Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 49839 words

Chapter 2 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt

Ads the beginning of article before Image

23 Jun 2024

469

Ads at the middle of Article

yana faɗa yana kashe mata ido ɗaya.




Komai bata samu damar cemasa ba ya umarce ta data cigaba da akinta.




Yana zaune yana kallonta har ta kammala ta zuba masa yaci, amma yace sai tare za suci tace sauri takeyi ta koma gida yace duk batare za su cibashi bazai ciba.


Da kyar ta yarda ta zauna sukaci.


Bayan sun kammala ta ɗauko maganin sa tabuɗe ta bashi yasha kana tayi masa sallama tace zata wuce.


Har takai ƙofa ya ce gobe tazo har tace ba zata zoba ya yi kamar ya yi kuka, da taga haka tace masa zata dawo.




Haka Hafsat taci gaba da zuwa wajansa har ya samu sauki.


Ranar koda taje ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya ya yi kyau sosai, gashi abu ga mai kyau jinin fulani gashi kuma nira ta zauna masa.




Tunda ta shigo suka kife junan su da wani kallo mai wuyar fassarawa haɗi da sakarma ko wane murmushi mai ciki da so da ƙauna.






Alamu yayi mata data ƙaraso.


Ba musu taje gareshi,tasowa yayi daga wajan dayake zaune yazu daf da ita.


Kallonsa tayi haɗe da gaidashi ya amsa jikin sa duk akasalan ce.


Tashi ya yi ya ɗauko mata ruwa haɗi da wani lemo mai haɗe da wata ƙwaya wadda shi ka dai yasan ko tame ce ce.


Zuba mata ya yi tasha aikuwa tunda tasha ta farajin wani sauyin yanayi a jikin ta, lokaci ɗaya wata muguwar sha'awa ta taso mata.


Shi kuwa tunda tasha lemun yake binta da kallo har yaga maganin da yasa ya fara aiki ajikin ta lokaci ɗaya.


Akuwa lokaci ɗaya ya fara shafar jikin ta haɗi da yima ta kalamai masu kashi jiki,yana yadda yaso da ita haka yaci gaba da romance ɗinta har ya samu ya rabata da mutun cinta.


Koda maganin ya sake ta tayi kuka har tagaji kuma ta jefeshi da miyagun kalamai sosai ya
ji zafin kalaman ta.


Amma ya dake yaci gaba da bata haƙuri,amma ko kallo bai isheta ba.


Haka tasanya kayanta tayi tafiyar tagida.


Aikuwa tun daga ranar duk wata hanyar da zai ganta ta rufeta,shiko duk inda yasan zai ganta yaje amma bai gantaba haka har ya haƙura,ranar yana kwance yara sa miya ke masa daɗi agarin sokoto dan har ya yi niyar ya bar garin ya koma garinsu ,sai wata dabara ta faɗu masa lokaci ɗaya yamike yaje wajan wata abokiyar karatun Hafsat ya gaya mata abunda ake ciki kuma ya bata kuɗi masu yawan gaske yace idan
ma tashirya su abunda zai bata sai tayi mamaki.




Sosai Hajara ta ruɗe dan haka ta ɗau alƙawarin ko ta halin ƙa-ƙane sai ta kawo masa Hafsat.


Aikuwa tun daga lokacin Hajara ta liƙema Hafsa duk inda Hafsat take Hajara na can,dan shi Safiyya ta jama Hafsat baya dan Hajara kowa yasan ta ba yarinyar kirki ceba.




Watara na suna fira da Hajara sai ta ɗauko mata labarin Anwar da rashin lafiyar da ya yi yanzu haka yana kwance ba shida lafiya sosai.


Duk da abunda tafaɗa ya dake zuciyar Hafsat amma tadake bata cema Hajara komai ba.


Sai ma magana tama ta akan ta daina yi mata maganar sa dan har da faɗa sai da sukayi kafin su rabu.




Dare nayi Hafsat ta kasa kwanciya ba abunda take tunani sai shi,sosai ta matsu safiya ta waye taje gidan sa tagano ko ya ya tashi.


Tun shidda da rabi ta fito daga gida ta kama hanyar gidan sa.


Koda taje sai da ta musu knocking a ƙofar gidan maigida ya buɗe ƙofa ya fito.


Gasheshi tayi kana ta tambaye shi ko Anwar nanan.


Yace baya gari dan ya kwana biyu baya nan,sosai taji zafin rashin samun sa dan yanzu wani son shi ne takeji wanda ji take idan bata ganshi ba zata iya mutuwa.




Godiya tama Baba maigida kana ta kama hanyar makaran ta.




Har akatashi shoocl bata ga Hajara ba kuma duk inda tasan zata ganta taje amma bata same taba.


Ba ƙaramin tashin hankali ta shigaba lokacin da takira wayar Hajira akace kashe take.


Alokacin duk wanda ya ganta yasan bata cikin natsuwar ta.


Danhar Mamar ta ta tambaye ta amma sai tace wata exmas ce za suyi mai zafi shiyasa take jin tsoro.






Addu'ar samun nasara Mamar ta tama ta haɗi da bata shawara.


Dadare tana kwance ta kuma gwada kiran Hajara tace ko zata samu,aikuwa cikin sa'a tana kira tafara ringing.


Ringing da bai wuce uku ba Hajara ta ɗauka tace,


"Ya aki ciki ne Hafsat?".


Sai da Hafsat ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "kina ina yanzu?".


Kai tsaye tace, ina layin bugi".


Sai Hafsat tace, "Subuhanallah, miyakai ki layin bugi kuma?".


Sai Hajara tace, "tambayana kikayi nabaki amsa,dan haka bana sun dugon surutu".


Sai Hafsat tace, "kodama numbar Jawad nake son ki bani idan kina da ita ko kimin misalin wajan da zan samun sa".




Aikuwa Hajara najin me tace ta bushe da dariya haɗi da cewa,"komai kikeso nabaki ki sameni wajan da nafaɗa miki yanzu nabaki abunda kike so".


Duk da dariyar da tasa mata tayi mata zafi amma sai ta dake tace, "dan Allah Hajara ki bani wallahi bazan iya zuwa layin bugi ba,bare yanzu da dare".






Sai Hajara tace, "tunda abunda kike nema bai dameki ba sai anjima".


Har zata katse waya sai Hafsat tace,"zanzo ki gayamin dai-dai ina zan sameki.


Tace, "dakin zo kikirani zan fito".


Tace kada ki kashe waya gani zuwa.


"Aa bazan kasheba".


Aikuwa suna gama waya jikinta har rawa yake ta shiyar taje ɗakin Mama tace zataje gidan su Safiyya ta karɓo jikarta dake hannuta dan karatu zatayi.




Mama tace to taje amma kar tajima.


Tana fita taje bakin ti-ti ta tare mai adai-daita ta faɗa masa sunan inda zai kaita.


Bayan ƴar tafiyar da sukayi ya kaita wajan, tun abakin wajan zaka fara ganin mata da maza suna kai kawo kuma dukkan su ba mai shigar kirki.


Gabanta ne ya fara faɗuwa har taso ta juya kuma ta fasa.


Waya ta ɗauko takira Hajara tace gata nan ƙarasu.


Bata jima da kiran Hajara ba ta ƙarasu cikin wata shiga kace ita ba ƴar muslmiba......








*#Vote*
*Comment*
*Shere*










*©SUMY NA'IGE*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*












*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMMY M NA'IGGE✍🏼•*


```Don neman cikon labarin👇```


~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~






*NA 4📑*


*__________📖* Shigar da Hajara tayi Hafsat tabi da kallo har ta buɗe baki zata yi magana sai Hajara tace, "zo muƙarasa daga ciki kina tawani kallona sai kace yau kika fara ganina".


Sai Hafsat tace, "ni kawai kibani abunda nice dan bazan iya shaga wannan wajanba".


Wani kallo Hajara tabita dashi kana tace, "abunda ki ke nemane bai dame kiba dan haka kin ga tafiya ta" .
tana faɗar haka takama hanyar zuwa inda tafito.




Da sauri Hafsat tabita tana kiran sunan ta amma sai tayi kamar bata san da ita.


Ɗakin da taga Hajara tashiga nan ta fara ƙuƙarin shiga,warin wiwi da sigari ne suka bige hancin ta,aikuwa lokaci ɗaya taje da baya,dan bazata iya shaga ɗakin ba.


Wayar ta ta ɗauko ta sake kiran Hajara tace,


"Hajara gani ƙofar ɗakin da kika shiga, dan Allah kifito ki ba ni".


Wata tsawa Hajara ta daka mata kana tace,


"Idan bazaki shigo ba kina iya tafiyarki".


Wani maƙaƙi ya rufe mata zuciya har taso ta tafi sai kuma wani abu ya taso mata wanda ita kanta bata san ko na meye ba.




Sai da ta ɗauke sheɗar ta kana ta buɗe labulen ɗakin ta shiga.


Abunda tagani ne yayi matuƙar bata tsoro da mamaki.


Dan gabaki ɗaya ɗakin maza da mata ne,kuma ba mai shigar kirki a cikin su.


Sosai abun yaba Hafsat tsoro dan kowane namiji rungume yake da mace.


Dan ko Hajara kwance take ajikin wani sugar boy daga ita sai wata vest mai haɗe da brazier wadda ta bayanar da surar jikin ta sosai.


Wani kallo tabi Hafsat dashi kana tace, "kin tsaya ma mutane akai, in bazaki shigo ba saiki tafi".


Hafsat tace, "Hajara dan Allah kibani wallahi sauri na keyi".


Batari da ta kalle taba tace "gashinan zuwa yace ki jirashi".


aikuwa tana cewa haka sai wannan sugar boy ya yi sauri yace wa ashe itama ƴar hannuce to abamu muɗana". yana faɗa yana kallon Hafsat wadda ta haɗe fuska sai kace akwai wanda ya tilasttamata zuwa wurin


Hajara hara zata buɗe baki tayi magana sai wayar ta tafara rura.


Ɗauka tayi haɗe da faɗin "ka ƙarasu?".


banji me akace ba a ɗayan ɓangarin iya dai tace gatanan zuwa.


Kallon Hafsat tayi dake durƙushe a ƙasa tace, "kizo muje".
daga haka bata sake magana ba ta fice warta.


Itama Hafsat da sauri tabi bayan ta.


Wajan wata mota tanufa itama Hafsat tabi bayan ta.


Aikuwa suna ƙarasuwa wajan motar sai sukayi ido biyu da Anwar, lokaci ɗaya wani sanyi ya ziyar ci zuciyar ta ai bata san sanda ta faɗa jikin saba tana sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.


Jikin sa ya matse ta yana jin wani abu a zuciyar sa.


Gaba ɗaya ya manta da wata Hajara dake tsaye sai da tayi gyaran murya kana ya ɗago da idanun sa waɗan da suka fara sauyawa zuwa launin ja.


Tace, "kizo muyi magana dan sauri nakeyi jirana ake".


Raba jikin sa da Hafsat yayi kana ya dube ta yace, "tabari na zo".


Nesa kaɗan da ita suka yi kana Hajara ta dube shi tace,


"Nagama aikina dan haka kabani abunda kace".


Tun bata rufe baki ba ya ɗauko wasu kuɗi masu yawan gaske ya bata,aikuwa tana gani yawan kuɗin da yabata bakin ta ya kasa rufuwa sai godiya take zuba masa dan har jikin sa tasu tafaɗa ya ɗaga mata hannu alamar ka da ta soma,sosai tayi masa godiya kana ta buɗa baki tace,


" duk akan Hafsat zaka bani wannan kuɗe,sai yanzu na tabbar da son da ka ke yi mata mai yawan gaske ne,amma bari gaji yadda nayi nasamu kanta".


Karasuwa tayi gab da kunnin sa kana ta faɗa masa wata magana.


aikuwa tana gama faɗa masa ya bita da wani kallon mamaki kana yace,


"Amma gaskiya banji daɗin haka da kika yimin ba" har ya buɗa baki zai sake wata magana sai ga Hafsat ta ƙaraso wajan da suke jikin ta na karkarwa tace musu gida zata koma dan Mamar ta har takirata a waya.


Sallama yayi da Hajara kan sai yakira ta,kana ya dau Hafsat ya kaita gida.


To tun daga wannan lokacin duk abunda yace da Hafsat bazatayi masa musuba,sai wani son shi da kaunar sa da suka addabe ta wanda yasa takejin zata iya rabuwa da kowa akan sa.


Wanda a halin yanzu ta koma kamar matar sa, dan sai yadda yace da ita....




*Cigaban labari*


Bayan Safiyya ta fita taci gaba da shirin ta bayan ta kammala tafito domin ta gaida iyayanta.


Bayan ta gaishe su kana tayi beark bayan ta kammala Mama ta dube ta tace,


"Hafsat anjima zan aikeki gidan Hajiya tah ki ƙarɓomin saƙo daga can ki gaya mata zaki koma makaranta sai kun gama jarabawa".


Tace, "tau Mama Allah ya kaimu ajima lafiya"nan suka cigaba da firar su.


Suna cikin fira wayar ta tafara rura,sunan da taga ya baiyana saman screen ɗin yasa da sauri ta saka wayar slient,sai da ta tsinke kana tayi sauri ta mike taje ɗakin ta haɗe da cema Mama tabari tazo Safiyya ce zata gayama sunan wani book wanda zata nemu mata shine za ta je ɗakin ta dubu dan yana cikin jikar ta kuma ta manta sunan shi.


Komai Mama bata ce da itaba har ta fice.




Tana shiga ɗakin ta ya koma kira,da sauri ta ɗauka haɗe da faɗin "Hayateey kayi haƙuri wallahi muna tare da Mama ne shiyasa ban ɗauka ba" .


yadda ta ke maganar kamar tana gaban sa.


Yace, "naji amma anjima zaki dawo ko?".


Cikin muryar rarrashi tace, "kayi haƙura zuwa Monday na dawo, dan anjima Mama tace zata aikeni shine ma nake sun na kiraka na faɗama kayar da naje?".




Ataƙai ce yace, "ban aminta ba kuma anjima nake son ki dawo dan ina buƙatar ki" yana kai ƙarshin zancin ya datse kiran bata ri da yaji me zata ceba.


Wayar dake hannuta ta fara kallo dan ita bata ma san me zata cewa Mama ba.


Dabara ce ta faɗu mata dan haka ta hau gado tayi kwanciyar ta har lokacin da za'a aikin ta ya yi.


Kiran ta Mama ta farayi amma tanaji taki ta karɓa har Mama tagaji ta shigo ɗaki.


Tasheta Mama ta farayi dan a tunanin ta bacci take bata san ko idon ta biyu ba,tayi hakan ne dan kada taje aikin da za'ayi mata.


Kanta ta ɗago kamar mai bacci gaske Mama tace,"Hafsat ki tashi kije rana tafito sosai kinji".


Magana tayi mata cikin muryar marasa lafiya tace, "Mama kiyi hakuri ki aike su Marwan wallahi kaina ke ciyo" ta faɗa haka kamar tayi kuka.




Sannu Mama ta fara jeramata haɗi da kawu mata magani dan tasha.


Aken da bata zoba kenan sai da Mama takira Abban su Hafsat tace masa yayi mata izine taje wurin Hajiyar ta karɓu saƙo.


Aikuwa Mama nafita Hafsat tamiƙe kamar ba itace ke sheiɗa ɗaya-ɗaya ba.


Koda Mama ta dawo Hafsat tace taji sauki dan kan ya daina ciyo.


Dare nayi ta fara tunanin yadda zata cewa Mama zata tafi makaranta.


Dan ya da meta da kira kuma ta rasa yazata cewa Mama.


Wanka tayi ta shirya ta kama hanyar ɗakin Mama dan ta gaya mata zata koma makaranta.....






*#Vote*
*Comment*
*Shere*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*






*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*






*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*








~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~






*SHAFI NA 5📑*


*__________📖* Labulen ƙofar ta ya ye kana ta shiga ɗakin.


Saman sallaya ta same Mama dan haka ta ƙaraso a hankali ta samu waje ta zauna tana jiran Mama ta shafa.


Bayan Mama ta shafa itama Hafsat ta shafa haɗi da gaishe da Mamar ta.


Bayan Mana ta amsa sai Hafsat ta ɗagi da kanta ta ce,


" Mama yanzu abokiyar karatuna ta kirani tace Malamin mu ya bada wani Asignmen tun Jumu'a bayan fitowarmu kuma yace Monday za'ayi summitng kuma ni ban masani ba sai yanzu kuma yace a makin teat ɗin mu ne, kuma rashin yin sa gareni babbar matsala ce.


Sai da ta kai ƙarshin zancin mama ta ɗago ta dubeta kana tace,


"Kina nufin yanzu na barki kije?".


Kai ta ɗaga ma mama alamar " eh".


Sai mama tace,


" Tare da Safiya zaku je?".


Sai Hafsat tace, " a'a Mama kinsan ba department ɗin mu ɗaya da ita ba".


Sai Mama tace, " to gaskiya Hafsat abar wannan tafiya har da safe" har zata koma wata magana sai ga Abban Hafsat ya dawo daga masalaci.


Bayan ya shigo ya zauna san gama gaisheshi kana Mama tayi masa bayanin da Hafast tama ta, kuma tafi ɗa masa yadda tace da Hafast .


Bayan ta gama yace, " a'a baza mu hanamata zuwaba, kuma kinsan wannan karatun da takeyi yana buƙatar kula sosai dan haka tashi ga kuɗi kije kinji ƴar Abba ". yana faɗa yana dubanta.


Sai Mama tace,


" Kafison ta tafi?".


Yace, "eh haka yafi abunda na ke so shine muyi mata fatan alhairi".


Bayan Abba ya bata kuɗi ta ɗau kayan ta tayi musu sallama tafice.


Bayan tafiyarta Mma ta dube Abba kamar tayi kuka tace, " yanzu karatun Hafsat bana son shi dan gabana yana yawan faɗuwa akan karatun Hafsat shiyasa yanzu bani da wata natsuwa akanta".


Sosai Abba ya yi mata magana akan ta aje wannan maganar gyafe kawai suyi mata fatan alhairi.


Tana fita takirashi tace ina yake gata ta tafito.


Faɗa mata wurin ya yi , ba ɓata lokaci taje ta sameahi.


Tana shiga mitar shiko ya yaja suka tafi.


Ti-ti taga ya miƙe yana ta tafiya dan ba hanyar gidansa ce taga ya bi ba, dan haka ta dubeahi tace,


Hayati naga sai miƙi ti-ti kake hala ina zamu je?".


Batare da ya ɗago ya dubeta ba yace, " Zamfara".


" Yanzu da dare nan hayet?".


Yace, " eh yanzu nake da ra'ayin zuwa, in bazaki je ba na saukeki".


Tace, "a'a kayi haƙuri idan na ɓata ma".
Ta faɗi haka ciki da ƙanƙan da kai da tsoro.


Bai sake cewa da ita komai ba har suka isa Zamfara.


Hotel suka sauka ɗaki ɗaya ya kama musu , bayan sunyi wanka sunci abinci kana ya bata wasu ƙananun kayan bacci ya umarceta da sa su, jiki ta narawa ta saka su waɗanda da su da babu duk ɗaya suke a jikinta.


Jikinshi ya jawota ya rungumeta haɗi da shaƙar ƙamshin jikin ta, lokaci ɗaya ya fara romance ɗinta.


Hannunsa yasa ya fara shafar duk wani ilahirin sassan jikinta.


Sosai take jin daɗin abinda yake mata dan haka ta ba da kai sai yadda ya yayi da ita, sosai ya bata wuya a daren ranar, dan sune basu kwanta ba sai biyar saura na asuba.


Kuma asuba nayi ta farka tayi sallah kana tazo tana kwanta.


Shima yana gama sallah ya kwanta haɗi da jawo ta jikin sa , romance ɗinta ya fara duk da yanzu bata so amma saboda jiya ba ƙaramar wahala ya bata ba, amma bazata iya ce masa bata so dan kar ransa ya ɓace.


Sai bakwai da wani ya barta, kushi ba dan ya gaji ba sai dan meeting ɗin da yake dashi 7:30.


Wanka ya yi kana ya yi beark yayi mata sallama ya tafi yace sai ya dawo.


A dawo lafiya tayi masa haɗi da addu'a sai kace mijinta😏.


Yana fita tayi wanka ta shirya tabi lafiyar gado dan bacci ne a idon ta sosai.


Haka suka cigaba da zama garin Zamfara har tsawon kwana biyar.


Zaune suke saman kujera ita dashi sai wayarta ta fara kaɗawa, har taso ta ƙi ɗauka kuma sai ta ɗauka, tana karawa kan kunninta ba abinda aka fara ce da ita sai, " kina ina?".


Sai Hafsat tace, ina ruwanki da inda nake".


Sai Safiyya tace, " to wallahi bari kiji yau zuwa gobe na baki , duk inda kike ki dawo , kuma inba haka ba zanje gida na faɗamusu abunda ake ciki, dan na gaji da ganinki cikin wannan muguwar rayuwa". tana faɗar haka ta datse kiran saboda wani kukan baƙin ciki da yazo mata.


Tana kuka tana faɗin, " me Hafsat ta nemi ta nema ta rasa da da zata riƙa bibiyarshi kamar mijinta".


Kuka tashiga rairawa kamar ta cire zuciyar ta jefar saboda baƙin ciki kuma ba abinda yafi ƙona mata rai gashi yanzu saura sati ɗaya a fara exmas amma ita Hafsat ba itace gaban taba.


Tunda suka gama wayar da safiyya jikinta tane ya yi sanyi sosai kan ta ɗago ta dubeshi dan shima ita yake kallo kana ta buɗe baki tace,


Safiyya ce takirani har tana yiminbarazanar zata gayawa su Mama bana schocl, kuma nasan tunda tace zatq faɗa to sai ta faɗa, dan Allah kayi haƙuri mu koma dan nasan halin Abba ko kasheni zai iya yi".


Ta faɗi haka hawaye na fita a idonta.


Haɗi fuska ya yi haɗi da goge mata hawaye dake fita a idonta yace,




" Dan takiraki ta gaya miki haka shine harda wani tada hankali, aikinsan duk bazata faɗa ba saboda tana faɗa za'a dakatar da karatun ku , kuma ai zata

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads