Showing 18001 words to 21000 words out of 49839 words
Chapter 7 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt
ta ɗauka haɗi da kara wayar a kunnin ta.
Ba'ayi magana ba dan haka itama batayi magana ba, sai can taji ance "Hafsat".....gabanta ne ya faɗi sabida ko a cikin mafarki taji wannan muryar zata shaida ta.
Ƙo ƙarin katsa wayar ta fara sabida gudan kada ya haifar mata da wata matsala.
Kamar yasan abinda take da niyar aikatawa dan haka ya fara magana kamar zayi kuka yace, "Hafsat nasan ni mai lafine amma dan Allah kada ki barni wallahi nasan kin fikowa sanin irin son da nake miki Hafsat,ki taimakeni kada ki barni,kuma wallahi yanzu ashiryi nake da na aureki Hafsat please kada ki barni dan yanzu haka tunda kika barni akwance nake nakasa cin komai I love you My Sweet baby inasonki over"....haka dai yayi ta cika ta daɗan baki har ta fara jin wani abu ya ɗarsu a zuciyar ta.
Hankali ta ɓuɗa baki tace, "kana wata magana kamar da gaske, amma kabari gobe mayi magana"..tana faɗin haka ta katse kiran dan ko magana ƙasa-ƙasa takeyi masa sabida bata so Safiyya ta gane dawa take waya.
Irin yadda yaji tayi magana ya gane cewa zayi nasara dan haka tana katse kiran yayi wani tsalle haɗi da yin wata shewa mai ciki da jin daɗin samun nasara.
Abukin sa dake kusa dashi yace, "hala anyi nasara da zaka buga wannan uwar shewa?".
Sai da Anwar ya murmusa kana yace, "sosai,dan gobe nasa zata zo nayi yadda nake so da ita inyaso da yamma na bar garin kaga ko baza ta saki gani na ba kuma nima bazan saki tunata ba daga ƙarshe ma na manta da ita".
Sai wannan abukin sa Lawal yace, "shegin kaya kaki fa Anwar,kana yadda kaso da Hafsat wallahi,amma tunda kai ka gama da ita ni mi zai hana ka haɗani da ita ko naji wannan daɗin da kake kwasa a wurin ta".
Kallon baka isaba ya wurga masa kana yace, "dan kaji nace zan manta da ita, to bari kaji koda ace na koma gada wallahi duk lokacin dana so na kusan ce ta sai ta yarda kai bari kaji in har ban aure ta ba to bawani ɗa namijin da zai aure ta dan banji zanyi iya yarda wani ya kusan ce taba in bani ba".
Sai da ya kai ƙarshin maganar sa Lawal yace, "ai gani nayi kana da Hajara.....aikuwa tun bai kai ƙashin zanci ba ya katse shi da faɗi idan kana so muci gaba da mutun ci kada kasa kiyimin zancin wata Hajara"....yana faɗin haka ya tashi ya shige bedroom ɗin sa dan ba ƙaramin bacin rai yake ba idan aka taso masa zancin Hajara.
******
Koda gari ya waye bayan sun karya Baban Safiyya ya aiko kiran Hafsat a ɗakin sa.
Da Sallama ta shiga ɗakin sa haɗi da gaisheshi, bayan ya amsa ya dube ta kana yace, "Hafsat jiya nace kibari nayi shawara,to gaskiya nayi tunani akai kuma nayi shawara, dan haka kiyi haƙuri da abinda zan faɗa miki gaskiya bazan iya bari kije ba a matsayena na mahaifin ki kuma mariƙin ki,ba dan komai yasa nace haka ba sai dubin abinda ya faru ne tsakaninki da iyayenki ,kuma babban abinda ya hana na barki shine cikin da kike ɗauke da shi,dan haka kiyi haƙuri idan Allah yace kije nan gaba sai kije idan kuma bai kaddara ba sai kiyi haƙuri,dan ni yanzu burina ki sauka lafiya kuma kusamu miji nayi muku aure ke da Safiyya,dan gaskiya naso na ƙi barinku ku ƙarasa wannan karatun sai kuma naga koda na ƙi barinku to ba aure zakuyi ba dan haka nace da zaran kin haihu zan muku aure keda Safiyya insha Allah".
Tunda taji Baban Safiyya yace ba zata jeba gabanta ya bada dummmmm to tunda ga wannan maganar bata saki jin miyake faɗa ba, dan gabaki ɗaya hankalinta baya jinkin,sosai maganar sa tasa ta damuwa,amma bata nuna masa ba,sai ma cewa datayi "bakomai Baba Allah ya tabbar muna da alhairi".....tana faɗin haka ta koma ɗakin su.
Inda tabar Safiyya nan tazo ta same ta,Safiyya naganin tashigo ɗaki jikin ta a sanyaye sai tayi saurin cewa, "Hafsat me Baba yace ne naganki a haka?".
wayin cewa tayi kana tayi mata bayanin yadda yace mata,tana mata bayani amma sai ta nuna bata damu ba,amma a zuciyar ta ita kadai tasan mi take kiyastawa aciki.
Sosai Safiyya taji zafin haka dan da badan tasan halin mahaifin ta da magana ɗaya ba da tasake tunkarar sa.
Haƙuri tacigaba daba Hafsat har ta nuna mata ita ko ajikin ta,kuma Allah ne bai nufi tajeba,amma a zuciyar ta ita kaɗai tasan me take shiryawa.
Haka suka cigaba da fira har sukayi aiki suka kammala.
Biyu dai-dai ta shirya zowa school dan biyu darabi Hafsat ke da luctura,ita ko Safiyya yau bata da luctura kuma batajin daɗin jikin ta bare ta raka Hafsat makaran ta,dan tunda taji baza a bar Hafsat taje ba taji jikin ta duk ba daɗi, dan har ƴar ƙwalla sai da tayi.
Tana sauri tashiga makaranta, ita kuma Hajara zata fito,gabaki ɗayan bata lura da ita ba sai da taji sunyi karu dawani mutum,dan haka da sauri Hafsat ta ɗaga kanta,aikuwa tana ɗaga kanta dan taga dawa tayi karu,waza tagani inba Hajara ba.
Gaban tane yayi masifar faɗuwa lokacin da tayi ido biyu da Hajara,Addu'ar neman tsari ta farayi a zuciyar ta,har dai tasamu ta buɗe baki tace , "kiyi haƙuri dan Allah wallahi ban lura dake ba".....tana faɗin haka ta ƙarasa daga cikin makaran ta batari da taji me Hajara zata ce da ita ba.
Ita ko Hajara ranta inayayi dubu ya ɓaci dan haka tayi kwafa haɗi da antaya ma bayan Hafsat wani kallo kana ta wuce.
Saura kaɗan tayi late dan tana shiga malamin ya shiga.
Ƙarfe 6:00,dai-dai suka gama lecture,da sauri tafito dan tasamu bus tashiga takoma gida cikin lokaci dan tasan halin Mama ko takoma kan lokaci sai tayi mata faɗa bare ma bata koma ba,amma ina dan tana ƙarasuwa bus ɗin natashi da mutane cike.
Aikuwa tana ganin sun ɗaga tabuga wata ubar ƙara haɗi da faɗin "ya Allah!.
Gashi mafiyawan mutane sun watsa,amma ya ta iya dole tajira zowan wata bus.
Tana cikin tsayin jira bus sai ga wata ƴar budurwa tazo wajan ta wadda bazata wuce sa'arta ba tace, "Hafsat mikikeyi anan har yanzu baki je gida ba".
Sai da Hafsat ta kalle ta haɗi da tunanin ina tasan ta kana tace, "ina jiran bus ne".
Sai wannan budurwar tace, in badamuwa kizo musaukeki dan bus kam ba yanzu ba".
Irin kallon da Hafsat tayi mata ne yasa tace, "nasan haliki baki da yadda,amma tunda bazaki jeba ni zan tafiya ta tunda ke ko ƴan class ɗinku bazaki gane ba".
Sai Hafsat tace, "a'a wallahi,ina tunani idan nasanki ne,amma kiyi haƙuri muje ai nagode ko bakin hanya ne ki sauke ni sai na ƙasa".
Sai wannan buduwar tace "har gida sai munkai ki".
murmushi Hafsat tayi haɗi da godiya kana suka tafi bakin wata baƙar motar da akayi picking wadda ko glass ɗinta baki ne.
Suna karasowa wajan motar ta ɓuɗe mata murfin motar tace, "Hafsat shiga".
Gaban tane ya faɗi amma sai tayi bismillah ta shiga.
Tana shiga sai aka rufe marfin da sauri suka tada mota suka wuce batari da wannan budurwar ta shiga ba.
Suna tafiya sai wannan buduwar tayi murmushi kana tace, "Hafsat kenan inkinsan wata baki san wata ba"....tana faɗan haka itama tashiga wata motar ta bar wajan.....
```Comment dinku nayin kad'an fa```
*#Vote*
*Comment*
*Share*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
~~WattpadSummy M Na'ige~
*SHAFI NA 15📑*
*__________📖* Mamar Safiyya ce ke kwalama Safiyya kira,da sauri safiyya dake ɗaki tafito haɗi da faɗin, "gani Mama".
Kallon ta tayi haɗi faɗin, "har yanzu Hafsata bata dawo ba?tana can ta tsaya wajan shiri-ritar da ta saba kenan".
Sai Safiyya tace, "a'a mama kila bus ce bata samu kan lokaci ba,amma bari nakirita naji ko sun taso"....tana faɗa tana shiga ɗakin ta dan ta ɗauko wayar ta.
Koda takira wayar akace mata wayar kashe take,amma duk da haka bata haƙura ba sai famar kira take tana faɗin, "tasan duk wayar ta ba kashe take ba network ne ,dan haka tace bari ta aja zowa ajima idan bata dawo ba tasake kira duk da tasan tana kan hanya"...tayi maganar ne ita Kaɗai.
Sunanan suna jira har akayi magarb har a kazo da isha'i,kuma gashi duk aka kira wayar ta sai ace kashe take,sosai hankalin Safiyya ya fara tashi dajin Hafsat shuru bata dawo ba.
Ita ko Mama sai zoba masifa take wai Hafsat ta tsaya wajan shiriritar da tasaba,sosai faɗan kema Safiyya ciyo dan abin yazo ya haɗe mata waje ɗaya, ga rashin jin Hafsat ko a waya ga masifar Mama.
Mama nacikin wannan masifar sai ga Baba ya dawo gida,nan Mama tashiga yimasa bayani wai Hafsat tun safe da taje makaranta har yanzu bata dawo ba,sosai hankalin Baba ya tashi,aiko yace bai ga zama ba,bari yaje makarantar yagani ko wani abu ya tsaida ta?.
Har zai fita sai Yayan safiyya Saminu yace, "Baba kada kaje ka wahal da kanka, dan nasan ba inda taje sai gidan saurayin ta".....ai tun bai kai da rufe bakin sa ba, Baba yayi cikin sa yana masa faɗa,sai da Baba yayi masa faɗa sosai kana ya bar gidan da sunan yaje ya nemu Hafsat.
Har zai fita ya kwalama Safiyya kira yace tazo sutafi tare dan ita tasan kan makarantar,ba musu ta ɗauko mayafin ta tafito suka tafi.
******
Hafsat na shiga cikin motar, wani mutum wanda bata san ko waye shi ba ya rufe mata baki haɗe da ɗaure mata fuska,dan duk ihu da take ba mai jinta har suka tada mota suka bar makaranta,Basu tsaya da ita ko ina ba sai wani gidan.
Tunda sukayi packing ɗin motar gaban ta ke famar dukan uku-uku,ina ba ambatun Allah ba ba abinda takeyi a ranta,tanaji suka ɓuɗe marfin motar suka fitar da ita,sai da suka isa da ita parlour gida kana suka kwance mata fuska haɗe da buɗe mata baki.
Aikuwa tana ɗago idonta wazata gani inba Anwar ba,wani uban zabura da tayi kamar bata ɗauke da komai ajikin ta.
Nunisa da ɗan yatsa ta farayi har tasamu ta ɓuɗa baki tace, "Anwar dama kaine kasa a ɗaukoni?minayi ma Anwar? mikake nema dani?dan Allah kabarni hakanan na huta,wallahi ina cikin gararin rayuwa,wadda sabida kai na faɗa acikin ta,duk abinda kayimin baiyi isheka ba sai ka kasheni ne!to gani kashini,macuci azalumin,kayimin ciki kuma karabarni,sanidiyar ka nabar iyayena"....ai tun bata kai da rufe baki ba ya wanke ta da mari har guda biyu,wanda lokaci ɗaya ta rasa inda kanta yake.
Nunin ta ya farayi da ɗan yatsa kana yace, "waye sa'arki da zaki riƙa buɗe baki kina faɗi masa magana sun ranki ehh?Narabaki da iyayenki kuma yanzu zan rabaki da wadda kika fiso dan haka wallahi sai kinyi dana sanin faɗamin maganar daki kayi" ..yana faɗa yana nuninta da ɗan yatsa.
Waɗanda suka kamuta ya duba kana yace,"koje ko nemunin Safiyya duk inda take,kuma nabaku zowa nan da gobe"....ai tun bai kai da rufe baki ba,cikin hanzari da kaɗuwa da maganar sa tafaɗa jikin sa tana faɗin,"Anwar dan Allah kada kayi min haka wallahi na yarda duk abin da kakeso zamakashi amma kada kataɓa lafiyar Safiyya,dan Allah na ruƙeka"....tana faɗa tana wani kuka mai kunar zuciya.
Har yaran nasa zasu tafi dan cika umarinin da ya basu sai kuma ya tsaida su yace suji rashi falo zasuyi magana da Hafsat.
Bayan sunfita ne ya dubeta kana yace, "idan har baki son nataɓa lafiyar Safiyya to sai kin yarda da abinda zance,amma idan baki yarda ba wallahi ba makawa sai nasa anɗauko min ita gobe,amma idan kinyar da to ba damuwa".
Kallon sa tayi kana tace, "inaji kafaɗa idan zaniya ɗan".
Yace, "dole ma ki iya,kuma daga yau zaki zauna gidan nan har tsawun sati ɗaya,kuma duk abinda kikasan kina min wancan lokaci zakiyi min shi a yanzu, dan haka idan har kin yarda to amma idan baki yarda ba sai nasa su ɗaukomin ita gobe".
Idontane ya cigaba da fitar da hawaye kana tace, "dan Allah kayi haƙuri Anwar kabarni na koma gida, na yarda sai na riƙa zowa har sati ya cika"....tun bata rufe bakin taba ya kwalama yaransa kira yace gobe su ɗauko mishi Safiyya.
Cikin hanzari ta faɗa jikin haɗi da faɗin, "na yarda Anwar duk abinda kakeso zan maka amma kada kataɓa lafiyar Safiyya,amma kasani yanzu bani da wata isassar lafiyar da zan riƙa abinda nake maka a da,dan kasan cikin dake jikina baya bani lafiya"....tana faɗa tana share hayen ta.
Wani kallo yake jifa ta dashi kana yace, "yanzu kina nufi har yanzu biki zobar da wannan cikin ba? to bari kiji daki zobar da karki zobar duk ɗaya suke a wajena dan sai kinyi abinda nace kiyi"...yana faɗin haka ya kama hanyar bedroom ɗinsa batare da yasake magana.
Itako faɗuwa tayi saman kujerar parlour ta fara rera kuka kamar ranta zai fita,tana kuka tana ruƙun Allah ya kawo mata mafita.
Koda suka kawo bakin gate ɗin makaranta tsit yake sai ɗai-ɗaikun mutane dake wucewa amma ba alamar wata bus.
Cikin makaranta sukayi packing ɗin motar su,cikin hanzari Safiyya ta fito ta nufe class ɗinsu,koda ta ƙarasa ba kowa aciki dan haka da sauri ta wuce hostel wajan abukan karatunta,abukiyar karatun ta Maryam ta fara cin karu da ita, Safiyya tace, "yauwa Maryam, nace Hafsat tashigo makaran ta yau kowa?".
Sai Maryam tace, "eh ta shigo dan kusa dini ma ta zauna har aka gama luctura".
Safiyya tace, "wallahi ita nake nema dan har yanzu bata koma gida ba".
"Aikuwa ana gama lecture tace bari tayi saura tashiga bus dan bata son magirb tayi mata kan hanya"...cewar Maryam.
Har Safiyya zata wuce sai ga Saratu ko ita abukiyar karatun suce, har zata wuce taji suna zanci Hafsat dan haka ta ƙarasu garesu tace,
"Safiyya Hafsat kam tajima da tafiya dan gaban idona ma tashiga wata mota baƙa ita da wata yarinya,amma ban san yariyar ba, ina dai yawan gani yarinyar tare da Hajara".
Gaban Safiyya ne ya bada dummmmm,lokaci guda jikin Safiyya yayi sanyi,dan da ƙyar tasamu ta ɓuɗa baki tace musu, "nagode bari na koma gida wata ƙila ta isa"....tana faɗar haka ta kama hanyar da zata kaita wajan da tabar Baban ta.
Tana isa wajan sa ta ɓuɗe mota tashiga tana mai faɗin, "Baba muje ƙila ta isa gida,dan antabbartarmin da tashiga mota".
Tana faɗin haka bai tsaya wani jiraba ya tada mota suka bar makarantar.
Koda suka isa gida akace bata dawo ba,sosai hankalin Baban Safiyya ya tashi,irin tashin hankalin da Safiyya taga yashiga ne dan haka taje wajan da yake tsaye tace,
Baba ka daina tada hankalinka akan ɓatan Hafsat,Hafsat bata ɓace ba, ta dai je gidan saurayin ta wanda yayi mata ciki,abinda yasa nace haka sabida ko jiya da dare bayan mun kwanta, dan ita atunanin ta bacci nake, inajin abinda tace dashi,naso nayi mata magana tunjiya amma na fasa nace sai naga tasake wayar dashi....sai da ta numfasa tace, zan yarda wancan lokacin asiri yayi mata amma yanzu nasan bawani asiri atare da ita.....nan dai tagaya musu asirin da Anwar yayi mata a wancan lokaci.
Baban Safiyya ya kalle Safiyya jikin sa asanyaye yace, "zaki iya gane gidan nasa kikai ni gobe?".
Shuru tayi bata bashi amsaba,kafin ta buɗa baki tayi magan Yace, "dole gobe ki kaini gidan, dan bazan iya barin ta awajansa ba,amana na ɗauko ta fa,dan haka ko ina Hafsat take sai na nemuta,dan ban sani ba ko yanzu asiri ne yayi mata"....yana faɗin haka ya fice daga gidan gabaki ɗaya.
Kukan datayi ne har ya saukar mata da zazzaɓi mai tsanani dan koda yafito daga bedroom ɗinsa kwance yasame ta saman kujera jikin ta sai famar karkarwa yake saboda zazzaɓi.
Hankali ya ƙarasu gareta,hannunsa ya kai jikinta lokaci ɗaya ya ɗauke yana mai faɗin, meke damun ki hala naji jikin ki da zafi?".
Komai bata ce dashi ba sabida ko bakinta ta ga-gare ɓuɗewa bare tayi magana.
Dayaga alamun bazatayi magana ba yace, "wallahi ba ruwana da wani zazzaɓi, duk baki tashi kika fara aikin ki ba wallahi gobe sai anzomin da Safiyya"....aikuwa tana jin furicin sa,da sauri ta zabura ta miƙi zaune haɗi da faɗin, "nashirya mi zanyi maka yanzu"....abinda tayi ne ya bashi dariya dan haka ba san lokacin da yayi dariya ba...
*#Vote*
*Comment*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
~~WattpadSummy M Na'ige~
*SHAFI NA 16📑*
*__________*📖 Nuni ya yi mata da ta zauna saman cinyar sa, ba musu ko ta tashi ta zauna,tana zama ya sanya wata sassanyar ajiyar zuciya,ɓsabida jin fatar shi da ta ta sun haɗu waje ɗaya, shi kansa ya san yana son Hafsat so ba nawasa ba amma a zahirin gaskiya ba za'iya auren ta ba duk son daya kemata,kuma ba dan komai ba sabida yariga da yasanta ƴa mace,kuma da ta yarda zata zubar da cikin wata ƙila ya yarda ya aure ta.
Jikinsa ya ƙara sanya ta, kana ya fara shaƙar ƙamshin dake fita jikinta, hannun sa ya kai saman sassan jikin ta ya fara shafar ta, lokaci ɗaya yaji wani sanye ya mamaye zuciyar sa,sosai yake son taraiya da Hafsat ba dan komai ba sai dan yadda ya ke samun natsuwa da ita sose.
Ita kowa tunda taji ta saman jikin sa wasu hawaye masu zafi suka fara fita a idon ta,uwa uba lokacin da ya ɗora hannusa saman jikin ta,jikin ta ne ya fara karkarwa sabida baƙin cikin ɗaura hannusa da ya yi kuma ga ciyo da ke ɗawai niya da ita.
Bukinsa ya fara ƙoƙarin ɗaurawa saman nata, lokaci ɗaya ta fara ka-karin amai haɗi da sauka saman jikinsa, Wani baƙin ciki ne ya rufe shi bai san lokacin da ya kifeta da mari ba kana yace,
"Wallahi Hafsat muddin ki na buƙatar kanki da lafiya ki bi abinda nake so, dan wallahi ko aman jini ki kai sai nayi yarda nake so dake ko nayi miki abinda har ki mutu bazaki mantani ba,dan haka maza kije ki gyara jikin ki ki sameni bedroom yanzu nan".
Yana faɗa yana kama hanyar da zata sada shi bedroom.
Sanin halinsa da tayi dan haka ta tashi taje ta gyara jikin ta kana ta sameshi a bedroom ɗin sa.
Koda ta shiga ɗakin yana waya yana faɗin, "My love kin san na kusa dawowa kuwa?,dan haka ki fara shirin, dan kin san dana dawo ba jimawa za'ayi aure na dake".
Daya ke hands-free yasa dan haka tana jin dun abinda suke fada.
tace, "hmm My dear har kasa naji ƙunya".
Murmushi