Showing 24001 words to 27000 words out of 46793 words
Chapter 9 - DINYAR MAKAHO Book 1 Complete Document by Ummu Maheer Miss Green txt
masa cikin mutunci Hajiya ta kalli Umma ta ce"ni yanzu naga mutumin ya fita amman sai naga ransa kamar a ɓace ya ke?".
Ɗan murmushi Umma ta yi sannan ta ce"eh haka ne Hajiya Amman shi da mutuniyarsa ne wato Noor."
Da sauri na kalli Umma ina nuna kai na,cikin shagwaɓa na ce"kai Umma ni wallahi ban masa komai ba".na faɗi hakan tamkar zanyi kuka don har idanuwa na sun fara tara ƙwalla,don daman tunda naga ran yaya Ahmad ya ɓaci nima sai naji nawa ya ɓaci,kuma sai naji duk haushin Ya sayyadi ya kamani don sai nake ganin duk shine ya janyo komai.
Ya sayyadi yana fita ya hango Ahmad ajikin motarsa,ya sunkuyar da kansa ƙasa kana ganinsa kasan aƙwai abinda ke damunsa.
ya sayyadi ya ƙarasa kusa dashi,har ya ƙarasa kusa dashi bai ma san ya iso ba,sai da ya sayyadi ya dafa kafaɗarsa ya ce"Mlm Ahmad kenan kai da kace kai namiji ne?ashe tun yanzu zaka zubarda mazantakarka.?"
Sosai ran Ahmad ya ɓaci,ya kalli ya sayyadi ya ce"kai ka isa ka sakani inyi abinda banyi niyya ba?to bari kaji idan ma kana tunanin wai in cire Noor a zuciyata kasan kaima baka isa ba,ita ƙauna Allah ne yake ginata azuciyoyi guda biyu ba wani bawa ba,don haka sai kowa ya gwada sa'arsa."
Murmushi ya sayyadi ya yi sannan ya gyara tsayuwarsa ya ce"hmm ya Mlm Ahmad kenan,kai kana tunanin don ka fini kuɗi da kyau sai ta zaɓeka ta barni?idan ma kana tunanin hakan to ka daina don ni nasan ayanzu babu wanda Noor take so sama dani,saboda dani ta saba kuma dani ta rayu don haka tun wuri ka fita daga rayuwar Noor tunda ai bugeta kayi,kuma yanzu ta samu lafiya don haka ka fita daga harkarta".
Murmushi Ahmad ya yi wanda bai kai zuciyarsa ba sannan ya ce"Hmm kana bani mamako wallahi,amman ni bazan zauna mu zama ɗaya ni da kai ba,don haka ni sai ka ga tafiya ta don inada ayyuka agabana".
Yana faɗar hakan ya shigewarsa motarsa abinsa,ya buɗaɗe ya sayyadi da ƙasar wajen ya fice da gudu a motar. . . . . .ran maza ya ɓaci Ahmad.
Sosai abin ya yiwa ya sayyadi ɗaci sai dai ta wani ɓangaren baiji haushin Ahmad ba don yasan duk acikin kishi ne.
Ya sayyadi yana fita,Hajiyar Ahmad ta ce"ikon Allah to shima wannan sai naga kamar fushin yake?yaran nan lafiyarsu kuwa"?.
dai dai lokacin na ɗan taɓa Hadiza don ta kaini banɗaki,ruƙoni tayi na fara takawa ahankali har muka shiga banɗaki,nan dai suka cigaba da hirarsu Zaliha tana gefe tana ɗan daddana wayarta tun bayan da ta gaishe da Umma sannan ta yiwa Noor ya jiki,sai ta nemi waje tayi shiru kuma ita daman ba mutunce me magana ba,idan kaji tana hira to bazai wuce da Ahmad ko Hajiya ba.
Umma ta ce"Hajiya ayiwa Ahmad godiya,don yanzu ya gama gaya min ce wa zai biya kuɗi don a fita dani ƙasar waje kan ciwon nan na wa".
Murmushi Hajiya ta yi sannan ta ce"ayya Babu komai ai Ahmad ya saba irin wannan wanda ma bai sani ba yake taimakonsa ina ga wanda ya sani?".
Nan dai suka cigaba da hirarsu har na fito daga banɗaki na samesu.
Da Hajiya zata tafi ta ajjewa Umma kuɗi masu yawa wai ma sai wani abin.
Umma ta yi mata godiya sosai,nima na yi mata godiya akan dukkanin hidimar da suke mana.
Da Hajiya zata tafi ta ajjewa Umma kuɗi masu yawa wai ma sai wani abin.
Umma ta yi mata godiya sosai,nima na yi mata godiya akan dukkanin hidimar da suke mana.ta ce"babu komai beauty na ai kun zama ƴan uwa yanzu kuma."
Murmushi na yi ina jin matar har zuciyata,tare suka tafi da Fatima sai su ajje ta akan hanya.
Suna tafiya Umma ta kalleni sannan ta ce"oh Noor kinga ikon Allah ko?shi haka rabbi ya ke ikonsa,da muna cikin wani hali amman yanzu cikin ikon Allah mun fara samun sauƙin wasu abubuwan,ki ga fa ciwon nan nawa shekara ta biyu kenan harda ƴar ɗoriya ina fama da ciwo,ɗan uwana da nake ganin zai kula dani ya yi banza dani,saboda ban haɗa komai dashi ba,saboda iyayensa ma tsintata sukayi shiyasa bai damu dani ba,amman sai gashi waɗanda ban haɗa komai dasu ba,suna taimako na tamkar dai daman cen sun sanni kuma sanin ma sananne don idan ba ɗan uwankane uwa ɗaya uba ɗaya ba,ba lallai ne ya kula da kai ba sai dai kayi ta bulayi bara akufai."
Murmushi Hadiza ta yi sannan ta ce"haka ne Umma shi daman haka Allah ya ke abinsa,sai kaga wanda baka haɗa komai dashi ba,ya taimakeka amman wanda ka haɗa dashi sai kaga ya manta da dukkanin lalurorinmu,yanzu dai Umma ni ki duba fa ki gani mahaifiyata ce,kuma ita ce ta kawoni duniya tasha wahalar na ƙuda ta,amman duk ta manta da wannan tunda ta haifeni na yi wasu ƴan shekaru a hannunta da suka rabu da mahaifina kusan shekara goma kenan amman har yanzu ban sake sakata a idaniya ta ba,ban san inda zan ganta ba ita kuma bata nemeni ba,tun da dai ai tasan inda zata ganni amman ta yi watsi dani ta manta dani. . . . . ."
Da ƙer ta ƙarasa faɗar hakan hawaye yana ƙwaranyowa aƙwarmin idanuwanta.
Sosai ta bawa zuciyoyinmu tausayi,Umma ta ce"Hadiza matso kusa dani kinji".
Da sauri Hadiza ta matso kusa da Umma tamkar dai daman tana jiran wanda zai lallashe ta.
Umma ta rungumeta tana ɗan bubbuga bayanta,don yarinyar abar a tausaya mata ne babu kulawar uwa babu na uba,to da wanne za taji?a barta taji da duka ɗaya mana?.
Umma ta ni sa sannan ta ce"kiyi haƙuri Hadiza kowanne bawa da irin ƙaddararsa kinji,kuma ni dai na tabbata ruwa baya tsami banza tabbas aƙwai abinda yasa mahaifiyarki ta yi hakan,don babu uwar da zata haifi ɗanta acikinta sannan kuma ta nuna bata ƙaunarsa,kin san dole aƙwai wata a ƙasa amman ba haka kawai bane".
Da sauri Hadiza ta ce"haba Umma ni yanxu me na yi mata?me na sani alokacin da ta rabu da mahaifina?ni dai nasan abinda yasa ta yi haka xafin mahaifina ne har yanxu bai goge aranta ba?amman kuma idan akayi duba ai ni banida wani laifi,kuma kamata ya yi ajanyo ni ajiki kuma in dinga ganin mahaifiyata akan lokaci shine zaisa in manta da baƙin cikin dana ke shaƙa acikin zuciyata".
"Haka ne Hadiza amman abinda nake so dake Hadiza ki dage da addu'ah,don ita addu'ah makamin mumuni ce Allah bazai taɓa taɓar da duk me yin addu'ah ba."
Hadiza ta ce"amma Umma. . . ."
Umma ta ce"amma me Hadiza?shin ni kinsan baƙin cikin dana shaƙa arayuwata?ni fa na taso ne na samu kai na a matsayin tsintacciya,ba'asan inda duk ƴan uwa na suke ba?sannan gidan dana zauna tun girma na har aure na ban samu wani farin cikin rayuwa ba,har na yi aure ma ban samu wani ƴan cin kai ba,ƙarshe ma ashe wani ƙasur gumin baƙin cikin na ƙara faɗowa?na samu ciki aka ƙwantar min dashi kusan shekara baƙwai sannan na haifi Noor,wani ƙarin baƙin cikin ma mijina babu ruwansa dani saɓanin ada da yake matuƙar sona tare da tarairayata,ashe ƊINYAR MAKAHO ya yimin wacce hausawa suke cewa ta nuna a hannunsa,ya nunamin so sosai ya nunamin matansa ba suda matsalar komai ashe dukkaninsu ba suda tsoron Allah,Hadiza ashe ke kinga na ki kaɗanne saboda ko babu komai kin san iyayenki sai wata ƙaddara ta gilma musu,to kinga anan addu'a ce kawai mafita."
Goge hawaye na nayi sannan na ce"haka ne Hadiza addu'ah ce abinda ya kamata ki riƙe,tabbas Hadiza Umma ta fi ki ganin rayuwa,wacce a kullum nake fatan Allah yasa itama tasan inda iyayenta suke ko taji ɗumin uwa da uba i'tama."
Dukkansu suka amsa min da amin.
*GIDAN SARAUTA*
. . . . .Fulanin Sura na fitowa daga sashen Sarki tayo ɓangarenta,zuciyarta sam babu daɗi a gameda abinda ya faru agidan Sarauta,anyiwa Sarki sata an ɗauke masa Taswirarsa wacce take ɗauke da komai na dukiyar Sarki,duk inda dukiyarsa take a faɗin duniya to tana cikin wannan Taswirar.
Tun daga kan hanya bayi ke tsugunna mata har ƙasa suna shimfiɗa mata gaisuwa amman ko ajikinta,bata ma ko kalli inda suke ba don ranta a jagule ya ke,don ita arayuwarta ta tsani taga Ran Sarki ya ɓaci don tana masifar sonshi,idan har ta ganshi acikin damuwa to tabbas itama tana cikin wani hali.
Tana shigowa sashenta ta tarar da Inaya a falo tana chart da wayarta tana sheƙa dariyarta.
Daka mata tsawa uwar ta yi sannan ta ce"wai ke Inaya yaushe zakiyi hankali ne?mu muna cen cikin tashin hankali amman ke kina nan babu abinda yasha miki kai?to tun wuri ma ki tashi daga kan wannan ɗan banzan chart ɗin,kuma nasan ba zai wuce da wannan ɗan banzan yaron kike ba."
Turo baki Inaya tayi sannan ta ce"haba Mom ni ina ruwana da wata taswira kuma?ni yanzu kinga kin katsemin chart ɗina me daɗi?don Allah Mom ki cirewa kanki tashin hankali mana?ke kullum idan masarautar nan ta shiga tashin hankali kema sai kin shiga?ni fa i'am tired for this".
Tana faɗar hakan ta shigewarta sashensu tana turo ƙofarta garam.
Sosai abin ya bawa uwar haushi ta ce"kai ni yanzu aduk cikin ƴaƴana babu wanda zan gayawa damuwa ta?ba ga masu auren ba,ba ga marasa auren ba?sai dai in zauna abu ya yi ta cin cikina".
Tana faɗar hakan ta shige ɗakinta tana rufo ƙofar don ta ɗan samu hutu.
Sosai gabanta ya yi wani irin mugun faɗuwa ganin wannan Taswirar da ake nema,ta dafe ƙirjinta tana fito da ficicin idanuwanta waje.
Hannunta na kakkarwa ta ɗauka tana ƙara dafw ƙirjinta,to waye ya kawo mata wannan Taswirar sashenta?me ya ke shirin faruwa da i'ta ne?.
A ta ke ta saki salati da ƙarfi tana kiran sunan "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".
Kukan ya ƙwace mata,wai me yasa duk irin wannan idan zata faru ta ɓangarenta ake samun matsala?duk wani sharri sai arasa wanda za'a ƙullowa sai ita?.
Da sauri ta tashi tana share hawayenta ta fara magana da ƙarfi tana ce wa.
"Ina!wallahi bazai yiwu ba,yadda aka ƙullamin wannan munafuncin wallahi nima sai na ƙullawa wata cikinsu."
Tana faɗar hakan ta cire kyakkyawar alkyabbarta ta fito,ta kalli ɗaya daga cikin kuyangunta wata me suna Ramma ta ce"Ramma zo inason ki kirawomin Magajiya yanzu,kice mata duk abinda take tazo ina son yin magana da i'ta".
Ramma ta amsa mata da "to"don tasan ita Fulanin Sura bata son jira ita ƴar war war ce.
Magajiya kuwa tana fita daga sashen Jakadiya sai ta wuce sashen Kilishi wato Uwar gidan Sarki Uwar sharri.
A babban Falonta ta same ta,bayi suna gefenta kowanne yana aikinsa Magajiya ta tsugunna ta ce"ranki ya daɗe Allah ya ƙara miki nisan ƙwana".
Kilishi tana jin haka tasan ce wa aikin da ta saka Magajiya ne ta aikata sa,don haka da hannu ta kori bayin na ta,ta hanyar ɗaga mata ƴan yatsunta biyu don wai ita aganinta Bayi basu isa ta ɗaga musu duka hannunta ba,hannun daya sha daƙwa daƙwan gwala gwalai da kuma zinare masu tsada.
"A'i ranki ya daɗe ai ki ya kammalu tuni na daɗe da aikata abinda kika saka ni".
Kallon ƙasa Kilishi ta yi mata sannan ta fara magana kamar bata so ta ce.
"Za ta kiraki yanzu don nasan halinta da mugun tsoro ga ta kuma da son miji kamar tattabara,kuma nasanta bata son jira ko kaɗan don haka inason ki nutsu kiji abinda zan gaya miki".
Ta faɗi hakan tana hararar magajiya.
Magajiya ta sunkuyar da kanta da sauri ta ɗaga hannu tana jinjina mata ta ce"a'i Uwar gijiyata babu abinda zaki sakani inƙi yi ko meye kuwa balle wannan ƙaramin aiki".
Cikin tsawa Kilishi ta ce"ke!Magajiya kada ki kawomin wasa anan,domin ba kiga wasa acikin idanuwa na ba,ni bana abu sai wanda yake da wahala shi nake zaɓa na yi,saboda nasan wanda na yi don shi sai yasha baƙin ciki wanda yafi wannan wahalar dana yi,don haka Magajiya ki gane ni fa bana abu sai yana da wahala".
Da sauri Magajiya ta ce"tu ba nake Uwar gijiyata za'a kiyaye gaba".
"To idan ta kiraki ta tambayeki inda zaki kai wannan takaddar kice mata akaita ɓangaren Fulanin Bare,kada ki sake ki canjamin wannan maganar,idan kuma ba haka ba ki tafi lahira lokacin zuwanki bai yi ba".
Da sauri Magajiya ta waro ƙananun idamuwanta waje sannan ta ce"ayimin afuwa Uwar gijiya ta,har yanzu banyi aure ba bare kuma na haihu na bar masu yi min addu'ah".
Ta faɗi hakan tana jan hawayen munafunci.
Kilishi ta daka mata tsawa sannan ta ce"yimin shiru uwar kuka,ba lokacin kuka bane yanzu lokacin aiki ne idan ba haka ba kuma asirinki ya tonu a masarautar nan".
da sauri Magajiya ta haɗiye damuwarta don tasan halin Kilishi ba tada mutunci ko kaɗan,kuma bata san darajar ɗan adam ba ko kaɗan ita dai kanta ta sani da kuma ƴaƴanta.
"Idan ta baki wannan takaddar kada ki yarda kowa ya gane abinda kika je ajjewa,idan kuma ba haka ba?to wallahi sai dai wani ba ke ba,don haka ki tashi ki fita cikin mutane don idan an tashi nemanki ba sai ansha wahala ba".
Da sauri Magajiya ta tashi har tana haɗa hanya,ta juyo muryar Kilishi tana ce wa"idan baki yi sauri zaki ga ne. ... . . ."
A'i da gudu Jakadiya ta arta don tana masifar tsoron Kilishi don tana jaddada rashin imaninta,duk da wani abun ma ba agabanta take yi ba.
Sai da kilishi taɗan dara dariya,duk da dariyar ba aƙidar ta bace ita kullum fuskarta a turɓune take kamar ta sha kunu.
Magajiya tana fita Fulanin usul ta shigo,wato me bin Kilishi kenan ita ce ta biyu ita Fulanin usul ita ce Fulani acikinsu,don ita ƴar uwar sarki ce ma don da babanta da baban Sarki Abdussalam ciki ɗaya suke,kuma rana ɗaya aka ɗaura aurensu dana Kilishi don ita Kilishi Ƴar waziri ce,ta na ce sai Sarki Abdussalam take so kuma a haka akayi auren shi Sarki baya sonta amman saboda biyayyar iyaye ya haƙura ya zauna da ita,gashi harda albarkar ƴaƴa goma,ita kuma Fulanin Usul itama itake son Sarki Abdussalam,kamar dai Kilishi don haka aka ɗaura masa aure dasu arana kuma ɗaya.
Sunyi kishi sosai a tsakaninsu,kiwaccensu na son ta haifi ɗa namiji amman sai gashi basu samu ba,ita Fulanin Usul ƴaƴanta taƙwas yanzu,tun suna son haifar ƴaƴa maza har ta haƙura saboda haka da aka auro musu ta uku wato Fulanin Sura sai suka haɗe mata kai,suka shiga makirci kala kala tasha faɗawa tarkonsu,amman banda tarkon asiri don ita Fulanin Sura bare bari ne mahaifinta shine sarkin bare bari,kuma suna hulɗa sosai da Sarki shine ke bawa Sarki Abdulsalam tsari saboda sarauta,a haka har ya bashi ƴarshi aure,da ya ke Sarki Abdusalam yasan halacci sai ya aure ta ɗin,Fulanin Sura mahaifinta ya bata tsari sosai tun kafin ta shigo cikin gidan Sarauta,don haka kuwa duk asirin dasu Fulanin Sura za suyi baya cinta.
Sai gashi itama Fulanin sura ta biyo sahunsu na haihuwar ƴaƴa mata,don sai da ta jera ƴaƴa mata biyar kuma daga ta biyar ɗin ta samu matsala a mahaifarta wanda sanadiyyar hakan aka cire ta,to kunga babu zancen haihuwa to fa tun daga haka sai hankalinsu ya ƙwanta.
Sai kuma wani tashin hankalin ya ƙara ziyartarsu.
Alokacin da mijinsu ya yi tafiya sai gashi ya dawo da dalleliyar amaryarsa,kuma balarabiya a wannan lokacin ba ƙaramin tashi hankalinsu ya yi ba,ganin muguwar kyakkyawa tare da mijinsu Fulanin Usul kuwa har ɗan ƙaramin hauka taso yi,da taga mijinta da zuƙeƙiya sai da tafi wata ɗaya ba tada lafiya ashe lokacin tana da shigar ciki ga kuma wani ƙaton baƙin cikin da taka ciki.
Ita kuwa Kilishi tana da muguwar dauriya sosai,amman duk da haka abin ya taɓa ta matuƙa don ita baki ɗaya ma dai na fitowa ta yi sam,ko da yaushe tana ɓangarenta idan ma ranar ita ce da ƙwana ƙin zuwa take sai tace wai ya bawa wata,don ita yanzu abinda ke ƙwaƙwalwarta kawai bai wuce yadda za taga bayan wannan balarabiyar ba,saboda a jikinta tana jin kamar ita ce za ta haifi Yarima,idan kuwa ta haifi Yarima sun shiga ukunsu saboda daman Sarki Abdussalam yana masifar son Zulaiha,ta tabbatar kuma idan har ta haifi ɗa namiji to sun riga da sun kaɗe har ganyensu,don tasan son da yake yi wa mahaifiyar ɗunguru gum kan Ɗan zai koma,sai su koma tamkar bayin gidan su da ƴaƴayensu.
Babu irin kitimirmirar da su Kilishi basa haɗawa Fulanin bare,wato mahaifiyar Yazeed amman sai dai kash!bai cika yin tasiri ba,saboda ita Ba mutum ce me shiga sabgar mutane ba,wani lokacin ma sai tayi wata biyu ko fin haka ma baka ganta ba,indai ba a fadar sarki ba don Sarki wani lokacin yakan haɗa kan matayensa don ayi hira.wani lokacin ma don Zulaiha yake yin taron saboda ya fuskanci sam har yanzu bata saki jikinta ba.
Abinda ya ƙara mugun tasar musu da hankali bai wuce yadda suka ga Fulanin bare da ciki ba,saboda duk ƴan gulmar da suke turawa ce musu suke a'i Ba tada ciki,saboda i'ta Sarauniya Zulaiha ko da yaushe acikin doguwar riga take,irin tasu ta larabawa me kama da alkyabba,kuma gashi cikin fari ba kowa ne yake ganewa ba.
A sanda suka lura da wannan cikin ba'afi sati ɗaya ba,Fulanin Bare ta haihu kuma gashi wasu binne binnen ma basu gama yi ba,sai sukaji haihuwar da tayi matuƙar girgiza tunaninsu da ƙwanyarsu,alokacin kuma Fulanin Usul ta haihu bai fi da sati biyu ba,sai ya kasance kuma ba tada lafiya don alokacin wani asiri da suka amso don yi wa Fulanin Bare sai Fulanin Usul ta manta maimakon ta binne sai ta jefar ya koma kanta,to shine take ta fama da ciwo ga kuma tashin hankalin haihuwar Ɗa namiji magajin Sarki da akayi. . . . . . . . . .✍🏿
*Hmm lallai ana wata ga wata agidan Sarauta,ni Miss green na ce gwara da Allah yasa ba agidan Sarauta aka haife ni da banu.🫣ko