Header Ads
Showing 90001 words to 93000 words out of 97223 words

Chapter 31 - JUHUD BY OUM HAIRAN .txt

Ads the beginning of article before Image

02 Jun 2024

965

Ads at the middle of Article

dauka ya Kira Abokinsa Kamil suka gaisa yace masa “cikin satinnan kana free ne?" Amsawa yayi da “eh" yace “ok zamuje Mali ne jibi" bai boye masa komai ba khamil yayi dariya sosai yace “tsohuwar zuma kishin ya gushe kenan?" Ya lura tsiya ya shirya yi masa don haka ya kashe wayar ya dauki ta Mom yanabin contact din ya lalubo number ya danna kira lkcn tana sallar Isha Muneefah ce tana wasa da wayar ta danna tana gwarancinta yayi murmushi yace “daughter bakin yazo kenan?" Nan sukayita shirmensu da yarinyar bayan ta idar ta karbi wayar tunaninta ko Muntaz ne ko Urwat tace “surutu ke gareta Mamana bata rabo da rigima" ajiyar zuciya yaja a hankali taji ya sauke numfashi yace “hakan yanada kyau ba lallai tayi kamar na Mom dinta ba" qamewa tayi a gurin jin muryar da batayi zato ba nandanan ta rinqajin zuciya na ayyana mata ta kashe wayar tana Shirin gimtse layin taji yace “ranar juma'a idan Allah ya amince zan shigo qasar ki fara Shirin zama amarya domin bazan kwana a garin nan ba saidake matsayin matata kamar yanda yake rubuce a allon qudura duk wanda yayi karambanin shiga wannan gonar ma saiya fice da kansa ko Kuma dole ta fitar dashi"








Murmushi tayi tace “tunaninka ne yake baka hakan nikuma inajin a raina qaddarata tayiwa taka nisa Ya Rasheed so don Allah kada mu wahalar da shari'a kayi zamanka a inda Allah ya ajeka idanma matsuwa akayi nayi auren naji zan fitar da miji tsakanin yau da gobe Amma kaikam nagama aurenka" murmushi yayi yace “au haba da gaske Kuma kikeyi? To ai kin manta da Abu daya ni idan nayi niyyar aiwatarwa yuwuwa yakeyi Meenah badon kanki da kaina ba don rayuwar yaranmu nayi niyyar abinda na furta saboda haka kada ki manta gyarane kawai Amma kedin matata ce domin da igiyar aurena uku akanki aka jingine aka dauranki wani.... Oh God banaso nake tunawa fah ki share kawai sainazo".......
Daga haka ya gimtse wayarsa yabarta da sakin lebe lallai wannan yazo da izala mara gemu dole ta takansa birki don bataji a ranta wannan tatsunniyar zata yuwu ba.










Ranar kwana tayi tana jujjuya kalamansa da safe kuwa bata sanar da kowa ba ta shirya nata ya nata ta gudu gidansa Aunty Kharimatu batare da kowa yasan inda ta tafi ba Kumbo Hami ta riga tasan me ta gudarwa saboda sunyi waya da Mom a haukan ma da takeyi tuni magana taje ga kakanta ya Kuma amsa har anyi duk abinda zaayi an wucce gurin da sahalewar Mai Martaba.
Tana zuwa gdan Aunty Kharimatu suka lalace da hira har dare tayi kwanciyarta dake mijinta matafiyi ne washegari ma sukaci gaba da harkokinsu har magrib batada niyyar tafiya suna falo suna cin dambum nama sukaji sallamar Jabir gabanta ya Fadi ya shigo yanayi mata dariya yace “girman kujera aunty babba kinada baqi a waje fah" harara ta zabga masa tace “munafuki suwa kak debomin?....." Bata gama rufe bakinta ba sukayi sallama suka shigo idanunsa na kanta ta kuwa hadiye fara'arta ta hade rai ta miqe ta nufi wani daki suka dubi juna shida Khamil sukayi murmushi suka zauna Aunty Kharimatu nata zolayarsa fadi takeyi lallai ango kasha qamshi ashe da gaske kana tafe"
Shafa sumarsa yayi Yana cire hularsa yace “wlh Ina tafe nazo na dauke matata mu tafi nagaji da zaman gwaurontaka" harararsa tayi tace “aa kuwa baka isaba wannan abu Babu shiri nifa sai dazun Kumbo ke fadamin Shirin da akayi nace halan ma waccan uwar taurin kan bata sani ba don ko dazun Saida tace batada muradin wani aure" numfashi ya sauke yace “tasan komai ai dama barinta nayi ta huta saboda rayuwar batada tsayi Amma an fuskanci qalubale da suke buqatar dogon hutun brain"...........








Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank






Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...






Juhud ba littafin kyauta baney ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....






*Oum Hairan*
[8/27, 9:03 PM] Oum Hairan: Dariya Aunty Kharimatu tayi tace "ah lallai to ubangiji ya kade fitina ya daidaitaku sai aje ayita hqr koda yake tsohuwar zuma ce Babu wani qalubale qalaunku zaku zauna wuyarta ku daidaita kanku......" Aunty Kharimatu bata gama rufe bakinta ba Juhud ta fito dauke da Muneefah da niyyar ficewa daga gdan Muneefah na ganin Rasheed ta fara zamewa a jikinta tana Kiran Dad sweet Dad biscuits...." Murmushin gefen baki yayi ya miqe ya nufi Meenah da takai bakin qofa yasa hannu zai karbe yarinyar ta juyo a fusace cikin bala'i tace “inada tabbacin bakada wata alaqa data wucce wan mahaifi gurin Muneefah domin kuwa qaddararta me qarfi ce itane ta sanya abubuwa da yawa suka faru a qarshe dai nida Kareem muka Samar da Muneefah saboda haka ikona ce"
Sakin yarinyar yayi yayi baya jikinsa na daukar sanyi yanajin saukar kalamanta na dukan zuciyarsa, batare da wata damuwa ba ta fice ta jefa yarinyar da keta kuka a mota ta shiga ta figi motar a mugun guje ta fice a harabar gdan tabarshi tsaye kamar dashe Yana qara maimata kalamanta, Khamil ne ya dafashi yace “nifa Ina mamakin yanda dangantaka tayi tsami haka tsakaninka da Meenah meye ya farune mutumin bakada dama ne fah qila Kaine ka tabo zuciyarta" janye hannunsa yayi yace “koma mene ban cancanci wadannan munanan kalaman akan yar qanina ba Amma zan gwada mata haihuwa ce tata nafita qarfin iko" Yana fadin haka ya fice Yana huci ran maza ya baci Jabir ne yazo yajasu suka nufi gda ganin motar da ta hau ta fito yasashi tabbatar da gidan ta dawo, bai shiga cikin ba ya nufi sashin baqin ya cire kayansa ya zauna yana fitar da iska me zafi zuciya na raya masa meye zaiyi ya rama wannan wulaqancin da Meenah tayi masa?






Ya jima bacci bai daukeshi ba sai juyi yakeyi da safe ya fiçe ya nufi cikin gdan Meenah bata tashi daga bacci ba a zahiri ba baccin takeyi ba kawai juyi takeyi, shiga yayi part din kumbo Hami suka gaisa ya wucce bangaren Alh Garbu suka gaisa yayi shiru na dogon lkc kamo hannunsa yayi yace “meye yake faruwa ne Dan Boko?" Qasa yayi da kainai Yana shafa sumarsa can Alh Garbu ya sake dubansa yace bai wucce kace kanason tafiya da matarka ba ko?" Jinjina kai yayi yace “hakane Alh inason jibi idan zan tafi mu tafi gabadaya saboda dawowa zatayimin wahala kusa" jinjina kai Alh Garbu yayi yace “shikenan zan fadawa kakar taku inyaso saisu fara Shirin abinne yazo Babu tsammani Amma fah akwai abinda bazan dauka ba cikin lamarin aurenku duk wani cin Kashi da akayi mawa Aminah a baya yanzu ko ita ta daukeshi ni bazan daukaba" ya jima yana kafa sharrudansa shidai Rasheed jinsa kawai yakeyi har ya gama ya tashi ya fice.








Lkcn da Kumbo Hami taji Shirin da Alh Garbu yayi taso tace aa Amma ya hanata katabus dole hakanan ta hqr tana jiran ranar zartaswa aikam ana samun Meenah da mgnr tayi tsalle ta dire tace batasan zance ba duk Wanda suke tunanin zai fada aji ya fada tayi kunnen uwar shegu Rasheed kam abokin gaba ya zama batako kallonsa bai wani damu ba saidai ya kalleta yayi murmushi ya barta tayi duk abinda yasan na dan lkc ne da lkcn ya wucce shikenan, ana gobe tafiyar da dare ya shiga har dakinta ya tarar da ita itada Aunty Kharimatu da Kumbo sai aikin rarrashinta sukeyi suna ganinsa suka miqe suka fita ya mayar da qofar ya rufe ya nufota ta miqe tsaye ya tsaya Yana murmushinsa na isa tare da zura hannunsa a aljihunsa ya harde qafarsa ya jingina jikin bango yace “banzo domin na baki hqr Kona rarrasheki ba saboda Ni nasan banyi miki laifi ba hasali ma nine nake tuhumarki so inada abinda yafi haka muhimmaci kin fadamin wata mgn ne da nakasa jureta shine nazo baki amsa Meenah yes na amince keda Kareem kuka Samar da Muneefah Amma kada ki manta kafin Kareem ya baki da nine na fara baki na farko kika zubarmin na biyu kika haifamin gashi ya zama saurayi so wannan kadai ya isa ya tabbatar miki ni na wucce kiyimin gatsali akan Muneefah Kuma ko kinaso ko bakiso dole kibarni da ita domin ba saboda ke nakejin yarinyar a Raina ba saboda mahaifinta yayimin kyautarta ne"








Shafa gemunsa yayi yayi murmushin gefen baki yace “shekarar Muneefah daya da rabi ki shirya karbar qaninta kowanne lkc daga yanzun ni bana wasa da dama amfani nakeyi da ita sosai" ficewa yayi daga dakin yabarta tsaye da zubar hawaye takaici kamar ya kasheta taja qwafa ta koma ta zauna.
Duk wani shiri da Kumbo Hami taso yi mata taqi bata hadin kai sai huci takeyi kamar ta kashe kowa haka takeji batasan meye yasa takejin haushin Rasheed ba ko ganinsa batason yi sauqinta daya dake tunda ta haihu Kumbo take hadata da magungunan da tasan bazasu cutar da itaba so data fahimci ba hadin kai zata bata ba saita tattara mata ta zuba mata cikin kayanta ta hade mata komai washegari kuwa da wuri suka dauki hanyar 9ja aikam anyi tafiyar kurame Babu me cewa wani qala garama shi da Khamil suna hira jefi² inda suka sauka ta tsaya tana kallo bata taba zuwa Lagos ba hakanan takejin to Ina ya kawosu?" Bai bata damar tunanin mafita ba motar office dinsa tazo ta daukesu suka nufi unguwar da yake da zama tasha mamakin gidan da aka kaisu ta tsaya tana qare mawa gidan kallo.








Plat ne me kyau sosai Rasheed akwai son qyale² ya qawata gidan tsaf ta tabe baki tajishi ya saqali hannun Muneefah ta sakar masa ita ya nuna mata dakunan yace gasunan keda yaranki duka sun isheku fatan nasara" dakinsa ya shige da Muneefah tabisa da kallon takaici ta gyada kai ta bude dakin kusa da ita ta shiga komai na dakin a tsare yake sosai abin gwanin birgewa gefe ga wasu manyan set na akwatuna guda 12 ta zubawa akwatunan idanu tana tunanin to na meyene?" Tabe baki tayi tace “nima dai da son wahalar da kaina kulle dakin tayi ta cire kayanta ta bude akwatun da ta taho da ita ta dauko wata qaramar riga Mara hannu ta shafanta turaruka ta nufi bayi tayi wanka ta fito ta shafa mai ta zura rigarta ta haye gado taja duvet tunda ba sallah zatayi ba nan take baccin gajiya yayi gaba da ita batasan sanda ya shigo ya kwantar mata da Muneefah ba sai wajen hudu ta farka taganta kwance ya cire mata riga daga ita sai Pampers tanata baccinta.








Yunwa ce ta fafareta ta miqe ta fito tana hamma ta nufi kitchen din taji qamshi na tashi ta qarasa da sauri ganinsa tayi dagashi sai boxes da headphones a kunnensa ya zage sai yankan alayyahu yakeyi ta juya zata tafi ashe ya ganta taji yace “kije ki huta idan na gama zan sammiki nasan cikinki ne Babu alert shiyasa kika fito
Yayi tsammanin zata kulashi yaga ta juya tayi tafiyarta ta koma dakinta yaci gaba da girkinsa Yana waqoqinsa bayan ya gama ya jera a dinning ya bude dakin ya isheta tana waya daga yanayin wayar yasan da Mom dinsa takeyi ya shafa kansa ya juya ya fice, koda ta idar bata nemesa ba har ya sake gajiya ya shigo ya tararta ta hade kai da gwiwa tanata jan zuciya ya matsa gabanta ya tsugunna yasa hannu ya dago kanta ta zame kannnata yayi mata murmushi yace “kinajin meye game dani?" Batace masa komai ba ta fara qoqarin tashi ta nufi parlourn yabi manyan bombom dinta da kallo yana lasar lips dinsa ya lumshe idonsa Yana tunano rayuwarsu ta baya da irin soyayyar da sukewa juna, zuciyarsa ce tayi baqi idanunsa ya kada yayi ja daya tuna Kuma fah irin abinda takeyi masa shine tayima Kareem shima ko?" Tuni hasken zuciyarsa ya disashe yaji wani qunci a ransa a fili da qarfi yace “Oh God meyesa hakan ta farune..........."










Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank






Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...






Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....






*Oum Hairan*
[8/28, 8:41 PM] Oum Hairan: Dafe kansa yayi ya koma ya zauna kalmar Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un tana kaiwa da komowa azuciyarsa shi kansa Yana jinjina baqin kishinsa baya iya jurewa abubuwa game da Meenah tun kafin takai haka, qwafa yayi ya miqe ya fito falon tana zaune Muneefah tana wasa ya nufi inda yarinyar take ya dauketa suka nufi dinning ya hadansu abinci yanaci Yana bata tanajan gemunsa Meenah na satar kallonsa har suka gama ya miqe suka fice ta Isa ga abincin ta diba daidai cikinta ta shige dakinta taci tasha yourghut dinta taje tayi brush ta sake kwanciya Basu suka shigo gidan ba sai Tara na dare tana kwance Muneefah ta shigo Yana biye da ita da qatuwar yar tsanarta ta fada jikinta ta miqe tana mata dariya tace “sarkin yawo kin sama abinda kikeso ko Ina kukaje"
Gwarancinta ta rinqayi ya nemi guri ya zauna batako kallai ba taci gaba da wasa da yarta shikuma Yana kallonsu ganin ba zai samu arziqin kulawa ba yasashi miqewa ya fice ya shiga dakinsa ta miqe tana murmushin mugunta ta nufi bathroom tayima yarinyar wanka tasa mata kayan bacci ta kwantar da ita ta kulle dakinta da key ta kwanta,. Ba wuyar bacci gareta ba nandanan bacci ya dauketa sai Kuma kashegari da safen ma shine ya tasheta ya shigo cikin shirinsa na tafiya office tunda ya shigo suka hada ido ta kawar dakai tare da lumshe idonta ya matsa kusa da Muneefah yayi kissing nata ya zubawa fuskar Meenah idanu yana ganin yanda take qifqifta idanu yaja fasali ya sauke bakinsa a kuncinta yace “kin tashi lfy" ajiyar zuciya ta saki wata kasala na saukar mata tace “normal" murmushi yayi yace “gud zanje office me kuke buqata"










Kada masa kai tayi ya zaro kudi a aljihunsa ya ajiye mata yace “is ok akwai ma'aikata a gidannan idan na fita zanyi musu mgn zasuzo kowa zai gabatar miki da aikinsa idan kina buqatar wani abu ko baby akwai dan aike saiki bashi" jinjina kai tayi ya sake sunkuyawa yayi kissing Muneefah ya fice tana binsa da kallo ita mamakin sanyinsa takeyi cikin kwanakin nan ta lura ya sauko sosai don ita kanta tasan da Rasheed din dane rainin hankalin da takeyi masa da tuni ya ladabtar da ita Amma yanzun ta fahimci kamar bama abun na damunsa.
Da wannan tunanin ta miqe ta shige bayi tayi wanka ta gyara jikinta ta fito tasa kayanta ta sanya dankunne ta nufi kitchen ga mamakinta a dinning ta tarar da kayan Karin kumallo ta fara budewa ko baa fada mata ba tasan aikinsa ne doya ce da taji qwai sai miyar albasa da attaruhu sai ruwan tea a flast da kayan hadi a gefe taja fasali ta zauna ta fara bawa cikinta haqqinsa taji dadin break din sosai tana Shirin tashi ma'aikatan suka shigo mace daya maza biyu suka gaisheta ta amsa musu macen tace “ranki ya dade ni sunana Jummai daga Daura Yallabai ya kawoni nan aikina shine shara da mopping da wanke² sai kula da Muneefah yace tsarin gdansa baa masa girki shine yakeyi ko Kuma ke kiyi" jinjina kai tayi dayan yace “nikuma sunana Hadi duk abinda ya shafi fita unguwa da aike zuwa waje alhakinane" juyawa tayi da dayan yace “nikuma dan ruwa ne aikina shine kula da fulawa da wanki da guga ranki ya dade sunana Badaru" yanda yayi mgnr yabata dariya tayi murmushi tace “yayi kowa yaje yayi aikinsa"










Godiya sukayi suka fita kowa ya kama aikinsa Jummai ma ta fara gyaran falon ita Kuma ta shiga dakinsa ta gyaro ta kunna masa turaruka ta fesa na fesawa ta wanke toilet ta fito ta shiga nata shima ta gyara biyun da suke rufe ne kawai bata shiga ba ta koma tayi kwanciyarta ta rashin aikinyi har daya sannan ta fito ta dora girki Jummai nayi mata hira har suka gama suka Muneefah nata wasanta tayi wanka ta shirya cikin wata atampa blue tayi mata kyau dinkin doguwar riga me aljihu tayi sallar la'asar ta kunna kallo tana kallo tana chat har biyar sannan taji tsayawar motarsa ya shigo da kaya niqi² a hannunsa Jummai ta miqe tana masa sannu da zuwa itakuwa hakimar kawar dakai ma tayi yasan tayi ne don yaji haushi yayi murmushi ya aje kayan yace “barka da gida ranki ya dade Allah ja kwana ya qara lafiya fulanin gobe" duk yanda taso da shareshi dole Saida yasa tayi murmushi tace “sannu da shigowa" cire rigarsa ta sama yayi ya rage dagashi sai singlet ya qarawa A.C gudu yace “nasha wahala yau inata qoqarin naga tafiyar nan bata ritsa dani ba Amma Saida ta fado kaina Meenah banson tafiya nabarki wlh....." Ai tuni ta fara hada gumi ta juyo da sauri tana cizge dankwali tace “tafiya Kuma Baffa'am tab wlh aa bazaa Kuma sakani a tara ba nikam qafata qafarka"










Murmushi yayi Yana kallonta a zucci yace yar iskar qarya zanyi maganinki ta ruwan sanyi ni zakiyiwa hauka! Amma a fili sai yace “to ya zanyi Meenah Babu damar tafiya da iyali Australia sunada mugun sanyi dole sai kaje kaga yanayin gurin tukunna ko zaka dauki iyalinka Kuma ma Banda abinki mu ai zaman gaba mukeyi Inna tafi dake amfanin me zakiyimin abinda bakaso ai nesa kakeyi dashi ko?" Girgiza kai tayi ta zame qasan kujerar tace “nikam mubar batun wasa wlh nasha wahala a wancan karon har zaucewa Saida nayi Saida Mom da Mai Martaba suka rinqa sawa ana yimin addu'a sannan na dawo hankalina ya Rasheed don Allah ki million nawa ne kabasu subarmin kai a gida ni idan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads