Showing 6001 words to 9000 words out of 49839 words
Chapter 3 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt
fiki jin haushi tunda tafiki son karatun". haka yaci gaba da yi mata faɗa da daɗin baki ƙarshe ma ya umarce ta data kashe wayar ta dan ko an koa kiranta baza'a same taba.
Dan yace bazaiyi komai ba sai yagama aikin da ya kawoshi.
Tun daga lokacin Safiyya ko ta kira wayar Hafsat kashe take, sosai hankalinta ya ƙara tashi dan har gadin sa taje amma mai gida yace ya yi tafiya , tunda taji haka gaba ɗaya ta rasa natsuwar ta har dai lokacin da Mamar Hafsat ta kirata tace takira wayar Hafsat kashe ko lafiya?.
Tace eh mama karatu ne yayi mata yawa dan har saƙo tabank na faɗa muku to nima ban dawo ba saboda hostel nake kwana.
Aikuwa Mama Hafsat na jin tare da Safiyya suke ta samu natsuwa kana tayi musu fatan alhairi.....
*SUMMY M NA'IGE*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*SHAFI NA 6📑*
*__________📖* Bayan ya kammala abunda zai kaishi suka dawo gida da sati ɗaya taneme ya barta dan taje school dan Monday za su fara exams.
Yace ta shirya ya kai ta amma kafin ya dawo gida ta tabbatar da tadawo dan baya son yadawo babu abunda zaici.
School ɗin ya aje ta kana ya ƙarasa wurin aikin sa.
Class ɗin su taje bata jima da zuwa ba aka fara lectura.
2 dai-dai suka gama lectures ďinsu,kuma suna fitowa bata tsaya komai ba ta kama hanyar fita.
Har zata fita daga cikin makarantar sai Safiyya ta ganta tana ta sauri,da saura Safiyya tayi ƙarasa gare ta.
Mayafin ta ta riƙo,lokacin da take daf da fita school ɗin.
Safiyya tace, "ina zakije dakike ta wannan sauri haka?".
Kallon sama da ƙasa tayi mata kana tace, "wurin da kika aikeni zan je" tana faɗa tana hararar ta.
Sai Safiyya tace, "koma dai me yau ba inda zaki dan Mama na can hankalin ta tashe tana sun ganin ki dan haka yau gida zamuje ta gannki ko tasamu natsuwa".
Hafsat tace, "Safiyya har sau uku taki ra sunan ta, bana son kina shiga rayuwa ta Safiyya kirabu dani nayi rayuwata,ki barni rayuwar ki ko tawa? kuma bazan je gidan ba inki haihu da uwarki kije kifaɗa ɗin ina gidan saurayi na".
Tana faɗar haka ta kama hanyar fita ta bar Safiyya sake da baki tana kallon ikon Allah.
Har zata fice sai ta dawo,gaban Safiyya ta ƙarasu kana tace, "daga yau kada ki kara shiga rayuwa ta dan ni tunda jimawa nafitar dake rayuwa ta dan haka kema ki barni bana son sa idon".
Mai adai-daita ta tara kana ta faɗa masa unguwar da zai kaita.
ita ko Safiyya gaba ki ɗaya mamaki da tsoro sun da baibaye zuciyar ta,dan gani take kamar ba kai sake Hafsat ke gaya mata wannan maganar ba,amma a ko da yaushe tana wa Hafsat fatar shiriya itada kullihin musulmi.
Bayan ta dawo daga school wanka tayi kana ta gabatar da sallah sannan tazo ta fara gyaran gida,tana kammalawa ta ɗura sanwa.
Saura ƙiris ta kammala sai gashi yadawo,aikuwa tunda taji horn ɗin motar sa gaban ta ya bada dummmm,saboda bata kammala girgin taba kuma tasan halin sa sarai baya sun jira.
Tana cikin wannan tunani tafara jin knocking ɗinsa.
Da sauri taje ta buɗe masa ƙofa dan kar ta ƙara ma kanta wani laifi.
Ƙarɓar jakar dake hannun sa tayi haɗi dayi masa sannu da zuwa.
Karɓawa yayi haɗi da ƙarasuwa daga ciki.
Ruwan wanka ta haɗa masa,bayan yayi wanka ya fito, ta tayashi shiri,bayan ya kammala shirinsa parlour ya fito dan yaci abinci dan ya kwasu yunwa yau.
Komai bai gani ba a dinning, dan haka ya ƙwala mata kira,ita ko tana can tana sauri taga komai ya kammala amma ina dan tana cikin haka taji yana kiran ta.
Da hanzari tazo gareshi,aikuwa tunda ta ƙarasu ya jefeta da wani kallo wanda yasa cikin ta juyawa lokaci ɗaya.
Tambayar ta ya farayi yace, "ina abinci na?".
Jikin tane ya fara karkarwa tace, "kayi haƙuri nakusa kammalawa".
Sai da yajefe ta dawani kallo kana yace, "sai yanzu kika dawo kenan?".
Kai ta fara girgiza masa tace, "a'a muna gama lectures na dawo wallahi ko ina banje ba".
Tsawa ya da kamata haɗe da cewa karya kikeyi kin dai tsaya iskancin kine shiya sa baki dawo ba" nan ya dinga cin zarafin ta har da kukan ta tana bashi haƙuri amma yaƙi ko saurarin ta,daga ƙarshe ma key ɗin motar sa ya ɗauka yafi ce a gidan.
Har ya fita ya dawo ya ƙwala mata kira, da sauri tafito daga kiching haɗi da durƙusawa gaban sa.
Tun bata kai da durƙusawa ba yace ta haɗa kayan ta tabar masa gidan sa.
Aikuwa yana faɗar haka da sauri ta faɗa jikinsa tana bashi haƙura,amma ina baya ko saurarin ta dan da ƙarfi yajaye ta jikin sa ya kifeta da wani azaftaccin mari har guda biyu kana yace, "kuma wallahi kafin na dawo kinbar gidan nan tunda ba na ubanki neba" yana faɗar haka ya ficewar sa yana huci".
Kuka takeyi kamar ranta zaifita dan ita ba komai yafi ƙona mata raiba irin yadda yace tabar masa gida, to ina zata je?.
Wani tunani ya faɗu mata arai aikuwa da sauri ta miƙe daga durkushin da take ta koma kiching taci gaba da aikin ta.
Bayan ta kammala girki, sosai ta fara gyaran gida,bayan ta kammala tasaka turare mai ƙamshin gaske wanda lokaci ɗaya yasa gida yabada wani ƙamshi mai sanyaya zuciya.
Toilet taje tayi wanka,bayan ta fito ta shafe jikin ta da ma yukka masu ƙamshi haɗi da hummara ta musamman,dressing ɗin english wears tayi masa wanda tasan yafi so sosai.
Tana gamawa ta ɗauko wasu turarukka ta feshe jikin ta dasu.
Tarigi ya ta ɗauru alwala,sallah magarb da isha'i ta gabatar kana ta fito parlour ta zauna zaman dawowar sa.
Batayi minti biyar da zama ba sai ga horn ɗin motar sa.
Aikuwa da sauri ta ƙara feshi jikin ta da turare haɗi da dauko lollipop tasaka a baki, ta fara tsutsu sai kace wata ƴar yarinya.
Bai ma tsaya wani knocking ba yasa key ya buɗe ƙofar.
Tsaye ya ganta tana masa murmushi haɗi dayi masa wani kallo mai ciki da so da ƙauna.
Jikin sa tafaɗa haɗi da faɗin "My Hubby nah, sannu da zuwa".
Har ya buɗa baki yayi magana sai tayi sauri ta haɗa bakin sa da nata tana shayar da shi lolopop ɗin da ke bakin sa.
Aikuwa tuni jikinsa ya karɓi saƙon da take bashi haɗi da shaƙar ƙamshin da ke fita a jikin ta.
Bare abu ga ma abuci son ƙamshi,sosai ta mantar dashi fushin da yakeyi da ita,tsayowar ce ta gagaresu dan haka cak ya ɗauke ta zowa bedroom ɗinshi.
Sai da komai ya lafa kana ya jawuta jikin sa sosai kana yafara magana ahankali yace, "My love jibi ne ta fiyar dan haka ki kasan ce cikin shiri dan tafiyar safe zamuyi".
Gabanta ne ya faɗi dan ita har ta manta da wata tafi ashe tafiyar na nan kuma gashi Monday za su fara exmas.
Jikin ta asanyaye tace, "Allah ya kaimu jibi lafiya".
"Ameen" yace da ita haɗi da kai bakin shi da nata ya fara kissing ɗin ta.
Duk abunda yake mata bata wani jin daɗin sa saboda tunda yayi maganar tafiyar jikin ta yayi sanyi dan tunani take anya zata bishi tabar exmas ɗinta?kum gashi aski yazo gaban goshi dan daf take da ta kammala degree ta afannin gaenacology kuma da bata ci wannan exmas ba zasu iya withdraw ďinta kuma gashi tana da carryover har guda biyu.
Suna cikin haka tace, "a'a gaskiya bazan jeba".
Ahankali yace, "mikika ce?".
Tace, "aa ba da kai naki ba".
*************
Yau takama Monday kuma yau zasuyi tafi kuma yau zasuyi exmas.....
Wani zatayi tafiya ko exmas......
*__________📖*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*SHAFI NA 7📑*
*__________📖* Yana gama shiri yafito dumin su tafi dan baya sun suyi rana.
Kiran ta ya farayi,ita ko tana can tana tunani ta tafi ko karta tafi,rasa me zatayi tayi,gashi tana tsoro rashin yin exmas ɗinta, kuma tana tsoron ɓacin ransa.
Kiran da taji yana mata yasa gabanta dukan uku-uku,alamun zai shigo ɗaki data ke ciki taji dan haka da sauri ta fara haɗa kayan ta cikin jikar da zata tafi da ita.
Koda ya shigo har tasa tufafin ta tana yafa mayafin ta,amma fuskar ta a ɗaure kamar tayi kuka.
Magana yayi mata yace, "kefa nake jira".
Tace,"nashirya mutafi" tafaɗa haka kamar tayi kuka.
Fitowa tayi ɗauke da jika a hannunta,jikin ta a sanyaye ta rasa ya zatayi,tana cikin haka taji yace, "muje zan kulle ƙofa".
Fita tayi ya kulle ƙofa kana ya shiga mota ya tada.
Gabanta ne ya tsanan ta faɗuwa sosai, lokaci ɗaya wasu hawaye suka fara fita a idon ta.
Magana yayi mata yace ta shigo sutafi.
Kamar bata ji shiba tayi sai da yayi magana cikin faɗa-faɗa kana tabuɗe motar tashiga tana mai saka kuka kamar wani yayi mata dole sai taje😏.
Aikuwa yana tada mota kukan da takeyi ya tsanan ta.
Dubanta yayi kana yace, "mi akayi miki da zaki saka min kuka,ko tafiyar ce bazakiyi ba ne?".
Kanta ta fara girgiza masa kana tace, "a'a kayi haƙuri na daina".
Yace, "to ki shafe hawayin ki dan bana son jin kuka kinji ko".
Hawayen ta tashafe haɗi da cemasa "to".
Tunda suka kama hanyar tafiya gaba kiɗaya hankalin ta atashe yake, dan tunda take dashi bata taɓa jin irin wannan tashi hankali ba kamar na yau,amma kuma bazata iya ce masa baza ta jeba,har suka fara fita daga cikin gari ba wanda ya cema ɗan uwansa komai.
Saura minti biyar afara exmas sai Safiyya tazo bakin class ɗinsu taga ko Hafsat tazo,aikuwa tana ƙarasuwa taga class ďin kowa yazo amma sit ɗin Hafsat wayam,gaban Safiyya ne ya bada dummm da sauri tashigo class ɗin.
Wata abukiyar karatun Hafsat, Naja'atu ta tambaya tace, ina Hafsat?".
Sai Naja'atu tace, "ai Hafsat ta daina zowa school dan tun dawo wa hutu sau biyu ta shigo class,kinga ma exam card ɗinta yanzu haka ita nake jira".
Safiyya tace, "bata da lafiya,amma nasan yanzu zata zo,bani card ɗin nabata dan sauran kayan ta ma na hannuna".
Ba musu Naja'atu ta bata.
Aikuwa tana ƙarɓa da sauri ta fito ta kama hanyar hostel,tana zowa tasumu arun niƙaf tasa afuskar ta ta dake ma ran,ta tashiga class ɗin haɗe da addu'oi Allah kasa kada agane ba Hafsat ce ba.
gaban ta na duka uku-uku haka taje ta zauna saman sit ɗin Hafsat batari da tawa kowa magana ba.
Ko minti biyu batayi da zama ba aka fara raba Question paper.
Ana kawo wa gaban ta,gabanta ya bada dummmm,addu'a takeyi Allah kasa kada ace sai ta ciri niƙaf ɗin da ta sanya.....
*To fah Safiyya kin iya ganganci*🤔
*# Vote*
*Comment*
*Shere*
*©SUMY NAIGE.*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*SHAFI NA 8📑*
*__________📖* Cikin ikon Allah ya aje mata Question paper ya wucewarsa batare da yayi mata magana ba.
Aikuwa yana wuce ta ta fara yiwa Allah kirari a zuciyar ta haɗi da godiya a gare shi.
Tunda ga lokacin taci gaba da rubuta mata exams har suka kammala ba tare da ta samu wata matsala ba, sai dai gaba ki ɗaya ta dawo hostel da zama dan bata da lokacin komai sai na karatu, kuma tunda ta fara rubuta ma Hafsat jarabawa ba wanda ya gane ba Hafsat bace in ba ƙawar karatun Hafsat ba Naja'atu.
Sosai taba Safiyya gudunmuwa wajan ganin tayi ma Hafsat jarabawa, duk da ba department ɗaya suke da Safiyya ba amma tayi ƙoƙari sosai dan gabaki ɗaya ta hana ma kan ta barci ko da yaushe tana library wajan karatu, tayi nata tayi na Hafsat, har Allah ya nuna mata ta gama lafiya sosai tayi rama saboda rashin natsuwa da rashin isashen bacci.
Tunani ta farayi lokacin da suka gama exams yadda zata koma gida ba tare da Hafsat ba, dan haka ta yanke shawarar taje gidan sauranyin nata ta gani ko zata ganta,har zata je kuma ta fasa saboda ba ƙaramin baƙin cikin ganin sa takeyi ba dan haka ta yanke shawarar takira ta a waya.
Miss call kusan biyar tayi mata amma bata ɗauka ba sai ga na shidda kana ta ɗauka batare da tace komai ba.
Safiyya ba tadamu da rashin maganar taba dan haka tace, "kidawo dan ni zan koma gida kuma kin san da naje zasu tambaye ki dan haka gobe zan koma ko ki dawo ko kada ki dawo na dai faɗa miki".
Bata ma bari taji me zataceba ta tsinke wayar.
Ita ko Hafsat tunda suka sauka ya kama musu hotal bata sake koda leƙo ƙofa ba dan baya barin ta.
Kuma yanzu ko lafiya bata isheta ba dan yanzu bata da wani kuzari, ga wata rama da takeyi duk tabi ta bushe kuma tana cin abinci amma kamar bata ci, sosai abun ke bata tsoro dan ita gabaki ɗaya tunda sukayi tafiyar nan bata cikin kwanciyar hankali, abu kaɗan ya isheta kuka.
Yau ma kamar kullum suna kwance yana romance ɗin ta son ran shi, sosai yake jin daɗin abunda yake mata, ƙoƙarin shigar ta ya fara amma tana ɗan kaucewa, saboda yanzu ko kaɗan bata son abun da yake mata dan yanzu da ya gama abunda yakeyi da ita sai wani azaftaccin ciwon mara ya taso mata wanda kesa jikin ta kar-karwa lokaci ďaya.
Sosai take wahala kuma duk wannan uban ciwon marar dake taso mata ta gagara faɗa masa ya dena amfani da ita ko suje hospital a'a ita baza ta iya faɗa masa ba dan kar ransa ya ɓaci.
Duk da tana ƙoƙarin hanashi amma shi bai masan tanayi ba.
Ba ɓata lokaci ya afka cikin ta ya fara abunda yake so da ita son ranshi.
Aikuwa yana gamawa ya ɗan kwanta dan ya huta yaci gaba da abunda yake yi.
Ita ko yana sauka daga kanta, lokaci ɗaya wani abu ya taso mata ƙasan marar ta, tun tana dauriya kar ya gane har abu yazo yafi ƙarfin ta, lokaci ɗaya ta fara fita hayyacin ta, duban sa ya kai gare ta aikuwa lokaci ɗaya ya zabura ya mike zaune haɗi da tambayar ta, "lafiya mike damun ki"?.
Ita ko batama san yana yi ba saboda a lokacin bata masan inda kanta yake ba.
Abun yaga yafi ƙarfin sa dan haka da sauri ya saka jallabiya ya ɗauke ta domin suje hospital.
Cak ya ɗauke ta ya kai mota, rasa asibitin da zai kai ta yayi, dan dare yayi gashi kuma bawani sanin garin yayi ba.
Masu gadin hotel ɗin ya tambaya yace su nuna masa hospital mafi kusa? dan matar shi ce ba lafiya haɗi da nuna musu ita a cikin motar.
Wani private hospital dake kusa da hotel ɗin suka nuna mai godiya yayi musu kana yaja motar da gudu bai tsaya ko ina ba sai cikin hospital ɗin.
Cikin gaggawa Likitoci suka karɓe ta, lokaci ďaya suka fara bata taimako .
Sun jima kanta kafin su shawo kan lamarin.
Bayan komai ya ɗan lafa kuma ta samu barci dan haka suka fito daga ɗakin da take.
Yana ganin sun fito ya fara tambayar su ya jikin nata?.
Komai basu ce dashi ba sai babban doctor daga cikin su yace dashi "ka biyo mu office".
Komai bai ce dasu ba ya bi bayan su.
Bayan sun isa office dukan su suka zauna, kana suka nuna masa kujera domin ya zauna.
Bayan ya zauna sai babba daga cikin Likitocin yayi gyaran murya kana yace, "da farko dai munyi nasarar ceto matar ka dan yanzu haka ta samu bacci kuma insha Allahu ina har takiyaye ƙa'idojin da zamu ɗaura ta akai to babu shakka zata samu lafiya sosai da sosai.
Sai abu na biyu muna tayaka murnar matar ka na ɗauke da juna biyu har na tsawon wata huɗu....." aikuwa tun Doctor bai kai da ƙarasa maganar ba yace, "what haɗi da faɗin ciki!.
Gabaki ɗaya Likitocin kallon shi suka farayi cike da mamaki.
Dubin doctor yayi kana yace, "Doctor kun duba da kyau kuwa? dan ni matata bata da ciki gaskiya".
Results ďin scanning ďinta dake gaban sa ya bashi yace, "duba kagani".
Karɓa yayi ya fara dubawa, abunda yagani ne yayi matuƙar bashi mamaki da tsoro.
Yana gama dubawa sai ya ɗago da kansa yana kallan Doctor kana yace, "Doctor na gani kuma na yarda tana da ciki amma ina son a zubar da shi dan ba yanzu zamu haihu ba, ko nawane zan biya kawai a zubar da shi".
Tunda ya fara magana gaba ki ɗaya Likitocin suka zuba mishi ido suna kallon shi har ya kai ƙarshen zancen shi.
Sai da ya gama kana babba daga cikin Ƙikitocin yace, "kafin na gaya maka komai ina son kasan wani abu ɗaya, lokacin da kake ba matar ka ƙwayoyin hana ɗaukar ciki to kasani sosai sukayi mata illah a mahaifar ta, dan ikon Allah ne yasa wannan cikin ya shiga cikin mahaifar ta har ya zauna ya kai wannan lokacin ba tare da ya zube ba,sosai mukayi mamaki lokacin da muka ga yadda mahaifar ta take dan sanadiyar wannan magani da kake bata mahaifar ta tafara lalacewa sosai, dan ko da wannan cikin ya kai matakin haihuwa to na tabbata bazata iya haihuwa da kanta ba sai ammata aiki, dan haka yanzu idan kace a zubar da cikin to za'ayi ɗayan biyu, dan sanadiyar haka mahaifar ta zata iya lalacewa bazata ƙara ɗaukar ciki ba ko kuma wajan cireshi ta rasa ran ta, kaga ko baza kayi fatar ko ɗaya a cikin waɗan nan su samu matar kaba".
Sai da Anwar ya nisa kana ya dube Doctor yace, "Doctor kada kaji komai nasan haka bazata faru ba, kawai a cire shi dan bana son cikin".
Gabaki ɗaya Likitoci da ke office ɗin kallon sa sukeyi dan abunda ya faɗane ya basu mamaki.
Sai Doctor yace, "banƙi ta taka ba amma sai nayi magana da matar taka idan ta aminta acire to ba komai zamu cire amma idan bata aminta ba to gaskiya ba zamu cire ba saboda aikine mai wuyar gaske?".
Sai Anwar yace, "kada ka damu da matata dan nasan zata aminta dan haka kuyi aikin kawai".
Sai doctor yace, "a'a sai naji ta bakin ta".
Sai Anwar yace, "ba damuwa idan ta farka zaka iyayi mata bayani".
Doctor yace, "ba damuwa".
Bayan gari ya waye kusan ƙarfe goma Hafsat ta farka, kuma Alhamdlillah dan ta samu sauƙi sosai.
Bayan tayi wanka tayi break tasha magani Doctor yazo ya duba ta kuma yaga jikin da sauki dan ba wata matsala yanzu dan haka yace bari yakira sauran Likitocin.
Aikuwa yana fita Anwar ya ƙarasu gareta wani kallo ya jefa mata haɗi da yimata ya jiki.
Bayan ta ƙarɓa yace, "ni zaki munafur ta, ashe kin san kina da ciki amma kika ƙi sanar dani, to bani kika cuta ba kanki dan ni bazan aureki da ciki ba dan haka tun wuri kisan