Header Ads
Showing 36001 words to 39000 words out of 49839 words

Chapter 13 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt

Ads the beginning of article before Image

23 Jun 2024

480

Ads at the middle of Article

ta ta tadawo hannunta.


Haka shima Abba, dan ako da yaushe ba abinda yake sai addu'a da sadaka, Safiyya ko ako da yaushe tana wajan su tana ɗan rage musu kyawar Hafsat, Yayan Safiyya shima ba'a barshi abaya ba, dan yanzu ko kasuwa yaje duk abinda ya sayo ma iyayenshi shi yakan sayo ma iyayen Hafsat, dan yanzu sose yake kula da iyayen Hafsat da ƙannin ta.



Ƙarfe goman dare jirgin su Anwar ya sauka ƙasar india, Sulaman ma haka ya sauka najeria.




Anwar na fitowa cikin jirgin sai yaga har abukinsa ya zo ɗaukar sa, sose sukayi murna da ganin junan su, ba ɓata lokaci ya ɗauke shi zuwa masaukin sa dake cikin makarantar, da yake koshi abukin nasa karatu yake amma shi wannan sheƙar zai kammala.






Ɗaki ɗaya ne mai ɗauke da gado da wadirif, iya haɗuwa ɗakin ya haɗu da idan ka ganshi sai kace ba school ba, ba wani ɓata lokaci ya shiga toilet yayi wanka ya ci abinci kana ya kwanta bacci.






Shima abunkin nasa yana ganin ya samu bacci shima ya kwanta.


Koda gari ya waye bayan sunyi breakfast Anwar ya sanar da abukin sa abinda ke tafi dashi.




Sai da ya kai ƙarshe sai Abukinsa Nura ya dubesa da kyau yace, "ko dama nasan wannan zuwa ba danni kazo ba, amma ba komai zan tayaka neman abinda kazo nema har sai kasameta, da yake tunda ƴan najeria suka zo ban wani haɗu da suba, amma kabar Monday duk wani ɗan makarntar zai fito kuma insha Allah za'a dace".




Murmushi Anwar yayi kana yace, "shiyasa nake sonka, dan tunda nayi bincike na gano makartar kuce nace abu yazo gidan sauki".


Yana faɗar haka suka tafa haɗi da dariyar samun nasara.






Tunda Sulaiman ya tafi jikin sa duk ba daɗi sai ji yake kamar wani abu zai same sa, amma haka yaci gaba da addu'a har a kazo ɗaukar sa.






Tana cikin bacci ƙarfe ukun dare sai ta farka cikin razana sabida wanin mummunar mafarkin da tayi, wanda ya bata tsoro matuƙa, ba wani ɓata lokaci ta tashi taje toilet ta ɗauru alwala tazo ta tada sallah.....







*#Vote*
*Comment*
*Share*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*












*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*








~~WattpadSummy M Na'ige~






*SHAFI NA 26📑*






*__________📖* Basu jima da fitaba saka samu ɗan acaɓa wanda zai kaisu wannan ƙauye, koshi da ƙyar yayar da zai kaisu, tafiya suke amma tafiyar taƙi ƙarawa dan ɗan acaɓa yaga haka yasamu waje yayi parking kana yace, "ku sauka". Sauka sukayi sun ɗauka ko wani abu zai gyara.




Dabansu yayi yace, "wai nawa ne zaku bani da har zaku kawuni cikin wannan jeji?".


Hajara tace, "nawa kake so mu baka?".
Yace, dubu biyu zaku bani".


Kuɗi Hajara ta zaro ajikarta ta miƙa masa, karɓa yayi haɗi da tada babur ɗinsa, Zahara na ƙoƙari ta hau shiko yaje babur da guda ya bar ti-tin, kururuwar kirasa suka fara amma ko alamar ya tsaya babu.


Hannu Hajara ta ɗaura akai tana faɗin, "yau munshiga uku".... kafin ta rufe baki sai ganin motar ƴan sanda tayi a gabansu, tashin hankali wanda ba'asa masa rana, kafin su ankara ƴan sanda biyu sun fito cikin motar suna faɗan, "ƴan isaka, duk kune ke ƙara lalatamuna ƙasa". Suna faɗa suna saka su cikin mota, kuka Hajara da Zahara suka fara suna faɗin "wallahi mu ba isakanci ne yafitar da muba".... kafin ta kai ƙarshin zancin ɗaya daga cikin ƴan sanda ya buga mata kulki abaki, bashiri sai ga jini ya fara tsiyaya abakin Hajara, Zahara naganin haka taja baki ta rufe kukan ma da take haɗiye shi tayi batare da ta shirya ba.


Ƴan sanda suna sasu suka ja mota sai police station ɗin dake cikin ƙauyi garin.




*********
Koda Sulaiman ya isa school bai ma bi takan lectura ɗinshi ba, ya fara neman Hafsat, sai da yaje class ɗinsu ya ganta zaune suna karɓar karatu sannan hankalinshi ya ɗan kwanta, tunani yayi yace gwara yaje yaga ko suna da lectura yashiga, yana gama wannan tunani ya kama hanyar da zata sadashi class ɗinsu.


Gab da zai bar block ɗin su Hafsat, aikuwa sai ya hango Anwar zaune gab da class ɗin su Hafsat.

Gabansa ne yayi mummunar faɗuwa, lokaci ɗaya yanemi natsowar sa ya rasa, maganar abukinsa Jabir ne ya tuna, kuma lokaci ɗaya ya fara girgiza kai yana faɗin, "kenan da gaske ne,waye yaba Anwar address ɗin Hafsat, sai wata zuciya tace itace ta bashi da bata bashi ba taya yasan makarantar da take har yasan class ɗin da take.




Jiri ya fara ɗaukar sa lokaci ɗaya, dole yasamu waje ya zauna haɗi da laluba wayar sa aljihu, Aunty Shemah ya kira, tana ɗauka ko Sallamar datayi bai tsaya karɓa ba yace, "Aunty, bayan tafiya ta wani yazo wajan Hafsat?".
Yayi magana ciki da ɓacin rai.


Sai da ta sauke numfashi kana tace, "Sulaiman, wai mikake son zamane akan Hafsa?, yariyar da bata damu da kaiba wadda bata masan kana son taba, haba Sulaiman ka sassautawa rayuwarka gami da Hafsat ko kasamu natsuwa".


Ba abunda yace da ita sai ƙara mai-mai tamata tambayarsa.


Abun taga bana wasa bane tace, "a'a ba wanda yazo kuma ba inda taje sai yau da tafita makaranta".


Tana faɗar haka lokaci ɗaya ya sauke ajiyar zuciya kana ya datse kiran.


Warin da yake zaune nan yaci gaba da zama har ta fito daga lectura, yana ganin sun fara fitowa da sauri ya tashi ya ƙarasa bakin class ɗin nasu.


Fitowar ta keda wuya ita da Zeenatu yaja hannunta haɗi da karɓar hand out ɗin dake hannunta, ita abin tsoro ma ya bata, tabayan class ɗinsu yabi da ita har sukaje wajan datayi parking ɗin motar ta, magana taso tayi mishi, amma irin yadda taga fuskarsa haɗe yasa taje bakinta tayi shuru, magana yayi mata fuskarshi haɗe, yace ta bashi key ɗin mota, ba musu ta ɗauko ta bashi, buɗewa yayi tashiga kana yashiga yaje motar bai tsaya ko ina ba sai gidan Aunty Shemah.




Yana yin parking tabuɗe marfin mota tafito, shima ya buɗe ya fito, koda ya fito har tafara takawa zuwa cikin gidan, cikiin zafin nama ya zawuta ta faɗu jikinsa, kallon-kallon suka farayi tsakanin su, rabata da jikin sa yayi kana ya fara magana cike da ƙunar zuciya yace, "waye Anwa?!.


Gabantane ya bada dumm, lokaci ɗaya jikinta yayi sanyi haɗi zubda hawaye masu zafi saboda tunawa da wannan sunan da tayi, tana cikin haka taji yasake tambayar ta.




Rasa miza tace masa tayi, dan bata san ya akayi ya san Anwar ba, kuka ta fara mai cin zuciya tace karda ace wani abu zai samuna, tafaɗi haka duk acikin zuciyar ta.




Magana ya fara cikin faɗa-faɗa yace, "ashe har yanzu kina tare da Anwar Hafsat, gayamin me Anwar keda wanda bani da, nasan ke kika bashi address ɗinki dan ya kawo miki ziyara, to bariki ji wallahi duk son dana kemiki zan iya ajeshi muddi kikace zaki cigaba da hulɗa da Anwar"....har ya buɗe baki yayi magana amma takasa fita sai ƙoƙarin riƙe zuciyar sa yake wadda ke masa zafi kamar tafasa ƙirjinsa ta fito.




Tunda ya fara magana Hafsat ke kallonsa dan ita gabaki ɗaya tarasa wajan da yasan Anwar, faɗuwar dataga yana ƙoƙarinyi kuma gashi riƙi da ƙirjinsa alamun zuciyarsa na ciyo, ai bata san lokacin da tazo garisa tana kuka tana ƙoƙarin tareƙo shi kar yafaɗi amma ina, dan koda ta isa gareshi ya kai ƙasa, rasa mizatayi tayi kuma takasa ƙarasawa cikin gida kuma takasa ƙarasawa garishi komawa tayi kamar wata zararriya kuka ma yaƙi zo mata bakin tane tasamu ya buɗe lokacin tasamu ta fara anbatun Allah, aikuwa tana fara anbatun Allah sai gashi tayi hanyar part ɗin Aunty Shemah ciki da tashin hankali.




Parlour tasamu Aunty Shema tana duba wani book dake hannuta, cike da tashin hankali tace, "Aunty kizo karya mutu!".


Da sauri Aunty Shemah ta ɗago kanta arazane tace, "waye zai mutu?".


Kasa magana tayi, hannun Aunty Shemah taje suka tafi batari datayi magana ba.




Tun kan su isa Aunty Shemah tagan shi kwanci rai ga hannun Allah, ai da hanzari taje gareshi, kasa magana tayi lokaci ɗaya taje wajan maigida takirasa yazo suka sashi mota taje suka wuce hospital.


Taimakon gaugawa likitoci suka bashi, cikin ikon Allah sai gashi ya farfaɗo, alurar bacci sukayi mishi kana suka fito.



Suna fitowa Aunty Shemah ta taresu da yajikin nasa, tabbar mata da sukayi jiki yayi sauƙi dan nan da awa ɗaya zai farka da ikon Allah.




Sai a lokacin ita da Hafsat suka saukar da ajiyar zuciya mai sanyi.




Cikin ikon Allah yana cika awa ɗaya ya farfaɗo, kuma alhmadullah dan yasamu sauƙi sose, likitocin naganin haka suka basu Aunty Shema damar ganin sa.




Aunty Shemah ta fara shiga ɗakin, aikuwa tunkan ta ƙaraso gareshi yace, "Aunty ina Hafsat?".


Mamaki abin ya bata amma ta basar tace, "Sulaman miyasameka haka har ya tadamaka da ciyon zuciya?".


Kafin yayi magana sai ga Hafsat tashigo ɗakin, ƙarasowa tayi wajansa kana tamasa yaji, bai karɓa ba sai jefumata tambayar da yayi.


Yace, "da gaske wajanki yazo, kuma har yanzu kuna tare?".




Sai da tashefe hawayen da suka zuba a idonta kana tace, "Yaya Sulaiman kabar wannan zanci har sai munfita daga nan, bakaga bakada lafiya"..... Tun bata rufe baki ba yace,


"Idan har kina son nasamu sauki to ki gayamin gaskiya".




Ita dai Aunty Shemah sai kallon su take saboda mamaki da tsoron Allah duk yacika ta.


Ahankali ta buɗa baki tace, "wallahi duk abinda kake magana akai bansan dashi ba, to waya ga yamaka nayi alaƙa da Anwar, kuma waya gaya maka har yanzu munatare, wallahi ni tunda na bar Anwar bansaki ganin saba har ila yanzu, kuma dan Allah kadaina yimin zancishi in har kana son ganin farin ciki na".
Tafaɗi haka tana mai haɗa hannayen ta waje ɗaya.




Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke kana yace, "duk zan baki amsoshin tambayoyinki amma ba yanzu ba, kuma daga yau na ba zaki sake fita school ba har sai ya bar ƙasar nan".




"badawa".
Haka tace dashi ataƙaice.


Ita dai Aunty Shemah ba abinda take sai kallon ikon Allah, dan sose abun nasu ya bata mamaki, kena duk ciyon sone yatada mishi da ciyon zuciya .


Bata ida mamaki ba sai da taga Sulaiman ya tashi tsaye kamar bashine suka kawo rai ahannun Allah ba.


Duban su tayi bata ce dasu kumai ba, tace, "to tunda kungama muje gida".
Tana faɗin haka ta kama hanyar fita batare da tajira mi zasu ce ba.




Bayan ta suka bi har suka kawo wajan mota, buɗewa sukayi suka shiga kana taje motar, basu tsaya ko ina ba sai gida....






Tundaga lokaci Hafsat bata sake fita makaranta ba, shiko Anwar, ba inda bai je nemataba a school ɗin amma bai ganta ba, har hostel yasa adubu masa amma bata can, kuma gashi lokaci ya tafi amma baiyi komai ba, sose hankalinsa ya tashi na rashin ganinta, har yake tunanin kodai Hajara bata bashi address ɗin dai-dai ba, yace ko idan ya bincika bata bashi dai-dai ba, to sai ya wahalar da ita, dan sose ranshi ya ɓaci na rashin ganin Hafsat da baiyi ba.




Da yaga alamun bata cikin makarantar ya fara shirin dawowa gida n9....






*#Vote*
*Comment*
*Share*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*












*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*








~~WattpadSummy M Na'ige~






*SHAFI NA 27📑*










*__________📖* Anwar yana gama shirin tafiya lokaci kawai yake jira, amma ransa bai yi daɗi ba sose, dan yaji zafi rashin ganinta, yana cikin haka sai ga iyayensa sun kirashi bayan ya ɗauka haɗi da gashesu, Abban sa yace, "Anwar nace kaje gidan Yayan ka Aminu kuwa? duk dana san baya ƙasar amma kafin ka dawo kaje ka kaima iyalinsa ziyara".


Shi sam ya manta dawani Yayanshi sai yanzu da Abbansa ya kirasa.


Anwar yace, "to Abba zanje zuwa anjima dan yau ma nasun na taso amma tunda zanje gidan Yaya Aminu to sai gobe dan nasan idan naje Aunty Shema nacewa sai na kwana kafin nadawo, har ma idan taji nayi sati garin nan".


Abba yace, "ba damuwa amma daga kwana ɗaya ban aminci ka kuma kwana ba, kadawo gida sabida akwai aiki da yawa a office".


Yace, "tau Abba insha Allahu zan dawo, ka gaishemin da Mumy tah".




Abba yace, "naƙi kai kakirata".
Murmushi Anwar yayi kana yace, "yanzu kuwa Abba". Yana faɗar haka ya datse kiran.


Mumy sa yakira suka sha fira kuma ya tabbar mata zaije gidan Yayanshi Aminu daya ƙara kwana ɗaya sai ya dawo gida.




Tunda ya hanata zuwa makaranta bata sake zuwa ba, kuma shima tunda suka dawo hospital bai ƙara dawo gidan ba.


Tunani maganar sa ta farayi inda yace wai in har tana tare da Anwar zai barta, tana kawowa nan tayi ƙwafa kana tace, "yau da a ce duk abinda ke duniyar nan na Anwar ne, kuma zai malkamata shi to bazata ƙarɓaba bare ta dawo masa sabida ƙinsa da take.


Tana cikin wannan tunani taji marata tafara ciyo kaɗa-kaɗan magani ta ta tashi ta ɗaku tasha amma kamar ma anci ta ƙara dan wata ƙirsa ce tamata aikuwa bashiri tafara birgima a cikin ɗakin, sose take wahala indan zatayi period kuma idan ciyo yazo har ƙafafu take riƙe mata shiyasa yanzu da take kwance ta kasa tashi ta ɗauku magani bare ta ƙara sha taji ko zata samu sauki.




Anwar kiran Yayanshi Aminu yayi ya bashi address ɗin gida, aikuwa da bashi bai tsaya wani ɓata lokaci ba yabi address ɗin gida sai gashi har ƙofar gida.


Knocking yayi musu ba jimawa akazo aka buɗe masa yashiga, parlour yashiga da sallamar sa, Aunty Shemah ce dake zaune ta ƙarɓa masa haɗi da ɗago kanta ta dubeshi sose.


Aikuwa tana gininsa ta faɗaɗa murmushi haɗi da faɗin, "wazan gani a gidannan".


Murmushi yayi haɗi ƙarasowa ya zauna kusa da kujerar da take zaune.


Gasheta ya fara kana yace, "ina Affan?".


Tun kan tabashi amsa sai gashi yafito da gudu yana faɗin, "Aunty zansha Ice cream".
Yafaɗa haka kamar zayi kuka.


Tace, "baka ga Uncle ɗinka bane naji baka gasheshi ba".


Sai alokacin ya lura da mutum zaune, aikiwa da saurin shi yashiga jikinsa yana murna yana faɗi" "Uncle ɗina yaushe kazo, kazo kabani lce cream".


Aunty Shema tace, "shi bai san komai ba sai abashi lce cream". rigama taga zaiyi musu kuma bazai bari su gaisa ba dan haka ta tashi taje ta ɗauko masa ta bashi, yana murna ya karɓa yana faɗin, "naje wajan Aunty Hafsat".


Aikuwa yana faɗin Hafsat sai da gaban Anwar ya bada dumm.


Kallon Aunty Shema yayi yace, "baƙine daku a gidan ?".


Tace, "eh ƙanwata ce tazo".


Yace, "oky".
Tace, "saukar yaushe Anwar kuma ya kabar su Mumy da Daddy?".


Wallahi nayi sati ɗaya ƙasar nan, gabaki ɗaya na manta da kuna ƙasar nan ai da nan zan sauka, amma kuyi haƙuri dan ƙila yau ma zan kuma dan naso nayi muku kwana ɗaya amma gaskiya bazan iyaba sabida ƙasar duk naji bata yi min daɗi".
Yakai ƙarshin zancin damu baiyane afuskarsa.


Aunty Shemah tace, "bawani kai dai dan Yayanka bashi ƙasar ne shiyasa baza zauna ba, kuma na gode".




Yace, "a'a Aunty zan dowo nan bada jimawa ba insha Allah".
Gabaki ɗaya jikinsa duk yayi sanyi kuma kamar kar yaji Affan ya faɗi sunan Hafsat.


Aunty Shema tace, "amma sai zuwa anjima zaka tafi ko?". Yace, eh".


Suna cikin haka sai ga Affan ya fito ɗakin Hafsat da gudunsa yana faɗin, "Mumy zo Aunty batada lafiya".


Gaban Anwar ne ya ƙara faɗuwa yarasa dalilin haka.


Aunty Shema tace, "mike damunta?".
Komai baice da itaba sai ma hannuta da yaje, ba musu ta tashi ta bishi zuwa ɗakinta.


Kwance ta sameta sai birgima take atsakiyar ɗaki, da sauri Aunty Shemah tazo gareta tana faɗi, "subuhanallah, Hafsat meke damunki, irin yadda taga tana riƙi ciki ya tabbatar mata cewa marata ce ke ciyo, dan haka ta ɗauko magani ta bata tashi.


Bata jima da bata maganin ba ciyo ya fara lafawa, bawani ɓata lokaci bacci yayi awon gaba da ita.




Aunty Shemah na shiga ɗakin Hafsat, sai ga Sulaima ya shigo parlour ɗauke da sallama abakinsa, Anwar dake zaune yana kallon labaru ya amsamasa tare da miƙa masa hannu suyi musabaha, hannun ya bashi sukayi musabaha


Kafin ya bashi hannu sai da ya kalleshi sose ya tabbatar da Anwar ne, ranshi ne ya ƙara ɓaci, kenan shi tamaida marar hankali ita da Aunty Shema, to yaji ba ita ta bashi address ďinta ba to yanzu waya bashi na gidannan, yana cikin wannan tunanin sai Aunty Shemah tafito daga ɗakin Hafsat.


Tana fitowa taga Sulaiman ya sadda kansa ƙasa, ƙarasowa tayi tana faɗin, "waye nake shirin gani yau a gidannan".


Ɗago kansa yayi haɗi da sanya wani murmushin sannan ya gaishe ta.


Sai da ta zauna ta amsa kana tace, "yanzu nake shirin nakiraka nace maka Hafsat ba lafiya, amma yanzu tasamu sauki dan tana shan magani bacci yayi awun gaba da ita, sai idan ta farka sai ka ɗan dubata tunda ita naga alamun ba duba kanta take sonyi ba".




Dubanta yayi yace, "tana inane?".


"Tana ɗaki". Haka tace dashi.


Tashi yayi yashiga ɗakinta, kwance ya ganta kuma da ganin baccin datake bana daɗine ba, dan lokaci-lokaci sai ta yatsane fuska.


Karasowa yayi wajanta hannusa ya ɗura kan nata yaji ko da zafi, ba zafi sose amma da alamu tana jin jikin.




Anwar zaune yake amma duk lokacin da suka anbace Hafsat, sai yaji gabansa ya faɗi, sose yaso yaga wannan Hafsat sabida shidai yana jin wani baƙun al'amari atare dashi gami da ita, amma sai ya basar dan yasan wannan ba ita bace.


Bayan ya gama dubata ya fito kafin ta tashe yayi mata wasu tambayoyi.


Falo yasame su Aunty da Anwar zaune suna fira, har yaso yafita kuma sai yadawo ya zauna, bai jima da zamaba Anwar ya miƙi yana faɗi, "Aunty ni zan tafi dan so nake na sauka cikin lokaci dan Daddy yace min aiki yayi yawa office".


Alamun rashin jin daɗin ne ya bayyana fuskar ta tace, "bawani ba kadai yi niya ba, kuma na gode ka gada su Mumy".


Haƙuri ya bata tare da tabbatar mata bajimawa zai dawo kuma wajanta zai sauka.




Addu'ar sauka lafiya ta masa sannan yayi ma Sulaiman sallama ya fice.


Yana fita Sulaiman ya dube Aunty Shemah da idonsa da sukayi ja yace, "Aunty waye wannan?".


"Anwar ƙanin Baban Affan ne, da Babanshi da Babanshi uwa ɗaya Uba ɗaya".




Yace, "tun yaushe yazo nan?".


"Iya karsa awa ɗaya" tace dashi.


Har ya buɗe baki yayi magana sai ga Hafsat ta fito riƙi da ciki tana faɗin, "Aunty ki kaini hospital zan mutu".
Tana faɗa tana tangaɗi alamun zata faɗi, saura ƙiris ta faɗi Saulaiman dake zaune yayi sauri ya tare ta tafaɗa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads