Header Ads
Showing 66001 words to 69000 words out of 97223 words

Chapter 23 - JUHUD BY OUM HAIRAN .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

956

Ads at the middle of Article

bakin qoqari" zama tayi dabar a gurin gumi na karyo mata tace “ni Kuma Mom in bisa Saudi haba Mom don Allah kice masa aa inada abubuwan da sukafi binnasa muhimmaci anan Mom inason in nemi dangina su hadani da dangin mahaifiyata idan naci gaba da zama a haka akwai matsala please Mom kisa baki don girman Allah"








Murmushi Mom tayi tace “wannan duk me sauqi ne ni na daukar miki alqawarin bibiyarsu har zuwa lkcn da zaa dace kibani address nasu" sunkuyar da kanta tayi hawaye wani nabin wani itadai bataso ba taso tayi komanta da kanta miqewa tayi ta koma dakinta ta kishingida zuciyarta na zafi haka yinin ya kusan qarewa kiran duniya da yakeyi mata taqi dagawa itafa bayan zafin tsanarsa saboda mahaifiyarsa da tayi harma da ganin rashin dacewar wannan auren nasu duk da tasan ba haramci a ciki Amma wata halal din ta cancanci bari don kunya.
Da la'asar tana kwance Mom ta turo qofar ta shigo da sallamarta ita da wata mata Meenah dake kwance ta miqe suka gaisa da matar Mom tace “wannan itace nakeyi miki mgn aurenta na farko yazo a wani yanayi baayi mata komai ba so data haihu an gyarata Amma anja shekaru kusan shekara antafi biyar shine yanzun nake buqatar ki qure fasaharki wajen gyarata ko nawa ne mijinta yace zai biya" suna hirarsu wannan Hajiyan na fito da saiwoyi da magunguna tana yima mom bayani tare da turaruka itadai tabe baki kawai takeyi bata yarda abin gaske ne ba Saida taga an dauki wani qoqo an zuba wani ruwan tsumi an dauko wasu barbade barbade anyi an gwamutsa da danyan madarar shanu wai sun miqo mata tasha.
Ta dubi Mom da idanunta daya kawo ruwa zatayi mgn ta kuwa daure fuska tace “aini dama nasan ban isa dakeba Aminatuh nunamin bani na haifeki b...." Da sauri ta karbi qoqon maganin jikinta na rawa ta kafa bakinta ta shanye daqyar tana kakarin amai matar tayi murmushi tace “wannan shi kadai ma idan Tasha na kwana biyar ya wadatar bare zaa hada da wasu tun daga wannan rana Juhud ta bani ta lalace da magunguna wasu tsarki wasu Sha wasu dafawa itadai bakinta har daina tantance dandano yayi cikin kwanakin batada aikin daya wucce kuka.










Wayar ma da Kareem ke kiranta ta jefashi a blacklist ko ya Kira baya samunta hakan tasa dole ya qyaleta yasan duk inda yau takai da jimawa gobe tana tafe yanaji a jikinsa wataran wannan qiyayyar zata shude tunda da babu ita daga baya ta wanzu to watarana itanma zaa nemeta a rasa, da wannan tunanin ya tattarata ya zubanta ido akayita shirye²n tariyar tata shine da Mom da Ya'isha da Aunty Hamida suketa digiminsu dakin uwar ango da yan'uwansa Babu me ko lale da bikin hasali ma ko bangaren da ake shagalin basuyi itama amaryar haka saidai idan Mom tayi mata dole sannan take dan motsawa hakana aketa kaiwa da komowa su Ya'isha sune yan jeran amarya har zuwa lkcn Zahrah bata dawo ba aka gyarawa Juhud dayan bangaren kamar yasan zaiyi mata biyu dama tsarin mace biyu yayiwa gidansa bayan sun gama gyarawa sun zubanta duk wasu kayan alatun rayuwa suka kullo suka taho gda sunata yabawa da kudin da Kareem ya narkar a furniture dinta lallai ba qaramin so yakeyiwa Meenah ba.
Ta dauki gyaran jiki na ban mamaki abinka da farar fata har wani yellow takeyi yanda Mom ke rawar jiki a wannan bikin ko Rasheed ne ya dawo ba lallai tayi ba ko lalle da akayi mata dishi² ya kama jikinta saboda tsabar gyara hatta gyaran gashi a gda akayishi yin duniya suje gurin gyaran taqi tana maqale a daki kamar wata mara gsky ko yaushe cikin kukan rashin mijinta take da anbarta da wannan damuwar ma da tafi mata fiye da wannan da aka qara mata








Ranar juma'ar Mom taga ikon Allah yini Meenah tayi tana kuka tana kiran Rasheed duk dauriyar da Mom takeyi a wannan karon Saida ta kebe itama taci kuka ta gode Allah Mom bata qara tsinkewa da lamarin Aminah ba Saida magrib da Kareem ya turo da motocin daukar masa amarya tunda ta fice a sashin su Mom din aka nemeta aka rasa babu wanda hankalinsa bai tashi ba amarya ta bace da aka fadawa Kareem neman zaucewa yayi ya nufo gdan afujajan suka shiga nemanta lungu da saqo domin sun tabbatar da cewa tana cikin gdan kasancewar masu tsaron qofofin gdan sunce Babu wacce ta fita gabadaya sun gama karade gdan babu dalilinta sai a qarshe Mom tace aje bangaren Rasheed ko can tayi haka Kareem da Mai Martaba suka nufi part din ga mamakinsu suka tarar dashi a bude suka kalli juna babu furuci suka kutsa ciki yayi qura sosai part din haka suka rinqa dubawa can cikin wani daki suka rinqa jiyo shassheqarta har rige² sukeyi wajen shiga dakin sukaja sukayi turus dukkansu ganinta zaune gefen gado rungume da wani hoto a qirjinta sai kuka takeyi me ban tausayi.
Wani abu me nauyi ne yazo ya tokarewa Kareem maqoshi ya furzar da iska me zafi ya juya ya fice daga dakin sai Mai Martaba ne ya qarasa shiga ya kamo hannunta Babu musu ta miqe tanaci gaba da kukanta idonta lullube da alqyabba ya fito da ita harabar gdan Ya'isha ta nufosu da sauri suka sanyata a mota tana qarawa kukanta sauti tana Kiran sunan Baffa'am Sarki junior dukkan wanda yake a gurin hatta Mai Martaba Saida tasashi sharar hawaye.








Hakanan suka nufi unguwar da gidan nasa yake Mai gadi ya bude musu suka shiga sukayi parking Aunty Hamida ce take riqe da hannunta har cikin gdan suka haura da ita saman itama kamar dayan sashin dakuna biyu ne sai wani qarami da alamun local kitchen ne wanda koda zaka buqaci wani abu da dare basai ka sauka ba, daya cikin dakunan suka bude suka shigar da ita sosai Hajiya Kulsum aminiyar Mom ta qara yimata nasiha akan biyayya ga mijinta itadai Babu abinda da takeyi sai kuka da rawar sanyi zazzabi ne yake neman rufeta Ya'isha ta matso jikinta ta sunkuya tace “ke banza ce wlh Ni banga abin kuka ba to kukan mafita ya zame miki kome?" Dagowa tayi ta sauke idanunta sa suka jima da komawa jajaye saboda kuka tace “shi....shikenan da gaske na rasa Baffa'am dina Ya'isha Kuma akeso nayi rayuwar farin ciki....." Muryarta ne ya kama rawa Ya'isha tace “mun shigai Aunty Hamida ku Kira mijinta zata tayar mana da aljanu" yanda jikinta ke tsuma ne yasa Hamida yarda ta Kira wayar Rasheed ya daga muryarsa can qasa shima rawar tasa muryar takeyi yace “ya aunty Hamida ya akayi?" Cikin zaquwa tace “Meenah ke neman rikice Mana mun kasa gane kanta don Allah kazo idan kana kusa" kashe wayar yayi dake dama Yana gdan duk motsinsu yanaji ya dauki doguwar riga ya saka ya bude qofar ya fito idanunsa kamar garwashi saboda ja dake duk yafisu Rasheed haske shi fari ne sosai daka kalleshi zaka gane kukan shima yakeyi.
Kuka Fadila ta saka da ganin yanda yayan nata ya zama wani kalar tausayi tace “tunda yarinyar nan ta shigo zuri'armu muka daina cikakken farin ciki Ya Kareem kaima duk ta susutaka yanzu kukannan don ita kakeyinsa....."
Hanya ya saita mata cikin zafin zuciya yace “kowa yaje na gde" binsa sukayi da kallo ya dubi Hajiya Kulsum yace “Mama wlh idan akaci gaba da hayaniya a gdannan tsaf zan haukace brain dina tana neman daina aiki" sumsum suka rinqa ficewa daga gdan saida suka fice gabadaya ya tsaya yana jin tashin motocinsu gabansa faduwa yake daqyar ya tura qofar da sallama ya shiga dakin ya tsaya tsakiyarsa Yana qarenta kallo tana zaune ta dora kanta jikin gado sai tsumar jiki takeyi a sanyaye ya isa gareta ya tsugunna gabanta yakai hannunsa zai dago kanta gabansa ya fadi ya janye ya sake saita idanunsa akanta yace “meye yake damunki?" Kamar me jiran yayi mgn ta dago kumburarrun idanunta suka shiga cikin nasa ya kawar da kansa ya dake zuciyarsa yakai hannunsa jikinta yajishi zafi zau yaja numfashi ya miqe ya dauki wayarsa Yana zagaya dakin can yace “Inada petiant a gdana kazo da wuri don Allah" da haka ya kashe wayar yaci gaba da zagaya dakin can yaji ana qwanqwasa qofar ya sauka ya bude suka shigo tare Dr Razaq ya fara tambayarta yanayin da takeji tayi masa shiru shikam Kareem ido ya kafeta dashi can da tambayar ta isheta tace “Kaje Dr Razaq bakada maganin matsalata Allah ne kawai zaimin magani" wata iska Kareem ya furzar ya juya ya fice Dr Razaq ya biyosa yaganshi tsaye ya hade kai da garu ya dafashi yace “ka daina Sanya wannan damuwar a ranka Ranka shi dade kanada heart problem idan komai zaike damunka to rayuwarka tana cikin kwale²"
Juyowa yayi ya dubi Dr Razaq yace “kana nufin Meenah zata soni nima?" Dariya tambayar tabawa Razaq yace “kama qaddara a ranka tasoka fiye da kowa ta gama karfa ka manta kaine ta fara so a rayuwarta ko ka manta Karin mgnr hausawa da suke cewa so baya tsufa saidai masoyan su tsufa bature kuma yace true love never end" wani murmushi yayi yace “na gde Dr Razaq zan jira lkcn da zan gasqata hakan".............








Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank






Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...






Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....






*Oum Hairan*
[8/8, 9:07 PM] Oum Hairan: *0032* Sallama sukayi ya rakashi ya hau motarsa tare da karbar magunguna bai koma gdan ba shima ya shiga tasa motar Yana duba agogo 8:30pm ya jinjina kai ya fice a gdan kai tsaye wani restaurant ya nufa yayi musu siyayyar abinda zasuci ya juya ya koma gdan ya kulle ko Ina ya nufi saman Saida ya shiga dakinsa yayi wanka ya sanya kayan baccinsa ya fito ya bude nata dakin tana zaune inda ya barta har yanzu kukan takeyi gabadaya lamarinta ya tsinka masa lakar jiki da gaske take jin damuwar a cikin ruhinta.
Aje ledar dake hannunsa yayi ya tsugunna a gabanta ya kamo hannunta ta fuzge ya zauna sosai a gabanta ya dafe kuncinsa da hannayensa biyu ya zuba mata manyan idanunsa da a baya suke firgitata da sanyata shiga taitayinta baiji a ransa ko yace ta tashi suyi nafila zatayi ba shiyasa ya janyo ledar yace “Ya'isha tace tun shekaran jiya bakici abinci ba ko meye dalili?" Shiru tayi masa yaja fasali ya furzar da iska ya bude ledar ya fara yaga mata Naman yanda zataji dadin ci ya dauko yakai mata bakinta ta kawar dakai yayi murmushi yace.
“Lamarinki abun mamaki ne Meenah sai naga kamar kina jayayya da hukuncin ubangiji ne ya kamata ace rayuwarki kadai ta ishenki darasin da duk wani abu da Allah yayi zaki tarbeshi hannu biyu wlh duk da nakasance me qulafuci da addu'ar idan kedin Alkhairi ce gareni ki zama gatana ki zama mallakina bantaba furtawa wani burina a kanki ba na fawwalawa ubangiji na yarda duk abinda yayi daidai ne so Kuma sama taka cikin lkcn da ban tsammata ba kiran Mai Martaba ya shigomin yana fadamin na tanadi sadaki a hannuna daga dubu hamsin zuwa abinda Allah ya horemin nazo masallacin Fada yana nemana bansan meye zai faru ba hakanan na tafi Ina zuwa naga dogare sun budamin na shiga kamar yanda baa nemi izininki ba nima baa nemi nawa ba wlh kudin aljihuna kawai Mai Martaba ya karba dubu tamanin yabada umarnin a daura nidai na nemi guri na zauna Ina jiran naji auren waye zaa daura kawai naji ance yace shi a matsayin waliyinki ya bada aurenki gareni akan sadaki naira dubu tamanin bisa sharadin zanyi miki lefe kamar yanda al'ada ta tsara"






Shiru yayi yana mayar da numfashi sannan yaci gaba da cewa to meye laifina cikin lamarin nan Meenah?" A qufule ta dago tace “meyesa bakace bakaso ba?" Murmushi yayi yace “ko bake bace zan karba balle Kuma ya kasance dadaddiyar addu'ata ce ubangiji ya amsamin tare da tabbatarmin da ita kamar mafarki so ni a tsarina bana jayayya da duk abinda nasan ba ikona bane, Meenah a baya kema haka kike saboda kedin dalubata ce bansan meye ya sauyaki ba kinga inada maganganu da yawa da nakeso mu tattauna da zasu zame mana mafita Amma farko don girman Allah badon halin Abdulkareem kici abinci muyi sallah wlh ko Isha banyi ba saimu zauna"
Yanayin magiyar tasa tasata dole ta dauki Naman takai bakinta yaji dadin hakan sosai ya miqe ya shiga bathroom ya dauro alwala lkcn daya fito ta gama ya tattare ya fita da kayan ya dawo ya isheta a bayi tana brush da alwala, abin sallar ya shimfida yajasu sukayi Isha sukayi nafila raka'a biyu ya sanya hannunsa ya dafa kanta ta zame zata miqe ya miqe ya riqeta tare da matseta a jikin bango ya fara karanto addu'o'insa cikin larabcinsa me Sanyaya jiki sunkai 10 minutes a haka sannan ya saketa yana binta da kallo har zuwa lkcn bata daina dauke hawaye a idonta ba miqewa yayi ya dagata ya zare mata alqyabbar jikinta ya sake ware lafayar jikinta tana tureshi tana komai ta durqushe da sauri yayi dariya wai kunyarsa takeji Meenah da lkcn data fara period shine mutum na farko daya fara sani shima a lambu ya isheta tanata kuka wai taji ciwo daqyar ta fada masa yayi mata bayani.
Sautin dariyarsa ce tasata dagowa ya zauna tare da daganta gira yace “ashe kinajin kunyata Meenah yaushe kika farajin kunyana?" Harara ta galla masa yace “ko a jikina ki kwana kinayi yanzun dai Bari na barki ki kwanta ki huta abinki Saida safe" ficewa yayi yaja mata qofa tabisa da kallo tare da miqewa tayiwa dakin key ta haye gadon tayi kwanciyarta badon tayi bacci ba saidon tabawa zuciyarta damar tunanin abinda yake damunta.








Batasan lkcn da bacci ya dauketa ba a sama ta rinqajin ana taba qofar ta miqe tana miqa tare da yin salati tace “wayene?" Cikin sanyin yanayinsa na dabi'a yace “kinyi sallah ne?" Bata bashi Amsa ba ta nufi bathroom ta watsa ruwa ta dauro alwala ta fito ta sanya doguwar riga ta tayar da sallar bayan ta idar tayi azkhar ta sake zubewa a gurin duk da ba wata hidima tayi a bikin ba tanajin gajiya a jikinta sosai, bacci ne ya sake dauketa bata farka ba sai 10:30pm shima din wayarta ce taji tana ring baqon layine ta Kara a kunnenta yace “barka da safiya ki fito kinyi baqi"
Miqewa tayi tasa rigarta ta bude qofar ta fito Sarki ya rugo da mugun gudu ya rungumeta ta dagashi daqyar tana dariya yaron yace “Mom jiya nayita kuka daban ganki ba ashe gdan Uncle kika dawo nima na dawo nan" murmushi tayi tace “surutu dai kazo ka dameni ko" tsuke fuska yayi zaiyi kuka Kareem ya matso ya karbeshi yace “ba tun jiyan nace kazo mu taho ba kace kai bazaka tafi kabar Mom dinka ba to yanzun fah zaka taho ko shima aa?" Da sauri ya daga kai yace “eh" Mom dake tsaye tayi dariya tace “aikam baka isaba yaro muna tare aurena dakai mutu ka raba" kuka ya saka Yana cewa “nin...Ni Mom banasonki kinmin tsufa ni gurin Mom dina da uncle zan dawo"








Dariya sukayi dukkansu ta nemi guri ta zauna Hamida tace “jikin yayi sauqi kenan tunda na tafi nakasa sukuni dake na kwana a raina" sunkuyar dakai tayi ya miqe yace Mom me zaa kawo muku gdan namu bai gama tsaruwa ba Hajiyan sai yanzu ta fito" kiransa Mom tayi tace “kazo kayi zamanka bama buqatar komai tun jiya da sukaje suka sanar dani halin da ake ciki na kasa sukuni shiyasa nazo naganku yanayin Alhmdllh komai zai wucce insha Allahu Meenah hqr zakiyi da abinda Allah ya hukunta, Aminatuh nice na haifi Rasheed Amma bazanyi shaidarsa kamar yanda zanbada shaida akan Kareem ba kin samu miji na nunawa saa daya tamkar da dubu idan kin kwantar da hankalinki insha Allahu komai zaizo qarshe ita rayuwa kowa da irin tasa jarrabawar Babu me taya wani dakon kayan da ubangiji ya qulla masa dole shine zaiyi dakon kayansa rabon dake tsakaninku me qarfine Allah ne kawai yasan adadinsa saboda haka kuyi hqr da jarrabawarku"
Kallon kallo sukeyi kowa da abinda keyi masa yawo a ransa Mom ta miqe tace “Inason mgn dake Meenah miqewa tayi tabita suka haura saman dakin baccinta suka shiga Mom ta zauna a gefen gadon ta kama kunnenta tace “ki kiyayi shiga haqqin Kareem kawaicinsa da kararsa ta game kowa zai iya zubanki ido akan duk abinda yaga baki da raayi koda kuwa shi zai cutu hqrnsa abin jinjinawa ne shiyasa yake wahala idan ciwo ya ganshi don Allah kada ki zama silar wargatsa masa rayuwa kinji"








Kwantar da kanta tayi a cinyar Mom tana shassheqar kuka ta dauko wasu turaruka masu qamshin gaske na humra da na wuta tace muje a jerasu a show glass din fita sukayi suka jera ta fito da wani garin magani ta dauko danyen nonon raqumi ta barbada a ciki ta miqa mata tace “shine yayi saura da jiya kikaqi sha duk yanda kike tunanin fitinar Rasheed Kareem yafisa saboda akan hakan har so akayi a raba aurensa da Zahrah kwanakinsa bai qare ba yanzu Kuma gashi zaki zauna ke daya da sunyi hqr ma sun barta ta dawo da kin samu sauqin wani abun don Allah banda rowa Meenah shidai abinnan in kin hanashi ma ba ado zakiyi dashi ba Kuma ba kwanaki zaa qara masa ba idan wa'adinki yayi shima nasa yayi please a kula don Allah" sosai Mom ta rinqa bata shawari a fakaice saida taga ta dan sake sannan sukayi musu sallama suka tafi shima ya fice a gdan ta shiga bathroom tana wanka ta jiyo wayarta tana ring batabi takanta ba Saida ta gama shirinta tsaf sannan ta dauka number Ya'isha ce tabi suka gaisa tace “ya amarci jiya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads