Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 49839 words

Chapter 12 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt

Ads the beginning of article before Image

23 Jun 2024

477

Ads at the middle of Article

min shuru kamar baki san waya kira ba".




Tambaya ta jefamasa tace, "yanzu kana ina ne".




"Kaduna". haka yace da ita ata ƙaice..... kana yace da ita wani aiki nake son nasaki shine nace bari naji ko zaki iya?".




Tace, "inaji faɗa idan zan iya zan faɗa idan ma bazan iya ba zan faɗa".




Yace, "zaki iya, yace, address ɗin makarantar da Hafsat take nake so asamun na andia".




Wata dabara ce ta faɗu mata tace, zanyi maka amma da sharaɗin".....yace, "faɗi sharaɗin naji".




Tace, "a'a sa idan kazo zakaji sharaɗin".




Yace, "ba damuwa idan kinsamu sai ki faɗa nazo inyaso sai ki faɗamin sharaɗin kafin ki bani address ɗin".




"Naji zanje na samu, amma idan har ba ka yarda da sharaɗin ba to koda nasamu bazakaji komai daga waje na ba".




Yace, "kar kidamu". haka dai suka cigaba da waya daga baya kuma sukayi sallama.




Tunda lokacin Hajara ta bazama neman address ɗin Hafsat na andia....










*#Vote*
*Comment*
*Share*










*©SUMY NA'IGE*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*












*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*








~~WattpadSummy M Na'ige~






*SHAFI NA 25📑*


















*__________📖* gidan iyayen sa ya sauka ya gaishesu kana ya wuce gidansa, part ɗinsa ya wuce kai tsaye bai ma bi taka matar tashi da Baby da aka haifar masa ba ,tana parlour zaune ita da ƙanwar ta da wasu ƙawayen ta, alamun shigowarsa taji dan haka ta dube ƙawayen ta tace dasu dan Allah kujira ni ina zuwa, tana faɗar haka ta ɗau Baby ta kama hanyar part ɗinsa, duk da bata da cikakin sanin da zata ce shine amma jikinta har wani karkarwa yeke burinta ita dai ta ganshi gata gashi.






Yana isa part ɗinsa, ko kayan jikinsa ba tsaya yarage ba ya ɗau waya yakira Aunty Shemah, bayan ta ɗauka sun gaisa yake tambayar ta Hafsat, sai da ta wani haɗe rai kana tace, "ai kana da number ta".




Yace, "na ɗauka kuna tare ne amma kiyi hakuri naji kamar ranki ya ɓaci".




Tace, "a'a ba haka bane kawai naga ko iyayena baka bari na ji lafiyar su sai ka ɗauku min wani zance".




"kiyi haƙuri Aunty na". Tace, "ba komai, ka kirata kaji dan naga yau kamar bata jin daɗi"..... ai tun bata kai ƙarshin zancin ba ya datse kiran nata.




Number ta ya kamu ya saka kira, kwanci take kamar mai bacci amma ba bacci take ba, tunanin mafarkin datayi jiyane takeyi, wayar tace da ta shiga rura ta mai data daga duniyar tunani, wayar ta ɗauku haɗi da danna picking ta kara a kunni ta.




Sallama tayi masa ya amsa, bayan ta gasheshi haɗi da masa ban gajiya kana yace, "naji muryarki kamar mara lafiya?".


Murmushi tayi kana tace, "lafiya ta ƙalau ya Baby tah".


karki tambayeni dan sai da nace kizo ki ganta kikace a'a, kin ga ko ba dole na faɗamiki ya Baby take ba".


Tace, "kayi haƙuri Babban Yayana". har zayi magana sai aka turu ƙofar ɗaki, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai yaci gaba da firarsa.




Jikita a sanyaye ta fara takawa har ta kawo wajan da yake kwance, Baby ta aje kusa dashi kana ta zauna zaman jiran ya gama waya, baya ya gama kana ta ƙaraso kusa da shi tana faɗan, "Baban Baby barka da zuwa".




Sai da ya ɗau Baby kana ya amsa mata haɗi da tambayar ta lafiyar ta.




Baby ya zubama ido wadda tunda ya ɗauke ta yaji sonta na shiga zuciyar sa, huɗuba yayi mata yana gamawa sai Maryam ta dubeshi tace, "wani suna zaka saka mata?".




Batari da wani tunani ba yace, Hafsat".


Dubansa tayi da kyau tace, "kenan ka canja suna dan na zata sunan Mumy zaka sa".




Yace, "a'a sai wani lokaci nasa insha Allah".




Haka dai ya daure yana fira da ita kana ya tashi yaje yayi wanka ta kawu masa abinci yaci, amma duk abinda yake ɗiyar na hannusa, wanka ne kawa da zaiyi ya ijeta.




Yana cikin haka sai akaturu ƙofa, abukin sa Jabir yagani tsaye yana masa wani kallo, a hankali ya buɗe baki yace minayi zaka yimin wannan kallon haka".


Kafin ya bashi amsa Maryam ta gashe da Jabir kana ta ɗau Baby ta fice.


Bai ce dashi komai ba sai da ya shigo cikin parlour yace, "wai yaushe zaka gama course ɗin da kajeyi ne?".


Sai Sulaiman yace, "sai ta gama ".


Jabir yace, "wallahi ni nasan bawani course da kaje, kajene dan kayi tsaron ta, to bari kaji wallahi baka isa ka tsareta ba, dan yanzu kazo nan amma bakasan meke faruwa acan ba, ni dai shawara ta gareka ka dawo kacigaba da aikin ka kuma kariƙe matar ka duk yafiye maka bin sauran wani".....tun bai kai ƙarshe ba ya ɗaga masa hannu yace, "Jabir daka ta!".




Idonsa ya ɗago ya kalleshi waɗan da saka sauya lokaci ɗaya yace, "bari kaji Jabir wallahi ko ɗa ɗay-ɗaya har ashirin Hafsat ta haifa tare da Anwar ba ta hanyar aure ba wallahi sai na aure ta muddin tace ta amice da haka".




Jabir yace, "har yanzu baka san waye Anwar ba, kuma waye Hafsat ba, kuma nasa ko yanzu Anwar yaje ga Hafsat zata yarda dashi dan tana masa son bana wasa ba".


Irin yadda yada yaga bacin rai afusakar Sulaiman dan haka ya tashi ya kama hanyar fita, sai da ya kawo gab da ƙofa kana yace, "nasan baka san me nasani ba gami da Anwar ba, to bari kaji yanzu haka Anwar yahe india". yana faɗar haka ya rufe ƙofar ɗakin da ƙarfi kana ya bar gidan ciki da ƙunar zuciya.




Aikuwa Sulaiman najin haka basan lokacin da ya tashi zaune ba, "yana faɗin wallahi ƙarya ne".






Ba tsaya wata-wata ba ya ɗau kye ɗin motar ya bar gidan, School ɗin su Hafsat yaje neman Safiyya da ƙawar ta Naja'atu.




Shiko Jabir ba abunda ya tsana kamar yaji abukin sa yace zai aure Hafsat, dan shi aganinshi bata dace da Sulaiman ba, dan shi abinda yafi tsana hulɗa da talaka.




Koda ya isa school ɗin ba kowa ya samu ba, sai ɗai-ɗaiku, sabida ana weekend dan haka ya samu wata cikin ƴan makarantar taje hostel take ki rumasa Naja, amma koda taje Naja batanan taje gida weekend.




Koda ta zo ta gaya masa hauka ne kawai baiyi ba, kuma gashi bai san gida ko ɗaya daga cikin su ba, dan haka ya shigo mota ya dawo gida, Allah ne ya kaishi gida lafiya dan yadda yake gudu kamar ya gaji da ransa.


Yana zuwa gida ya kasa zama ya kasa tsaye, dan haka ya shiga mota ya kama hanyar gidan iyayen sa.




Parlour ya tarar da Mumy sa da Abbansa, tunda ya shigo suka zuba masa ido suna kallon sa, Abban sane ya fara magana yace, "Yaro na mike damun ka na ganka haka kamar kana cikin tashin hankali?".


Sai da ya sauke ajiyar zuciya yace, "eh to Abba dan akwai wani abinda ya taso gami da karatun da naje can india shine nake son gobe na koma"......tun bai rufe baki ba Mumy sa tace, "kar kasoma dan idan ka ga ka bar ƙasar nan to anyi suna, na gaji da wannan ƙaƙale-ƙaƙale naka fa, tunda akayi auren nan baka zauna ba bare ku fahinci juna kai da Maryam, dan haka ba inda zaka je".




Sai da ta gama Abban sa ya dube shi kana yace, "my Son kaje kashirya idan Allah ya kaimu gobe sai kaje ɗin".


Har Mumy zatayi magana Abba ya ɗaga mata hannu haɗi da faɗin "fatar alhairi kawai nakeson kiyi masa".




Ba dan ranta yaso ba tayi masa fatan alhairi haɗi jadda da masa yaje ya tambaye Maryam duk abinda bata da tagaya masa.




Yace tom haɗi da tashi dan yaje ya fara shirin komawa, har zai fita Abbansa yace, "son wani suna kake so asawa yarinyar nan".




Sai da ya sosa ƙyya kana yace, "Hafsat". Yana faɗa ya fice bai jira cewar su ba.




Wani sanye daɗi ne ya mamaye Mumy ita da Abba, sai Abba yace "mun gode da wannan kyautar".


Ita Mumy kasa magana tayi sabida daɗi, dan sunan mahaifiyar ta ne, kuma tunda ɗiya ta taso asa mata amma ƴan uwan Abba suka hana sai yanzu da Allah ya yarda asa ga jikar ta.






Kafin ya koma gida sai da ya tabbatar da ya samu bisa da duk wani abun da yake buƙata.




Lokacin da ya faɗawa Maryam tafiyar sa, har kuka sai da tayi amma dayake mai sanye ce daga baya tayi masa addu'ar tafi lafiya da dawo lafiya.




Tun shida na safe jirginsu ya ɗaga zuwa india, sune basu sauka ba sai cikin dare.


Koda ya isa masaukin sa sose yagaji dan haka ya watsa ruwa ya kwanta.






*****
Tunda tayi sallah asuba bata sake kwanciya ba, gyaran gida tayi kana ta hada musu beark, bayan ta kammala taje tayi wanka tashiriya, cikin sauri tayi beark sannan tazo ɗakin Aunty Shemah tace zata tafi sabida lectura ne da ita da safen nan, key ɗin mota Aunty Shemah ta bata haɗi da iyimata adawo lafiya sabida ita yau bazata je ba.




Karɓa tayi da sauri ta ƙarasa wajan aje mota, tana shiga tayi mata key ta fice da sauri sabida gab take da ta makara.




Anwar tunda yayi sallah asuba ya tashi ya shirya dan tun yau yake son ya fara ne manta, sabida bashi da lokaci, dudu sati ɗaya ne zaiyi ƙasar, abukin sa na shiryawa suka fita zuwa cikin makarantar.







Sulaiman sabida ya gaji bai farka da wuri ba, dan ko sallah yau sai da ya makara baiyi ba, kuma yana gama sallah sai da ya kwanta, aikuwa koda ya farka rana ta fara fitowa, cikin hanzari ya shirya ko beark bai tsaya yayi ba ya kama hanyar gidan Aunty Shemah.






Koda yaje parlor ya tarar da ita tana beark, sallama yayi kana ya shigo, ido da baki ta zuba masa sai kallon sa take kamar yau ta fara ganin sa.




Ƙarasowa yayi ya zauna kana ya gaisheta, ba ta karɓa ba sai jefa masa tambayar da tayi "miya dawo da kai yanzu?".




Sai da ya ɗau kofin tea kana yace, "akwa abinda ya mai dani, Aunty ina Hafsat?".




"Hafsat ta mai daka ko".




A'a Aunty, su Mumy na gaisheki kuma sunci kin daina kiransu".




Shareshi tayi dan sose ya bata haushe ace ya dawo jiya.




Sai da ya ta kurata da tambaya tace, "taje makaranta".






Ƙofin dake hannunsa ya aje yace bari nazo.




Mamaki ya cika ta, dan haka takasa baki sai kallon sa takeyi, dan ta lura yadda yadamu da Hafsat ita bata damu da shi ba, sai ma gani take kamar batasan yana son ta ba.




Tanayin parking ta fito haɗi da kulle motar, tana cikin haka sai ga ƙawar ta Zeenatu ta ƙaraso tace, "kizo muyi sauri mutafi dan munkusa mu makara, "tace to muje" .


Tafiya suke suna fira har suka kusa kai class.


Anwar da abukinsa sai sauri suke su isa wajan da suke tunanin zasu ganta, tafiya suke ita da Zeenatu, shiko Anwar yana bayan su shida abukinsa, dan har yasu ya ijesu ya wuce sabida basa sauri sai wata tafiya suke kamar basa son taka ƙasa, kuma ga hanyar da zata sada su class ɗinsu akwai cinko so da yawa, abukinsa ne ya riƙeshi yace mubi komai cikin natsowa insha Allahu zaka ganta".




Badan yaso ba suka biyewa tafiyar su har suka kawo hanyar da zata sada su class kana suka raba hanya.






********
Kamar wadda aka koro sai gata tashigo ɗakin tana faɗin, "Zahara! Zahara!.


Da sauri ta fito daga toilet tana faɗin, "Hajara lafiya kuwa kikazo min haka?".




Tace, "ina lafiya tunda Anwar ya asirceni duk abinda yace namasa shi zan masa, amma ni duk abinda na nuna masa ina so wallahi bayayimin, gashi yanzu nabashi address ɗin shegiyar yarinyar nan, dan haka nake son ƙarfe ukun dare ki rakani muje wajam Malam kinga sai na kwanan anan iyaso lokaci nayi muje".






Sai Zahara tace, "to mi kike son iya gami dashi Anwar da Hafast ".




Hajara tace, "ni so nake iya masa abinda baya ganin kowa sani, sannan ita ko akorota daga karatun da take a india, dan na tsane jin tana can , kinga idan ta dawo tana gani tana ji muyi Aure da Anwar inya so tazo tanamuna wanki da wanke-wanke".




Tafawa sukayi haɗi da sanya dariya mai ciki da ma'anuni da yawa.






Tun biyu da rabi na dare suka tashi suka shirya kana suka ɗau hanyar gidan Malamin su....














*#Vote*
*Comment*
*Share*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*












*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*








~~WattpadSummy M Na'ige~
















*SHAFI NA 24📑*












*__________📖* Bayan kwana biyu suna zaune da Aunty Shemah parlour suna fira sai suka jiyo sallama bakin ƙofar parlour, tun kan su ƙarɓa sai affan ya zo da gudu yana faɗin, uncle, uncle".
Sulaman hannayensa ya ware Affan ya shiga jikin sa yana faɗin, "my son lafiya kake?".




Sai da suka ƙaraso cikin parlour kana Affan yace, "eh uncle". surutu ya fara mishi amma Sulaiman bai kulashi ba ya kai dubansa ga Aunty yace, "My Aunty ya kuke ya gida?".




Kafin ta amsa masa ya kai dubansa ga wajan da Hafsat ke zaune duk ta ta kura, dan ba wani kayan kirki ne ajikinta ba kuma gashi yayi musu bazata, tana so ta gaisheshi amma ta kasa sabida yadda ya kifeta da ido, shiko yaƙi ya janye idon sa, sai jira yake ta gaisheshi, ita ko ta kasa buɗa baki ta gaisheshi, muryar Aunty Shemah ce da yaji ta amsa masa haɗi da tambayar sa yaushe zai je gida, sannan ya mai da duban sa ga Aunty Shemah yace, "wata ƙila gobe na wuce".


Tace, "bawani wata ƙila dole gobe kaje, sabida zuwanka dole ne dan inba kaje ba sai aɗauka dan baka sonta ne zaka ƙin zuwa".




Suna cikin firar sai Hafsat ta sulale tayi ɗakin ta.




Duban Aunty yayi da kyau kana yace, "kada ki damu Aunty insha Allahu gobe zanje".
haka suka cigaba da fira har wani lokaci.


Duban wajan da Hafsat take zaune yayi, amma sai yaga bata wajan, dubar parlour ya fara amma bai ganta ba, lura da haka da Aunty Shemah da tayi sai tace, "wai Sulaiman me ke son afkuwa ne gareka gami da Hafsat?". murmushi yayi haɗi da sose ƙyyar kansa, bata jira cewar saba tace,
"bari na turumaka ita". tana faɗar haka ta tashi taje ɗakin Hafsat.




Bata jima da tafiya ba sai ga Hafsat tazo parlour sanye da wata atamfa wadda akayi ma ɗikin riga da sikit, sose kayan suka karɓe ta duk da ba wata kwaliya tayi ba.




Zama tayi kan kujera da ke nasa dashi kaɗan kana tace, "ina wuni Yaya Sulaiman". Bai amsa ba sai ido da ya zuba mata yana kallonta kamar yau ya fara ganin ta.




Har zata sake maga yace, "ƴan matan Aunty ya karatu". Murmushi tayi haɗi da sadda kanta ƙasa kana tace, "alhamdullah".


Shuru ya biyu baya sai can tace, "ashe Yaya munsamu ƙaruwa, Allah ya raya akan sunnanh". da yake matar shi ta haihu shine Aunty Shemah ta gaya mata kuma dan haka ma zai koma najeria yayi weekend ya dawo dan iyayen sa sun da meshi akan sai yaje, kuma in bai jeba za suga kamar dan bai son matar ne yaƙi zuwa, ba dan ranshi yaso ba ya amnci zai je.




Kallon ta yayi yace, "ko zaki je gobe muje tare in zan dawo sai mudawa tare?".... kafin ya kai k'arshin maganar tace, "a'a ni ba inda zanje sai na kammala karatuna gaba ki ɗaya". kallon baki isaba yayi mata kana yace, "idan ƙarshin shekara tayi naga mai barikin anan".




Murmushi tayi tace, "Yaya Sulaman ai nasan ko kai bazaka bari na koma najeria ba sai na kammala".


Yace, "hmmm nasan ko yanzu aikwai abinda ya hana ki zuwa, da ko dan kiga sahibinki zaki zo muje".
yafaɗi haka zuciyar sa na ƙuna dan ba abinda yafi tsana kamar ya tuna Anwar.




Duban sa tayi ido cikin ido tace, "wake nan?".


Sai da ya aikai mata kallo mai kama da harara yace, "kin fi kowa sani".


Tsaf ta gano wajan da ya nufa amma sai ta sauya magana tace, "gobe da ƙarfe nawa zaka je".




Ƙyaleta yayi kamar bai jiba har ta koma mai-mai ta masa amma bai ce mata komai ba, kuma tasan sarai yaji ta amma ya ƙyaleta.




Tashi yayi ya kama hanyar fita batari da yace mata komai ba, tana ganin haka da sauri tazo gareshi tana faɗi, "haba Yaya Sulaiman me na maka yanzu nan". tana faɗa kamar zatayi kuka.




Hankan da tayi magana ne yasa ya dubeta, lokaci ɗaya yaji son ta na ƙara fizgarshi, ji yake kamar ya jawota jikin sa, a hankali ya fara taka ƙafar sa har yazo gab da ita, kallon ta yayi ido cikin ido da yace, "ba abinda kikayi min sai dai ina son ki kulamin da kanki kafin na dawo, duk da nasa Aunty na iya ƙoƙarin ta amma dan Allah ki ƙara kula".




Kwarjini yayi mata dan haka ta kwada idon ta kyafe ɗaya tana faɗin,"kar kadamu Yayana insha Allah zan kiyaye". irin yadda suke magana da junan su gwanin ban sha'awa.




Har zai tafi tace, "bakayi sallama da Aunty ba?".


Yace, "zan dawo gobe kafin na wuce". bai bari yaji mi zata ce ba ya fice warsa.




*******
Duk wata hanya da zata samu masa address ɗin ta bi kuma cikin ikon Allah ta samu masa sunan makarantar da take, amma abu ɗaya ne bata samar masa ba, wanda ita kanta bata sani ba gidan data ke zaune.




Bayan ta kammala komai ta kirashi ta faɗa masa, yace ta turu masa, sam ta manta da alƙawarin da suka yi tsakanin su, bawani ɓata lokaci ta tura masa da address ɗin, sai da ta tura masa kana ta tuna, sose hankalinta ta ya tashi, dan haka ta ɗau mayafinta ta fice taje wajan ƙawar ta zahara .




Shiko Anwar tana tura masa bai tsaya ɓata lokaci ba ya fara bincikin makaranta, bayan kwana biyu da fara bincike ya gano duk wani abinda yake buƙata, dan haka ya fara shirin tafiya.


Ana gobe zai tafi yaje ya same iyayen shi ya faɗa musu cewa gobe idan Allah ya kai mu zai tafi india, addu'a suka mishi haɗi da fatar tafiya lafiya da dawo lafiya.




Safiya na waye wa ƙarfe bakwai jirginsa ya ɗaga zuwa india.








Shiko Sulaiman tunda sassafe yazo yayi musu bankwana ya wace filin jirgi yashiga jirigi ya wace najeria.


Mama ko tunda suka dawo daga garinsu ta ɗan ji sanyi har ta ɗan dawo dai-dai amma ba kamar daba, dan burinta a kullum ta ga ƴar

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads