Showing 15001 words to 18000 words out of 46793 words
Chapter 6 - DINYAR MAKAHO Book 1 Complete Document by Ummu Maheer Miss Green txt
da sari.
Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?
"Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.
08179523215
*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku , domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144, A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA * Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.
*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*👇🏽
*ingantaccen maganin infection *
Ingantaccen maganin basir
Ingantaccen maganin gyaran nono
Ingantaccen maganin gyaran hips
Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake
Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah
Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.
Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.
Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa 💯 kuma wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.
Akwai zallan hadi na amarya
Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.
Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka 👇🏽
Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu 🤐
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)
Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki duba 😉
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.🤐
Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu 💯👇🏽
Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa 😉 duk basuda side effects 👌
Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka
Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da laushi da ruwa a farjin mace 😉
Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI 😉
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI * direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu, amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.
*_📲Typing_*.
*_🪁ƊINYAR MAKAHO...!🪁_*
_(Ta nuna a hannunsa)🍀_
_*UMMU MAHER(MISS GREEN ce)🍀*_
_*AREWA BOOK👉🏼*_
ƊINYAR MAKAHO:: https://arewabooks.com/book?id=6387a8e97dd221ff54205a4f
*GAWURTATTU 5🔥*
------------------------
P. 7&8
............."Allah sarki bawan Allah ashe zan gan ka?".ta faɗi hakan tana kallonsa tamkar dai yau ne ta fara ganinsa,kowa na ɗakin kallonsu suke sosai na mamakin inda Umma ta san Ahmad.
Har yanxu shi Ahmad ɗin bai gane fuskar Umma ba,amman dai yana kallonta ko Allah zai sa ya tuno inda ya santa,sai dai har yanzu bai gane inda ya santa ɗin ba.?
Umma ta nisa sannan ta ce"Bawan Allah nasan baka gane ni ba?saboda halin rayuwa da kuma irin rashin lafiyar da ta sameni,dukkanin halittuna sun canja ayanzu Yaro ba lallai ne ka gane ni ba,amman zan tuna maka inda ka sanni ka tuna watarana shekaru biyu kenan da suka wuce naje kasuwa wasu Gurɓatattun mutane suka biyo ni?ka taimakeni daga hannunsu?to ni ce wannan baiwar Allahn,ko da yaushe ina nemanka don inyi maka godiya amman ko kafin wani lokaci wannan cutar ta kamani wacce ba tada ranar ƙarewa."
Tana faɗar hakan wasu hawaye masu zafi suka zubo mata,Hadiza dake gefe ta sharewa Umma hawayen dake ta ƙwaranyowa aƙwarmin idanuwanta tamkar dai an buɗe famfo.
Ahmad ya ce"Allah sarki tabbas na tuno da wannan ranar,wannan ranar ita ce rana mafi muni arayuwata duk da ta kasance ranar dana fara taimako irin wannan,Sai dai nima tun daga wannan ranar ne na haɗu da wani irin ciwo me wuyar magani,wanda ayanzu ma nake shirin fita ƙasar waje saboda shi".
Da sauri Umma ta kallesa,duk da ciwon da take fama dashi ta ce"bawan Allah ban gane me ka ke nufi ba?kana nufin kai ma ayadda ka ke ɗinnan ba kada lafiya"?.
Wani irin murmushi Ahmad ya yi wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo,sannan ya ciga da ce wa"Tabbas wannan ranar ita ce rana mafi muni arayuwata,don kuwa waɗannan mutanen sune suka sakani acikin wannan baƙin cikin dana ke ciki,sai dai ni na kasance musulmi kuma na karɓi ƙaddarata,kuma nasan ta hanyar taimako ne komai ya sameni,kuma nasan daman tunda ƙaddara ta ce sai hakan ua sameni don babu wanda ya isa ya goge ƙaddararsa."
Tun kafin ya faɗi Ƙaddarar data sameshi Hawaye suka jiƙa fuskar Umma gashi kuma tana matuƙar jin tausayinshi aranta,don bata san wacce irin cuta ce ke damunsa ba?.
Share hawayenshi ya yi da abin goge gumi,sannan ya ce"ayanzu haka ina fama ne da ciwon oda,wanda sanadiyyar dukan da sukayi min ya janyomin ciwon oda,ayanzu haka an ciremin oda guda ɗaya saura guda ɗaya,ayanzu haka da guda ɗaya nake amfani tare da taimakon Allah da kuma taimakon likitoci."
Sosai abin ya bawa kowa tausayi.
Abinda basu sani ba shine Noor duk taji wannan hirar da sukayi tun daga farko har ƙarshe,wasu hawaye masu zafi suka zubo mata a ƙwarmin idanuwanta,sosai Ahmad ya bata tausayi ashe daman shine wanda mahaifiyarta ta bata labarinsa,mutumin daya taimaketa daga hannun mugaye masu muggan makamai?.ta rasa dalilin daya sa asanda mahaifiyarta take da lafiya bata isa ta fita ba,sai kaga sai anso cutar da ita abin yana ɗaure mata kai tare da gula ƴar ƙaramar ƙwaƙwalwarta,ita dai tasan ba komai ne dasu ba?sai dai ma aji tausayinsu a basu?to me suke nema da mahaifiyarta?kukanta ne ya fara fitowa fili duk sai hankalinsu yayo kanta,musamman ma Ahmad wanda jikinsa har rawa yake don ya iso wajen Noor ɗin,don yadda yake jin wannan kukan na ta tamkar kukan aradu a sama.
sosai Noor ke kallonsa,ko da ba'a gata mata ba tasan abinda ya faru da ita balle taji duk abinda ya faru da i'ta ɗin.
"Sannu Noor Allah ya baki lafiya".
Cewar Umma wacce taji daɗin farkawar Noor har ranta,tana matuƙar son Noor sosai a kullum addu'arta bata wuce Allah ya bawa Noor miji na gari ba.
Ahmad ne ya fara ƙarasowa wajen da take,bai san lokacin da ya riƙo hannunta ba,ya damƙe su sosai kamar wani zai ƙwace masa ita sannan ya ce.
"Sorry Noor"
"ki yafe min ba asan rai na na kaɗe ki ba".
Motsawa ta yi tana son cire hannunta cikin na sa,amman ya ƙi ya bata wannan damar,adole ta haƙura ta bishi da manyan eyes ɗinta waɗanda suke rikitar da mazaje ba mazare ba.
Wani irin abu yake ji daya ke kallon Noor,ashe bai ga tsantsar baiwar Noor ba sai yanzu,ya yi murmushi har sai da dimples ɗinsa ya lotsa.
Noor ta lumshe idanuwa ta buɗesu akan Ahmad wanda ya zamar mata kamar wani sabo,don indai Noor za tayi magana sai ta lumshe idanuwanta,shine mutane da dama suke ganin wai iyayi ne kawai amman ba halittar ta bane.
Kusan shiɗewa yaso yi a zaune ganin abinda Noor ɗin ta yi,idanuwan sukayi wani farrr tare da kaɗawar gashin idanuwanta waɗanda ke atsaye xara zara.
Bai san lokacin da ya saki hannunta ba,ya yi saurin ja ba Hajiyar Ahmad ta ƙaraso tana yimin sannu,na yi murmushi ina kallon matar don sai naji tana matuƙar burgeni.
Ta ɗan shafa kaina sannan ta ce"sannu Beauty na,yanzu me ke miki ciwo"?.
Ɗan murmushi na yi ina kallon fuskar Ummana wacce itama ni ɗin take kallo,don duk hankalinta yana kai na.
"Babu abinda ya ke min ciwo Hajiya ƙafata ce ke ɗan yimin ciwo amman yanzu da sauƙi".
"Masha Allah,Allah ubangiji ya baki lafiya Ni yanzu zanje gidane aƙwai ƴar ƙanina wacce ke karatu awaje na to nasan tana cen hankalinta a tashe gwara in koma gida,amman gobe insha Allah zan dawo kinji beauty na".?
Ɗaga mata kai na nayi irin na masu shagwaɓar nan,sannan mukayi sallama taje sukayi sallama da Umma sannan ta tafi Ahmad sai kallona ya ke,yana wani irin murmushi ni har na fara gundura da irin kallon daya kemin,na sunkuyar da kai na kawai don ni ban saba kallon namiji ba,ko da a unguwar mune kuwa ban fiya wuce majalissar maza ba sai dai in canja hanya saboda bana son takura ko kallo,gashi ni kuma Allah ya yimin ƙirar da za'a kalle ni ɗin.
Suna tafiya Hadiza ta lallaɓo dai dai kunne na ta raɗamin wani abu,murmushi kawai na yi sannan cikin shagwaɓa na kalli fuskar Ummana na ce"Umma kinga Hadiza ko?Allah idan na samu lafiya sai nayi maganinta".
Murmushi Umma tayo sannan ta ce"Hmm wa ke shiga tsakaninku ƙwayi faɗanku ma ku shirya amman ni dai ba dani ba".
Sosai Hadiza ke dariya sannan ta ce"to idan kin isa yanzu ma kizo ki rama mana?kin riga da kin zama gurguwa zaki wani ce zakiyi faɗa"?.
Na ɗaure fuska sosai kamar zanyi kuka na ce"Umma kinganta ko?Allah ni ta koma gida kawai,gwara taje cen su ƙarata ita da Inna Lami don ita ce dai dai da Hadiza".
Dariya Hadiza ta yi sannan ta ce"Hmm wai ni baku san ma me ya faru ba"?.
Hararta na yi sannan na ce"oho ke kika Sani don kunfi kusa ke da Inna Lamiyo".
Dariya sosai Hadiza ta yi harda riƙe ciki sannan ta ce"Hhh ai kuwa dai munfi kusa,amman kin san yau Me Inna Lami ta aikata kuwa"?.
Umma ce ta yi magana yanzu ta ce"a'ah bamu sani ba sai kin faɗa"?.
"Hmm da Hajiyar Ahmad ta miƙo mata kuɗi da gudu ta amshe,wai da Hajiya take ce wa ina mahaifina a faɗa masa zancen tahowa ta asibiti kinsan me ta ce?ce wa ta yi wai in tafi babu komai babu abinda zai ce,ita da rakiyarmu har ƙofar gida."
Ta faɗi hakan tana dariya sosai.
Nima ƴar dariyar na yi sannan na ce"Hmm ai na Inna Lami kaɗanne ma don nasan na gidanmu sai yafi na Inna Lami don su Inna Saude sun taka Inna Lami akan son abin duniya,ita da take da kuɗi ma ta yi haka balle kuma su da basu da komai,idan ma sun samu sai dai ya ƙare abin bokaye da ƴan tsibbu".
Sosai Hadiza ke dariya har tana sakkowa daga saman kujerar da take.
Na ce"muguwa Hadiza kinji mugunta,bani labari insha don ƴan gidanmi nasan har ɗan ƙaramin ya ƙi xa'a tayar."
"Hmm ai Da Inna Saude da Inna Lami an kusa hawa sama a faɗo,don ita Inna Saude ta tafi wajen Baba yo munafunci anan aka bawa Inna Hafsatu ƙyautar Naira dubu biyar,ina baki labari mutuniyar ki Inna Saude na dawowa taga an bawa Jerry ɗinta kuɗi ai sai aka hau rigima,ke daga baya ma agaban Hajiyar Ahmad Inna Saude ta karɓw kuɗin hannun Inna Hafsatu,in taƙaice miki dai Hajiyar Ahmad sai ta bawa Inna Hafsatu haƙuri ta bata wani,don Inna Saude ƙin bada na hannunta ta yi wai sai dai kowa ya raba asara,matarki ta yi mirsisi ta tura kuɗi hammata".
Sosai muke dariya hat da Umma gwanin ban sha'awa.
Sai ga Ahmad da Dr Xain sun shigo,Dr Xain ya ce"ah lallai patient ɗina ta samu lafiya har da dariya irin wannan"?.
Murmushi na ɗanyi,ina dafe da kai na wanda naji yana matuƙar saramin kamar zai cire.
Ban san Ahmad yana kai na atsaye ba,sai naji yana ce wa"Noor kanki ke ciwo ko?kema me ya kaiki dariya kina fama da rashin lafiya?ko jinin da aka saka miki sai yanzu ya ƙare,don Allah ki dinga kulamin da kanki".
Suɓul da baka Ahmad ya yi,don na lura shi yana da matuƙar kunya,amman wataƙila akaina bazai iya yin kunyar ba.
Dukkansu kallon Ahmad suke yadda ya dage yana faɗar maganganu akan ɗan ciwon kan dana ke yi,ko da Ahmad bai faɗa ba tabbas kowa yasan aƙwai abinda ya ke aransa.
Lokaci ne kawai zai nuna hakan,koma ace tun yanzu lokacin ya nuna aƙwai ayar tambaya akan Ahmad ɗin,don idan kajo kare na shinshina takalmi yasan abinda ya gano.
Dr Xain ya yi murmushi sannan ya ce"come down Barrister Ahmad ka daina damuwa da hakan,shima hirar da takeyi yana cire mata kewar wasu abubuwa nw da dama,saboda idan ta zauna ita kaɗai za tayi ta tunani ne wand mu likitoci bama san hakan ta kasance da marar lafiyarmu,munfi son ya dinga samun emotion mai kyau."
Sai sannan Ahmad ya zauna sannan ya ce"amman Dr babu matsala ciwon kan na ta ko?".
"Babu komai wannan jinin da aka ƙara mata ne,so bai gama shiga jikinta ba sai ahankali rashin jini shine ya ke kawo hakan,amman ahankali komai zai yi dai dai insha Allah".
Ɗan murmushi ya yi wanda ke ƙara masa kyau akoda yaushe,don Ahmad kyakkyawane ajin farko,babu macen da zata ce bata son Ahmad don ya haɗa komai daya kamata duk mace taso shi.
Juyar da kaina na yi daga barin kallonsa,don bana son ya ramfoni da kallonsa,amman ina tuni ya gane kallonsa dana ke yi,ya sakarmin murmushi da sauri na juyar da kai na.don wani irin abu dana ji araina kuma wanda ban taɓa jinsa akan namiji ba.
Ana cikin haka,wasu samari suka fara shigowa da kaya cikin ɗakin,katan ɗin ruwa da katan ɗin maltina da madara sai su lemo dasu apple masu yawa.
Sosai na bisu da kallo har suka ajje kayan,ina mamakin daga ina waɗannan kayan kuma suka fito?sai dai nasan bazasu wuce daga wajen Ahmad ba,don dai nasan wa muke dashi da zai yi mana wannan hidimar?amsar shine babu?don nasan ƙanin Umma ko zamu mutu da yunwa bazai zo inda muke ba,don tun tasowa ta zan iya irga sau nawa iyalinsa suka zo inda muke,wai su masu kuɗi kuma suna ƙyamar shigowa cikin talakawa.
bayan sun gama shigowa da kayanne Ahmad ya tashi tsaye sannan ya ce"To Umma ni xan tafi sai Allah ya kaimu gobe Insha Allah zan dawo da wuri duk da ina da meeting a Abuja amman zan ɗagasa zuwa Jibi".
Ya faɗi hakan kana asunkuye,alamun yana jin kunyar Umna ɗin.
Umma ta ce"Haba Ahmad ai da ka barshi ma ka tafi Taron na ka,saboda kada ya haifar da wata matsalar,indai Don Noor ne ai ta fara samun lafiya ma".
"A'ah Umma idan ma na tafi nadan bazan wani aiwatar da abin kirki ba,gwara dai in dawo inga jikin na ta kafin jibi kuma in wuce Abuja ɗin".
Sosai suke kallonsa,wai har yana ce wa ma idan ma ya tafi ba zai iya aiwatar da anin kirki ba?kowa mamakin abin ya ke,don yadda ya ke nunawa Noor kulawa abin ya yi yawa.
Yana faɗar hakan yasa kanshi ya fita,yana ɗan sosa ƙeyarsa don yasan ya yi rashin kunya,ga mahafiyar Noor awajen amman yana suɓul da baka.
Murmushi kawai ya tsinci kansa dashi har ya shiga mota ya auce gidansu wanda ke Nassarawa G.R.A.yana tuƙi Idanuwansa na hasko masa da fuskar Noor da wannan idanuwan na ta masu matuƙar tafiya dashi.
Yana isa gida ɓangaren Hajiyarsa ya fara nufa,Ya shiga babban falonta wanda ya yi matuƙar haɗuwa da tsaruwa,Zaliha ya tarar a falon Hajiyarsa ta yi wani irin mugun tagumi da hannayenta duka guda biyu.
Sosai ya yi mamakin wannan tagumin na ta,ya matsa kusa da ita ya zauna sannan ya ɗan karkaɗa mata hannayensa amman Zaliha bata ɗago ta kallesa ba.
Sosai ya yi mamaki don ganin ƴar ƙaramarta da ita amman ace ta faɗa cikin irin wannan tunani haka?.
"Zaliha!Zaliha!!Zaliha!!!.
Da sauri ta zabura zata gudu,idanuwanta sukayi rau rau sannan ta ce"Allah Yaya ka tsorata ni sosai,ina nan ina tunanin rashin dawowarka da wuri."
Ɗan murmushi ya yi sannan ya ce"au don ban dawo da wuri ba shine kika zauna zaman tunani?to Allah ya shirye ki"?.
"Allah yaya ban saba ganin ka daɗe awaje irin haka ba?Hajiya ma yanxu ta shigo take gaya min wai ka buge wata yarinya ne amman yanzu da sauƙi sosai,kuma har tace kaima ka taho amman kusan awa ɗaya naga baka dawo ba,kamar wanda xai taho daga wani garin?."
Ta faɗi hakan cikin shagwaɓa sosai kamar za tayi kuka.
Ruƙo hannayenta ya yi sannan ya ce"to yanzu dai tashi ki kawomin abinci ɗakina,zanje wajen Hajiya Yanzu ki jira ni fa"?.
Murmushi Zaliha tayi sannan ta ce"to Yaya ina nan ina zaman jiranka".tana faɗat hakan tayi hanyar kitchen don haɗo masa abincin.
Yana shiga ɗakin ya samu Hajiyarsa tana waya,ya jira har sai da ta gama tukunna don tana magana da wani balarabe ne wanda suke yi mata safarar kaya daga Dubai zuwa Nigeria.
Tana gamawa ta kalli ɗan na ta,Sannan ta yi murmushi ta ce"Baba na ka dawo?ya ka baro Beauty na"?.
Ɗan murmushi ya yi yana ɗan sosa ƙeyarsa sannan ya ce"Beautynki tana nan lafiya jikinta kuma da sauƙi sosai Hajiya."
Murmushi ta yi sannan ta ce"to Allah ubangiji ya bata lafiya,ni yarinyar ta ƙwantamin sosai azuciyata wallahi".
Murmushi Ahmad ya yi sannan cikin shagwaɓa ya ce"Ni Hajiya sai naga kamar kinfi sonta ma dani".?