Showing 3001 words to 6000 words out of 97223 words
Chapter 2 - JUHUD BY OUM HAIRAN .txt
ankara ba har cikin Aminatu ya isa haihuwa cikin dare ciwo ya turnuketa gashi Maddibo bayanan a lkcn ya tafi Nigeria sawo wasu shanaye.
Gwaggo Lami tanajin Aminatu tanata nishin ciwo amma taqi ko leqota saida Buba ya fito fitsari yajiyo ya nufi dakin da sauri ya isheta cikin mawuyacin hali a lkcn ta gama jigata kan da ya sawo kai amma yaqi qarasa fitowa aikuwa ya ruga da gudu yaje ya taso wata dattijuwa me suna Suwai suka taho tare kafin kace wannan dakin Aminatu ya cika da mutane amma ko qeyar Gwaggo Lami Cikin ikon Allah ana kiran Assalatu aka samu Aka ciro yaron daqyar Amma Aminatu batasan wake akanta ba gashi jini yaqi tsayawa Suwai tayi iyakar qoqarinta zamani bana asibiti ba amma ina saida ubangiji yayi ikonsa Aminatu bata ko kalli fuskar danta ba Allah ya karbi rayuwarta.........
Mutuwar Aminatu ta girgiza duk wani mutum dake rayuwa a wannan ruga hakana aka tashi Manzo ya tafi Senegal ya sanarwa da iyayenta suka taso suka taho tare, tabbas Baffa Dodah ya tausayawa Moddibo matuqa da irin halin dimuwar daya riskeshi a ciki daqyar da qarfin Addu'a ya dawo daidai amma duk da haka daya kalli Jaririn da Aminatu ta tafi tabar masa sai ya kama hawaye kwana sittin da haihuwar jaririn aka rada masa Suna Haruna su Baffa Doda sunso tafiya da Haruna amma Moddibo yaqi yasa musu kuka yana roqonsu idan sun barshi zaike dauke masa kewar Aminatu.
Badon ransu naso ba suka tafi sukabar masa wannan jariri hakanan Wannan yaro yaci gaba da rayuwa tun yana tsumman goyo cikin rashin kulawa da qyara indai kinga anyiwa Haro wanka to Dattijuwa Suwai ce ta daukeshi a qarshe ma dole Maddibo barmata shi yayi itake kula dashi da komansa duk da cewa kwana Saba'in da rasuwar Aminatu Gwaggo Lami ta haihu hakan baisa taji tausayin maraici ta bawa wannan yaro nono ba watsin da tayi da wannan jariri yasa shikuma Maddibo ya dauki qaunar duniya ya dora masa komai ya samo na Haro ne Buba dake yarone me hankali kuma ya dan fara tasawa bai damuwa da wannan fifikon hasali ma tausayin Haro yakeji inda Bangel ya taso da qiyayyar haro shima Rubado daya tashi qarami da wannan aqida da uwarsu ta koya musu ya tashi Haro ba mutunne me hayaniya ba wannan tasa ko fita sukayi kiwo sai su kamashi su zaneshi da zarar sunga Buba ya kauce haka zai dawo gda yanata kuka Suwai da Moddibo suyita rarrashinsa.
Rayuwa tayita tafiya a haka har suka tasa sukakai munzalin girma Al'adarmu ta fulani yaro yana kaiwa sha takwas akeyi masa aure suyita tsalle tsallensu da matarsa har hankali ya iso musu su rungumi junansu wannan ce ta faru da Buba da Bangel buba yanada Sha tara bangel yanada Sha bakwai akayi musu aure Buba aka aura masa Jumme shikuma Bangel Asubi Jumme mace ce me kawaici da hqr itakam Asubi irin mijinta ce sai ya kasance Haro ya tare a gdan Buba komansu tare sukeyi ko shawara buba zaiyi baya shawara da yan uwansa da suke ciki daya saidai Haro saboda nutsuwarsa tasa tunanin manya yakeyi.
Rayuwar ta farayi mawa Haro dadi ya saki jiki da Jumme sosai duk abinda ya samo daga Jumme sai Suwai lkcn da shekarunsu suka kai ne aka daura masu aure Lariya itace matar da aka bawa Rubado shikuma Haro aka aura masa ni nima kamar yanda aka dauko Aminatu daga Senegal haka nima aka daukoni aka kawoni jumme ce tayi murna da zuwana ita da Suwai sune suka karbenu hannu biyu surukarmu kam ko kallo ban isheta ba mijina kuma dan'uwana dan qanwar mahaifina Haro ya qaunace ya nunamin kulawa dayake dama ba qarama sosai aka kawoni banyi wannan bambadancin da amare sukeyi ba muka zauna lafiya da mijina a hakanne Jumme ta Haihu haihuwar farko ta haifi Abdullahi wanda kuke kira da Hammah Audi shekaru biyu kuma Asubi ta haifi Rubado basa jana nima bana shiga cikinsu daga asubi har lariya Jumme ce kawai muke mutunci matuqa ana haka na samu cikina na farko nasha wahala sosai da yakai haihuwa Na haifi namiji Umaru ya fara girma sosai yakai kusan shekara uku ya kama qyanda wannan qyanda bata barshi ba saida ta tafi dashi munji mutuwar yaron sosai, bayan rasuwarsa ne harin barayin shanu ya addabi Lardin Wandu babu shiri Moddibo ya debo halwarsa muka dungumo Niger daga niger muka tsallako Nigeria muka samu matsugunni a Wannan guri da ya zama sabuwar Wandunmu"
Bamu jima da dawowa ba ciwon Ajali ya kama Moddibo ansha jinya sosai a lkcn da ajalinsa ya rigaya ne yasa aka kira masa yayansa yayi musu nasiha akan zumunci sannan ne ya ware wani kaso me yawa a cikin shanunsa yace wadannan na gadon mahaifiyarsa ne Aminatu daya rinqa kula masa dasu sune sukayi yawa haka, nanfah Bangel da Rubado suka kalli juna sukayi qwafa suka tashi suka fice daga dakin bayan fitarsu ne yake sanar dashi cewa akwai wasu shanun da ya bayar aka tafi dasu kudu kiwo da Buba da Haro ne sukaci gaba da jinyar mahaifinsu har kwana ya qare ya tafi yabar baya da qura qurar da itane kema kikazo kika tadda burbushinta.
Maitar da suke iqirari ta fara ne daga lkcn da nake haihuwa yarana suna mutuwa Asubi ce ta fara cewa wai ni nake cinye kayana saida na haifi yara takwas duk suna mutuwa sannan ne Allah ya bamu ke kika tsaya wai ashe duk yaran dana rinqa haifa maza suna mutuwa Ubayenku ne suka sanya hannu kawai saboda tunanin idan Haro ya mutu yanada da Namiji bazasu samu komai ba kedin ma sunso hallakaki Allah yaqi basu dama kika rayu da tsangwamarsu saboda kyawun da ubangiji yayi miki tun kina qanqanuwa dumurmur dake kamar kazar gidan gona saurin girmanki yafi komai bawa mutane mamaki Hasiya da Adama da Baraka duk sa'anninki ne amma duk kinfisu girma ko tallan nono muka tafi kafin akulasu an kulaki sau dari wannan tasa uwayensu sukejin hasaadar hakan akwai wani furuci da Gwaggo Lami tayi kafin mutuwarta watarana mun dawo daga tallen Nono wani Alhajin birni yabaki kyautar Yar dolin wasa (yar tsana) kinzo gda kuka fara fada da yan uwanki akanta har kika fasawa Baraka baki, ina daki ta kamaki ta zaneki sannan tace indai su baraka jininta ne to saita lalataki sai kinyi abin kunya a rayuwarki ko tana raye ko bata raye, badai kyaune yasa kowa yake nannan dake ba to kyawun saiya zame miki fitinar da zata addabi rayuwarki.............
*THIS BOOK IS NOT FREE... REGULAR GROUP 300 VIP 600 VIA BANK ACCOUNT 0255526235 FAUZIYYA TASIU UMAR GTBANK OR CARD FOR THIS NUMBER 09013718241 ONLY WHATSAPP OR VTU ONLY FOR DIS 09031307566*
*Shares Please*
*Oum Hairan*
[7/12, 9:44 PM] Oum Hairan: *JUHUD*
*(OUM HAIRAN)*
*( Pure love sex nd romantic)*
*FP THREE*
*SUBSCRIBE*
_DUNIYAR LITTAFAN HAUSA TV_
https://www.youtube.com/channel/UCcAjVQ74qod9_dL0e_AqkiQ
*TUNATARWA*
Kowa yakanyi maka jaje a lkcn da wani abunqi ya same idan abin farin ciki ya sameka qalilanne sukeyi maka dariya har zuci, kada kasa dariyar mutane a ranka harta rudeka kaji cewa kowa sonka yake masoyin gaskiya shine wanda yake tare dakai a kowanne irin yanayi farin ciki ko akasinsa.🤏🏼
*CIGABA*
Inajin ciwon abinda Gwaggo Lami take fada akanki amma ban isa nayi magana ba abu daya na sani shine inayi miki addu'a ki kasance ya ta gari abar Alfaharin iyaye, kwanci tashi girma ya fara zuwar miki komanki abin mamaki ne gabbanki sunada saurin nuna girma hakan yasa tun kina qarama na sabar miki da saka hijjab irin na kanawa, sosai kike ganin tsangwama qyama cikin Yan'uwanki Hasiya Adama da Baraka Amma baki damuwa kodan kin taso kinganmu a cikin wannan qangin ne oho.
Wata rana Naje tallan Nono birni na dawo na tarar dake kina kuka na shige daki kika biyoni nake tambayarki meye yake faruwa sai kike fadamin Asubi ce ta bugeki saboda kunyi fada da Baraka tace miki kilakin birni kin bugeta hakanan na hqr bance komai ba ashe mgnr nan har gurin iyayenku maza taje da dare Baffanki yazo yake tuhuma ta wai waye yake zuwa yake siyan nono a gurina a sulluwa (mota) daga birni?"
Dagowa nayi na dubesa nace yaron Alh Idi ne da ka hadamu dashi a kasuwa yake zuwa karbar masa nono" numfashi Baffanki ya sauke ya kira sunana na amsa yace “shin Indo kinasa ido akan Aminatu kuwa?" Sake ware injin idona nayi akansa nace “Wai mekake tunanine Haro nikam bangane inda zantukanka suka dosa ba" sake gyara zamansa yayi ya dafe kansa yace “dazu na dawo daga kiwo na Ishe Ribado da Bangel suna tattaunawa naqarasa domin mu gaisa shine suke cemin wai dazun sunga wani me Sulluwa yazo ya dauki Aminatu a mota sunyi hanyar birni" dafe qirji nayi cikin kidima da gigita nace “aa Haro wlh zancene Juhud yau babu inda taje tallanma nice na fita saboda tacemin batajin dadi" jinjina kai yayi yace “shikenan adai qara kulawa" ashe wasan baa fara ba.
Tun daga wannan lkcn suka dora mamu qahon zuqa babu dama mutum yazo siyan nono gurinmu sai suce iskanci yazo ba keba nima a haka nake a gurinsu duk da cewa Baffanki baya bawa abin muhimmanci, tsaka da haka Hammanku Manga ya dawo daga neman kudi yaganki ya nuna yana sonki da murna baffanku yazo min da mgnr domin a lkcn duk anyiwa su baraka aure saura ke kadai kin rasa ko matayi a rugarmu dama maqota saboda sharrin maitar da suka liqa mana.
Duk da zuciyata bataso ba amma banja ba saboda bansan raayinki ba hakanan baffanki ya nemoki ya tambayeki game da Manga domin shi yace ma kun gama daidaitawa nan kikayi tsalle kikace bakiso naso na matsanki ki karbeshi amma sai baffanki yace tunda bakiso babu meyi miki dole ko bayan ransa hakanan naja bakina na tsuke babu kunya yaje yace da yan'uwansa kince bakison Manga nan suka qara sanya masa tsura ashe dama asali ba manga ne yace yanasonki ba sune suka kitsa masa ya aureki sai susan yanda zasuyi su hallaka babanki su kwashe dukiyarki,
Abu kamar wasa gaba me tsanani ta shiga tsakaninsu ko gaisawa basayi watarana da dare har mun kwanta Bangel yazo yayi sallama da Baffanki ya tashi ya fita bansan me suka tattauna ba nidai naga ya dawo yana huci na tambayesa yake cemin Aishatu don Allah ko bayan raina karki yarda ban aminta Aminatu ta auri Manga ba na haramta hakan idan har hakan ta faru bazanyi farin ciki ba" jikina yayi sanyi ya kwanta ranar kwana yayi yana juyi yana hawaye idan na tambayeshi sai yacemin shidai bai aminta Aminatu ta Auri Manga ba a lkcn inata fama da rashin lfy mukaje gun me magani yace cikine dani amma ya kwanta.
Ban wani damu ba duk da cewa Baffanki kullum cikin kawomin magani yake hakan baisa cikin nan ya tashi ba wata biyu tsakani sukayi wani gagarumin rikici daya sanya suka qara kullatar juna ashe a wannan dare sukayi taro suka yanke shawarar tunda yaqi basu hadin kai kawai su kasheshi su huta mana inyaso sai manga ya kada shanun yayi kudu dasu kinga zaace barayin shanh ne suka kasheshi.
Maddibo Buba ne yaji wannan shirin nasu a daren kuwa ya kira Haro ya sanar dashi abinda yan'uwansa suke shiryawa yaja fasali tare da murmushi yace “babu komai Allah yafi kowa sanin abindake qarqashin qasa dana ban qasa yafi kowa sanin daidai" daya dawo bai sanar dani ba nidai naga ya tashi cikin dare ya dauko wata qaramar adaka ya bude ya zaro wasu abubuwa masu walwali yabani yacemin Aishatu wannan abin da kike gani ba komai bane face dutsen Lu'ulu'u wanda yan birni suke cewa diamond wannan kuma gwal ne nasan kinsanshi don Allah ki nemi guri kiyi musu mugun boyo asalinsu na Mahaifiyata ne Aminatu naketa ajiyarsu domin Aminatu kada kibari wani yasan dasu a hannunki sunfi shanun can da kike gani garke guda daraja domin kuwa yanzu a duniyar mutanenmu wane da wane ma ba kowane yake iya mallakar diamond ba koda bayan raina zasu qwace komai ya kasance Aminatu ta tsira da wadannan abubuwan"
Na dade ina tunani kafin na tashi na haqa rami a qarqashin gadona na zubasu a ciki insha Allahu a yau zan baki abinki ki daura a qugunki su zame miki jigida iya wuya kada ki bari su kubce miki kinji" jinjina kai tayi Innatu taci gaba da cewa “washegari da safe na damawa Baffanki fura yasha ya kada shanu ya tafi kiwo nikuma na dauki nono na shiga gari acan suka cim masa da rana lkcn kin tafi kaimasa hura suka sareshi akansa da qirjinsa ya fadi jini nata malala kince kinga shanunsa lkcn da aka kadasu akayi hayi dasu amma bakiga wanda ya kada dinba kina binsu har kika ishe inda Gawar mahaifinki take yashe a qasa kece kika dawo kika fadawa Maddibo cewa an sari Baffanki kuka dunguma kuka koma nidai bayan na dawo na ishe wannan mugun labari shine tunda na yanke jiki na fadi bantashi ba nake zaune a wannan halin tsayin shekara biyu kwatsam sai cikina ya fara motsi nasa kika kiramin Jumme na sanar da ita dake tasan da batun kwanciyar cikin ta sanarwa da Maddibo Shi kadai yayi murna ya rinqa karbomin magani ashe a gefe Bangel da Rubado zargina sukeyi da Buba wai yana shigowa dakina ya dade hakanan sukaje suka kitsawa Jumme tazo har dakin nan tayimin tatas ina zaune babu halin magana a cewarsu ma wai wannan cikin na jikina ba na Haro bane na Buba ne Juhud Allah daya tsakanina da buba daga sannu sai idan ya kawomin magani ko nonon da zaki fita dashi talle.
A haka muke rayuwa har kawo yanzu da komai ya qara lalacewa Juhud kullum mutanen nan basu fadin alkhairi garemu kullum cikin yi mana kalen sharri suke yanzu haka kwanaki uku da suka wucce Jafaru makiyayi ya dawo daga kudu ya kawo shanaye guda dari da ashirin yace na Baffanki ne to tun jiya sukebin kaina akan na yarda a daura aurenki da Manga nikuma gashi Baffanki yabarmin wasicin ko bayan ransa bai aminta a hadaki aure da Manga ba a yau bayan kin fita diban ruwa har barazana sukayi min da rayuwata Juhud bandamu ba indai akan burin Haro ne su kashenin ma kansu sukayiwa.
*ASALIN LABARI*
Jikin Juhud ne ya qara sanyi hawaye na sunturi a kucinta tace “yanzun wadannan sune kadai dalilan da suka sanya Suka kashemin Baffina Amma aka kasa daukar mataki akansu Innatu wannan wacce irin Al'umma muke ciki meson kanta? Shafa nadaddiyar sumarta tayi itama cikin hawaye tace “haka rayuwa ta zama kina gani fah tunda Baffanki ya rasu ko nono sun hanamu tatsa saidai su tatse subawa matansu suje su siyar idan kinga mun samu nono a rugarnan to Moddibo ne ya tatso mana Juhud ya zakayi ne da qaddararka ni yanzu burina a duniya naga kinyi aure kin samu matsugunni saboda wannan rayuwar bata yuwuwa a haka"
Fadawa tayi jikin Innatu tana kuka me cin zuciya itakam da Innatu zata amince da sun bar rugar nan tunda baa sonsu amma tasan bazata aminta ba, da wannan tunanin bacci barawo ya saceta.
Washegari da wuri ta dauki tallan nononta ta tafi tasha cike da doki yau tayi niyyar idan tayo ciniki har Balangu zata sawowa innatu ko tsiren quli tana tafe tana yan waqoqinta harta isa gari koda taje yan nonon gurin ya cika batada guri dole ta koma gefe ta rakuye tana wasanninta na quruciya dagowar da zatayi taga wani baqin hadari ya gangamo tana juyawa taga Fulanin duk suna hade karensu gashu batayi cinikin kirki ba donma ta datsa yariman ne ta dibarwa wani na dari biyu shiyasa da haka zata koma.
Ganin hadarin na gangamowa yasata miqewa jikinta a salube tana juya dari biyun ta gama kasaftata tasai mawa Innatu maganin ciwon jikin hamsin tasai mata balangun dari ta riqe hamsin a hannunta ko batirin fitila sa siya, daukar qoranta tayi ta aza aka ta juya kenan zata tafi taji wata mota tayi horn a bayanta ta juya taga me motar ya zuge glass wani matashin saurayi ne me qwarjinin gaske fuskarsa a daure ya bude bakinsa kamar wanda akayiwa dole yace “na nawa ne?" Cikin fullanci yayi mgnr tayi saurin Amsawa da cewa na dubu Uku ba dari biyu" dubanta yayi yace “harke?" Kallonss tayi da rashin fahimta ya daganta gira yace “inaso ki juyemin da sauri" daidai lkcn taji gabanta ya yanke yabads wani dam ta dafe qirji da sauri tana waige² yace “ko bakiji ne?" Da qaraji yayi mgnr taja numfashi ta miqa masa har qoran tace banida ledar da zata dauka duka kaje da qoran ka dawo mani dasu wataran" karba yayi yasa a bayan motar ya zaro dubu biyar ya bata yace “gashinan har kudin qoranki bana shigowa garinnan sai idan wani babban uzuri ya taso" karba tayi tayi godiya ta juya da sauri ga mamakinsa kawai yaga ta take a guje ya saki baki yana kallonta a fili yace “lkc guda nutsuwarta ta gushe ko meye yaja hakan?" Tabe baki yayi ya daki kansa yace “kaima Cornel Rasheed da shiga abinda babu ruwanka kake" cikin kasuwar ya shiga yayi siyyayarsa ya juya da motarsa yabi wata siririyar hanya.
Itakuwa koda ta kwasa a guje duk nisa dake tsakaninta da rugarsu haka ra rinqa cin gudu harta fara hango rugar tasu nesa sosai gabanta ya qara yankewa ya fadi ganin wani baqin hayaqi yana tashi ta sashin da bukkarsu take, da sassarfa ta nufi gurin kawai taji an wafci hanunta da qarfi dagowar da zatayi taga Moddibo Buba ne idanunsa sharkaf da hawaye yana janta yana kallon bukkar tasu dakeci da wuta,
Da qarfin gaske ta turje cikin fitar hayyaci tace “Innatuuuu!" Saurin rufe mata baki yayi yaci gaba da janta bai qyaleta ba saida yabar sashin rugar da ita ya tsaya jikin wata itaciya yana sharce hawaye ya dubeta yace “Haka Allah yake ikonsa Aminatu a wannan qarnin babu wani abu dazan iyayi miki face na saki a hanya kibar yankin nan gabadaya Su Bangel basu da Imani Ina zargin sune suka sanyawa dakin Indo wuta suka qoneta ina daji Audi yaje yake fadamin har yana cemin yanzu Hakama Ribadu da Manga