Header Ads
Showing 9001 words to 12000 words out of 49839 words

Chapter 4 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt

Ads the beginning of article before Image

23 Jun 2024

471

Ads at the middle of Article

abunyi".


Da sauri ta ɗago da kanta ta kalleshi bakin ta na kar-karwa tace, "wani ciki, wallahi ni banda ciki kuma da'ace inada ciki da kai kanka zaka sani".


Wani kallo ya watsa mata haɗi da jefa mata wasu takardu yace, "duba kigani".


Jikinta na kar-karwa ta ɗauka ta fara dubawa aikuwa tana gama dubawa ta zabura haɗi da sanya hannu akai tace,"ciki gareni fah!.


Wasu hawaye suka fara bin kuncin ta haɗi da durkusawa ƙasa ta fara kuka mai tsoma zuciya.


Tsawa ya daka mata haɗi da faɗin tayi shuru zaiyi magana da ita.


Hannun ta ta ɗaura kan bakin ta kana tace, "na daina".


Yace, "abunda nake so dake idan Likitoci suka tambaye ki kin yarda azubar da cikin kice eh kin yarda, dan idan baki yarda ba to wallahi bazan aureki ba kuma sai dai kije kisamar masa uba amma ba niba".


Jikin ta na kar-karwa tace' "na yarda ko ma basu tambayeni ba na yarda kuma kayi hak'uri kada ka fasa aurena please".


Har zai sake magana sai ga Likitoci sun shigo ɗakin.


Ƙarasawa sukayi gaban gadon da take kwance, bayan sun gaisa sukayi mata ya jiki kana sukayi mata bayanin da sukayi ma Anwar har wanda yayi musu na azubar da ciki.


Bayan sun gama yimata bayani sai ɗaya daga cikin su ya dube ta yace, "kin amince azubar da cikin?".


Duƙar da kanta ƙasa tayi wasu hawaye masu zafi nabin kunci ta, tunani ta fara idan aka cire shikenan baza ta sake haihuwa ba kenan?ko ta rasa ranta, kuma yace bazai aureni da ciki ba to ya zanyi?.


Shurun da sukaji tayi ne yasa suka yi mata magana kallon su tayi da idon ta dasu ka sauya zuwa ja, sosai ta basu tausai dan haka suka ce da ita kin amince?".


Sai da ta rufe idon ta kana tace, "a'a ban amince ba".


Tun bata kai da rufe bakinta ba Anwar ya daka mata tsawar da tasa ƴan cikin ta kaɗawa.


Bai ma damu da Likitocin dake wajan ba yace, "me kika ce? baki amince ba?".


Jikinta na kar-karwa tace, "Hayat kayi haƙuri dan Allah ka taimaki rayuwata".


Har zaiyi magana sai ɗaya daga cikin Likitocin yace, "Malam bari kaji koda a ce ta aminta azubar da cikin tomu ba zamu zubar ba, dan mu ba aikin mu bane, idan kaga zaku iya zama har ta samu sauƙi to bazamu hanaka ba amma idan kaga baza ku iyaba to zaku iya ƙarawa gaba amma mudai bazamu zubar mata da ciki ba bare ciki har na wata huɗu".


.


Yace, "ko minti biyar baza muyi anan ba bare har na sa kuɗina taci gaba da kwanciya anan".


Kallon ta yayi yace, "ki tashi muje sai kije can ki haifar musu shi dan wallahi kar ma ki soma cewa nawa ne" yana faɗar haka ya kama hanyar fita batare da yaji mi zasu ce dashi ba.


Suma Likitocin fita sukayi har sun fita sai ɗaya daga cikin su ya dawo ya sameta sai kuka takeyi kamar ranta zai fita yace,


"Shawara zan baki duk yadda yaso kada ki yarda a zubar miki da ciki dan ke zai cutar, shi a kowane lokaci yake son haihuwa zai iya wani aure ya haihu amma ke shikenan baza ki saki haihuwa ba har abada, dan haka ki tashi kije yana jiranki " yana faɗar haka shima yafice daga ɗakin.


Sai da tayi kusan minti biyar kana ta tashi ta fara bin bango ta fita a ɗakin har ta kai wurin da motar sa take.


Tun bata ƙarasu wajan saba ya fara afka mata wata muguwar harara.


Motar ta buɗe ta shiga aikuwa tana shiga yaja motar da ƙarfi kamar zai tashi sama ya fice.


Suna isa hotel ɗin ko kallo bata ishe saba ya buɗe motar ya barta ba tare daya kalleta ba.


Haka tafito tana tafiya a hakali har ta isa ɗakin da suke.


Koda ta shigo yana toilet yana wanka wuri tasamu ta zauna, bata jima da zama ba ya fito yayi kamar bai san da zaman mutum a wurin ba.


Har ya gama shirin sa zai fita kana ya dube ta yace, "ki tattara naki da naki dan gobe zamu koma gida kuma wallahi ba zaki sauka gidana ba sai dai kije gidan ubanki" yana faɗin haka yafice warsa batari da ya tsaya yaji mi zata ceba.


Yana fita ta fara kuka mai ban tausai, tana cikin kukan ne Safiyya takira ta kuma abunda yasa tak'i magana dan kar taji tana kuka.


Haka ya barta har dare batare da ya sake wai-wayar taba.


Kuma babbar matsala duk baifi rashin ƙarfin jikin da bata dashi ba kuma ga yunwa ta dame ta dan tun safe rabun ta da abinci gashi yanzu dare yayi kuma har yanzu bai dawo ba.


Har barci ya fara ɗaukar ta sai gashi ya dawo, da sauri ta tashi dan a tunanin ta ko zata samu wani abun da zataci koda tea ne tasha.


Koda ya shigo sarai ya gan ta amma sai yayi kamar bai ganta ba har yaje toitel yayi wanka yazo ya kwanta, sai ta ƙaraso da sauri gareshi tace, "Hayat dan Allah ka taimakamin da ko ruwan tea ne wallahi yunwa nakeji?" tana faɗa kamar tayi kuka.


Kallo ma bata isheshi ba bare tasa ran zai ƙarɓa mata magana.


Data ga alamun bazata samuba dan haka ta zo ta kwanta.


Bata jima da kwanciya ba ya fara jawota jikin sa yana wasa da ita son rashi, ita ko tunda taga abunda yake son yi da ita ta fara masa kuka tana faɗin, "dan Allah kayi haƙuri ka barni wallahi banda lafiya kuma yunwa nakeji".


Yi yayi kamar bai jita ba haka yayi yadda yake so da ita kafin ya barta.


Sosai tayi kuka a wannan daren dan iya wahala ta wahala dan har ƙaramin suma sai da tayi, kuma tundaga lokacin bata koma barci ba har gari ya waye.......




























*#Vote*
*Comment*
*Shere*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*














*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*






~Wattpad ~Summy M Na'ige~






*SHAFI NA 9📑*


*__________📖* Bayan ta idar da sallah asuba tajima kafin ta ta shi sabida ko da ta tashi faɗuwa zatayi dan bata da wani kuzari a jikin ta.


Tana kan sallaya ya tashi ya je ya yi wanka kana ya yi sallah, bearkfast yaje ya karɓo musu,yana dawo ya kai duban shi gareta kaifin ya yi mata magana ita tafara gaisheshi ciki da ladabi.


bai ma karɓa ba yace, "kizo kiyi bearkfast dan yanzu na keson mu kama hanya kuma idan ki ka tsaya wasa sai na barka". yana faɗa yana antaya mata harara.




Ahankali ta tashi kayan da yanuna mata na beark su ta ɗauka ta haɗa tea ta farashi,sosai taci kayan da ya kawo mata,sai da taji ta ƙoshi kana ta tashi taje toilte tayi wanka.


tana cikin shiri sai gashi ya fito cikin shirinsa na tafiya,ko kallon ta baiyi ba ya kama hanyar fita.


Ɗakin da taga yana ƙoƙarin rufewa yasa da sauri ta ɗauko kayan ta tafito waje ta karasa ya fa mayafin ta.




Key ya kai ma masu hotel ɗin kana yazo ya ɓuɗe mota ya shiga itama tashi kana suka kama hanyar garin sokoto.


Tafiya sukeyi amma ba wanda yace ma ɗan uwansa komai har sukayi nisa sosai.




Wayar Hafsat ce tafara ruri dan haka ta ɗauko ta duba wake kiran ta.
Safiyya taga ya bayyana dan haka taja tsaki kana ta ɗauka.
Safiyya tace, "Hafsat kina ina wallahi yau zan koma gida kuma kin sa za su dame ni da tambayar ki dan Allah kidawo mutafi tare".


Sai da ta kai ƙarshen zancin Hafsta tace, "wai Safiyya ke waci iri ce,nace kirabu dani kinƙi to bazanje gidan ba kije ki faɗa kinji kuma bari kiji kada ki saki kira na sabida ba ajiya ki ka bani ba ehe". tana gayamata haka ta tsinki kiran.




Duk abunda takeyi yana kallon ta amma ya yi kamar bai san ta nayi ba.




Haka suka cigaba da tafiya har suka shiga garin sokoto.


Suna kawowa Flyover
ya yi packing ďin motor sa yace, "ki sauka dan ni zan wuce".


"Haba Hayat kayi haƙuri muje gidan ka idan na ɗan huta zuwa ajima sai naje gida".


Wata tsawa ya daka mata wandda tasa tafice daga motar bata shiyar ba.


Har zai tada motar tace,"Hayat bani da kuɗin da zan ƙarasa gida kuma bazan iya ƙarasawa da ƙafa ba gashi kuma dare ya yi".




Ko kallon ta bayi ba yaja motar sa ya bar ta tsaye a hanya.


Hawayen da kifita a idonta ta goge kana ta ɗau jikar ta tafara tafiya kan ti-ti.


Mai napep ta tsayar dashi, ta faɗa masa sunan unguwar da zai kaita.


Bai tsaya da ita ko ina ba sai ƙofar gidan su.


Fita tayi tace dashi zata shiga ta karɓo masa kuɗi yace to.
Sallam tayi ta shigo cikin gidan,aikuwa ƙannin ta najin muryar ta suka fara yimata oyoyo kamar za su kayar da ita gashi ba wani ƙarfin jiki ne da itaba.


Da ƙyar tasamu suka sake ta,ita ko Mama tunda taji suna oyoyo ta san ƴar ɗiyar tace ta dawo dan haka da sauri tafito waje sabida ta ganta.






Gaban tane ya yi muguwar faɗuwa lokacin da taga Hafsat,dan gabaki daya ta rame tayi fari sosai.


Har zata tambaye su Mama sai suka haɗa ido da ita,murmushi Hafsat ta ƙaƙalo tace, "Mama ya nasameku?".






Bata karɓa ba dan kallon ta takeyi sosai dan kamar tana son ta karantu wani abu,sai Hafsat ta katsa mata tunani tace, "Mama nafa tsayar da mai napep ban bashi kuɗi ba".






Sai Mama tace, "dole na kifeki da ido wannan ubar ramar da fari da kikayi Hafsat, lafiya kike kuwa?".




Tace, "Mama bari na sallame mai napep nazo".


Tambayar ta kuɗin sa tayi ta faɗa mata sai Mama tabaiwa ƙaninta Ammar ya kai masa.


Sai Mama tace, "kinyi tsaye ki ƙaraso daga ciki".


Parlour Mama ta shiga ta zauna Mama tace,"Hafsat mike damunki ki ka yi wannan ramar haka?".




Sai da ta ƙaƙalo murmushi tace, "Mama wahalar exams ce ta ramar dani" tana faɗa tana yin ƙasa da kanta.




Sai Mama tace, "a'a Hafsat da alamu akwai ramar zazzaɓi aciki".


Tace, "eh Mama dan jiya ma naje hospital suka rubutumin magani kin gama tagarda maganin" tana faɗan haka tana buɗe zip ɗin jikar ta ta ɗauko mata tagardar maganin da aka rubuta mata a can hospital ɗin da ya kaita dan cewa ya yi tunda bata yarda azubar da cikiba to ko magani ba zai saya ba.




Ɗaukowa tayi taba Mama itako Mama takira Marwan tace yaje pharmacy ɗin Baban shi ya karɓo magani.


Karɓa yayi yaje itako Mama tace Hafsat ta koma ɗakin ta tayi wanka tayi sallah t azo taci abinci ta sha magani.


Tashi tayi taje ɗakin ta, tana shga kafin tayi komai wayar ta ta dauko ta fara kiran Anwar.




Kusan missed call biyar tamasa amma bai ɗaga ba daga ƙarshe ma kashe wayar sa yayi gabaki ɗaya.




Sai da taji ya kashi wayar kana ta tashi taje tayi wanka tayi sallah magarib da isha'i.


Tana idar da sallah Marwan ya shigo ya kawo mata magani da abinci.


Bayan ta ci abinci tasha magani ta koma ɗauko waya ta ƙara kira ko ya ɓuɗi?.






Amma har yanzu kashe take,tunani tafarayi ko taje gidan sa dan gabaki ɗaya bata da natsuwa dan ita kanta tasan ko tana samun natsuwa sai ta ganshi,kuma tasan Mama baza ta barta tafita ba.


Tana cikin wannan tunani barci ya fara ɗaukarta saboda maganin da tasha har da na barci akwai.








Ko da babanta ya dawo daga masallaci har barci yayi awongaba da ita dan ko da Mama ta aiki Marwan ya kirata ta yi bacci sai Babanta yace ka da a tasheta abarta sai da safe sai su gaisa.




Ko da gari ya waye Mama taje ɗakin ta dan ta kira ta, amma sai ta tarar har yanzu bacci takeyi bata tashi ba, abin ya ba Mama mamaki da taga har rana ta kusa fitowa Hafsat bata tashi ba sabod tasan ba halin taba ne baccin asubah.




Tayar da ita ta farayi tana kiran Hafsat tashi kiyi sallah rana tayi, miƙa ta farayi alamun zata tashi Sai ta fara magana cikin muryar bacci tace,




" Mama rana ta fara fitowa?".




"Eh Ki tashi ga Abbanki can yana jiranki ku gaisa saboda yanzu fita zai yi,Tashi tayi ta nufi toilat Cikin hanzari tayi wanka sannan ta daura Arwala.




Ita ko Mama tana ganin ta tashi ta shiga toilat sai ta fice daga dakin






Koda tafito bata tarar da Mama ba dan haka ta gabatar da sallah kana ta shirya tafito taje ta gaishe da Abbanta.




Da sallama ta shiga parlour,bayan sun ƙarɓa mata ta ƙaraso gaban Abban nata wanda tun shigowar ta yake kallon ta ciki da so da ƙaunar ƴar tasa.


Bayan ta gaisheshi ya karɓa kana yace,


"Hafsat ashe har ciyo kikayi?Allah ya ƙara sauki kuma kiri ƙa shan magani muga kwana biyu abunda Allah zaiyi".






Ya ƙara da faɗin "ya exmas da fatar kun kammala lafiya?".




Tace, "eh Abba mungama sai dai muna baran addu'ar samun nasara".






Sosai ya yi musu addu'ar samun nasara ita da Safiyya kana ya yi musu sallama yafita wajan aiki.


*********
Bayan kwana biyu da dawowar ta tasamu sauƙi sosai dan har cikowa ta farayi ba kamar lokacin da tadawo ba.
Kuma tundaga ranar da ya sauke ta bai saki nemanta ba kuma bai saki ɗaukar wayar taba dan ko takira ba zai ɗauka ba shiyasa gabiki ɗaya bata cikin natsuwa dan yanzu burin ta taganta tari dashi dan haka taje tagayawa Mama zataje gidan ƙawar ta ta dubata sabida batada lafiya,da kyar tasamu Mama tabarta amma tace kada tajima.




Wanka tayi ta shirya cikin wata koriyar atamfa ɗikin rika da sikt ne sosai suka karɓe ta tayi kyau abunta har ta ɗauko turare tasa jikinta sai ta tuna Mama bazata barta tafitaba idan tasa shi ba, dan haka ta saka shi ajika ta har sai tazo gidan sa haɗi da wani mitsi-tsin gyale.




Babban hijab tasaka ajikin ta kana ta fito tanufe ɗakin Mama.






Da Sallama tashiga tace, "Mama zan tafi".




Kuɗi napep Mama tabata haɗi da ƙara faɗamta karta jima.




Karɓa tayi haɗi da faɗi, "bazan jimaba". kana taficewar ta.


Tana fita ti-ti ta tsayar da napep,sunan unguwar da zai kata tagaya masa, shiga tayi yaja suka tafi.






Basu tsaya ko inaba sai bakin gidan sa.


Bayan ta sallame mai napep ta ƙaraso bakin gate ɗin gidan ta fara knocking,bata jima tana knocking ba maigadi ya leƙo yaga wanene?aikuwa yana ganin ta ya yi sauri ya buɗe mata ƙofa haɗi da gaisheta.




bayan ta ƙarɓa take tambayar sa ko Anwar nanan?.






Yace "eh yana ciki".




Part ɗinsa ta ƙarasa , kafin ta isa ga part ɗinsa ta buɗe jikarta ta ɗauko turare tafeshi jikinta dashi kana taciri hijab ta sanya wannan mitsi-tsin gyale wanda dashi da babu duk ɗaya.


Ƙofar da zata sadata da falon shi tashiga kai tsaya.


Ahankali take tafi har takawo gab dashi yana zaune yana kallon labaru bai masan ta shigo ba.








Ƙamshin turarin da ya bige hancin sane yasa ya dago kansa, aikuwa suna haɗa ido dashi ta fara sakar masa murmushi mai ciki da nuna tsan-tsar so da ƙauna.


Har yaso ya ƙoreta amma yadda yaga ta ƙara kyau kuma ga ko ina nata ya ciko musammam abunda ya keso wato dukiyar fulani.


Irin kallon da yake matane yasa tafara tafiya ɗaya-ɗaya har ta ƙaraso gareshi.








Ahankali tazo ta zauna saman cinyarsa haɗi da kai masa kiss abaki tare da faďin,"I miss you so much My Hayat nah".




Aikuwa yana jin bakinta cikin nashi lokaci ďaya yaji wata Sha'awa tabi jirumasa bai san lokaci da yafara kissing ďinta ba cikin zafin nama.








Hannunsa yasa cikin rikar ta yafara shafar duk wani ilahirin jikin ta,musammam abu son shi sosai yake matsar su itako sai ƙara narke masa takeyi ajiki tana wani nishi ɗaya-ɗaya.






Cak ya ɗauke ta ya yi bedroom ɗinshi da ita,kayan jikin ta yacire mata kana yacire nasa romance ɗin ta yafara cikin zafin nama kana yashiga aiki, sosai ya bata wuya dan har wani abu taji ya tsaya mata amara amma bazata iya cewa ya daina ba.




Sai da yagaji dan kansa kana ya sauka daga gareta ciki da samun gamsuwa dan shi yake masifar sonta,sosai yake samun natsuwa gareta.




Itako yana gamawa ta gagara tashi dan gabiki ɗaya marar ta ta ƙulle, gawani ciyon da takeji a ƙasan ta.


Shi bai masan tanayi ba, jan yota jikinsa yayi yafara baccin hutu itako ta jima kafin taji dama-dama,daga baya bacci yayi awun gaba da ita.




Sai kusan ƙarfe shidda yabar ta ta koma gida koshi sai da taga neman halakata yake ta sanya masa kuka da kyar ya barta ta tafi gida.






Shiko duk abunda yake mata da gayyane yakeyi sabida burinshi yaga cikin ya zube.




Tun ahanyar zuwa gida taji mararta na ciyo kuma gawani zazzaɓi da ya taso mata lokaci ɗaya.


Batafi minti biyar da shiga gida ba cikin ta yafara juyawa kamar abunda ke cikinta ya fito.




Kuma gashi ita kadai a ɗakin, tajima kwance tana birgima a ɗakin sai can Mama ta shiga ɗakin ta dan tayi mata faɗan jimawar da tayi bata dawo ba sabida ƙarfe huɗu tayi da ita ta dawo.






Aikuwa ko da Mama tashaga ɗakinta halin da ta sameta ne ya yi matuƙar razanata.


Rasa me zatayi tayi sabida gabaki ɗaya tafita hayyacinta ga kuma wani jini dake fita ta ƙasanta.




Da gudu Mama tashiga ɗakin su Marwan tace "yakira mai napep Hafsat ba lafiya za su kaita hospatal".


Dayake ba suda nisa da ti-ti yana fita ya tsayar dashi suka ƙaraso gida.






Shida Ammar da Mama suka ɗaukota suka sa a napep suka wuce hospatal ko mayafi babu ajikin Mama sabuda firgita😢.......








*#Vote*
*Comment*
*Shere*








*©SUMY NA'IGE•*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*










*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*








~Wattpad ~Summy m Na'ige~






*SHAFI NA 10📑*






*__________📖* koda suka isa hospital emregency room suka kaita,ba ɓata lokaci aka fara bata taimako cikin gaugawa.
Tunda suka shiga da ita Mama sai safa da marwa takeyi a harabar hospital.


Marwan Mama tasa yakira Abban su yafaɗa masa abunda ake ciki,kana yaje gida ya ɗauko mata hijab ɗinta.


Tare suka shigo da Abba hijab ɗinta Marwan ya bata tasaka Abba yace, "ina suka kwantar da ita?".


Jikin Mama sai rawa yake tace, "Abban su har yanzu basu fito ba"....tun bata kai da ƙarasa maganar ba sai ga doctor yafito daga cikin ɗakin.


Da sauri Abba da Mama suka zo wajan sa.
Tambayar su ya yi ko su suka kawo Hafsat? sai Abba yace, "eh".
Magana doctor ya yi musu yace su biyushi office.


Bayan ya shiga office ya zauna suma suka shigo kallon su ya yi yace, "wanene mijin ta ?".


Kallon-kallon suka fara tsakanin Mama da Abba.


Sai Abba ya buɗe baki yace, "bata da miji mune dai iyayen ta".


Doctor kallon Abba ya yi sosai kana ya nuna masa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads