraki kamar Yan fashi sun shigo unguwarmu" daga wannan tajishi shiru kalamansa sun tsayanta a rai zuciyarta ta karye tabbas lamarin Kareem akwai taqawa da tsoron Allah baitabayin Abu don jin dadin kansa ba komai zaiyi yanayine don mafitar Al'umma Kareem yakai masoyi a gurinta.
Miqewa tayi zumbur lkcn da taji Ya'isha ta rushe da kuka tana cewa Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un Allahumma ajirni fih musibati Mom da gaske Ya Kareem sun kasheshi ya mutu shikenan bazai qara dawowa duniya ba Muneefah ta zama marainiya....."
Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...
Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....
*Oum Hairan*
[8/22, 8:04 PM] Oum Hairan: Da mugun gudu cikin fitar hayyaci Juhud ta fito daga dakin da take cikin gigita ta cacumi Rasheed dake shigowa idanunsa kamar garwashi ta jijjigashi tace “da gaske ko gizo kalamin Ya'isha sukemin Ya Kareem ya mutu....." Zubanta idanunsa yayi so yake yayi mata mgn ya kasa sai kawar dakai da yayi hawaye suna zubo masa yasa hannunsa ya janye nata, ganin yanda yake goge hawaye da tissue yasata zama a gurin dabar ta daura hannunta akanta ta rushe da kuka tana cewa Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un" Ya Kareem kada ka mutu dom girman Allah ya kasance mafarki shudadde Wanda bazan qarayinsa ba har abada wlh na aminta da kai zan dawo gareka na qara Haifa maka qannen Muneefah nasan shin....shine burinka a duniya....." Dagota Mom tayi tace “kiyi hqr Meenah shirya mu tafi" Babu wani shiri ta sunkuci Muneefah da taketa bacci abinta baccin asara abin tausayi mota ta debesu gabadaya harda Alh Garbu suka nufi airport dake abin na manya ne nandanan suka Isa Nigeria kamar a qasar suka kwana goma na safe suka shiga Daura lkcn an gama shirya Kareem da Zahrah zaayi musu sallah mazan suka tsaya wajen jana'izar sukuma suka shige ciki.
Addah Abulle tana ganin Juhud ta miqe ta nufeta da sauri ta karbi Muneefah ta rungume ta qara rushewa da kuka tace “shikenan ya tafi Meenah yatafi yabar Mana duniyar Babu shi din Babu Zahra wayyoh Kareem dama inada dama Dana dawo dakai duniya nabarka da zabinka da yarka daya mafi soyuwa a ranka kullum kana fadamin bakajin dadin rayuwa baka tare da Muneefah ashe ita kadaice rabonka ita zaka tafi kabarni da ita Kareem wayyoh Ni Zainabu na cuci kaina na cuceka Kareem Allah na gde maka da bakabani saa ba lkcn da malam Mati yabani magani yace nabaki kici a waina da tuni Babu Aishatu da tuni Ni da kaina na kashe bayan dana kaicona Ni Zainabu Allah ya isa Dada Hanne da Hajiya Bilki kune kukayita dorani a keken bera ashe kaini zakuyi ku baro yau na rasa Kareem ban barshi ya rayu da farin ciki ba ya tafi da jin ciwon nice silar rabashi da matarsa mafi soyuwa a duniyarsa...."
Surutai taketayi kamar wacce ta zautu hakan yasa wasu mata daga cikin danginta sukazo suka kamata suka tafi da ita daki tana kuka tana kiran Meenah Kareem shikenan Kareem ya tafi yabarmim duniyar Ina nutsuwata da hankalina yayi na kasa gane nauyin qaddararsa?" Kowa ka gani a falon kuka yakeyi mutuwar Kareem tabar tambari ba iya Daura ko Katsina kadai ba hatta arewacin Nigeria baki daya duk Wanda yaji labarin mutuwar ko baisanshi ba sai yaji alhini a jikinsa duniya tayi rashin nagartaccen mutum me hqr da kawaici kunya da kara wannan dabi'ar tasa yake soyuwa a zuciyar duk wanda yayi mu'amala dashi ta kusa kota nesa ranar anyi yinin alhini Juhud kam zazzabi ne ya rufeta sosai bana wasaba hawaye yaqi tsayawa a idanunta tayi danasanin zabar Rasheed akan Kareem ta zabi Rasheed tabar Kareem Rasheed din ya tattarata yayi watsi da ita yaqi saurarenta.
Haka suka yini yinin koke² da dare kowa ya nemi guri ya kwanta itakam koda ta kwanta kasa rintsawa tayi rayuwarta da Kareem zamantakewarsu da yanayin salon qaunarsa me tsayawa a rai shudaddiya wacce bazata dawo ba tanayi mata yawo a kwanya saidai kawai lkc zuwa lkc ta dauke hawaye, wajen 10:30 taji ana taba qofar dakin data shiga ta kulle kanta ta miqe a wahalce ta bude ta dan ja da baya a tsorace ganin Rasheed ne jajayen idanunsa akanta ya miqa mata Muneefah da tayi bacci tasa hannu ta karbeta ta juya ta nufi cikin dakin taji muryarsa data shaqe da alamun yaci isasshen kuka yace “Duk da bansan irin radadin da kikeji a zuciyarki ba na rashin masoyinki uban yarki nasan kinajin fiye da abinda nakeji tabbas akwai daci daci mafi dacin daci rabuwa da abinda kakeso a lkcn da kake tsananin buqatarsa yaune kika farajin kwatankwacin abinda naji lkcn dana rasa hanyar dawowa gareki kwanyata ta daina fadamin daidai aka rinqa nunamin ke cikin wani yanayi dana kasa ganewa har yanzu and end aka nunamin ke wani mutum ya hankadaki cikin wani dogon rami Wanda na yanke shawarar binki mu mutu tare Meenah bayan na biki bansake sanin komai da hankali zai tuna ba sai bayan shekara bakwai dinnan Amma ko a cikin yanayin zautuwar qwaqwalwata ban mantaki ba duk wani furucina kece bansan ya ake tunani ba Amma idan na zauna kece kikemin gizo da siffofi mabambata"
Numfashi ya sauke ya juyo idanunsa na zubar hawaye yace “meye kike tunani ranar da Allah ya Amsa addu'ar masoyana ya dawo dani hayyaci na laluba naga bakinan na tambayi kina Ina akacemin kina matsayin matar wani waninma qanina Meenah taya zan iya yafewa kaina bata lkcn da nayi na nakasa rayuwata saboda ke? Nakasa yafewa kaina kema na kasa yafe miki girman cin amanar da nakeji a Raina kinyimin domin bana mantawa kintaba yimin alqawarin zamu rayu tare zamu mutu tare ya akayi tun Ina raye kika zabi rayuwa da wani bani ba?"
Duk da kalamansa sun kashe mata jiki Amma yanayin da take ciki yasata juyowa a fusace tace “qaddara Abdulrasheed dukkanmu akanta muke rayuwa Babu Wanda ya isa ya tayani dakon tawa kamar yanda Babu Wanda ya tayaka Babu Wanda ya taya Ya Kareem Allah madaukakin Sarki ya sardanta ku biyun daka kuna cikin qaddarata kaine kakeja da lamarin ubangiji ni bana jayayya Ya Kareem ma baitaba jayayya ba kullum nunamin yakeyi bayin kansa bane girman rabone da hukuncin Allah saiya Sanya Muneefah tsakaninmu Kuma na dade da sanin tun baya ma shine akan daidai kai kana rayuwa ne a doron son zuciya saboda haka Baffa'am tun da sauran mutuncinka a idanuna ka fice cikin rayuwata kafin na keta alfarmarka na shiga nayi fata² da qimarka Meenah daka sani a baya ba ita bace yanzu yanzun Aminatuh ce a gabanka me taqama da asali kyawun nasaba arziqi da ilimi kada ka manta bayan tafiyarka na samu shahadar zama Barrister Aminah Haroon Moddibo so nasan yancina banason kowa cikin rayuwata ta yanzu"
Shigewa tayi daki ta banko qofar ta murda mata key ta haye gado ta zubawa yarta ido tana mata tunanin rayuwarta ta gaba babu bangonta na farko kwanciya tayi bacci ya qauracewa idanunta kamar yanda ya qauracewa idanun Rasheed sosai yake jujjuya kalamanta ya rasa a ma'aunin dazai sanyasu ta fada masa kalamai masu wahalar gogewa a zuciya tabbas shima saida ne daga yanda ta watsar dashi da lamuransa na rayuwa yasan tabbas da gaske ba Meenan daya sani a baya bace, to Amma meye yasa ita ta kasa gane tayi masa laifi me girman daya dace duk hukunci ya dauka akanta?
Busar da iska yayi ya gyara kwanciyarsa tare da dauko takardar da Mai Martaba yabashi dazu dazai shigo bayan ya fito daga dakin Meenah yace Kareem ne yabashi yace abashi kafin ya rasu. Tashi yayi ya kunna haske zuciyarsa na bugawa ganin yanda takardar ta bushe da jini ya warwareta ya fara karantawa da larabci yayi rubutun fassararsa kamar haka.
_“Assalamu Alaika ya dan'uwa mai albarka na rubuta maka wannan takarda ne a lkcn da Raina yake tafiya ga ubangijin daya halicceshi, badon komai ba saidon inason na qara baka hqr akan laifin da kake tunanin nayi maka na auren matarka Allah yasani ban aureta don cin mutumci ko tozarci a gareka ba, Ni Abdulkareem Mahfuz na zabeka na mallaka maka amanar yata qwaya daya tilo ta zama taka dama nasan takan ce don Allah Abdulrasheed kada kabari Meenah da Muneefah suyi kukan rashina musamman Muneefah ita kadai gareni Kuma na mallaka maka ita halak malak"_
Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...
Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....
*Oum Hairan*
[8/23, 7:30 PM] Oum Hairan: Matse takardar yayi a tafin hannunsa jikinsa Yana tsuma zuciyarsa nayi masa wani zugi ya miqe a gadon ya rinqa zagaye dakin nasa a tsarinsa na gaskiya ji yakeyi kamar bazai iya sake zama da Meenah ba yanajin ciwon abubuwan da suka faru a baya so yanzu ya zaiyi da wannan nauyin da Kareem ya dora masa a halin yana gargarar mutuwa? Tambaya ce da yakasa amsawa kansa ita dole akwai sarqaqiya cikin wannan al'amari komawa yayi ya kwanta ya kasa bama kansa mafita sai zafi da zuciyarsa takeyi kawai.
Abu daya da yasan ya zame masa dole shine daukar amanar Muneefah da Kareem ya damqa masa to Amma ta yaya zai karbeta a gurin mahaifiyarta bayan yasani yanajin yanda shaquwa take tsakaninsu ko giyar wake Meenah tasha bazata bashi yarta ba, da wannan tunanin ya samu bacci ya dan daukesa da safe yana fita falo ya ishe kowa suka gaisa yanata raba idanun ganin Meenah Babu alamarta hakan ya tabbatar masa tana dakin daya isheta jiya yaja fasali ya dubi Amrah yace “shiga ki daukomin Muneefah" miqewa tayi ta nufi cikin dakin ta tarar Meenah tayima yarta wanka tanayi mata kwalliya ta zauna suka gaisa tace “Big Cele yace akawo masa Muneefah"
Bataso ba saidai batada ikon hanawa ta gama shiryata Amrah ta riqema yarinyar hanu suka fito ya dauketa suka fice daga falon Mom tana kallonsa batace masa komai ba, kwanaki bakwai din da Meenah sukayi suna karbar gaisuwa ta fahimci abubuwa da yawa sosai Addah Abulle tayi laushi batada aiki sai kuka tunda ta haifi Muneefah bazata iya cewa ga ranar da Addah ta dauki yarinyar ba sai cikin kwanakin nan da taketa nan nan da ita danma Rasheed ya hanata sakat akan yarinyar duk wani motsin da Muneefah zatayi tana gareshi.
Kwanaki goma da rasuwar su Kareem bayan komai ya fara nutsawa Meenah da Kumbo Hami suka fara Shirin tafiya Rasheed baisan me akeyi ba sai a daren da zasu tashi Mom ta kirasa lkcn bai dawo daga yawonsa ba kasancewar har yanzun bai koma bakin aiki ba yana hutune take sanar dashi su Muneefah zasu tafi, Saida yaji wata faduwar gaba yace “tafiya Kuma Mom na zaci sun dawo kenan?" Murmushi Mom tayi tace “basu dawo ba to yanzu haka ma Shirin kaisu airport mukeyi" tana Fadi masa haka ta kashe wayar ta dubi Meenah da hankalinta take kan Sarki junior da yaketa kukan sai yabita itama hawaye ta share tace “makarantarka junior kabari idan akayi hutu zanzo ko na turo a daukarmin kai kaji" daqyar ta rarrasheshi ta samu ta sulale ta shiga mota suka tafi abin mamaki wai harda Addah ayi musu rakiya ashe dama tunda suka rabu da Mai Martaba tayi aure batafi wata biyu ba ta kasoshi tanason Mai Martaba ya dawo da ita dakinta shikuma yaqi.
