Showing 6001 words to 9000 words out of 46793 words
Chapter 3 - DINYAR MAKAHO Book 1 Complete Document by Ummu Maheer Miss Green txt
ya kamani na kasa cewa komai saboda firgici da kuma mamakin jin hakan.
A hankali ta miƙe jikinta duk yayi sanyi sannan ta ce"Hmm Noor daman nasan zakiyi mamaki sosai,yau kusan ƙwana biyu kenan dana je gidansa ya nemeni da wannan mummunar maganar,Noor nayi mamaki kuma na tsorata sosai,ashe dukkanin hidimar da yake min ashe so yake ya fanshe abinsa."?
Ta kalleni tana hawaye.
Nima hawayen nake sosai sannan na ce"Haba Hadiza kinsan da wannan maganar amman kuma kikayi shiru kamar babu abinda ke damunki"?.
"Hmm Noor kenan,to yaya zanyi da rayuwata?wa nake dashi da zangayawa?so kike na gayawa yayarsa ƙaninta na nemana?ko kuwa so kike na faɗawa Baba na?wannene acikinsu zai yarda dani"?Noor na faɗa miki ne don ki sani kuma ki tayani da addu'ah".
"insha Allah Hadiza zan tayaki da addu'ah,kuma babu abinda zai sameki sai ikon Allah,Amman Hadiza kin faɗawa Baba Hassana kuwa"?.
"Ban faɗa mata ba Noor na rasa ta yadda zanyi in faɗa mata,don ba ƙaramin firgitani yayi ba akan cewa duk wanda na faɗawa to na zama gawa,kema na faɗa miki ne don zuciyata ta samu salama,yanzu dana faɗa miki na rage jin raɗaɗin dana keji".
"Kuka na fashe dashi sannan na ce"Hadiza me yasa xakiji tsoronsa?don yace miki zaki xama gawa?Shi daba Allah ba?Allah ne kawai yake da rai da kuma mutuwa,babu wani bawa daya isa ya kashe wata rai face da hukuncin ubangiji,don haka kada kiji tsoro ki faɗa mata Allah zai kawo mana sauƙi insha Allah,idan kuma bazaki iya faɗa mata ba to ni zanje in sameta in faɗa mata,sai a haɗashi da hukuma don idan ba haka ba,zai lalata miki rayuwarki ƙarshe kuma kiyi nadamar yin shirun."
Da sauri Hadiza ta rufemin baki sannan ta ce"Noor ki rufamin asiri don Allah,mutumin nan yana da kuɗi ba kaɗan ba koda an haɗashi da hukuma bazai kamu ba".
Saurin cire hannunta nayi daga bakina na yarfeshi gefe sannan na nuna ta cikin fushi na ce"yafi ƙarfin Allah ne?wallahi Hadiza ki tashi ki farka idan ba haka ba,zai lalata miki rayuwarki abanza da hofi,ƙarshe yace bai ma sanki ba kinga wa gari ya waya"?.
Fashewa tayi da kuka sannan ta rungumeni ta fashe da kuka me ƙarfi.
Rungume ta nayi sannan na fara shafa bayanta a hankali tamkar ƙaramar yarinya,har ta tsagaita da kukan na ta nima har yanzu kukan nake na tausayin ƙawar tawa,wato duk rayuwar da kake ciki sai kaga wani ya fika.
"Noor ki tafi gida kin bar Umma ita kaɗai,kuma bana so ki ɓoyewa Umma wannan maganar,saboda nasan Umma aƙwai ibada,kuma bayan haka ma Umma tamkar uwa na ɗauke ta,nasan zata taya ni da kai kuka wajen ubangiji."
Sallama mukayi da ita,ta kama hanyar gidansu tana tafiya tamkar wacce ƙwai ya fashewa aciki.
Nima duk jikina babu daɗi,ga matsalar dana ke ciki ga ta aminyata Hadiza,abin ya damu ƙwalƙwakwata ina ta tafiya ina sauri-sauri don inzo gida in kalli sanyin idaniya ta wato mahaifiyata,duk baƙin cikin dana ke ciki idan na kalli mahaifiyata ina jin sauƙin raɗaɗi sosai.
Na tsallaka titi na farko na taho don tsallaka na biyu sai naji. ..
da gudu Drivern ya fito daga cikin motar yayo kai na,ganin har jini ya fara ɓata wajen dana ke shima ogan nasa da sauri ya fito,yayo kai na farar cort ɗinsa ta jiƙe da jini ya ɗagani cak.da sauri suka shiga cikin motar duk hankalinsu a tashe.
General hospital suka nufa,wato aminu kano teaching hospital taimakon gaggawa aka fara bani,aka shiga dani emergency don bani taimakon gaggawa.
Zagaye kawai saurayin yake don duk hankalinsa ya tashi sosai,Wayarsa ce ta fara ruri amman bai iya ɗaga wayar ba saboda tashin hankali,tunda yaka bai taɓa buge ko da ɓera ba balle kuma mutum.
Ganin kiran ya yi yawa ne yasa ya ɗaga,daga cen ɓangaren aka fara magana.
"Haba Ahmad baka saba kaiwa haka ba?lafiya kuma har yanzu baka dawo ba"?.
"Hajiya wallahi yau ina cikin matsanancin tension ne,na shiga cikin wani hali sosai wata yarinya na buge yanzu".
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
"Ahmad wani asibiti ne?".
Faɗa mata sunan asibitin ya yi sannan ya ajje wayar,ya zauna ya kalli rigarsa wacce duk jini ya ɓatata,hankalinsa ya ƙara tashi sosai yana addu'ar Allah yasa kada ta mutu don ta zubar da jini sosai.
Ba'a fi minti talatin ba sai ga Mahaifiyar Ahmad,duk itama hankalinta a matuƙar tashe.
Ta kalli rigar Ahmad ɗin wacce duk jini ya ɓatata,tsoro ya kamata sosai ta ce"sannu Ahmad me ya akayi hakan ta faru"?.
"Hmm Hajiya ƙaddara,da kuma rabon sai na fito daman sai da kika ce kada na fito amman yanayin aikina yasa babu yadda zanyi dole dai sai na fito hakan ta faru."
Kusan minti talatin sannan likitocin suka fito,da sauri Ahmad ya ƙarasa kusa dasu yana tambayarsu ya jikin na ta.?
Likitan ya ce"kai ne ka buge ta?".
"Eh nine na buge ta,gama ɗan sandan da muka taho dashi".
Likitan ya kalli ɗan sandan sannan ya ce"ok ka biyoni office".
Yana faɗar hakan Ahmad yabi bayansa don yaji abinda likitan zaice,gabansa sai faɗuwa yake kamar zai faɗo ƙasa.
itama Hajiyar Ahmad ɗin binsu tayi don hankalinta ya kasa ƙwanciya,yadda taga jini ajikin Ahmad to ta tabbatar da cewa wannan yarinyar idan bata mutu ba,to tabbas tasha wuya sosai.
To acen ɓangaren kuma,mahaifiyar Noor na cen duk hankalinta ya gama tashi,gashi ita ba ƙafa ba balle ta tafi nemanta.
Ta rasa yadda za tayi,daman tana da alwalarta ta yi sallarta a zaune,ta ɗaga hannayenta sama tana kuka tana roƙar ubangiji.
"Ya Allah kaga xuciyata,kaf duniyar nan daga kai sai manzonmu muhammad(S.A.W)dasahabbansa da kuma matayensu,sai ƴata Noor kaf duniyar nan bayansu sai ƴata,ina masifar sonta har cikin ƙoƙon xuciyata,Noor shekararta Shida a ciki na,ba shekara ɗaya ba har shekara shida,haka nasha wuya na haifeta ya Allah duk inda take Allah ka karemin ita da karewarka,sannan Allah ka tsaremin ita da tsarewar ka,ba wayo na ko dabara ta ba,Allah na tabbatar da ka amshi roƙo na,Ya Allah kai ne kace mu roƙeka zaka amsa mana,to Ya Allah na kawo kuka na gare ka akan rashin dawowar ƴa ta gida,Allah ka tsaremin ita Amin ya Allah".
