Header Ads
Showing 96001 words to 97223 words out of 97223 words

Chapter 33 - JUHUD BY OUM HAIRAN .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

968

Ads at the middle of Article

na aiki yanzun sauran diban malamai"
Da rashin fahimta ta dubesa tace “Makarantata Kuma?" Murmushi yayi yace “Oh Sorry na manta ban fada miki ba diamond dinki da old gold dinki aka siyar diamond din ansai dashi 5.5 million gold din Kuma ansai dashi 2.7 million so sai mukayi shawari da Mom akan meye zaayi miki da kudin Wanda zai amfaneki ya amfani Al'umma so shine aka Gina masallaci a garinku kasancewar suna fama da matsalar rashin ruwa da rashin gurin ibada in akayi ruwa saidai suyi a dakunansu an Gina Bohol guda biyu a farko garin da tsakiyar Wandu masallacin Kuma a tsakiyar garin aka ginashi da niyyar ubangiji ya rinqa kaiwa iyayenki ladan, so abinda yayi saura sai aka yanke shawarar Gina makaranta Boko ce hade da islamiyya da Kuma tahfeez yanzu haka sun kammalu komai da komai kinada rarar 2.9 million a account din Sarki junior yanzu yau nasa gidan TV na NTA da AIT Da Kuma Arewa24 sunzo sun dauka tallan makarantar zaa fara tallatata mun Kuma fitar da sanarwar daukan qwararrun malamai domin samun abinda ake nema am kisan meye sunan makarantar?"










Girgiza kai tayi hawaye na kwarara a idanunta yayi murmushi ya goge mata hawayen yace “MahfAish academy sunan yayanki Mahfuz Aisha academy....." Rungumeshi tayi ta rushe da kuka tana kissing dinsa ta ko Ina tace “Banjin akwai wata kalma data saura a duniya da zanyi maka gdy da ita mijina Allah ya azurtani da mafi qololuwar alkhairin duniya daya hadani da miji na gari Ina alfahari da samunka matsayin uban yayana Allah yabarmin kai ka dade kayi qarko...."
Gabaki daya sun shagalce a gurin sun manta da anyi ruwan Aunty Hamida itadai data fahimci sun manta da ita sumsum ta miqe tabar musu gdansu suka shagalce a gurin dama tunda aka tafi da Sarki school aka dauke Muneefah
Kwanaki sukayita tafiya komai Yana tafiya cikin nasara rayuwa tanata albarka abubuwa duk suka rinqa shudewa Mom itane ta takura Meenah akan sai ta ziyarci dangin mahaifinta badon taso ba haka Rasheed ya dauketa sukaje har Jos suka shiga rugarsu abin mamaki bata taba ganin rugar data samu ci gababa kamar rufar Wandu an gyara musu ita harda makaranta da hanya ga wutar NEPA ta aminta mutane duniya sukeyima bauta Wai yau itace Baffa Ribado da Baffa Bangel suke kuka suna bata hqr akan abubuwan da suka faru da irin sharrance sharrancen da suka rinqa yi mata.
Murmushi kawai takeyi tana share hawaye lkc bayan lkc da dare ne bayan komai ya lafa take tambayar Ina Hammah Manga nan aka zauna ana bata labarin Wai an kasheshi a dalilin kidnapping din wani Dan siyasa da sukayi sojoji sukaje sukayi barin wuta akansu ko gawarsa baa tsinta ba.








Sosai ta jinjina lamarin tare da yimasa fatan rahama ta kwana dayanta a dafe wai saigashi sune harda soya mata manshanu da tatso mata danyar Madara Baffa Moddibo yayima Sarki da Muneefah kyautar saniya aikuwa Sarki yace saidai a daukar masa abarsu dake ba wata babba bace Rasheed da taya bera Bari yasa aka daureta aka sanyata a mota sunata yi musu dariya suka dauki hanya cike da jin dadi zuciyar Juhud yan uwan da suke qyamarta yau itace suke qauna sunata Sanya mata albarka da abubuwan alkhairin da suka samu ta dalilinta.
Cikin wata biyun da sukayi suka juya Lagos hada kan yayansu suka tafi daga Muneefan har sarkin aka Sanya a makaranta taci gaba da rainon cikinta suna qara samun shaquwa da kula da juna da haka cikinta ya isa haihuwa ta dawo Daura Kwananta uku da komawa kuwa ta sunkuto yaranta uku wannan abu ya tsuma dangi ita kanta tayi mamaki saboda cikin nata ba wani shararren girma yayi ba sannan ko a hoto biyu suke cewa da ita sai gata da uku duk maza nan fah wannan family ya kacame kowa mgnr haihuwar yakeyi ranar suna yaran sukaci sunan Babban Haroon mai bi masa Abubakar sai Abdulkareem qaramin aikuwa ansha shagali kamar baa taba yiwa wannan Fam Haihuwa ba kama daga Daura Mali da Jos kowa yayi bajinta su Rasheed harda kyautar kujerar hajji yayima mutum uku Baffa Moddibo da Baffa Ribado da Baffa Bangel saboda murnar wannan haihuwa.








Bayan komai ya lafa yaso su koma Lagos ta kafe Saida tayi arba'in sannan suka koma da qarin me raino daya Ladi itama mutuniyar kirki sukaci gaba da rayuwarsu cikin gdyr Allah da amincewarsa Rasheed kullum likkafa ci gaba takeyi yau matsayin General Rasheed Gen Mahfuz yake amsawa inda makarantar Meenah kullum take qara habaka abin gwanin birgewa da hamdala shekara biyu Meenah ta qara haihuwar ya mace daga kanta tace ta gama abinka da yan bokon qarshen zamani suka fita India aka juyar da mahaifar gabadaya ta dawo taci gaba da kula da yaranta.
Sannu a hankali maqiyanta irinsu Fadila Dada Hanne Hajiya Bilki da wasunsu na boye sai gashi duk sun zama yan koranta idan taje Daura har zuwa sukeyi gaisheta musamman Fadila data zame mata kamar aminiya yanzu duk duniya bata da qawar data wucce Meenah hakan ya samo asali ne daga yanda Meenah ta shiga ta fita taga sun daidaita da mijinta ya mayar da ita dakinta cikin yayanta, itama Addah Abulle daqyar bayan auren datayi Mai Martaba ya dawo da ita dakinta inda ta dauki soyayyar duniya ta dorawa yaran Meenah guda biyu Muneefah da take yar danta da Kuma Kareem qarami da yaci sunan danta duk wani tanadinta nasune sauran jikokin gdan har tsiya sukeyi mata wai ita ta fiye son kai, itadai Meenah saidai tayi dariya tana mamakin yanda komai ya wucce kamar ma baayi ba idan tai tsai sai kawai taji hawayena tsiyaya a idanunta da zaran ta tuna yanzun muma duka wataran shudaddu ne gushewa zamuyi a manta da tarihinmu mu dusashe kamar baa haliccemu ba, a wannan ritsin tsoron Allah yake qara ziyartar ruhinta takanji duk duniya tayi mata zafi kullum addu'arta Allah kada ya jarabci yaranta da irin jarabtarta Allah ya Basu qaddara me sauqin dauka ya Sanya musu albarka cikin cinsu da shansu da motsinsu a kowanne yanayi yabawa mijinta qarfin gwiwar nemo halal a ko Ina take.










_Tammat bi Hamdullah_








_Tabbas komai yayi farko zaiyi qarshe yau dai Juhud yazo qarshe Ina gdy ga ubangijin bayi me kowa me komai daya bani ikon farashi da kammalashi lafiya kamar yanda na tsara._
_Kurakuran dake ciki ubangiji ya yafe Mana badon halinmu ba amfanin ciki Allah ya bamu ikon amfana baki daya._
_Bazan rufe ba sai nayi gdy gareku masoya da baku qasa a gwiwa wajen qarfafamin gwiwa da kudadenku da lkcnku tabbas Ina alfahari daku Ina fatan ubangiji ya sadamu a dausayin zumunci na masuyin soyayya dominsa._






_Kada ku manta next book dina _*YAFI ZAMAN AURE!*_ _yananan tafe da irin tasa rikita rikitar very soon insha Allahu._


_*Oum Hairan*_
. *************************⬇**********************
************* Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************


DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.


Visit > https://www.aihausanovels.com.ng


Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com


******* FOLLOW US ******


Facebook: Ai Hausa Novels


Twitter: Ai Hausa Novels


Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels






Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.


********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads