Showing 33001 words to 36000 words out of 46793 words
Chapter 12 - DINYAR MAKAHO Book 1 Complete Document by Ummu Maheer Miss Green txt
dawo kenan?to meye na sanɗar ai gwara ki shigo kanki tsaye tunda an dawo daga yawon asiri,ai dole ayi sanɗa indai mugun abune ai kanki zai ƙare don ni dai kinsan na fi ƙarfinki".
Da sauri Inna Saude ta ce"haba Hafsatu kiyi a hankali mana?kada munafukai su jiyo mu".?
Ɗan murmushi Inna Hafsatu ta yi sannan ta ce"to me yasa da zaki je bamu je tare ba?kika ɗebi ƙafa sassafiya kika fita?ai kya neme ni muje ko?indai har abin ba munafurci bane ba"?.
Babu abinda Saude ta ɓoyewa Hafsatu dangane da tafiyarta sannan ta ƙara da ce wa"kai Hafsatu gaskiya mutanen nan shegune,gasu ƙarfaffu dasu kamar goyon gidan Zoo,ji bi fuskata yadda wata tsinanniya ta ya ƙushemin ita?".
Ta faɗi hakan tana nunawa Inna Hafsatu.
Sosai Inna Hafsatu ke dariya harda riƙe ciki,sai da tayi me isarta sannan ta ce"oh ni ƴa su muga ciwon?".
Da sauri Saude ta yi baya tana ce wa"anƙi a nuna miki ɗin,banza muguwa kawai tsabar wulaƙanci ina faɗa miki magana kina dariya?a'i kamata ya yu ki tausayamin ko?amman da yake ke agidanku rashin tausayi ya ƙare shine zaki hau dariya ɗiyar bare bari kawai".
Sosai abin ya zamar musu faɗa,don ƙarshe ma Inna Saude itace ta haƙura ta shiga ɗaki,don da yake ƴaƴan Inna Hafsatu duk suna gida sai sukaso shigarwa mahaifiyarsu,don ita ƴaƴan Inna Saude yadda take da yawon jaraba to suma haka suke,don basa zama agida kulli yaumin suna cen wajen yawo.
Ƴaƴan Inna Saude uku ne agidan miji,sai ɗanta babba yanzu wanda ke shirin aure,sai ƴammata har uku waɗanda dukkansu sukayi girma sosai amman babu mijin aure.
Sai ƴaƴan Inna Hafsatu guda biyu da ta aurar,sai ƴammata biyu dake gabanta don ita ba tada ƴaƴa maza duk ƴaƴanta mata ne.
*GIDAN SARAUTA POV*
. . . . . . . .kai tsaye Magajiya ɓangaren Fulanin Bare ta wuce,wato mahaifiyar Yarima Yazeed sashenta bai fiya hayaniya ba,don itama ba mutum ce me hayaniya ba,a hankali take tafiya cikin sanɗa sanɗa har Allah ya bata damar buɗe ɗakin Fulani a hankali.
Allah ya bata sa'a Fulani na ɓanɗaki,don haka bata san wanda ya shigo ba,a hankali ta ɗaga wata ƙwalba aɗakin ta ajje ta yadda ba lallai ka hango abinda ke ƙasan ba,cikin sanɗa sanɗa ta fara fitowa har ta rufo babu wanda ya ganta kai tsaye ta koma sashen Fulanin Suura.
Fulanin Suura ta ce"ai wallahi tallahi tunda tace ita sharri za ta dinga yimin to tayi ta banzar,don wallahi ni bazan barta ba idan ta samu wasu na ƙyaleta."
Magajiya ta sunkuyar da kanta tana ƴar dariya sannan ta ce"Ranki ya daɗe daman aike ce kike barinta,amman da Kilishi da Fulanin Usul ai basu kyaleta,to kinga ai su sun zauna lafiya ko?to don haka kema yanzu ki saka ɗanba da ita,kada ki yarda ta dinga mulkarki wai don ku baku da ƴaƴa maza,idan ba haka ba wallahi wataran ma sai tayi yunƙurin mayar daku bayinta".
Cikin tsawa Fulanin Suura ta ce"Ke!Magajiya ni za'a mayar baiwa?to wallahi tallahi idan ma mafarki kike to kiyi maza ki farka,don ni nafi ƙarfin wata mace balle wannan nunar ranar".
Shiru Magajiya tayi tana ƴar dariya ƙasa ƙasa yadda Fulanin Suura baza taji ba,sannan ta ce"Ranki ya daɗe a gafar tamin suɓutul kalam na yi".
Fulanin Suura ta ce"ato gwara dai ki gyara zancenki don kamar yadda ta gaji Sarauta to nima haka na gaje ta."
Magajiya a zuciyarta ta ce"wannan sarautar taki ta banza da wofi,Sarautar fa iya ta yarensu ce fa?ita kuwa Sarauniya Xulaiha mahaifinta Sarkin ƙasar Masar ne fa baki ɗaya masu matuƙar kuɗi da kuma Daula".
Magajiya na ta tunaninta ashe Fulani Suura na mata magana bata ji ba,sai da ta ƙara.maimaita maganarta wajen ce wa"Ke Magajiya dake fa nake?tashi ki tafi baƙi zanyi don ni yadda kika saba zamarwa su Kilishi ni baza ki zaunar min ba,don ni har yanzu ban yarda dake ba"?.
Sosai ran Magajiya ya sosu amman bata ce komai ba,da sauri ta fice tana ƴam surutanta.
ɓangaren Kilishi ta yi tana zuwa ta same ta a falo bayi na zagaye da i'ta wasu na yi mata tausa wasu kuma suna ɓare mata kayan marmari.
Kilishi na ganin Magajiya ta bawa bayinta damar tashi daga wajen,suna fita ta dawo da hankalinta kan Magajiya.
Tun kafin Magajiya ta yi magana ta ce"dakata Magajiya ba sai kinyi magana ba,nasan komai ya tafi dai dai don haka yanxu ba sai anjima ba zan baki kamashonki".
Tana faɗar hakan ta fiddo da kuɗi ƴan rafas masu yawa ta miƙo mata sannan ta ce"yauwa ga wannan kuɗin nan sai kici gaba da tarawa uwar tarin kuɗi".ta faɗi hakan tana hararar Magajiya.
Don ita Magajiya duk wani kuɗi da za'a bata to fa bata kashewa ajjewa take,wai dai ranar aurenta ta fito dasu tayi hidima gashi kuma har yanzu auren ya gagara.
Magajiya ta yi murmushi sannan ta ce"Uwar gijiya ta A'i dole ne kiga ina ajje kuɗi,babu abinda nake buƙatar gani sai ranar aure na ilahi ya nuna min wannan ranar".
Kilishi ta kalleta sannan ta ce"to tashi ki tafi zanyi ɗan wani tunani ne".
Da sauri Magajiya ta fice don tasan halin Kilishi,idan tace bata son abu to tabbas ɗin bata so ɗin.
Tana fita ta tashi kai tsaye ta fita wajen Sarki Abdussalam duk da ranar ba ita ce dashi ba,amman haka ta daure ta wuce kai tsaye ɗakin ta shiga abinta ba tare da ta nemi iso ba.
Tana shiga ta tarar da Sarauniya Zulaihat wato Fulanin Bare.
Ko kallon inda take bata yi ba ta zauna tana kallon mijin na su sannan ta ce.
"Ranka ya daɗe Sarki Uban sarakai,Allah ya ƙara maka nisan ƙwana ya ƙara maka ƙarfin gani da kuma kula damu yadda ya kamata".
Ɗan murmusawa ya yi sannan ya ce"barka dai Kilishi an iso lafiya"?.
Sai da ta harari Fulanin Bare sannan ta ce"lafiya ƙlau Me martaba Allah ya ƙara nisan ƙwana".
Kallonta ya yi sannan ya ce"To ya akayi ne Kilishi".?
Ya yi hakanne don baya son abinda zai janyo wata husuma saboda yau ba ranar ƙwanan ta bane,ranar ƙwanan Sarauniyar zuciyarsa ne wato Sarauniya Zulaiha ƴar Larabawan Masar.
Bata ji daɗin gutsire mata hirar da ya yi ba,amman duk da haka tasan za ta samu wani karsashin.
Sai kuwa ta ce"daman Ranka ya daɗe akan ɓatan Taswirar dukiyoyinka ne?amman ka gafarce ni akan maganar da zan faɗa maka."
Ɗan murmusawa ya yi da kyakkyawar farar fuskarsa sannan ya ce"ina jin ki Uwar gida".?
"Yauwa daman ni a tawa shawarar me zai hana a bincika gidan nan dukansa,ciki kuwa har da ɗakunanmu mu matayenka saboda kasan wannan rayuwar,kuma ni abinda nake gani wane zai shiga har har fadarka ya ɗauki wannan abin,matuƙar ba wani na jikinka sosai ba?ni dai a duba maganar nan tawa sai a saka Jakudunmu su duba dukkanin Ɓangarorinmu dama wasu sashen."
Shiru ya ɗanyi sannan ya ɗago ya ce"eh kin kawo shawara amman zanyi tunani kan hajan insha Allah".
Sosai ranta ya sosu amman bata nuna ba,don shi Sarki ba a masa musu ko jayayya don duk yadda kake dashi baka isa ba.
Haka ta tashi jikinta duk babu ƙwari tana hararar Fulanin Bare,ta yi kyau sosai cikin wata alkyabbatar me ɗaukar hankali ga jikinta ya yi wani irin mugun fresh sai walƙiya ya ke.don daman Fulanin Bare hatta gyaran jiki duk wata ake zuwa ayi mata da kuma tsumin turaruka.
*********
*Yarima Yazeed*
. . . . . . .ƙwanansu biyu suka baro su Muhammad da tarin kewarsu,don wannan ɗan ziyarar daya kai musu sunji daɗinta sosai,kuma sun ƙara shaƙuwa sosai sai dai sam basa shiri da Fareeda don sam jininsu bai haɗu ba,wani lokacin ma Shi da kansa Yazeed ɗin ke musu magana akan yadda sukewa Fareeda amman abin na damunsu don suna jin haushin lalata rayuwar ɗan uwansu da ta farayi,duk da daman su sun san kansu kuma sun san me suke aikatawa sai dai kullum suna roƙar Allah yasa koda basu daina abinda suke ba to su rage wani.
Suna dawowa ya kalli Fareeda ya miƙa mata mukullin ɗakin dake kusa dashi ya ce.
"Fareeda amshi wannan mukullin,wannan shine ɗakinki aƙwai komai na buƙata acikin gidan nan,ni kuma daga yau zan koma wancen plat ɗin,zan dinga shigowa ina duba ki amman ki kula da kanki".
Yana faɗar hakan ya fara buɗe ɗakinsa,don aƙwai hanya da zata sada shi da ɗaya plat ɗin,computer ɗinsa kawai zai ɗauka don ɗaya sashen ma aƙwai kayansa aciki,don tun kafin su dawo ya saka aka ƙwashesu tsaf.
Da sauri Fareeda ta ɗan riƙe lallausan hannunsa wanda ke tafiya da ita tare da ƙwantaccen gashi wanda ya ƙwanta luf luf.
Wani irin kallo Yaxeed ya yi mata,sai da ta haɗiye wani irin yawu me tsayawa arai,sannan cikin tsoro ta ce"yi haƙuri Prince Insha Allah bazan sake ba,amman don Allah inason muyi wata magana da kai,wallahi nima duk abinda ya faru a baya na tuba na bi Allah da kuma Manzonsa,haƙiƙa ina cikin damuwa Prince wallahi na rasa wanda zan gayawa,ayanzu ba nida wanda ya fika Prince kai ne uwata kuma kai ne ubana,Iyaye sunce sun yafewa duniya ni tunda har na musulunta ba tare dana faɗa musu ba,sun kore ni har abadan Prince bani da kowa yanzu idan ba kai ba".
Tana faɗar hakan ta fashe da wani irin kuka me mugun ƙarfi.
Ta tsugunna a ƙasa tana kuka me taɓa zuciyar duk wani me sauraro.
Duk da yana da muguwar dakiya amman kukan Fareeda ya taɓa zuciyarsa,sam baya son yaji mace na kuka arayuwarsa sai yaji duk wata nutsuwarsa ta gushe.
Cikin Muryarsa me amsa amo tamkar namijin zaki ya ce"ok tashi ki zauna".
Zama tayi akan lallausar kujerar da ke falon,shima ya samu waje cikin ɗaya daga cikin kujerun sannan ya ɗan kalli gefe,muskilanci ya motsa sannan ya ce.
"Fareeda tabbas kina cikin wani hali,don iyaye sune komai arayuwar ɗansu,kuma suna taka gudummawa me ƙarfin gaske arayuwar ƴaƴansu,nasan irin ƙunar da kike ji amman zanso kisan wani abu guda ɗaya,ki kasance me yarda da ƙaddara ita ƙaddara babu ɗan adam ɗin da bata raɓa,amman ki kasance me miƙa lamuranki ga ubangiji shine ya ɗora miki kuma shine zai ya ye miki ita,sannan daga ƙarshe insha Allah a satin nan zan samo miki aiki,sannan zan samo miki ƴar aiki mace ko zata dinga ɗebe miki kewa."
Shiru kawai tayi don har yanxu bata ji maganar daya kamata Prince ɗinta ya faɗa ba.
Tana masifar son Prince tun bata kai haka ba,bata san me yasa yake wulaƙanta ta ba?gashi ita kuma Allah ya ɗora mata mugun sonshi ta yadda baza ta iya rabuwa dashi ba,rabata dashi kuwa dai dai yake da rabuwa da numfashinta,a shekaru zasu kusan zuwa ɗaya da Prince,koma ta girmesa don Yaxeed yaro ne sosai,sai dai Allah ya yi masa ƙira da zubi tamkar shine ya ƙera kansa,ga baiwa ta iya magana da kuma kalami.da ace ita me son nasiha ce to da tuni Yaxeed ya zama malaminta,sai dai ita yanzu duk wata nasiha da zai yi mata gani take tamkar sarewa yake mata acikin kunnuwanta,abu ɗaya takeson ji shine bai wuce Prince ya furta mata kalmar so ba,tana sonshi sosai har bata san adadin son da take yi masa ba.
Yana gama faɗar hakan ya tashi tsaye,sannan ya ce"idan aƙwai abinda kike buƙata ki faɗamin don ni yanzu idan na fita daga nan zaki ƙwana biyu baki ganni ba,don ina da aiki sosai dana bari ba tare dana ƙarasa ba."
Shiru ta yi wasu hawaye na zuba daga idanuwanta sannan ta ce"ba komai".
Tana faɗar hakan ta tashi ta buɗe ɗakin ta shige da gudu ta faɗa kan gadon ɗakin wanda yasha lallausar katifa,da kuma lallusan zanin gado ta fasa wani ihu me ƙarfi.
Tana barin waje Yaxeed ya kalleta sosai,sam baya son yaga wani yana cikin baƙin ciki musamman ma idan a ƙarƙashinsa yake sai yaga tamkar yana zaluntar mutum ne,ɗaga kafaɗarsa ya yi ya wuce sashensa yana ɗan tunanin aikin da ya bari.
Yana fitowa ya danna wayarsa ya bada umarnin a kawo masa coffie,Fareeda kuma a kai mata abinci ya faɗi abincin da Fareedan ke so.
Bayan an kaiwa Fareed abinci shima aka kawo masa coffie ɗin,sai dai abinda cook ɗin ya faɗa shine wai Fareeda ta cillo masa abincin wai tace baza taci ba.
Yaxeed ya ɗan kalli mutumin yaga yadda Fareeda ta ɓata masa jikinsa,sosai ransa ya ɓaci don haka ya bashi haƙuri mutumin ya fita.
Tun daga ranar ya bada umarnin kada a ƙara kai mata abinci idan yunwa ta isheta da kanta za ta fito taci don haka ma a kyaleta.
Ai kuwa Fareeda ta gasu sosai,don da kanta ta fito tana sanɗa ta shige kitchen ɗin.
Yaxeed yana kallonta ranar yana aiki a falon da computer ɗinsa.
Ɗan murmushi ya yi don shi bai fiya yin dariya ba,ya cigaba da aikinsa kawai yana tunanin kirawo mahaifiyarsa.
Waya ya ɗaga ya kira ta,ya lumshe idanuwansa bayan yaji muryarta,ya gaisheta cikin girmamawa sannan ya shiga zuba mata shagwaɓa.
Fareeda kuwa bayan ta haɗo kayan snacks wanda ta gani cikin fridge sai taga Prince ɗinta zaune ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yaba waya tare da shagwaɓa.
Sosai abin ya bata mamaki,tare da tsayawar wani malulu acikin zuciyarta.
Wato shi Prince sai ya ɓatawa mutum rai sannan kuma yazo yana wani shagwamewa a waya?shi ko iya rarrashin ma mutum baiyi ba.haushi ya kamata zata wuce ɗaki sai dai sam baza ta iya hakan ba,don zuciyarta wani irin lugude take mata na masifar son Prince,ga wani irin kishi daya lulluɓe mata zuciya don yadda taga yana waya yana shagwaɓewa aƙwai ayar tambaya,sai da ita iya zamanta da Yaxeed bata taɓa ganinsa sa wata ɗiya mace ba wai ta fuskar so,sai dai ta wani abun wanda ayanzu tana ganin kamar ya daina duk da tana ganin ta hanyarta ne ya fara abinda yake aikatawa,wanda ba kowa ne ya san da hakan ba don ita kaɗai tasan Prince ɗinta.
ya daɗe sosai yana waya da mahaifiyarsa,har sun gama sai kuma yaga ta ƙara bugowa ya ɗaga ba tare daya ce komai ba.
Fulanin Bare taja numfashi sannan ta ce"to ɗan gado wato miskilancin ne ya motsa ko?".
Ɗan murmusawa ya yi sannan ya ce"Ammi na na gaji ne sosai shiyasa".
Fulanin Bare ta ce"to ɗan hutu na manta ban faɗa maka ba,Ƙannenka Twins Afra da Afreen zasu zo maka hutu daga America,kasan sunyi graduate to nayi nayi dasu akan su dawo gida sunƙi,wai suj daɗe basu ganka ba suna son zuwa".
Ɗan murmusawa ya yi yana ɗan shafa gemunsa ya ce"Ammi ni fa kin san banason hayaniya kada suxo fa suyi ta sakani magana".?
"Haba Baba na bazasu sakaka magana ba,ai yanxu sunyi hankali ba kamar da ba".
tashi ya yi yana haɗa kayansa waɗanda ke wajen,wayar kuma na kunnensa Da sauri Fareeda ta taho tana taya sa ƙwashe kayan bai hana ta ba,har ta.kai ɗakinsa ta dawo tana zama shi kuma ya wuce ya yi ɗakinsa.
Sakin baki Fareeda ta yi tana mamakin irin halin Yaxeed,sam babu ruwanshi da damuwar wani,damuwarsa ma bata cika damunsa ba balle ya janyowa kansa hawan jini.
Sosai ta ƙulu,ta koma ɗakinta ta ɗauki wayarta ta kirawo ƙawarta Sanjana".
ƙawarta ce ƴar asalin India itama tana nan kusa dasu wani gari Le mains,don bayan iyayenta sun kore ta cen Le mains ɗin taje,sai dai sam hankalinta ya kasa ƙwanciya tafi son ta ji ta kusa da Prince ɗinta,sai gashi Prince ɗin na ta yana ƙoƙarin zuba mata ƙasa a ido.
Tana ɗagawa suka gaisa har tana tsokanarta wai Fareeda ta Yaxeed prince.
Mai makon ko da yaushe yadda take jin daɗi,sai aka samu akasin haka don kuka ta fashewa da Sanjana kuka tana yin kukanta iya iyawarta.
Sosai hankalin aminiyar tata ya tashi ta ce"a'ah Fareeda lafiya kuwa?ko wani abinne ya faru da Prince ɗin"?.
Kasa magana tayi ta cigaba da kukanta,Sanjana tayi zuciya zata kashe wayar sai ta ce"don Allah ki yi haƙuri kada ki kashe,zan faɗa miki abinda ke damuna Wallahi tunda na dawo Prince ya juyamin baya,kin san fa tunda ya dawo gani ya ke kamar ni ce na lalata masa rayuwarsa,ya ƙi kallona da idanunsa sam dana mats masa don muyi hira nasiha ya hau ni da ita."
Dariya sosai Sanjana ke yi sannan ta ce"Hmm ai ni Fareeda kina bani mamaki wallahi?ta yaya za'ace namiji ya yi ta juyaki kamar wata wai na?mazan turawa na binki amman kina wulaƙantasu?meye basu dashi?idan ma kuɗi ne aƙwai waɗanda suka fishi amman ke kin dagr sai wannan ɗan rainin hankalin kawai don yana da ky.. . . . . . . . .."
Da sauri Fareeda ta tsayar da ita wajen ce wa"da kata Sanjana bana son irin wannan kalamin kan Prince ɗina,ki kiyayi bakinki don Prince ɗina ya fi ƙarfinki,kuma da kike wannan maganar an gaya miki prince ɗaya yake da sauran maza?balle wasu turawa?to bari kiji yana da Qualities me mugun ƙarfi wanda ni akansa zan iya rabuwa da kowa ciki kuwa har dake".
Sosai ran Sanjana ya ɓaci cikin fushi ta ce"Hmm Fareeda kenan?kina bani mamaki sosai tun muna ƙanana muke tare dake amman duk a banza sai daga bayz kika samu Prince ɗin amman shine kike wulaƙantani ko?babu komai daga yanzu na barki da Prince ɗin, don haka kada ki ƙara nema na awaya ko a hanya kada ki yarda ki nuna kin sanni".
Tana faɗar hakan ƙit ta kashe wayarta.
Sosai hankalin Fareeda ya tashi,don tasan aduk ƙawayenta babu kamar Sanjana,sau tari awasu lokutan idan ta shiga wata matsalar ita ce ke solving ɗin matsalar,amman yanzu gashi sun ɓata ya zama dole taje har Le mains don ta rarrashe ta. . . ... . . ✍🏿
Miss green ce🫵🏾
07068606171
*Bazan ga ƙaunar da kuke nunamin ba,har sai kun taya ni da share da kuma comments me ratsa zuciya,ina alfahari da masoyana aduk inda kuke.*
Masu yimin copy na littafi,kuna ɗorawa amadadin ku kukayi,babu komai bazanyi Allah ya ida ba,sai dai in gode muku don na san duk cikin love ne,amman aji tsoron Allah🙏🏼🙏🏼🙏🏼.
_Ummu Maheer_
*DINYAR