Ko a airport din daqyar aka karbi Muneefah a hannunta tanata kuka so take ta roqi alfarmar abata yarinyar take gani ko ta rinqa samun sauqi Amma tsoro ya hanata furtawa saboda ta fahimci suma dangin uwarta sunason kayarsu da hakadai jirgin su Meenah ya daga sukuma suka juya domin komawa inda sukafi wayo cike da kewar juna.
Wannan tafiya ta zamewa Rasheed tamkar famin tsohon miki a cikin zuciyarsa abubuwa sun fara dawo masa sabbi duk da cewa izza da dagawar da Meenah ta rinqayi masa ta girgizashi baitaba tunanin akwai juyin da duniya zatayi Meenah ta rinqa kallonsa watsi dashi kamar tunda Allah yayita batasan anyi ruwansa ba.
Wata biyu abubuwa suka zama tarihi akaci gaba da cudawa kamar yanda aka saba kowa yasa abinda yake gabansa a gaba Rasheed ya koma aikinsa gabadaya sun ajeshi guri guda a Lagos inda kullum tunaninsa zuciyarsa da ruhinsa yake Mali gashi tun a farkon da abubuwa suka lalace da Meenah ta rinqa kiransa yayi block na numberta itama tayi block nasa koya nemeta baya samunta wannan tasa dole ya nemi sabon layi dal saboda zuciyarsa taqi sabawa da rashin sauraro da jin abinda zuciyarsa take muradi saidai rashin saar da yayi daya Kira sai yaji layukan dukka a kashe girman kansa na masifa ya hanashi tambayar wani cikin yan'uwansa layinta yabari akan cewa idan ya koma yasan yanda zaiyi ya sata a wayar Mom.
Hakan kuwa akayi bai iya hqrn wata biyun da yayi niyyar yi a Lagos ba ya dauko hanya ya taho Daura bayan ya huta da dare suna hira da Mom a dakinta tanayi masa fadan zamansa haka yayi murmushi yace “mom kamar akanki nake duk kinbi kin damu nayi aure" jinjina kai tayi tace “to ai Rasheed nidai naga cikar kamalar mutum shine hade kansa da iyalansa guri guda kai Kuma na rasa inda kanka yake kunqi ku daidaita da yar'uwarka Meenah Kuma ka kasa samo madadi jiya ma Baffanmu yakirani yake tambayata akan lamarinka da Meenah ance mata aure tace karatu ance ta dawo hannunka tace har abada kaima ya tuntubeka kayi masa shiru wai meye yake faruwa ne"
Goge gumi yayi ya gyara zamansa yace “ni bawai Meenah ce bazan dawo da ita cikin rayuwata ba aa Mom abubuwa ne sun kasa gogewa a mind dina Kuma na fahimci kamar itama ba nine a gabanta ba yanzun" murmushi Mom tayi tace “hakane bakai ba aure ne ma bakidaya bashi gabanta so Amma idan kaje zaku iya daidaita kanku" shiru yayi yana nazartar kalaman Mom tace “zanji dadi idan hakan ta faru Rasheed Meenah tanasonka kanason Meenah ga yaranku guda biyu baikamata ku Bari shaidan ya raba kanku ba babu wanda ya isa cikinku ya canza wannan qaddarar kama godewa Allah da rabon Muneefah bai kasheka ba Rasheed rabon ya mace zafi gareshi shiyasa kullum yanada kyau karinqa yima kanka addu'ar Allah ya rabaka da auren mace me yayan wani a cikinta duk son da kake mata idan rabon nan ya yunquro to sai dayan biyun ta faru kodai a rabu ko Kuma a mutu"
Jinjina kai yayi jikinsa ya qara sanyi abinda Kareem yayita qoqarin fahimtar dashi kenan ya kasa fahimta yau kam ya gane Kuma ya fahimta wayar Mom ya dauka ya fice daga dakin nata ya shiga mota ya nufi gidansa ya shiga ciki Saida ya dangana da dakin baccinsa ya cire kayansa ya fada bathroom yayi wanka ya dawo ya kwanta gabadaya dakin manyan hotunansa ne shida Meenah saina yaransa Sarki da Muneefah ya zubawa hotunan idanu a fili yace “lkc yayi da yakamata da dawo da farin cikina" wayarsa ya