Dai dai nan ta shafa,tana shafawa taga an ɗaga labulen ɗakinta..ta hango hasken fitilar nefa a tsakar gida,wacce ita babu wannan gatan a ɗakinta,tunda ta lalace shikkenan yau kusan shekara biyu kenan tun sanda ta fara wannan ciwon.
"Ke!".
Sai lokacin ta gane wanda ya ɗaga mata labule,Mahaifin Noor ne tsaye sai harararta yake kamar zau dake ta.
Ta daure daga wani mugun haushinsa da take ji ta ce.
"Ina yini Baban ya. . . ."
Da sauri ya dakatar da i'ta da faɗin"ke Fatima kiyi a sannu fa,rashin mutuncin da kikeyi dake da ƴarki ya fara i'sata,ya za'ayi yarinya ta fita tun rana amman har yanzu kusan ƙarfe takwas na dare bata dawo ba?ko daman haka kika koya mata?don taje yawon karuwanci ta samo miki abinda zakiyi ƙarya?don dai nasan badon yunwa ko don wani abuba,don dai kinsan gidana ba gidan yunwa bane".?
Sosai take kuka hawaye ya wanke mata fuskarta,ta tsani cin mutuncin Isma'il sam be sam mutuncin ɗan adam ba,shiyasa san bata fiya shiga hulɗarsa ba,musamman ma yanzu da ba tada lafiya.
"Ba dake nake ba?kinyi min shiru munafuka sai ana magana kiyi wani wuƙi wuƙi da idanuwa na rashin gaskiya ko?to bari kiji idan na ƙara auna minti talatin bata dawo ba,to sai ranki ya yi mummunan ɓaci,don sai kin fita kin bar min gida na".
Sosai gabanta yayi wani irin mugun bugawa,Fatima ta dafe ƙirjinta wasu hawaye masu mugun zafi suna ƙwaranyowa daga ƙwarmin idanuwanta.
Lallai rashin imani irin na Isma'il ya yi yawa,yanzu ayadda take ɗinnan idan ya kore ta ina zata je?idan ya kore ta dawa zata haɗu,mutane nagari ko akasin haka?.
Inna Saude tana ganin shigowar mijinta ta ɗaure fuska ta yo da ɗaurinta gaban goshi sannan ta ce"oh amman Isma'il kana bani mamaki?yanzu da kaje tattaunawa kukayi ko me?baka kore ta ɗin ba?shine ka dawo min nan kana wani hura hanci?".
"Ai na bata nan da wasu mintina,wallahi indai bata dawo ba korarta zanyi daga gidana don daman wallahi ta isheni,mata kamar wata musaka ita ba ƙafa ba ita ba wata mamora ba.?"
***********
Suna zama likitan ya ce"yauwa daman na kiraka ne saboda inyi maka bayanin komai,wannan yarinyar ta zubar da jini sosai,ta yadda dole ne sai anyi mata ƙarin jini,don ma jininta me ƙarfi ne sosai da an rasa rayuwarta baki ɗaya,amman Allah ya taƙaita karaya ɗaya ce a ƙafarta sai kuma ƙarin jini da za'ayi mata Leda huɗu sai wasu magunguna da zan rubuta mata yanzu."
Wasu ƴan rubuce rubuce ya yi sannan ya ɗago ya ce"yauwa to waɗan nan magungunan zaka sayo,sannsn maganar jini kuma siya zakuyi ko zaku bayar?".
Da sauri Ahmad ya ce"zan bada Leda ɗaya sai in siya guda uku ɗin".
Hajiyarsa ta ce"kai Ahmad ka siya mana?meye dalilin da za a ɗibar maka jini kuma kaima kasan ba kada lafiya"?.
"Babu komai Hajiya a ɗiba ai taimako ne,shi taimako ana yinsa ne don taimako don gyara lahirarka".
Ba don ran Hajiya yaso ba ta haƙura kawai,ta bar zancen don yanzu ba lokacin da za'a zauna ana musu bane.
8:00pm Dai dai lokacin Ya sayyadi ya sauka akan lifan ɗinsa,ya tsaya aƙofar gidan ya kasa shiga,ya samu wani yaro ya aikasa gidan ya ce.
"Kai idan ka shiga kace wai Noor tazo inji ya Sayyadinsu".
yaron ya ce"to".
Daman ɗakin Mahaifiyar Noor ne a farko,don haka kana shigowa da ɗakinta zaka fara cin karo.yaron ya shiga ɗakin ya ce"wai inji ya sayyadinsu Noor wai tazo".
Da ɗan sauri Umman Noor ta ɗago hawaye duk ya gama wanke mata fuskarta,ta ce"kai kace wai haryanzu bata dawo daga makaranta ba,nima nemanta nake yanzu."
Tana faɗar hakan ta fashe da kuka me tsanani.
Yaron yana fita ya ce"wai ance har yanxu bata dawo daga makaranta ba, mamanta ma nemanta take".
Sosai gabansa ya yi mugun faɗuwa,ya kalli yaron sosai kamar yaga hoto,ya rasa wani irin tunani zaiyi to ita Noor a ina ta tsaya ne?.
Wata dabara ce ta faɗo masa ya hau mashinsa ɗinsa,bai tsaya ko ina ba sai gidansu Hadiza don yasan duk inda Noor take to Hadiza ta sani.
Allah ya taimakesa ya sameta a ƙofar gidansu,da alama aikenta akayi ya sauka ya ƙarasa ya ƙwala mata kira don yaga ta kusa shiga gida.
Cikin tsoro ta juyo ta ce.
"a'ah ya sayyadi lfy kuwa na ganka haka"?.
"Ina fa lafiya Hadiza?ƙwarki aka nema aka rasa,shine naxo don inji ko kinsan inda take?tunda nasan aminiyarki ce kuma tare kuke tahowa".
Tunda ya fara maganar ta tsaresa da manyan idanuwanta,ta dafe ƙirjinta tana cewa"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga ɗaka ban fito ba..ɗaxu fa tare muka rabu,ta tafi gida nima na tafi wallahi tun daga nan ban ƙara sanin inda tayi ba".
Ta faɗi hakan tana fashewa da kuka sosai,jin ihunta yayi yawa ne yasa ya sayyadi ya ce"ke Hadiza shiga gida,ba kuka zakiyi ba addu'ah zakiyi".shima cikin dakiya ya faɗi hakan don bai san yana mugun son Noor ba sai yanzu.
Yanzu ta ina zai fara nemanta,ya share hawayen fuskarsa da handcachep ɗin hannunsa,sannan ya hau machine ɗinsa yabi hanyar gidansu Noor.
Ya tsallaka titi na farko ya tsallaka na biyu,sai wani tunani ya faɗi masa,ya sauka daga kan machine ɗin nasa ya gaisa da wasu samari daya gani sannan ya ce.
"Don Allah bayin Allah ɗazu bakuga wata yarinya ƴar fara ba?sanye cikin uniform ɗin makarantar islamiyya tana da ɗan matsakaicin tsayi."?
Wani daga cikinsu ya ce"haba mlm mufa tun safe muke wajen nan,tamkar masu jiran taimako nan ce majalissarmu sai dare muke tashi,kuma mutane da yawa suna zuwa wucewa,wasu mu kallesu wasu kuma bama sanin sun wuce,amman mu bamu ga wannsn yarinyar da kake nufi ba."
Da sauri ɗayan ya ce"a'ah fa ku tsaya ko dai wacce aka buge ce ɗazu a mota?don ma bamu san ƴar waye ba da tuni mun shaida a gidansu."
Da sauri ya sayyadi ya ce"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,don Allah ina kuka ga sunyi"?.
"To mlm muda ba binsu mukayi ba?ta ina zamu san inda sukayi".
Ɗaya daga cikinsu ne ya faɗi hakan.
Da sauri Ya sayyadi ya hau machine ɗinsa zuwa gidansu Hadiza,ya aika yace yana kiranta Hajja kishiyar mamanta sai masifa take tana cewa.
"shi kuma wannan ya sayyadin uban me zaiyi miki da daddaren nan kamar wani tsohon ƙwarto.?"
Ita dai Hadiza saka hijabinta tayi ta fita da gudu.don ko saurarenta bata yi ba,ta fito waje don tunda ya sayyadi ya shaida mata ba'a ga Noor ba,taji duk hankalinta ya yi matuƙar tashi.
Aguje ta fito tana gaki sannan ta ce"ya sayyadi an ganta"?.
Bayanin komai yayi mata sannan ya ce"yanzu shge gaba muje gidansu Noor don mu sanarwa da mahaifiyarta komai."
Tana kuka ta shige gaba,tana gudu kamar ƙaramar yarinya Ya sayyadi na binta a baya har suka zo ƙofar gidan.
Da gudu Hadiza ta shigo gidansu Noor,kai tsaye ɗakin mahaifiyar Noor ta nufa tana ta haki kamar zata faɗi.
Umma na ganinta ta ƙara sautin kukanta tana cewa"Allah sarki Hadiza ashe kinji labarin ɓatan Noor ko"?.
fashewa Hadiza tayi da kuka sannan ta ce"umma yanzu ya sayyadi yake shaidamin wai wata yarinya ɗazu an buge ta,kuma ana tunanin Noor ce yanzu haka ni da ya sayyadi zamu bi asibiti,zamu fara zuwa general hospital don mu duba muga ko Allah zaisa a dace".
Inna Hafsatu dake laɓe jikin labule tana jin duk abinda ke afkuwa,ta ce"Hmm Allah dai yasa ta mutu ma kowa ya huta."
Ya sayyadi da Hadiza suka wuce asibitin don dubawa,Ita kuma Umma na gida sai kuka take carbi yana hannunta tana ja tana kuka,Noor ita kaɗai ta mallaka a rayuwarta ba tada kowa sai Noor,ta taso cikin rayuwa ta ƙunci da baƙin ciki saboda ta kasance ita ƴar tsintuwa ce,tun tana ƙarama aka yarda ita wani bawan Allah ya ɗauketa,yana da mata ɗaya sai ɗa ɗaya shima bayan an tsinceta ne aka haifesa,sai dai matar mutumin ba tada mutunci ko kaɗan,ita dai kanta kawai ta sani sai na ɗanta to a haka tayi wannan rayuwar har Allah ya kawo lokacin da tayi aure.tana tunanin canjin rayuwa ashe wani bala'in ta ƙara afkawa.
Don kuwa ko wata ɗaya bata yi ba,ta fara cin karo da masibu kala kala don awajen Isma'il kawai take samun farin ciki sai mahaifiyar Isma'il ɗin,don daman sanda ta auri Isma'il matansa biyu itace ta uku,ta aure shine badon kuɗinsa ko kyau ba,don Isma'il aƙwaishi da kyau ga fari kamar tsada,don kana ganin Noor kasan cewa ƴarsa ce.
*****
*Yarima pov*
. . . . .kai tsaye taronsa ya wuce a ɗakin shugaban ƙasar France,har kowa ya hallara shi kaɗai ake jira.
Ya zauna yana fuskantarsu,suma duk hankalinsu yana kansa suka gaisa sannan suka fara abinda ya kawosu ya huɗe taswirar wata gadar jirgin ƙasa da yayi wadda ya za na ta,babbar hanya ce ne nisan tsiya wacce idan tafiya mutum zaiyi,sai ya yi ƙwana uku huɗu akan hanya ba tare daya je,hanya ce akan dutse wacce turawa da dama suka yi yunƙurin yi amman basu samu basirar yinta ba,sai gashi yaro ƙarami ya zana ta ya fitar da hanyoyi daga cikinta.
Yazeed aka bawa ƙwangilar yin aikin,shugaban ƙasa ya ware kuɗi tsaba akan wannan hanyar,don yana bala'in jin daɗin aikin Yazeed don yaro ne me fasaha da kuma basira kuma gashi ba mutunne me cin amana ba,don ko nawa zaka basa ya ajje maka indai ba kuɗinsa bane to ya yi watsin makauniya dasu.
Suna fitowa daga taron yaji wayarsa ta cigaba da ringing,yaƙi ɗagawa sai daya fito daga wajen sannan ya samu wani waje wanda aka kewaye shi da fararen kujeru ya samu ɗaya daga ciki ya zauna,ya rage cort ɗinsa sannan ya ɗauko wayarsa ya buɗe yaga alamar an turo masa message,ya buɗe message ɗin ga abinda message ɗin ya ƙunsa.
*Yazeed umminka ce ina ta kiranka kaƙi ka ɗaga ko?ka manta da umminka ko to shikkenan na gode*
Duk cikin yaren larabci ta turo masa da saƙon.
Ɗan murmushi yayi ya shafa ƙwantaccen gashin kansa,sannan ya yi calling no ɗin Mahaifiyarsa wacce yake jinta har ransa don shi aduniya yana matuƙar son mahaifiyarsa.
I'tama kuma ya sani tana masifar sonshi da ƙaunarsa,tana tattalinsa sosai kamar wani ƙwai ko kuma ɗan jariri.
Tana ɗagawa taƙi yin magana tayi shiru,kamar yana ganinta ta ɓata fuska sosai tamkar tasha kunun tsamiya.
Shima kamar yana ganinta ya ce"Ummi yanzu nasan kin turɓune fuska kamar kinsha magani ko?sorry my ummi ayimin afuwa abubuwane da dama suka shamin kai."
Nan ma ƙin magana tayi,sai yaji duk babu daɗi sai ya fara magana cikin shagwaɓa tamkar yaro ya ce.
"Ummina kin dai na so na ko?.shikkenan bari in kashe wayar gobe zan dawo Nigeria".
Murmushi Fulani Zaulahait tayi,don daman tasan abinda zaice kenan kuma daman itama abinda takeso kenan,har ta gaji da yiwa Yazeed mitar ya dawo gida amman abu ya cutura,sabon da Yazeed ya yi da France bata tunanin zai dawo gida ta sauƙi,amman ta fara wani tunani akan abinda zaisa ya dawo gidan dole.
"Ummina kinyi min shiru ko"?.
"To me zance maka Yazeed?kai fa yanzu ba ƙaramin yaro bane,kasan abinda ya dace fa?yanzu idan har munason mu ganka sai dai muzo inda kake?ina son in ganka Yazeed amman kaƙi dawowa in ganka inji daɗi,kana son maganar da mutane sukeyi akanka ta tabbata ko"?.
Ya fara magana cikin shagwaɓa sannan ya ce"Ummi na wacce magana mutanen sukeyi?".
"Hmm bazan faɗa maka ba Yazeed amman ina masifar son in ganka,kuma kasan ba zai yiwu inzo France yanzu ba,saboda Twins suna gab da dawowa daga America kaga kuwa bazan taho in barsu ba".
"Yanzu Ummi kinfi son waɗannan emogies ɗin dani ko?".
"Eh nafi sonsu ɗin,ai su suna jin magana ta ba kamar kai me taurin kai ba".
Taɓa kansa ya yi kamar tana ganinsa sannan ya ce"haba Mom nifa kai na babu tauri,har yanzu ni kid ne(yaro).
Murmushi tayi son tasan halin shagwaɓa irinta Yazeed tasan idan ta biye masa sai su ƙwana yana mata