Showing 42001 words to 45000 words out of 49839 words
Chapter 15 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt
ta.
Gyafin Umma ma haka ta kasance.
Kusan ƙarfe goma sai ga sulaiman yazo wajan Aunty Shemah dan su yake suje suga ya jikin nata.
Bai jima da tahuwa ba sukaje wannan karum har da Affan.
Koda suka isa wajanta sai bacci take, mutsin da tajine shi ya farkar da ita daga baccin da take, ahankali ta buɗe idonta, wayar dake kusa da ita ne ta ɗauku ta duba lokaci, sose tayi mamakin wannan baccin da tayi, kuma yanzu wasai take jin jikinta kamar bata taɓa ciyo ba,juyawar da zatayi sai ganin Aunty da Sulaiman tayi suna mata murmushi, martanin murmushin ta mayar musu kana tace, "Aunty ku ƙaraso".
Affan ne ya antayo da gudu ya faɗa jikinta yana faɗi, "missing you Aunty na".
Murmushi tayi kana tace, "missing too Affan".
Tana faɗa tana jan kuma tunsa.
Har zai sake magana Aunty tace, "kada kacika mu da surutu nan ba gida mukeba hospital muke".
Murmushi Hafsat tayi haɗi da gaishesu.
Amsawa sukayi sannan sukayi mata yajiki?.
Tace, "gaskiya ni yanzu ba abinda ke damuna, ni kwai mu koma gida".
Sulaiman yace, "bari naje naji mi zasu ce idan suntabbatar da kin ji sauƙi sai muwuce gida.
Bai jima da fitar sa sai gashi ya dawo tare da faɗin, "Aunty sunce zamu iya tafiya dan duk wani bincike sun mata kuma sunce yanzu bawani matsala sai dai takiyaye shan magani".
Aunty tace, "insha Allahu zata kiyaye".
Daga haka suka juyo zuwa gidan Aunty Shemah.
*****
Tunda ya tashi bacci yaji sabon al'amari ajikinsa, dan jiyake kamar bashi ba, ya kasa tsaye ya kasa zaune, shidai burinsa yaganshi a sokoto yanzu.
Wayar sa ya ɗauka ya dan yakirata kuzai samu natsuwar abinda yakeji....
*#VOTE COMMENT SHERA*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
~~WattpadSummy M Na'ige~
*SHAFI NA 29📑*
*__________📖* Tana kwance ɗakin su Zahara, dan tunda suka dawo bata koma ɗakinta ba, bari tayi har ta ɗan dawo dai-dai, dan ta san da taje can ɗakinsu zasu cikita da tambaya miya faru da ita, tana cikin wannan tunanin taji wayar ta na ƙara, tsaki taja sannan ta ɗauka daniyar tayi piking, aikuwa sunan da taga ya bai yana kan screen ɗin wayar ai bata san lokaci da ta tashi zaune ba haɗi da faɗi, "Zahara zo kigani".
Tafaɗi haka ciki da farin ciki.
Zahara da ke toilet da sauri ta fito, kafin tayi magana Hajara ta nuna mata wayar ta da ke rura, sunan da taganine yasa tayi guɗa haɗi da ta ka rawa, sannan tace, "kada ki ɗauka barshi har sai ya kawo kanshi".
Hajara tace, "ko dama bani daniyar ɗauka, aikuwa haka tayi ta ƙarar har yagaji da kira ya aje wayar zuwa ajima ya koma kira ko zai ta ɗauka.
Anashi ɓangare ba ƙaramin haushi yaji na rashin ɗaukar wayar da batayi ba, lokaci ɗaya yaji gwara yaje da iran yadda yakeji shi baya iya zama bai gantaba, part ɗin iyayensa ya nufa cikin sa'a koda yaje lokacin suka fito dan yin beark, ƙarasowa yayi wajansu kujrar dinning yajewo ya zauna sannan ya gaishesu, bayan sun amsa sai Mumy ta dube Anwar da kyau, kana tace , "Autana, wai mike dumunka naganka yau duk kawani ya mutse kamar ba kaiba".
Sai Daddy sa yace, wallahi tunda yaje sokoto ya dawo nake ganinsa haka, kafaɗamuna idan akwai abinda ke damunka muji idan zamu iya baka taimako sai mu baka, amma katsaya kana tawani ɓoye muna abu, gaskiya bamasan haka".
Yakai ƙarshin maganar yana dubin Anwar ranshi kamar a ɗan ɓace.
Jikinsa a sannyaye yace, "a'a Daddy ba abunda ke damuna gaskiya, kuma da kukace duk na yamutse, ai kwanan ina fama da zazzɓi ne shiya kawo min haka amma yanzu alhmadulillah".
Ba dan sun yarda ba suka ce to Allah ya ƙara lafiya.
Daddy yasake magana haɗi da duban Anwar yace, "kuma kashin sati nasama za'aje neman aurenka da Saudat, ƴar gidan Alhaji Sambo".
Da dauri Anwar ya ɗago kansa yace, "mikace Abba!.
"Abinda kunnenka yaji shi nace".
Yace, "gaskiya Daddy ni ba ita nake so ba".
Ai Daddy da Mumy lokaci ɗaya suka ɗau salati kana suka ce atare, "baka sonta!!.
"Eh" yace dasu, ai tun bai rufe baki ba Daddy yace, "wallahi Anwar karya kasha kuma baka isaba dan bazaka maidani ƙaramin mutum ba, farko kace kana so yanzu kuma kace baka so, to bari kaji wallahi ba gudu baja da baya in har kaga ba iyiba to ɗayan mune bashi da rai".
Yana faɗar haka suka tashi domin su bar wajan ransu amatuƙar ɓace, wato su Anwar zai rainawa da hankali ya maidasu ƙananan mutane.
Shima ɗin ranshi amatuƙar ɓace ya tashi ya je ɗakinsa, key ɗin motar sa ya ɗauka, ai fusace yazo ya fige motar ya kama hanyar garin sokoto.
Gudu yake kamar ya fira sama cikin awa huɗu sai gashi yazo garin sokoto, hanyar da zata sadashi da unguwar da Hajara take zaune ya ɗauka, gudu yake ko kallon gabansa bayayi, kwatsam gaji abu yaba da gab gab, har yaso yaƙi tsayawa, amma irin yadda yaga mutane sun taso masa yasa ya tsaya amma ba dan ransa yaso ba.
Kuda yafito cikin motar yazo wajan dan yaga waya bige, wani mutum shi ba tsofo ba kuma shi ba yaro ba, yagani kwance da alamu ko numfashi bayayi, aikuwa Anwar na ganin haka hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba, cikin hanzari yasa wasu daga cikin mutanin aka ɗaukeshi a kasa mota kana suka wuce hospital.
*******
Kwance take kamar mai bacci amma ba bacci take ba, dan gabaki ɗaya hankalinta baya jikinta, wayar tace ta fara rura, ɗauka tayi batare da ta buɗe ido ba bare ta duba wake kiranta, muryarsa ce dataji yasa ta shaidashi .
Sallama yayi mata kana ta karɓa sannan ta gaisheshi, shuru ne ya biyu baya sai can yayi magana cikin kasalaliyar murya yace, "Hafsat".
Da taji haka sai da taji wani abu ajikinta kana ta buɗe baki can ƙasan maƙoshi tace, "na'am Yaya".
Sai da ya sauke ajiyar zuciya kana yace, "yajiƙin naki, ina fatar kinsamu sauƙi".
Tace, "sosai kuwa dan yanzu wasai nake jina kamar banyi ciyo ba".
murmushi yayi kana yace, "kodama nace bari na gayamin ko zakije gida kiyi hutun ƙarshin shekara a can? inyaso idan hutu ya ƙare sai nabiya miki kuɗin jirgi ki dawo".
Tun bai kai ƙarshin zancen ba tace, "Aunty Shema zata je ne".
Yace, "a'a ita sai ta kammala zata koma dan kwanannan mai gidanta zai zo".
To nima gaskiya bazanje ba, dan koni bazan sake komawa gida ba sai na gama karatu gabaki ɗaya, amma inaso idan kaje kayi min abu ɗaya, ka karɓumin number Safiyya da Naja'atu please".
Rasa mi zaice da ita yayi, dan haka yace, "tom naji, ƙoƙari datse kiran ya fara, sai tayi saurin faɗin, "in ba damuwa inaso na koma hostel da zama tunda mijin Aunty zai zo ka ga kar na takurasu".
Kasa magana yayi sai can yace duk yadda kikayi dai-dai ne".
Yafaɗi haka ransa a ɓace yana faɗa ya datse kiran batare da ya ji mizata sake faɗa ba.
Tanajin yadda yayi maganar tasan baiji daɗin abinda tace ba, amma ita gaskiya ji take idan yazo yatar da ita gidan kamar ta takurashi dan haka ma yasa tayi wannan tunanin.
Ummar Hafsat ce zaune tayi tagumi abin duniya duk yabi ya dameta ga Baban Hafsat tun safe yafita har yanzu bai dawo gida ba, kuma takira wayarsa amma ance kashe take, kuma gashi su Marwan har yanzu basu dawo ba bare tace su nemumatashi wata ƙila yaje wurin aikin sane, dan yanzu gabaki ɗaya duniya tayi musu zafi dan tun wancan watan aka sallame Abban Hafsat daga aiki, sabida wata sata da a kayiwa , company kuma a kace sai sun biya, haka Abban Hafsat ya tattara duk wata ƙadara tashi ya sayar yabiya su kuma suka sallameshi daga aiki, a cewarsu har dashi cikin masu yimusu sata, abubuwa duk sun tsaya dan ko karatun su Marwa ya tsaya sabida ba abinda za ayi afani dashi wajan cigaban karatunsu, abun dai sai wanda ya gani danshi yanzu sai sun fita kasuwa sunyi dako sannan zasu samun abinda suka ci, ko Baban Safiya yayi musu aike ko Abbas Yayan Safiya.
Yau ma kamar kullum akatashi ba komai a gidan, dan ko abin da zasu karya babu kuma gashi Abban Hafsat ko kwabo baya da, dan haka yace a bari yazo, fita yayi yaje wajan wani abokinsa ko da zai samu rance, to yana kan hanyar tafiyane ya kawo dan ya tsallake ti-ti bai san da wani abin hawa ba, dan haka yazo dan ya tsallaka, aikuwa yana dab da tsallakewa yaji wani abu yabashi gab-gab......
*#VOTE COMMENT SHERA*
*©SUMY NA'IGE*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
~VOTE & FOLLOW 4~
~Wattpad Summy M Na'ige~
*SHAFI NA 30📑*
*__________📖* Tun lokacin bai saike sanin inda kansa yake ba sai a gadon hospital, lokacin da ya farko, da ƙyar ya buɗe bakin sa ba abinda yake ambatowa sai sunayin Allah, yana cikin haka sai ga Anwar ya shigo, da sauri ya karasa gareshi yana faɗin, "Abba sannu ka farka? ya kakeji yanzu?".
Bai ce dashi komai ba, sai da ya kuma wata magana yace, "Abba ko kana da waya a kira iyalinka a shaida musu halin da ake ciki?".
Sai da Abban Hafsat yaji an ambace iyalinsa sannan ya ɗago da kansa ya buɗe baki da ƙayar yace, " ina tunanin banzo da waya ba, amma idan kana da ita sai nasaka number yarona ko mai ɗakina ka kira".
Yayi wannan maganar kamar sheɗar sa tafita daga jikinsa.
Sosai Anwar ya tausayawa halin da yake ciki dan har ga Allah bai da niyar ya tsaya, amma da yaga halin da wannan bawan Allah yake ciki yaji zai tsaya har yasamu ɗan sauki.
Wayar sa ya ɗauku ya miƙa masa yace, "Abba gashi kasanya number".
Ba musu ko ya karɓa, da ƙyara yake danna wayar har yasanya ya bashi yace yakira ya faɗa musu halin da a ke ciki.
Ringing da bai wuce uku ba aka dauka, Maryar namiji yaji dan haka yayi masa sallama, bayan sun gaisa yake faɗa masa Abbanka yace, "a sanar da ku yasa mu haɗari dan yanzu haka an kwantar dashi asibiti, amma da sauƙi dan har ya farfaɗo kuma shi ya bada number ka a kiraka"....tun bai kai ƙarshin zancin ba sai Marwan yafara magana cike da tashin hankali yace, "dan Allah wanne asibiti?".
Wata hospital ɗin kuɗe ce ya faɗa masa, yace gasu nan zuwa yanzu.
Aikuwa Marwan na gama waya da Anwar ya ƙarasa gida ciki da tashin hankali ya faɗawa Ummar su halin da ake ciki, hannun ta ɗura saman kai tafara kuka kamar ranta zai fita, da ƙyar Marwan ya rarrashe ta tayi shuru kana suka shiriya sukaje hospital ɗin.
Dayake hospital ɗin da ya kaishi sannan na ce aciki garin sokoto, dan haka basusha wahala wajan gane wajan da yake ba.
Suna shiga ɗakin da Abba yake suka tarar da Anwar zaune kusa dashi shiko Abba yana bacci, da sauri Umma ta ƙaraso garesa tana kuka tana faɗan, "dan Allah kar katafi ka barmu Abban Hafsat".
Yana cikin bacci yaji kukanta, dan haka ya buɗe idonsa, hannu ya ɗura saman kanta, ɗagowa tayi da kanta, alamun yayi mata da tayi shuru , ba musu ko ta ɗan rage kukan da takeyi.
Anwar dake zaune yanajin sun ambace Hafsat sai da gabanshi ya faɗi, shi bai san mike faruwa dashi ba, duk lokacin da yaji sunan Hafsat sai yaji faɗuwar gaba.
Tashi yayi yayi musu sallama yace zuwa ajima zai dawo.
Da fitarsa bai tsaya ko inaba sai wajan da a kace masa zai ga Hajara, yana isa kuma a kace yanzu suka bar wajan, yinin ranar duk inda yake tunanin zai ganta yaje amma bai ganta ba, sosai yaji zafin wannan lamar yayi danasanin zuwan sa garinnan yanzu, dan da yasan haka zata faru dashi da bai zo ba, kiran sallah da yaji anayi ne yasa yayi parking ɗin motar sa yashiga masallace, bayan an idar da sallah sai limamin wajan yayi karatu tare da karanta wasu ayoyi na alƙur'ani kuma ya fassarasu har inda ya kawo cewa duk wani bala'i ko musiba idan sun afku gareka to ka yawaita sadaka, kuma duk wani abu dakake san samu to yawaita sadaka, nan dai limamin yaci gaba da wa'azi da nuna mahin mancin sadaka, sosai Anwar ya natsu yana saurarin abinda ake magana akai, dan rabanshi da yaje wurin wa'azi ko ya saurareshi har ya manta, bayan limamin ya kammala kana a kayi sallah isha'i sannan Anwar yafito daga cikin masallacin, aikuwa bai bar unguwar da yake ba sai da yafitar da kuɗi masu yawan gaske ya fara sadaka, da yake unguwar da ya tsaya marasa ƙarfi sunfi yawa, aikuwa sai ganin mutane kake suna fitowa maza da mata yara da manya wajan karɓar sadaka.
Duk kuɗin dake hannunsa sai da yara bar da su, kuma suna ƙarewa sai ga wata tshowa tazo wajansa tana faɗin, "dan Allah Alhaji ka taimaka min wallahi ƴata ce bata da lafiya kuma likitoci sunce sai ammata aiki kuma wallahi bamu dasu dan yariyar marainiya ce".
Tafaɗi haka hawaye na zuba a idonta.
Rasa mai zaiyi yayi dan kuɗin dake hannunsa sun ƙare dan haka yaje mota ya ɗauko cheque, rabin million ya rubuta mata yace gasu ayi haƙuri, sosai ƴar tsohor nan taji daɗi lokaci ɗaya ta fara suburbuɗu masa da addu'oi tana faɗin, yadda kayaye min wannan baƙinciki kaima Allah yaya ye makashi haka ta cigaba da kwararo masa addu'a har yabar wajan.
Masalacin da yayi sallah ya koma, limamin masallacin ya je sukayi magana dashi a kan zai gyara masallacin, dan masallacin yana son gyara sosai, dan haka ba ɓata lokaci ya rubuta cheque ɗin million ɗaya ya bayar yace a gyara masallaci, sosai sukayi masa addu'a daga baya ya shigo mota ya dawo hospital dan yaga ya mai jiki.
Tuƙi yake amma sai jinsa yake kamar anɗauke masa wani abu aka.
Koda yaje asibiti jikin Abba Alhmdulillah dan sosai yasamu sauki dan shi abin har mamaki ya bashi, gaishesu yayi kana ya aje musu abinda ya sayo musu sannan yayi musu sallama kan sai da safe idan ya dawo, sosai suka yi masa godiya irin yadda yatsa ya jajirce akan ciyon Abba, dan yanzu sau tari mutum ya bige mutum amma ba zai tsaya ba bare ya bashi kulawa, wani ko ya tsaya da zaran ya kai shi asibiti zai gudu, amma shi ya tsaya har yana faɗin gobe zai dawo, tunanin da Ummar Hafsat keyi kenan.
Yana fita daga ɗakin sai ga Safiyya tazo ita da iyayenta da Yayan ta, Allah ne kawai bai haɗasu ba, dan saura kaɗan suyi karo da Yayan Safiyya akan hanya.
Yana fitowa a hospital bai tsaya ko ina ba sai ma saukin sa, yana shiga bayan yayi parking ɗin motar yafito bai tsaya ko ina ba sai falon gidan, zama yayi saman kujera three seated ya ɗan huta, dan yanzu ji yake kamar an ɗauke masa wani abu kai, wanka yaje yayi sannan ya kwanta, wayar sa ya ɗauku ya kira iyayensa ya shaida musu wani uzuri ya kamashi na gaugawa yanzu haka yana sokoto, basuce dashi komai ba sai fatan alhairi.
___________________
Suna gama waya da Anwar wata ƙawarta takirata tace, "wai hala Hajara baza kizo birthday ɗina ba, kuma kinsa za'ayi casu".
Aikuwa Hajara najin haka tace, "kar ki samu damuwa yanzu zaki ganni".
Tana gama faɗar haka ta tashi tashiga toilet tayi wanka, sosai ta ɗan ɗasa kwaliya kamar wani abu bai same taba.
Kallon Zahara tayi dake zaune tace, "Zahara zaki rakani shukura hotel wajan birthday ɗin ƙawata?".
"A'a bazanje ba dan kinsan ba wajan zuwa nane ba".
Cewar Zahara.
Tace, "ba damuwa ni zanje sabida nasan akwai harka".
Tana faɗar haka ta kama hanyar fita daga ɗakin.
Zahara tace, "ki tsaya mufita tare inyaso kowa yaje wurin da zashi.
Haka kuwa sukayi dan suna kawowa bakin ti-ti ko wace ta tsayar da mai napep ta faɗa masa wajan da zai kai ta.
Dai-dai shukura hotel aka aje Hajara, kuɗinsa ta bashi kana ta ƙarasa daga ciki, tun bata ƙarasa ba ta fara jin kiɗa natashi kamar zai tsaga ƙasa, koda ta ƙarasu wajan da aka kiɗan yacika sosai, maza da mata kuwa sai rawa yake kuma cikinsu ba mai shigar kirki, kace su duk ɗiyan arnane.
Tana cikin tafiya taji an rungumuta ta baya, juyuwar da zatayi dan taga kowaye, bashiri taji bakinta cikin nasa, a hankali yake tafiya da ita har ya ƙarasa gaban musu kiɗa, a hankali ya cire ta daga jikinsa, da sauri ta ɗago ido ta kalloshi dan taga kowaye, murmushi ya sakar mata itama ta mai dar masa da martani, dan ta gane kowaye, lokaci ɗaya a ka cigaba da kiɗa suna rawa ciki da shauƙi.
Bayan angama kiɗa da raye-raye kuwa yazo ya zauna a ka kawo abin mutsa baki, suna cikin haka ita dashi sai ga wasu ƙawayen su sun zo suka ci tazo minti biyu, ba musu ko ta tashe taje, wani ɗaki suka shiga da ita, zama sukayi saman kujerun dake jere a cikin ɗakin, basu jima da zama ba sai ga wata ƙawar su tafito tana tafe tana rangwaɗa kamar wata arniya, gaban Hajara tazo wani ƙofi ta miƙo mata tace, "karfi ki shanye dan ke kaɗai zan ba, kinsan kayan harka ba kuwa a ke baiwa ba".
Tafaɗa haka murmushi ɗauke a fuskarta.
Ba ɓata lokaci Hajara ta ƙarɓa ta kafa kai tanasha.
tunda ta fara sha suka fara wani murmushi mai ɗauke da ma'anuni da dama.
Bata ɗauke kai ba sai da ta shanye.
Ƙofin ta miƙo mata tana murmushin jin daɗi.
Fira suka tsayayi daga baya suka fito dan kowa yaje wajan da zashi.
Koda suka fito mafi yawan cin mutane duk sun watse dan suna can suna fira mutane har sun fara tafiya.
Koda Hajara ta zo wajan da suke zaune har wannan mutum yayi tafiyar sa.
Wajan ƙawayen ta taje suka cigaba da fira daga baya kowa ya kama gabansa.
Sabida dare yayi Hajara bata tsaya komai ba tadawo ɗakinsu sabida bata jin daɗin jikinta.
Tana zuwa ko ta kan Zahara bata biba tayi kwanciyar ta.
Tana cikin bacci taji kamar wani abu yana murɗarta, lokaci ɗaya ta sanya wata ƙara wadda yasa duk wanda ke layin sai da ya farka, Zahara dake ɗaki ɗaya da ita ciki matsanancin tsoro ta faraka haɗi da ƙarasawa wajan ta, ido tazara tare da ɗaura hannu a kai tana faɗin, "nashiga