Header Ads
Showing 39001 words to 42000 words out of 46793 words

Chapter 14 - DINYAR MAKAHO Book 1 Complete Document by Ummu Maheer Miss Green txt

Ads the beginning of article before Image

10 Jun 2024

547

Ads at the middle of Article

ciki.


Ana haka ta haihu lafiya,sanda mahaifiyata tazo komawa gidanmu na yi kuka sosai,saboda bana son ta dawo gidan ƴar jiya,ammsn mahaifiyata tana masifar son mahaifina shiyasa duk abinda zaiyi mata ba ta gani.
Wannan komawa da mahaifiyata ta tayi shine sanadiyyar rugujewar rayuwarta baki ɗaya."


Yana faɗat hakan ya fashe da kuka sosai.


Dukkanmu sai da muka tausaya masa dukkanmu hawaye ya jiƙa mana fuska,a hankali cikin sanyi na ce"Allah sarki ya sayyadi tun kafin ma ka gama na yarda rayuwarka tafi tawa muni".


kallona ya yi sannan ya ce"Noor ai har yanzu bakiji komai ba,dangane da rashin imanin mahaifina ba ki bari in gama to ananne zakiji zallar rashin imani."


Shiru na yi ina kallonsa don ban san wani irin rashin imani bane?bayan wannan muguntar da yake mata ba.
ya cigaba da ce wa"bayan mahaifiyata ta dawo mahaifina bai dai na dukkanin abinda yake ba,rana tsaka mahaifina ya ɗauki mahaifiyata zuwa asibiti wai zasuje ganin likita,Inna lillahi wa inna laihi raji'un Noor mahaifina ya siyarwa da mahaifiyata oder ɗinta guda ɗaya."


Sosai na fito da idanuwa na dukka waje,Umma da Hadiza suma dukka idanuwan na su awaje suke suna kallon ikon Allah.


"tabbas nasan zakuyi mamaki,mahaifina ashe yaudarar mahaifiyata ya yi ashe yana yi wa wani mutumi aiki a asibiti,yana kawo masa mutane su siyar da tasu,sai akayi akasi ba a samu ba daya rasa ta wanda zai bayar sai ya bayar da ta mahaifiyarmu silar hakan yasa mahaifiyarmu ta fara ciwo sosai,wanda daga farko ba a gane matsalar ba sai da akaje asibiti sannan likitoci suka bada shaidar ce wa an cire mata oder ɗinta guda ɗaya ne.


Sosai abin ya girgiza danginta dama ni kai na ɗanta,don alokacin Surayya ba tada wani wayo don bata fi shekara biyu ba ni kuma ina da shekara 14,ƴan uwan mahaifiyata sunyi yunƙurin kai mahaifina ƙara amman mahaifiyata ta hana yin hakan.


Munsha wahala sosai a lalurar mahaifiyata daga baya Allah ya amshi rayuwarta."
yana faɗar hakan ya fashe da kuka me tsananin gaske.


Sosai muma muke kuka ni da Hadiza,har Umma wacce ƙwance sai dai kaga hawaye na fitowa daga cikin idanuwanta abin tausayi.


Ina kukan na ce"to yanzu ya sayyadi ina mahaifin na ka?"


ɗan girgiza kai sukayi idanuwansa sunyi jawur sosai alamar baya son jin zancen mahaifin na sa.


Sai na jiyo muryarsa yana ce wa"Allahu akbar tun wannan ƙarnin da mahaifiyata ta rasu sai muka nemasa muka rasa,muma baya gabanmu don haka muma bamu ƙara nemansa ba,muka bar garin muka dawo asalin inda ƴan uwan mahaifiyarmu suke wato kano nan unguwar sheka."


Sosai abin ya ɗaure min kai na kuma jaddada rashin imani irin na rashin tausayin mahaifin Aliyu,duk rashin tausayin mahaifina dana ke gani ashe aƙwai ƙasurgumai waɗanda suka tattaka mahaifin na wa.


Ranar har ya sayyadi ya tafi duk jikinmu asanyaye ya ke,sai dai dare yana yi bayan Hadiza ta tafi gida sai ga yaya Ahmad.


Ina ƙwance sai dana tashi,ganin yaya Ahmad ya yi wani irin masifar kyau na ce "wow"amman fa acikin zuciyata don nasan har kun zaro ido don ganin zaƙewa ta.


Shaddarsa yasha bugaggiya kalar dark blue,kasancewarsa fari sai shaddar tayi mugun amsarsa,ya kafa hularsa zanna bukar wacce ta yi matuƙar dacewa da kayansa,na saki wani irin murmushi ina ɓoye fuskata.


Ya gane kunyarsa nake ji don haka ya ce"my Noor yau kuma kunyata akeji haka?da sauri na sunkuyar da kaina,ɗan murmushi kawai ya yi yana ɗaya daga cikin abinda yasa yake masifar son yarinyar,saboda duk ƴa macen da ta rasa kunya to fa ta rasa ma da fa babba arayuwarta.


Gaishe da Umma ya yi wacce ke ta mana dariya,ya kalli agogonsa wanda ya yi matuƙar haɗuwa ya ƙwanta sosai a farin hannunsa,azuciyata na ce"oh Yaya Ahmad ba dai gayu ba."?


Ina cikin tunanin naji ya ce"to uwar kunya ba daɗewa zanyi ba,kuma daman wajen Ummana nazo ba wajen Noor ba".


Ɗan turo bakina na yi dai naji yana dariya yana cewa"oh daman ƙwanwar nan tawa ta iya tsiwa"?.


dariya Umma tayi sannan ta ce"hmm ai wannan da kake ganinta tana ƙarama ai har dambe takeyi da maza,babu ruwanta tayi musu rashin kunya kuma ta tsaya don ƙarfin zuciya tace zata zane su,ƙarshe sai dai taci duka tunda dai daman bakinne kawai da ita babu ƙarfin sai tsiwar tsiya".


Sosai Yaya Ahmad ke dariya sannan ya ce"inye ka ga Kande uwar maza?ashe har da ƙatti kike faɗa?a to bari inyi a hankali tunda dai yanzu da ƴar caskale nake zaune".?


Sosai na fara kuka wiwi,na ƙwashemin baya da Umma ta yi,kuka nake sosai ina ƴan tirje tirje tamkar ƴar ƙaramar yarinya.


Shi kuwa Ahmad dariya yake,daman haka yake so yasa mutuniyar tasa kuka don yana masifar son shagwaɓa arayuwarsa.


Sai da Umma tayi min jan ido sannan na dai na kukan,na juya musu baya wai ni nayi fushi,Yaya Ahmad ya shiga rarrashi na ammsn da yake ni ba ƴar haɗin kai ba ce sai na fice daga ɗakin.


Anzo wajen!daman Ahmad so yake mutuniyar ta sa ta fita,ya yi maganar da ta kawosa wajen Umma.


Don haka ya kalli Umma sannan ya ce"Umma ki yimin gafara,don Allah ina neman wata alfarma awajenki?".


Ɗan murmushi Umma ta yi,don tun kafin ya faɗa tasan menene,don haka ta ce"ayya Ahmad ka faɗi ko menene ai kai mutum ne me kirki kuma ɗan albarka indai bai fi ƙarfi na ba zan maka".


Ahmad ya sunkuyar da kansa sannan ya ce"Umma don Allah don annabi ki bani Noor,wallahi ina masifar sonta har cikin zuciyata,ina kuma ƙaunarta don Allah Umma ki bani ita".?


Ya faɗi hakan yana tsugunnawa agaban Umma tamkar me neman gafara.
Umma ta ce"haba Ahmad ka tashi mana,akan mace ka dinga tsugunna min?macen ma kuma ƴa ta?a'i kasan babu abinda zaka nema awaje na in kasa ba ka shi,in dai Noor ce na baka ita amman yana da kyau ka tuntuɓi mahaifinta duk abinda ya ce to ni bani da ja akan hakan,sannan kuma ka nemi amincewar Noor idan har ta amince maka to tabbas Noor ta zama ta ka".


Ɗan murmushin jin daɗi ya yi,don yasan indai ta ɓangaren Noor ne ba shida matsala don tuni har sun ƙulla alaƙarsu a ɓoye don haka ba kowa ne yasan da hakan ba.


Ahmad ya ce"Umma na gode sosai da kulawa Allah ubangiji ya ƙara miki lafiya,kuma insha Allah zan gayawa Hajiyata da kuma ƙanin mahaifina duk yadda mukayi,daga bisani sai aturo nan wajen Baba ayi maganar".


Ɗan murmushin jin daɗi Umma ta yi,don bata shakku ko kaɗan akan Ahmad don tasan ba zai taɓa cutar mata da Noor ɗinta ba ko da kuwa bayan ranta ne.


Bayan sunyi sallama da umma yana fitowa yaga Noor a bakin ƙofar ɗakin,ita da wata mata sai hira suke abin ya bashi mamaki sosai don bai ɗauka Noor ta iya labari haka ba.


Daga bayanta taji ana magana Ahmad ya ce"to sannu uwar surutu aku me magana"?.


Da sauri Noor ta yi ɗaki tana dariya cike da kunyarsa.





Bayan Ahmad ya koma gida ya faɗawa Hajiyarsa duk halin da ake ciki,Hajiyarsa ta ce"kai masha Allah naji daɗi sosai da wannan maganar da kazo min da ita,yarinyar arziƙi me son mutane haka ma mahafiyarta Allah dai yasa muga wannan rana".


"Amin".


Ahmad ya ce yana fito da wata dalleliyar sabuwar waya dal aƙwalinta,ya ce"Hajiyata wannan wayar ta yi kyau kuwa"?.


Murmushi ta yi sannan ta ce"kai amman ta yi kyau wallahi,kamar shigen wayar da ka siyowa Zaliha ko"?.


Murmushi ya yi sannan ya ce"eh Umma duk iri ɗaya ce wayar kawai dai design ne ba ɗaya ba,Daman Noor nake son bawa wannan wayar kinga yanzu zasuyi wannan tafiyar kuma kinga idan babu waya babu yadda za ayi mu dinga gaisawa,duk da farko tare zamuje amman inason yau ba sai gobe ba zan tambayi mahaifinta akan wannan tafiyar don inji me zai ce"?.


Hajiya ta ce"eh haka ne Ahmad yana da kyau ka tambaya ɗin ka ga sai muji ko?"




Har wajen sana'ar mahaifina Ahmad yaje,wato sana'ar zamam majalissa wacce ke gefen layinmu don mahaifina baya sana ar komai yanzu sai dai sana'ar zaman majalissa.


Ko daya samesa shi kaɗai ne awajen,babu kowa masu sana'a duk dun tafi ƴan malaman makaranta ma duk sun tafi,sai mahaifina shi kaɗai ne ba shida sana'ar kansa.


Kai tsaye ya amsawa Ahmad buƙatar daya zo da ita,sannan ya ce"kawai ya turo don ganin kuɗi tingis a hannunsa don rabonda ya riƙe wasu kuɗi masu kauri tun zamanin kasuwancinsa.


Kai tsaye yana dawowa gida ɗakin Saude ya nufa.


Fatima ƴar wajen Inna Hafsatu na ganin aljihun Babansu acike ta yi wuf ta faɗa ɗakin mahaifiyarta,wadda ta sameta tana ƙwaɗawa ƙannenta tuwo da manja da yaji.


Jikin Fatima na tsuma ta fara maganar kamar haka.


"Inna wallahi ki tashi ma ki bar wannan ƙwaɗon,ga Baba cen na ga ya shigo ya yi ɗakin Inna Saude da sauri kuma wallahi kamar kuɗi na gano maƙudai".


Banza tayi da Fatima daman yanxu suka gama faɗa wai akan taƙi ɗaukar talla,wai ita yanzu ta girma don haka ba za tayi talla ba.


Ganin mahaifiyarta tayi shiru yasa ta ce"to shikkenan Inna wallahi Inna Saude ita kaɗai zata cinye kuɗin,don kinsanta da haɗama da baba kere da kuma cin rabon mutane."


Jin hakan yasa Inna Hafsatu juyowa sannan ta tashi ta fita,kai tsaye ta laɓe a labulen ɗakin sai taji Inna Saude na ce wa.


"A'i kuwa wallahi ko zanyi yawo tsirara bazan bari wannan yarinyar tayi aure tabar ƴaƴa na wata ƙwaila da ita,kuma naga har yanzu ko sha shida bata rufe ba,gani da ƴaƴa ye masu shekara talatin waɗanda ke gaba na muna jerawa,yo ba gwara yazo in masa gwanjon wata a cikinsu ba?to wallahi tun wuri ma ka gaya masa baza ka basa ƴarka ba,yazo nan gasu nan ya zaɓa ko ƴaƴan Hafsatu ban yarda ya zaɓi wasu ciki ba,don ita na ta tana samu ta aurar dasu ko da kuwa a ƙauye ne amman ni nawa a ƙauyen ma sun kasa shiga kamar waɗanda aka yiwa asiri ko kuma baki".?


Shiru mahaifina ya yi,tamkar wata uwarsa haka yake nutsuwa idan tana magana ko uwarsa dake Niger Lanta baya mata biyayya kamar yadda yakewa Saude.


Warce kuɗin hannun Mijin na ta tayi sannan ta ce"bani kuɗin nan bazan bar maka su a hannunka ba,kaje ka rabawa ƴan zaman majalissa ba bani su aƙwai abinyi akansu,saura kuma ka gayawa Hafsatu don babu ubanda zai ci kuɗinnan sai ni da ƴaƴa na."


Ta fai hakan tana irga kuɗin,dubu hamsin ne cif cif tana ayyanawa aranta wannan kuɗin,kyauta ma ya bawa mijinta ina ga kuɗin aure ma?ai wallahi baxa ta yarda ya auri Noor ba,don tasan idan ya aure ta ai ta huta ita da uwarta wacce ta tsana kamar mutuwarta,tabbas da za'a bata bindiga to kai tsaye sai ta kashe Fatima wato mahaifiyar Noor don yadda ta yi mata muguwar tsana.








Da gudu Inna Hafsatu ta shige ɗakin,ta wafto kuɗin da sauri tana watsa mata wasu ta ƙwashi rabonta sannan ta ce"wallahi ke dai Saude kinyi asarar rayuwarki,ko da yake daman bakin uwa na kanki sai dai ace Allah ya shiryar dake,kuma baki isa ki hana auren Noor da wannan yaron ba,muguwa kawai me baƙar aniya insha Allah ƙarshenki ba zaiyi kyau ba."


Tana faɗar hakan ta fice don ta ɗibi rabonta,abinda ta ɗauka ma yafi dubu ashirin don sun tasamma dubu talatin.


A'i kuwa Inna Saude sai ta haukace tana zage zage,tayo hanyar ɗakin Inna Hafsatu wai za ta amshi kuɗinta.




Inna Hafsatu irin ƙarfafan matan nanne don haka ta ce"wallahi tallahi kika shigomin ɗaki wallahi sai na karyaki na karya banza".


Inna Saude kuwa irin matan nanne sirara babu tsayi babu ƙiba saboda sabar saka masifa aransu sai kiga duk sun zama abin tausayi.


Zagi dai Inna Hafsatu ta sashi,don har uwarta dake kabari sai da ta zaga akan kuɗin da ta ɗauke mata.


Amman fa sai dai xagin babu kataɓus,don sunsha dambe ita da Inna Hafsatu kuma tasan halinta ba tada imani ko kaɗan,don tsaf za ta zaune akanta daman ga ta duk ƙashi.




Hmm mata mu gane wani abu guda ɗaya,ba wai cin abinci ke sa ƙiba ba wallahi ƙwanciyar hankaline,idan har kila zamo masifaffiya jarababbiya wallahi bazaki taɓa yin ƙiba ba sai dai ki yi ta tsotsewa ki zama taɓarya a shiga ɗaura miki zani.


Ranar dai anyi ruwan masifa agidan Mlm Isma'il,sau biyu Inna Saude na neman ta faɗa ɗakin Inna Hafsatu wai sai ta ɗakko kuɗinta,ita kuma Inna Hafsatu sai ta biyo ta da gudu,ta falfala da gudun tsiya ta ɓuya bayan Mlm Isma'il,don duk abinda suke yana kallonsu don shi ba mutum ne me faɗa ba,sai kuma abin ya haɗu da asiri sai ya zama Salamatu don kome zasuyi a gabansa bai iya magana sai dai ya yi tagumi yana kallonsu,ko kuma ya yi gaba abinsa zuwa zaman banza majalisa.
******


washe gari aka sallamemu daga asibiti,Ahmad yazo yau ma ya yi kyaunsa cikin farin yadin boyel me masifar kyau,irin me ɗan sharashara ɗinnan me adon siga siga kana ganinsa kasn me tsada ne don ba kowa zai sa irinsa.


Fatarsa ta ƙwanta sosai alamar tana samun gyara yadda ya kamata.

Kuma kafin yazo Umma ta yi min bayanin komai,kunya ta isheni na tabbatar lallai Ahmd ba shida kunya ashe har ya samu Umma da maganar?shiyasa ko da yazo yanzu na hau ɓoye fuska ta saboda nasan abin ai da kunya.


Sabuwar waya fil ya bani me masifar kyau,sosai nake juyata a hannuna saboda mamakin wai yau ni ce da waya haka?wacce ko a mafarki ban taɓa tunanin samunta ba?.


Da kansa ya zauna ya fara koyamin komai duk yadda zanyi.


Umma ma ta taya ni gode masa,da kansa ya ɗakkomu ya dawo damu gida ya tsaya ya siyi mana kayan abinci sosai komai sai da ya siya mana,muna ta yi mai godiya don Ahmad mutunne me mutunci.
A ƙofar gida muka tarar da majalisar su Babanmu,na kalleshi sosai ya ƙara zuƙewa sai fari da hanci da kuma idanuwa.


Azuciyata na ce"Hmm tashin hankali ma a'i ba zai bar mutum ya yi ƙiba ba,don Babanmu yana cikin wani hali sosai sai dai ayimai fatan samun lfy.


Ace ƴar ka ta ƙwanta a sibiti amman ka kasa zuwa ko da duba ta?a'i ko da matanka basu je ba a'i kai kaje ko?.


Har ƙasa na tsugunna na gaishesu sannan ni da Ahmad muka riƙo Umma muka shigo da ita gidan.


Mahaifina sai kallonmu yake tamkar wasu baƙi,kai tsaye muka shiga gidan,ɗakin mahaifiyata a hangame kamar ma sun shiga ɗakin,don gashinan duk an bincika kayan ɗakin.


Rai na ya sosu sosai,na kawar da kai don ko gaishe dasu Inna Saude dake tsakar gida banyi ba,don da alama ba a zaman lfy agidan don na ga kowa harkarsa yake,Ita Inna Hafsatu tana zaune da ƴaƴanta suna tsince shinkafa,ita kuma Inna Saude sun ƙure Radio suna jin garaya ita dasu Halima da Aisha guzumayen ƴaƴanta.


Don Halima shekararta talatin da biyu,ita kuma Aisha talatin cif cif sai dai kullum kaga sun tara taron yara ƴan iska,don ba auren ke kawosu ba zuwa suke don su ƙwashi rabonsu suyi gaba.


Aishar ce ma ta kula da shigowarmu don ni kaɗaice yanzu Ahmad iya soro ya tsaya,na goyo Umma na abaya har zuwa ɗakinta,sai kuwa Aishar ta ce.


"Inye ikon Allah,Ah lallai kin ƙaro wulaƙanci ƴar nan?au yanzu ko sallama babu haka zaki shigo mana gida da wata guzumar uwarki me mataccen jiki ashine zaki shigo mana gida?saboda yanzu kina ganin kanki ɗaya da kowa tunda me kuɗi na sonki?".


Ban kula ta ba,har sai dana dangana da ɗakin namu,na ƙwantar da Umma a hankali na ɗan karkaɗe wajen sannan na fito zuwa wajen Ahmad wanda ke soro.


Kallon gidanmu kawai yake har rufin ɗakin,yana mamakin yadda akayi gida ƙato gashi har yana son faɗuwa?ina zuwa na kallesa ina murmushi sannan na ce"yaya lafiya kuwa"?.


Murmushi ya yi sannan ya ce"a'ah babu komai wallahi ya Umman?".


Na ce"lafiyarta klau".


Hannu ya saka acikin aljihunsa ya ciro wata farar ta kadda,wacce ke manne ba zaka gane abinda ke cikinta ba?.


Ya miƙomin na amsa ina ɗan dubawa.


"Aishatu Noor ki kaiwa Umma kice inji ni,kuma tafiyarmu dai kin san jibi ne?don haka sai a fara shiri ko?munyi maganar da Baba."


Nan dai muka cigaba da ƴar hira,ban wani daɗe ba na dawo na yiwa Umma murmushi sannan na fara gyara ɗakin,na gyara ɗakin tsaf tsaf don daman ɗakin babu komai siminti ne kawai sai wata ƴar yaloluwar katifa don itama katifar wan Umma ne ya bata ta gidansa da ta lalace don da ita muke ɗan maneji".





A ranar Umma ta takuramin sai dana je gidansu,ma'ana gidan da aka riƙeta don bawan Allahn daya tsinceta Allah ya yi masa rasuwa sai matarsa yanzu kuma ra ɗan tsufa,sai dai har yanzu ba ta son Umma na ko kaɗan,Umma ke matsamin zuwa wajenta amman na tsani zuwa tunda ba ta son Umma na.


Kai tsaye gidan na ta na yi,gida an gyarasa ya yu tsaf tunda yanzu ɗanta ya yi kuɗi,amman sam baya taimakawa Umma na ɗan kuɗin daya ke biya na makaranta kullum naje sai an gama cin zarafina sannan za'a bani shi,Allah sarki duniya zumuncin yanzu ya yi ƙaranci sai kaga ɗan uwanka uwa ɗaya uba ɗaya amman baya taimakonka sai dai ƴaƴansu da kuma matayensu.


A babban falonta na samesu ita da jikokinta,amman ƴan ƙananan tana haɗa musu kayansu da alama ma gida zasu koma.?


Ko dana gaisheta bata amsa ba,balle ma ta ɗago idanuwanta ta kalleni sai naji duk rai na ya ɓaci.


Amman sai na tuno da nasihar da Umma ke yimin a kullum,musamman ma idan za ta aikoni gudan nasu takan cemin,Noor ita rayuwarnan haƙuri akeyi ko Allahn daya haliccemu haƙuri yake damu,badon haƙuri ba da tuni an taɓar damu saboda yawan saɓon da muke dashi.


Kai tsaye na fara gaya mata abinda ya kawoni,akan tafiyarmu ƙasar Masar da zamuyi.



Sai alokacin ta ɗago idanu tana kallona sosai har taso ma ta ɗan bani tsoro. . . . . .✍🏿
Sai naji tana ce wa"ke ni sa'ar wasanki ce da zaki dinga gaya min zancen banza?uban wa uwar taki take dashi da zai kaita har Masar"?.


Bance mata

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads