Header Ads
Showing 1 words to 3000 words out of 42022 words

Chapter 1 - BAKIN GIDA BY FATIMA SULEIMAN UMAR.txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

BAKIN GIDA
STORY AND WRITING
by
FATEEMAH S UMAR





ALHADULILAH mun kamala axumi lafiya cikin kushin lafiya Allah ya karbi ibadummu ameen
HAPPY SALLAH TO ALL MUSILIM






Munyi nasarar kamala *KANWAR* *MATATA* lafiya kuma yauma gamu da sabun labari *BAKIN* *GIDA* yadda muka fara lafiya Allah yasa mu gama lafiya ameen






*PAGE* 1-2



.............📖Yana kwance a kan bed idanuwanshi a rufe kamar me bacci amma a xahirin gaskiya ba bacci yakeyi ba tunani halayya irin ta family d'insu yakeyi kwata-kwata basuda halaya ta kware d'ai-d'ai nai a cikinsu na xabe daga barayi sai masu shaye-shaye sai masu bin mata da uwa uba sab'awa iyaye






yayi nisa cikin tinani aka murda kufar dakin aka shigo
wani saurayine ya shigo da baxai huce she karun na kwancenba
karasuwa yayi ya xauna a gefan bed d'in yana kalon na kwancen ahankali ya furta " *ALIYU* nasan ba bacci ka keyiba katashi magana xamuyi"






a hankali *ALIYU* ya bude idonshi ya kali saurayin yace "banasun damuwa yanxu xaka iya fita in na fito mayi magana" murmushi saurayin yayi ce " *ALIYU* be kamata dan wasu daga cikinmu basuda halaye masu kyau ka hadamu karinga fushi damuba kar ka manta kaimafa kana aikata ......"






tsawarda *ALIYU* yayi mishi ce yasa shi had'iye sauran maganar shi yace "Sameer kafice min a room tun ban sauya maka kamanni ba" sanin halin *ALIYU* na zuciya kuma xai iya yimishi ilah yasa yamike ya fece daga room din tsaki *ALIYU* yaja ya kuma ya kwanta yana maida nunfashi a hankali
da haka har bacci barawo ya sace shi






xaune suke a parlour sunata hira suna shewa da tafi dukansu yammatane kuma she karunsu ba xai huce 16-17-18-19 ba in ka gansu duk suna yanayin kama amma fa daya daga cikinsu da bata kaisu haske ba ta d'an banbanta a cikinsu








dukansu fararene dogaye irin siraran nanne kamar ka hure itakuba fa fara bace kuma ba baka bace tanada hanci ga idanu da suka fi ko mai kyau a face d'inta bakinta ba babba bane kuma red ne kamar tasa janbaki batada tsayi sosai tanada kauri daga kasa daga sama kuma siri riyace








duk hirar da suke suna shewa ita hankalinta baya gurin tana ma rike da wani english novel tana karantawa
haka Allah ya halici *FATEEMAH* bata kaunar hayaniya ko kad'an in ma sun xu kusa da ita sunayi bata samusu baki








wata daga cikin yammatan ce ta kaleta tace " gaskiya *DEEDEE* (da haka suke kiranta a gidan) kina mana yawa ke kinki wayewa arayuwar duniya kowa fa yanxu tsula tsiyarshi yake yi ko su su baban sunafa hulewa saike xaki dorawa kanki aiki danma yau fa ba'a dauko carbi ba Alkur'ani sai kace wata yar malamai yarinya ki wataya in xaki wataya lokacine watarana bayi zamuyi ba" wata daga ciki ce ta kara cabewa da "da ki rabu da ita Zakeeya dan wan-nan d'od'i minal lid'i wa innahu d'ufd'uf d'in baxata taba ganewa ba"








dariya sukasa gaba daya harda tafawa
wata daga ciki me suna Hafsat tace "kunga tunda bata dara'ayi ku rabu da ita ana dulene" Zakeeya ce ta kaleta tace "aidama bakinku daya da ita" "eh naji d'in baki mu daya"








haka suka cigaba da haya niyarsu itadai *FATEEMAH* ko kai bata d'aga ta kalesuba da taji hayaniyar ma tai mata yawa mikewa tayi ta bar musu parlour








kai tsaye dakin Ammi ta shiga ta tadda ita tana kan dadduma tana jan carbi daga gani yanxu ta idar da salah






book d'in hannunta ta ajiye ta nufi toilet tayo alwala ta fito dama da hijab d'inta kawai saita dako dadduma ta tadda salah
bayan ta idar ne ta yi addu'o'i ta shafa san-nan ta kali Ammi da har yanxu laximi take tace "Ammi barka da rana" da kai ta amsa mata san-nan ta daga hannu tai yi addu'o'i suka shafa tare sannan ta kali Deedee tace " *FATEEMAH* a kulum ina kara yi miki nasiha akan ki rike mutuncinki ke marainiyace baki da gata sai Allah kar ki sake kibar kud'i ko wani adoh ya rudeki ki xubar da mutuncinki karki la akari da yadda yan uwanki suke rayuwa ta y'an k'arya sufa duddumin su da kalo kar ki bari lattatun samarin gidannan suyi galaba a kanki kar kiyi la akari da y'an uwana ne iyayensu to fa yanxu kowa nashi yasani dan bayan y'ay'ansu xasubi dan haka tun dare be mikiba kisan me kikeyi *FATEEMAH*"








kaita a kasa batare da ta dagoba tace "insha Allah Ammi xan xama me kiyaye du ko kin ubangiji kuma xan rike mutuncin kaina" murmushi Ammi tayi ta shafa kanta tace "Allah yai miki albarka *FATEEMAH*" "ameen Ammina" ta bad'a tana kwantawa akan Ammi
dariya Ammi tayi tace "to mage uwar san jiki ni dagani" dariya Deedee tayi kawai batare da ta d'aga taba saima gyara kwamciya da tayi
haka suka ci gaba da hirarsu irinta y'a da uwa








*ALIYU* betashi ba sai da aka fara kiran salar axahar mikewa yayi ya shiga toilet yayi wanka ya dauro alwala yayi salah shi a daki dan har an idar da salah a masalaci
kuma d'abi arsace indai yayi bacci sai yayi wanka dan inwataran yayi na jin dadi wataran na tsarki yakeyi shiyasama yariga yaxamar mishi jiki








fitowa yayi daga part d'insu na maxan gidan yannu fi nasu dan yasamu yasha ko tea ne dan bayaji xai iya cin abunci yanxu
yana shiga ya tadda Usman yanata kalo a tv ko kalonshi beyiba ya huce kitchin ya had'o tea d'inshi ya dawo








xama yayi a daya daga cikin kujeron parlour ya fara shan tea d'in a hankali
*FATEEMAH* ce ta fito daga d'akin Ammi xata kitchin da sauri Usman ya kira sunanta "Deedee" "na'am" ta amsa batare da ta karaso ba
murmushi yayi ganinta yau ba hijab yace "ki xo mana ko ni xan karaso" kafa ta jawo a hankali dan duk a takure take ba hijab a jikinta






can d'an nesa dashi ta tsugounna ya kaleta yana murmushi yace "Deedee me xan samune yau" daburcewa tayi tarasa me xata ce mishi dan ita bata gane meyake nufi bama
shima hakanta ke dan fad'a kawai yayi dan ta jima a gurin yaji dad'i kare mata kalo aikuwa kalon nata yake ko kiftawa bayayi kuma abu daya yafi kurawa ido wato k'irjinta wanda rabinsu a waje yake








*ALIYU* ne ya juyu ya kalesu sai yaga irin kalon da Usman ke mata itakuma kanta yana k'asa batasan yanayi ba
wata uwar tsawa ya daka mata wadda tasata saurin mikewa batare da tayi niyya ba bai mata magana ba sai nuna mata hanyar bedroom da yayi ba musu tabar gurin da hanxari








kalonshi ya maida kan Usman wanda shima shi yake kalo harara ya hurga mishi wadda tasa shi dauke kai da sauri duk da Usman ne babba amma yana mugun tsoran *ALIYU* dan yasan yafi karfinsa kuma ko a jikima yafishi
da hannu *ALIYU* ya nuna mai ko far fita kalon mamaki yayi mishi wai kaninsa yaringa bashi umarni ganin yadda *ALIYU* yake hucine yasa shi ............!






wasa farin girki yanxu aka fara my fan's
yau ruwan comment kawai nakeso na gani










*PAGE* 3-4






...............📖Mik'ewa ya fice dan yasan hali xuciyar Aliyu xai iya dukanshi ma ayadda yake hucinnan


tsaki Aliyu ya ja shi yanxu a duniyarnan ba abunda ya tsana ka mar wan-nan *BAƘIN GIDA* nasu da ba komai a cikinsa saitaro jahilan mutane da dak'ik'ai wadda ba suda abunyi sai sab'awa ma halicin su kawai duniya ce a gabansu ba abunda yafi bashi haushi irin rashi jituwa na iyayensu wadda ya shafa harda y'ay'ansu da matansu ga maganar gado da kulum tak'i karewa
haka ya karaci tunaninsa bai samu mafitaba saima mikewa da yayi yabar gidan gaba d'aya






a b'an garen Deedee kuwa tunda Aliyu yayi mata wan-nan tsawar kanta yake sarawa sabuda ita Deedee tsawa tana cikin abunda in taji hankalinta xai iya gushewa na hucin gadi lallab'awa tayi ta hau kan bed ta kwanta ta runtse ido amma sai takeji kamar yanxuma ake tsawar a kunnan ta hannu tasa ta toshe kunan ta amma bata dai najiba kawai saitasa kuka me sauti






duk abunda takeyi Ammi na kalonta batai magana ba sabuda itama daga nan taji tsawar Aliyu kuma tasan *FATEEMAH* koya taji tsawa akwai matsala har suma ta tab'ayi sabuda tsawar da Aliyu ya duka mata ta shiga dakinsa dau ko cup ya ganta a ciki yai mata tsawa da tasa ta sume mishi amma duk da haka Aliyu baidai nayi mata tsawa ba






tashi tayi ta karasa kan bed d'in taga yadda jikin *FATEEMAH* ke rawa ga xafi da ya dauka kamar garwashi ajiyar xuciya ta sauke ta matso dai-dai kanta tafara tufa mata addu'i'o
ahankali kuma ta fara sauke ajiyar xuciya jikin nata ya rage rawa amma haryanxu xau yake dumi xaxxab'i me xafi ya rufeta tana sauke ajiyar xuciya da haka har bacci yayi awon gaba da ita
blanket Ammi taja mata ta rufeta a xuciyarta tana addu'ar Allah ya dubi wan-nan d'iyar tata ya rabata da sharri ma gauta kuma ha tsareta da ga hannu y'ay'an gidannan masu takurawa rayuwarta






samarine sunkai su 5 a parlour su na maxan gidan a xaune ba abunda yake tashi sai sautin kid'a suncika gidan da garar kid'a






3 rawa suke sosai hankali kwance daya yana saune a k'asan center carpet yasa kwalabe a gaba yana ta d'ad'ika






*ANNUR* dake xaune a kan kujera ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya ya kurawa phone d'inshi ido kana ganinshi kasan ba abun kirki yake kalaba sabuda yadda idonshi yai mugun yin red ga jikinshi da ya fara rawa-rawa






daya daga cikin masu rawarne ya kaleshi yayi murmushi yakuma kusadashi ya leka phone d'in yaga abunda yake kalo ya girgixa kai yaxauna yana cewa " *ANNUR* karaba kanka da kalon irin wan-nan abu buwan abanxa xasu haifarma matsala uwa uba kuma idonka xai iya makance wa dan haka kaiwa kanka fad'a tun dare bemaba"








red eyes d'inshi ya d'ago ya kaleshi yace "Sameer baruwanka da harkata kowa iskancinshi yake sonranshi kaima ba asan abunda kakeyi a bayan idon muba daga kai har wan-nan me fuskar shanun" dariya Sameer yayi yace "au *ALIYU* ne me fuskar shanu" "eh ko tsoranshi akeyi kawaidai ana d'aga mishi kafane ni danine Usman ina yayanka baxan raga makaba walahi sabuda taurin kansafa mutum 2 ne suke iya yimishi magana ayaran gidannan yaji daga yaya Sadeeq sai ya Faruq suma danyaga uwarsu d'aya ubansu d'aya amma ya raina Usman kodan yaga sakonshine" dariya Sameer yayi yace "duk wan-nan dugon sharhin akanshi shi kad'ai" "ai gaskiya ce ni kana b'atami lokaci zanje na rage xafi da wata baby yanxu" cikin tsoro Sameer ya kaleshi yace "wata fa kace haba Annur baza kayiwa kanka fad'a ka daina bin matan baxa ba ko"








na kan carpet ne cikin buguwa yace "kai barshi ya sha sha aninshi lokacine watarana bayi xaiyiba" murmushi Annur yayi yace "fad'a mishi dan uwa"
daga haka yaja k'afarsa yabar parlour






da kalon tausayi Sameer ya b'ishi yana mishi addu'ar shirya aranshi






wata hamsha kiyar matace ta fito daga bedroom d'inta tashiga na mijinta
yana xaune akan bed ya duba wasu docment yana dubawa tashiga da salama
amsawa yayi ya d'aga kai ya kaleta yayi murmushi yace "sannu da xuwa hajaju mutan maka da madina" xama tayi a kan ciyarshi tana wani fari da idoh saiwani muskuce-muskuce takeyi a jikinshi




kamu kugunta yayi yace "yadai meya faru" cikin salon kissa irinta matan bariki tace "haba baby yau kwana nawa rabunka da gida baka tunani xan iya fad'awa cikin wani hali da baka nan"



murmushi yayi yace "am so sorry my wife kisan inda najene da nisa kuma bansamu ganin malamin da wuriba" juyuwa tayi ta kaleshi tace "yauwa yakukayi dashi" "yace xancen gaskiya yayana Nura yana addu'o'in kariya dashi da y'ay'anshi amma indai shine yasan hanyarda xaibi ya lalatasu duka" dariya ta kwashe da ita tace "gara kowa ya lalace a gidannan ba y'ay'ana kawai ba subuda baxan xuba ido naga y'ay'an Maryam sunxama na kware nawa latattuba walahi ko xan tafi tsurara saina lalata y'ay'an Maryam, yau gobe xanje in ansuwa Zakiya magani farinjini agun yahyah kuma hajjama ta tafi nijar akan maganar Aliyu da Annur" "okey ba matsala saikin dawo itama Allah ya dawo da ita lafiya" yakara maganar yana xura hannu cikin rigarta






atare suka saki ajiyar xuciya a hankali ya furta "i miss you baby" sannan ya had'e bakinsu guri d'aya yadda suke sarrafa junansu baxakace sun haifi kamar Annur ba dan gakai xato yan 18 to 20years ne (kodayake ai ba babba bayaro aharkar)








Deedee bata tashi ba sai gurin 2:30pm warai ta tashi dan haka a gurguje tai shirin islamiyya bayan ta gama shiri ta dauko school bag d'inta ta yiwa Ammi salama ta fito d'akin mommy tashiga da salama ta tadda Hafsat tagama shirinta sukayiwa mommy salama suka huce islamiyya kuma duk fad'in gidan sune kawai sukeyin islamiya amma sauran iya boko sukeyi










sai 5:40pm suka dawo gidan a bakin get ne suka ci karo da Annur yadawo gidan har kasa suka gaida shi duk rashi tarbiyarshi yaji dad'i kuma yaji yaran sunkara shiga ranshi musamman *FATEEMAH* wace a kulum bashidda buri irin yaga ya malaki yarinya kodan yaraba Aliyu da ita amsawa yayi cikin fara'a batare da sun k'ara magana ba sukayi gaba
cikin rashin sani *FATEEMAH* ta yadda zadda zaujen d'inta da sauri ya dauke duk da basuyi nisaba amma yak'i kiranta dan da wan-nan book d'in xauyi anfani yajata d'akinsa ya shigarda kansa agurinta wani murmushi yayi a fili ya furta kinshiga hannu yariya............!






*ASALIN* *LABARI*






*PAGE* 5-6




wan-nan page d'in nakine sister *AMEENAH* *S* *OMAR* {maman minal} ina jin dadin kulawar ki gareni Allah ya k'ara mana zumunci ameen






*ASALIN* *LABARI*




Alhaji Muhammad sha hararran dan kasuwane yanada rufin asiri daidai gwargwado yanada mata 3 Hajiya Tine itace babba tanada yara 2 Nura shine babba wanda tunda ta haifeshi saida ta shekara 20 sannan ta haifi Zulaihat wanda itace yar auta a gidan






Hajiya maimuna tanada yara 3 Suleman sai Yuseef sai autarsu Sadeeya
sai Hajiya Rukayya tanada yara 2 Isyaku sai Sa'adatu






duk da rufin asirin daya ke dashi amma hankalinsa ba akwance yake ba dalilin rashin zaman lafiya a cikin gidansa kuma duk fitinarda akeyi a gidan bakowane ke hada taba sai Hajiya maimuna da yaranta gaba daya tahana kuwa sakat a gidan kuma bawanda ta kulata irin Nura dan gani Alhaji ya d'orashi akan dukiyarsa ba abunda besaniba daga cikin dukiyar Alhajin ba








tayi asirin tayi tugun waniyaci wani ya lalace amma har yanxu takasa galaba akansa


anahaka Alhaji ya biyamishi aikin Hajji yatafi acanne ya had'u da wata Maryam itakuma yar asalin jayahar Yube ce sunje aikin hajine da mamanta tunda ya ganta yakasa sukuni har suka dawo gida yayiwa mamarshi zance itakuma tayiwa Alhaji zancen








yaji dadi sosai kuma yace zaisa aimishi binkice akan asalin ita yarinyar
cikim 4mouth akai kumai aka gama aikai biki a ka kawo amarya Maryam garin Kano medile






tunda Hajiya Maimuna ta d'ora idonta akan Maryam taji gaba daya tsanar da takewa Nura 70% yakoma kan Maryam sabuda yarinyar akwai kyau ga tarbiya da biyya wan-nan sa'arda wani yayi ba d'antaba ba k'aramin bak'inciki tayiba








10mouth da biki Maryam ta haihu tasamu Abbakar suna kiranshi Sadeeq haka tacigaba da rainan d'anta 2year tsakani ta haifi Omar (Faruq)






lukacin ne shima Suleman yasamu mata ya aura me suna Sareena,
Sareena irin matannane yan duniya idonta ya bude dan haka take juya Suleman yadda taso kuma bayadda suka iya har ita hajiya maimunan ta saurara




dayake shi Alhaji muhammad in yaranshi zasuyi aure to kusa da ginda d'an uwanka zaka tare kuma komai nasu irin dayane shiyasa da Sareena taga Maryam tafita jin dad'i da kyau da komai ta tsaneta tasakota agaba sharin yau daban na gobe da ban
shima Yuseef da Isyaku suka samu mata akayi bikinsu ganin gidansu ba tazara kuma suna jikin juna yasa Alhaji Nura siyan filayan kusa dasu ya ya kara part 3 daya na yara maza daya na yara mata sai na baki dan wata zata zo acikin iyayensu ya zagaye gidan yai musu get








me makon hakan yayiwa iyayensu da su kansu dad'i sai kowa bakin ciki da hassada ta shiga cikin sunga yafisu samu
lukacin ne kuma Maryam ta sake haifar Usman wadda bakin ciki yayiwa Suleman yawa gashi shi haryanxu besamu haihu ba ga d'an uwansa sai samun yara maza yakeyi








Usman nada 1year Maryam ta sake samun ciki hakane yasa Sareena hauka cewa ta bazama neman haihu gurin malame da bukaye






cikin ikon Allah Maryam ta kara haifu d'an ta namiji wanda ya fi duk yaranta kyau ba abunda ya bari nata ranar suna yaci suna *ALIYU*








ba a d'ade ba matar Isyaku ta haihu ta samu Sameer




nan fa Hajiya maimuna ta bazama neman magani wai ko yaranta ne basa haihuwa






*ALIYU* nada 2years Sareena tasamu ciki murna a gurinsu ba'a magana 9mouth ta haifo d'anta namiji (tofa su Sareena abun nema yasamu) nanfa aka ringa hura hanci kai kace sauran ba maza garesuba akasa ma yaron Ibrahim sunan ma haifinta ana cemishi *ANNUR* bata dadeba matar Yuseef ta haihu tasamu Sa'ad kuma kamar had'in baki duk haihu ta tsaya musu






lukacin akayiwa Sa'adatu da Sadeeya da Zulaihat aure duk rana d'aya








after 19 year




abu buwa dayawa sun faru ciki harda rasuwar hajiya Rukayya sai haife haife da aka k'ara samu Maryam ta k'ara haihu yar ta Hafsat itama Sareena ta samu Zakeeya itakuma hajiya Nusaiba matar Yuseef ta k'ara haihu war Kamal da Yusira
itama matar Isyaku ta haifi Rudwan da Yaseera






Sadeeya da take aure a naija ta haifi yaranta 3 Hasana da Husaina

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads