Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 49839 words

Chapter 10 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt

Ads the beginning of article before Image

23 Jun 2024

475

Ads at the middle of Article

zuwa yanzu".






Ko kallon ta baiyi ba ya ɗau kayansa ya bar hospital ɗin, batari da an sallame shiba.






Har zai fita tayi sauri taci gabansa tace, "ina zakaje ne?".


Ko kallon ta baiyi ba ya ture ta gyafe ɗaya ya fice warsa.




Bayan shi ta biyu tana kiran sunanshi, yana jinta amma yayi kamar bai jiba.
Haka har yazo kan ti-ti ya tsayar da mai napep ya shiga tana kallo amma batayi gi-gin magana ba dan taga yau ba sauƙi, filn jirgi ya kashi, kuma yana sauka ba ɓata lokaci jiringin nasu ya ɗaga.
Tunda suka shiga motar ta haɗe kanta da ƙafafunta sai famar rusar kuka takeyi kamar wadda za'a raba da ranta.
Ko waɗan da suke tare a motar ba wanda bai mata magana ba, har dai suka gaji suka kyaleta, tana kuka haka dai har bacci ya ɗauke ta.
Cikin ikon Allah tara da rabi suka isa airport ďin Abuja, kuma koda suka ƙaraso ba ɓata lokaci suka shiga jirigi suka wuce India.


Minti talatin da ta fiyarsu sai ga Anwar ya dira garin abuja kuma aka tabbatar masa da basu jima da tashi ba.






Wata ƙara yasaka sabida wani bakin cikin da ya rufeshi, rasama abinyi yayi, sai can ya ciji yatsa kana yace,




"wallahi ko ƙarshin duniya kika kai Hafsat sai na nemuki, bari makarantar india".


Awa ɗaya da tafiyar su Hafsat sai ga Abbanta ya shigo garin abuja, ba ɓata lokaci yasa aka kawoshi airport ɗin garin, tambaya yayi ko jirigin india ya ɗaga aikuwa aka tabbatar masa da ya ɗaga nan da awa ɗaya da suka wuce.


Aikuwa ba shiri sai ga hawayen baƙin ciki sun fara zoba a idonsa, lokaci ɗaya ya fara rawar sanyi, kuma lokaci ɗaya ya hango halin da matar sa take ciki, ba shiri ya samu waje ya zauna haɗi da dafe kansa.....




*#VOte*
*Comment*
*Share*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*












*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*








~~WattpadSummy M Na'ige~






*SHAFI NA 20📑*










*__________*📖 Ya kai kusan minti talatin a wajan yarasa mi zaiyi, zaman da ya keyi yaga bashine mafita ba dan haka ya tashi jikinsa a sanyaye ya tafi.
Tashar mota ya koma, kuma cikin ikon Allah koda yaje mutan ɗaya ake jira motar ta tashi, haka yashiga bawani ƙarfin gwuwa atari dashi.








Safiyya da Yayanta suna shiga gida Baban ta yafara tambayar su ina Hafsat?.


Gaba ɗayansu kasa magana sukayi,dan kowane bakinshi yayi masa nauyi sose, tambyar su ya ƙarayi cikin faɗa², Safiyya har ta buɗi baki tayi magana sai kuma ta rushe da kuka tana faɗin,


"Baba dan Allah kayi haƙuri".... tsawa ya daka mata kana yace "baza ku faɗamin wurin da kuka kaimin ƴar ba?".
Abbas ne yayi ƙarfin halin buɗa baki yayi masa bayani, ai Mamar Safiyya najin haka ta faɗi ƙasa tana ba Baban Safiyya haƙuri, shi Baban Safiyya sabida baƙin ciki kasa magana yayi, bai ce komai ba ya saka takalman sa ya fice gidan, sabida yasan da ya buɗa baki ba zai faɗi abu mai kyau ba.
Sai bayan isha'i Abba ya sauka, masallaci yaje yayi sallah, yajima zaune yana addu'a samun mafita kana ya tashi yaje hospital jikinsa a sanyaye dan duk yinin yau ba abinda yasama cikin sa sabida tsananin tashin hankali.






A hankali ya shiga ɗakin da aka kwantar da ita, Ammar ya fara cin karu dashi yana zaune saman kujera yana kallon Mamar sa, buɗa ƙofar da akayi ne yasa ya kai dubansa ga ƙofa, Abban sa yagani, aikuwa da sauri yazo yatare shi haɗi da faɗin, "Abba barka da zuwa".




Sai da ya zauna kan kujera kana yace, "Ammar ya jikin Ummar taka?".




"Da sauki yace".


Dubansa yayi da kyau kana yace, "tun yaushe take bacci hala".




Yace "bayan fitar ka ba jimawa".




Tea ya haɗa yasha kana yace bari yaje gida yayi wanka idan ya dawo sai Ammar yaje.


Tunda taga Anwar yashiga ke-ke napep yabar ta tsaye takasa koda ɗaga ƙafa ta tafi bare ta mutsa, sose abin da Anwar yayi mata ya bata tsoro, to me Hafsat take dashi wanda ita bata da?, tunanin ne taga bashine mafita ba tayi kyafa kana ta tsayar da mai napep, sunan wata ungwa tafaɗa mishi tashiga ya kaita.






Abba na fita Umma ta farka haɗi da ƙiran sunan Allah, da sauri Ammar da ke kusa da ita ya ƙaraso gareta yana faɗin, "Umma ya jikin, mike miki ciyo?".






Buɗar baki tayi ahankali tace, "Ammar ba abinda kemin ciyo yanzu" sai da ta ɗan huta tace, "ina Abbanka yake ko har yanzu bai zomin da Hafsat ba?".




Ammar kasa magana yayi sai can yace, "kiyi haƙuri Umma nasan zai zo da ita".






Komai bata saki faɗa ba, amma tayi alwashin in har dai ta fita daga wannan hospital to ba shakka sai taje gida ganin iyayenta, dan tasan ko hakkinsu na kanta, amma ya ta iya tunda ba laifinta bane.






Bayan kwana biyu da faruwar haka jikin Umma yayi sauƙi sose dan har abinci tana iya ci da kanta, sai dai wasar ɓoyar da ake tsakanin Abba da Umma, dan yanzu baya son shigowa sai tayi bacci, dan baya son ta tambaye shi Hafsat.


Itako da ta lura da haka data ji alamun zai shigo sai tayi kamar bacci take har sai yafita kan ta buɗe idonta.




Yau Monday, Doctor nashigowa ya tambaye ta yatakeji gami da lafiyar ta, sai tace batajin komai, magani yarubuta mata haɗi da takardar sallama kana ya ƙara jamata kunne akan ta daina sa damuwa aranta.






Bayan Doctor yafita Ammar ya ƙira Abban sa ya sheida masa ansallamesu, ba jimawa kuwa sai ga Abba yazo sutafi, kayansu suka saka a mota kana suka shiga suka tafi gida, amma duk wannan abin Abba yakasa haɗa ido da Umma har suka ƙaraso gida.






Yana sauke su ya wuce wajan aikin sa, da yamma bayan ya dawo daga aiki har zai shiga gida sai suka haɗu da Baban Safiyya, bayan sun gaisa sai Baban Safiyya yace,




"Kunɓatar min da ɗiya hankalinku ya kwanta ko?".




Murmushi Abban Hafsat yayi kana yace, "ayi haƙuri Alhaji,fushin zuciya ne da sharin sheiɗan, amma dan Allah ayimana haƙuri wallahi yanzu haka ni kaɗai nasan halin da nake ciki, amma dan Allah kar ayi fushi damu a cigaba da sanyamu a addu'a".






Sai da Abban Safiyya yayi murmushi kana yace, "ba komai, kuma inaji ajikina ƴata tana hannun nagari, kuma insha Allahu lafiya zata dawo".....daga nan suka cigaba da firar su, daga baya sukayi ma juna sallama suka wuce.








Ƙarfi tara da rabi na dare, jirgin su Hafsat ya sauka a airplane ďin India, aikuwa tunda jirigin ya sauka taji gabanta ya fara dukan uku-uku, lokaci ɗaya wasu hawaye masu zafi suka fara antayu mata, abukin tafiyar sune Sulaiman yace, "Hafsat ki shafe hawayinki ki taso mu fita".....yana faɗa yana tashi domin su fita.




Bayan sa ta bi har suka zo matakalal jirgi, yana gaba tana biye dashi suma sauran na biye da su, aikuwa tana taka matakalar farko, sai wani iska mai haɗi da sanyin daɗi ya ziyarce ta, bashiri ta buɗa baki haɗi da ɗago harshin ta tafara yiwa Allah kirari.....












*#VOte*
*Comment*
*Share*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*












*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*








~~WattpadSummy M Na'ige~










*SHAFI NA 21📑*






*__________*📖 A hankali taci gaba da ta kawa saman mattakalar jirgin har ta sauko, suna sauka gaba ki ɗaya, ba jimawa sai gashi anturu motar da zata kaisu makarantar.




Bayan angama duba jukkunan su kana suka shiga mota suka kama hanyar da zata sa dasu da makaranta, basu tsaya ko inaba sai bakin gate ɗin makarantar, kafin su shiga da ga ciki sai Hafsat ta dago da kanta, dan tun lokacin da suka shiga motar kanta na kasa taƙi ta ɗago bare taga jajayin fata .




Aikuwa tana ɗago kanta sai da tayi suman zaune, dan ganin wannan katafariyar makaranta da tayi sai da tayi tasbihi ga Allah, makarantar tabi da kallo, wadda aka rubuta sunanta da manya haruffa, wato (GALGOTIAS UNIVERSITY).




Bata ƙarasa kallon ba direban motar ya shiga cikin makarantar, bai tsaya dasu ko ina ba sai gyefin saukar baƙi da ke cikin makarantar, bayan sun shiga sun zauna aka kawo musu abin motsa baki, bayan sun kammala kowanin su yayi wanka ya ɗan huta kafin safe sai su fara shiga makarantar.




Sulaiman ne ya kalle abukain tafiyar sa kana yace, "wai ina Hafsat?, ayya taci wani abu kuwa?, dan nasan ƙila bataci komai ba tana can tana sana'ar ta ta kuka".








Sai ɗayan wanda akekira da Safuwan yace, "wata ƙila bata ciba, amma bari nayi mata knocking idan ta fito zamu gani ko taci".


Yana faɗa yana tashi dan ya ƙarasa ɗakin da akayi mata ma sauki.






Knocking da bai wuce uku ba ta ɓuɗe, wannda tagani bakin ƙofar ɗakin yasa ta ƙaƙalo murmushi haɗi da yin ƙasa da kanta, kafin ta ɓuɗa baki tayi magana yace,




"Idan kin kammala muna son magana dake".


Tace "tom gani zuwa".




Yana barin wajan itama ta koma ɗakin ta shirya jikinta tasaka hijba kana ta fito wajan su.






Sallama tayi musu, suka amsa haɗi da bata izini sannan ta shigo.


Bayan ta shigo ta gaishe su haɗi da musu ban gajiya kana ta zauna.




Dukan su suka amsa kana suka tambaye ta ko taci wani abu ba kuka taje tanayi ba?.




Sai da tayi murmushi kana tace, "wallahi naci kuma na koshi".


Suka ce to hakan yafi sannan suka ɗan taɓa fira gami da yadda karatun su zai kasance a wannan ƙasar, bayan sun ɗanyi shuru sai Sulaiman ya dube su kana yace,




" Gami da zaman Hafsat hostel ne, duk da hostel ɗin ƙasar yana da kyau amma ina ga kamar zaifi in kin yarda ko kun amice sai na kaita gidan Yaya ta dan itama karatu takeyi anan kuma tanada miji da yaro ɗaya, amma shi mai gidan nata sai wani lokaci ya kan shigo kuma ba zai wuce kwana biyu ba ya koma, dan wancan lokacin da nazo acan na zauna kuma naga zaki fi jin daɗin zama acan gaskiya, amma inkunga hakan yayi muku kuma yayi miki".




Gaba ki ɗayan su sukayi na'am da maganar sa kana ya dube Hafsat da tayi shuru ba tace komai ba yace, "Hafsat mikika ce akan maganata".




Ahankali ta ɓuɗa baki tace, "ba abinda zance tunda ni ban san kan ƙasar ba, amma tunda kai kasan kan ƙasar duk yadda kayi ba komai, sai dai kar mutakura ta".




Yace, "a'a kar ki damu dan Aunty Shemah ta wuce haka".




Sai da suka gama tattaunawa kana tafito ta koma ɗakin ta kafin safiya ta waye aba kowane class sai kuma ta wuce gidan da zata zauna.


*******


Wata unguwace mai napep ya sauke ta, bayan ta sallameshi tashiga wani longo tana shiga tafiya kaɗan sai tazo ƙofar wani ɗaki, da yake ɗakunane jere a unguwar kuma da gani ɗakunan hayane, na tsaka daga cikin su ta tura ƙofa tashiga.




Ƴan mata biyu ne aciki ɗayan na kwance ɗayan na shirin kayan sawar su, aikuwa suna ganin ta gabaki ɗaya suka buga shewa haɗi da faɗin,




" Matar Anwar ce tazo wurin mu?".
Sun faɗi haka ciki da tsokana.




Tsaki ta musu kana tace, "kubarni da ɗan iska, wai yau ni zaima walaƙanci akan wata banzar yarinya, wallahi naga har yanzu kansa bai daina rawa ba, amma dani yake zanci".


Tafaɗa haka ranta amatuƙar ɓace.




Ɗayan wadda ke kwance mai suna Zahara ita tace, "me ya haɗaki da Anwar ɗin naki hala?".




Kafin tayi magana sai ɗayan mai shirin kaya wato Hafiza tace, "ta tsoniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ni dai wallahi Hajara da zaki bi tawa da kinbar Anwar da Hafsat, dan wallahi ko da zaki je wurin bokayin duniyar nan ba zai iya rabuwa da Hafsat ba, dan ni nasan son da yake ma Hafsat cikin jininsa yake, amma dan baki da imani kikabi kowace hanya kika lalata musu zama to gashi gaki ya aure ki .....aitun bata kai da rufe baki ba Hajara ta miƙi tsaye zata cikumo ta sai Zahara tayi saurin tashi tariƙi Hajara tana faɗin, "dan Allah Hajara ki kyaleta idan har ta isa tasa Anwar ya aure Hafsat, kuma bari kiji, wallahi Anwar koda mi yake taƙama sai ya aureki barin ni dashi, ai inyasan wata bai san wata ba".




Hafiza tace, "kanku akeji" tana faɗin haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice batare da tasaki magana ba.


Tana fita sai Zahara ta dube Hajara da tacika tayi fam, abu kaɗan take jira ta fashe, Zahara irin yanayi da taga Hajara tashiga yasa ta ƙarasowa jikin ta sose, haƙuri ta fara bata kan ta ɗura hannunta saman dukiyar fulaninta, haɗi da kai bakinta kan na Hajara,kissing ɗinta cikin sigar rarrashi.




Sai da suka gama fanɗarewar su kana Zahara ta ƙara matse Hajara jikita tana faɗi, "ke daina sama ranki damuwa, indai Anwar ne kina zaune zaki gansa dan haka ki bar komai a hannu na nasan yadda zanyi da shi".




Dubanta Hajara tayi, taga da gaske take dan haka tace, "nagode masoyiya ta, haka dai suka cigaba da firar su daga baya kuma Hajara tayi mata sallama ta koma unguwar su.


Tunda Umma ta dawo daga hospital ta daina sakin jikinta da Abba dan yanzu ma haduwa wuya take musu, yau ma da dare bayan ya dawo daga masallaci ta kai masa abinci yaci har yayi shirin kwanciya sai gata ta turu ƙofar ɗakinsa haɗi da sallama.


Bayan ya amsa mata ya ɗago da kansa ya kalleta ciki da son matar tasa yaci, "ƙaraso daga ciki Fatima".
Ba muso ta ƙaraso ta samu waje ta zauna nesa kaɗan dashi.




Har ya buɗa baki yayi magana sai tayi saurin cewa, "Abban Hafsat, dama maganar da zan faɗa itace, ina son zanje gidan iyayena dan ina son naje na gansu, ko banza najima banje ba,kuma idan naje bazan dawo ba har sai ka nemumin ƴata".
Tana faɗar haka ta miƙi dan ta fita.


Da sauri ya ƙaraso gareta yana faɗin, "haba Fatima miyayi zafi haka, dan Allah karki barni wallahi ni kaɗai nasan halin da nake ciki, kuma zanci zuwa gida ki bari idan nasamu huta muje tare, dan koni ina son naje naga gashesu"......ai tun bai kai ƙarshin zanciba ta fice daga ɗakinsa yana kiranta amma tayi kamar batajiba ta shige ɗakinta haɗi da rufe ƙofa.


Tanda ta rufe ƙofa ta fara kuka mai cin zuciya da baƙin cikin rashin inda ƴar ta take, amma a gaskiya baza iya cigaba da zama ba Hafsat ba, inhar yana son taci gaba da zama dashi sai ya nemu mata ƴar ta, dan gobe tunda safe zata ta kama hayar garinsu ko da kuwa ba zata gane gidan ba, dan ita gani take bazata gane gida ba, dan rabunta da gida kusan shekara ashirin, aikuwa tana tuna haka ta fara kuka maicin zuciya.




Ko da yazo ga ƙofar yaga har ta rufe, ai basan sanda ya dafe kansa ba haɗi da faɗin "ya salam".....kansa ne yaji ya fara sarawa, dan haka ya koma ɗakinsa ya zauna haɗi da ɗauko magani yasha kana ya kwanta.




Koda gari ya waye bayan sun gamala komai sun shirya sunyi beark aka turu azo dasu cikin school ɗin.


Bayan sunje aka ba kowa nasa abinda za'a bashi kana akayi musu jagora zuwa class ɗinsu.


Bayan sun gama lecture ne sai Saulaiman shida abakan tafiyar su suka kai Hafsat gidan Aunty Shemah, kuma gidan ba nisa da school ɗin, shiyasa batayi wuyar ganewa ba.




Bayan sun shiga gida Aunty Shemah ta karɓe su hannu biyu² haɗi da kawu musu kayam mutsa baki, bayan su ɗan ci abinda ta kawo musu nan Sulauman ya ƙara yimata bayani akan Hafsat itama Hafsat ya ƙara yimata bayani akan Aunty Shemah.






Aunty Shemah sose tayi murna da samun abukir zama, dan zaman kaɗaice bayayi mata daɗi, dan mijinta bayar da taje ko inaba daga makaranta sai makaranta,wani ɗaki ta nunama Hafsat tace tazo ga ɗakin da zata zauna ,tashi tayi tabi bayan ta tanuna mata ɗakin, sose ɗakin yayi mata kyau, dan ɗakine mai haɗe toilet da ƙaramin gado da wadiruf, bayan komai ya kammala sai Sulaiman yayi musu sallama yayi tafiyar sa.








*Wanene Anwar*








*#Veto*
*Comment*
*Share*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*












*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*








~~WattpadSummy M Na'ige~






*SHAFI NA 22📑*








*__________📖* Anwar hafafin ɗan garin kaduna ne, sunan mahaifin sa Alhaji Umar, fittacin ɗan kasuwa ne kuma babban ma'akacin gwamnati, yayi suna a cikin gari kaduna sose, dan kowa yasan Alhaji Umar dallah-dallah ,mahafiyar sa Hajiya Ruƙayya, suna da yara huɗu, Zainab, Hafsat, Sajida, sai autansu Anwar, iyayen su suna nuna musu so da ƙauna sosai, musamman Anwar da ya kasance auta, dukan su sunyi karatu mai zurfi sannan sukayi aure, yanzu Anwar ne ya yarage baiyi ba, kuma koshi iyayen sa na son yayi amma sai wani ƙaƙale² yake musu shi sai yayi karatu mai zurfi, bayan ya kammala karatun sa ne ya ƙaƙalo zuwa sokoto dan ya dubama mahaifin sa wani ƙamfanin shi, to acan ne ya haɗu da Hafsat har ya fara soyayya da ita, sosai yake son Hafsat kuma har cikin ransa aurin ta zaiyi sai daga baya sheiɗan ya shiga tsakanin.




*Cigaban labari*


Anwar dake airport sai kai da komowa ya keyi yarasa abinyi, ji yake kamar yayi tson-tso ya ganshi Indian, rasa abinyi yayi dan haka ya tsayar da ɗan aceɓa yace ya kaishi wata unguwa.






Dai-dai wani katafarin gida ya ajeshi, kud'i ya bashi bai ma tsaya karb'ar canjiba ya wuce cikin gidan, mai gadi na masa magana amma ga baki d'aya hankalin sa bai tare da shi shiya sa bai karb'a masa ba ya wuce cikin gidan.




Bai tsaya ko ina ba sai wani ƙayataccin falo wanda aka ƙawatashi da kayan ado na more rayuwa,iya haɗuwa wannan falon ya haɗu, ɗayan kujerun ya zauna haɗe da dafe kansa lokaci ɗaya yaji kansa ya fara sarawa, carpet ɗin dake shinfiɗe atsakar parlour ya kwata, bai jima da kwanciya ba bacci yayi awun gaba dashi.


Aunty Zainab ko da ta fito kwance ta ganshi a tsakiyar parlor, ba tama ganeshi ba sai data kara masa kallon kana tagane Anwar ne, da sauri ta ƙaraso gareshi tafara ta dashi tana faɗin, "Anwar lafiya katashi mike damunka?"....tafaɗi haka ciki da firgici.






A hankali ya fara ɓuɗa idonsa da sukayi masa jawur yace, "Aunty"..... girgizashi ta farayi ciki da tashin hankali tana faɗin, "mike damunka haka duk ka rame kayi baƙi, kafaɗamin dan Allah?".






Irin yadda yaga ta rikice duk tawani tada hankalinta yasa ya buɗa baki yace, "ba komai Aunty, lafiya ce ba nida kwana biyu amma yanzu

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads