Showing 12001 words to 15000 words out of 49839 words
Chapter 5 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt
kujera yace ya zauna.
Bayan ya zauna sai doctor ya kai duban sa ga Mama yace, "kefa miye matsayinki a wajanta?"...... tin kan Mama tayi magana sai Abba yace, "mahaifiyar tace".
kujere doctor ya nuna mata yace ta zauna.
Bayan ta zauna sai doctor yace, "ba abinda zan ɓoye muku gaskiya,muyi nasarar tsayar da jinin da yafara fita jikin ta,amma cikin da ke jikin ta nanan bai fita ba.....tun kan ya kai ƙarshen zanci sai Mama tace,
"a'a ba ƴata baca ka duba danni ƴata bata da ciki ka da kayi mata sharri" magana Mama keyi amma gabiki ɗaya bata cikin natsuwar ta.
Abba yace, "ka da kisa ke magana ki bari muji me doctor zai ce".
Abba kallon doctor ya yi yace "inajinka".
Doctor yace, "iya bin ciken da mukayi mata, munganu tana ɗauke da ciki har na tsawon wata huɗu, kuma cikin na gab da zubewa saboda irin yadda ....bai ƙarasa zancin ba saboda da nauyi maganar da zai faɗa, ya faɗa musu ko yanzu saduwar da ya yi da ita ne yajamata wannan ciyo sai yaƙi faɗa yace, amma yanzu tasamu sauki dan har barci ta samu sai zuwa ku san awa huɗu zata farka saboda mun mata allura bacci.
Yana kai ƙarshin zancin Abba ya sauke wata ajiyar zuciya haɗi da goge ƙwallar da ta zubo masa yace , "to doctor muna godiya".
Sai Mama tace, "yanzu Abbansu har ka yarda Hafsat na ɗauke da ciki?wallahi nikam ban yarda ba dan nasan ba halin ƴata bane" magana takeyi amma kamar zata faɗi.
Doctor ya dube ta bayan yaba Abba ta kardar maganin da za'a sayo mata yace da Mama "zaki iya gane ƴar taki idan kin ganta?".
Tace "sosai kuwa".
Sai yace, "zo muje kiga ko ita ce" yana faɗin haka ya tashi ya kaisu ɗakin da aka kai ta.
Suna shiga gadon da take kwance ya nuna mata yace, "gata ko ba ita bace?".
Kallon Hafsat Mama keyi wadda ke kwance tana barci bata masan abunda akeyi ba.
Gaban gadon Mama ta ƙaraso tace, "Hafsat! Hafsat! mi ki ka rasa wanda bamuyi miki ba,ci ki ka rasa ko sha? ! ki gayamin miyasa zaki sakamin da haka Hafsat!, kinsan aure kikeso meyasa bazaki gayamin ba" . tana magana tana wani kuka mai ban tausai.
Alamun zata faɗine Abba yagani dan haka da saure ya tare ta ta faɗu jikin sa sume.... ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba lokaci ɗaya jikin sa ya yi sanyi yama rasa me zaiyi.
Doctor ne yakira wasu nurse suka ɗauke ta aka ɗura ta kan godon yafara dubata.
Cikin lokaci kaɗan ta farfaɗo.
Sunan Abba ta fara kira,doctor yasa aka kirashi,yana zuwa yafita dan yaga ba komai ne ke damun taba sai ruɗuwar da tashiga.
Jikin Abba tafaɗa tana kuka tace, "ka ga abunda Hafsat tayi muna yau mu zata saka ma da ciki kuma ko ciki na shege! ".
ajiyar zuciya Abba ya sauke kana yace, "ta dai yi ma kanta, dan haka ki rage sa damu wa aranki,kuma ki tashi mu koma gida idan tafarka gasu Marwan nan su dawo tare".
Sai Mama tace, "da ka barni idan ta farka mu dawo tare sai kuje kai da su Marwan......tun bata kai ƙarshen zancin ba ya daga mata wata irin tsawar da yasa ta sauka daga gadon bata shirya ba.
komai bai ce da itaba ya kama hanyar fita ya barta.
Itama tana ganin yafita ta bi bayan sa.
Waje suka tarar da Ammar da Marwan suka ce sujira idan Aunty su ta farka su dawo gida tare.
Haka kuwa akayi tana cika awa huɗu ta farka.
Dubi- dubi tafarayi Marwan da Ammar tagani sunyi tagumin kamar sun san mike faruwa.
Ammar ne ya kula da farka warta dan haka da sauri ya ƙaraso gare ta yace, "Aunty ya jikin naki?".
Da sauki tace dashi kana tace, "Ammar ina Mama?".
Yace, "ta koma gida ita da Abba".
Yana faɗa mata haka wasu hawaye masu zafi suka fara bin kuncin ta sabida tasan yanzu kowa yasan tana da ciki.
Lokaci ɗaya tafara rera kuka mai ƙunar zuciya tana faɗin, "Ammar kada kugujeni wallahi nima ƙaddara ce ta afka kaina ni kaɗai nasan me nakeji gami dashi,duk duniya banajin abunda nakeji da shi ga kowa sai gareshi dan Allah ƴan uwana kutayani da addua, dan wallahi ina cikin wani hali".
Sosai ta baso tausayi duk da su kansu basu san me ake ciki ba.
Duk da Abba yace kada su kwana komai dare su dawo amma basu gaya mata ba sukayi kwanciyar su har safiya ta waye.
kuma basu fito ba sai da doctor ya dubata ya rabuta mata magani Marwan yaje ya sayo haɗi da kayan beark bayan tayi beark tasha magani suka kamu hanyar zuwa gida.
Abba da Mama ba wanda ya samu bacci a ckin su kowa nin su tunani abunda ƴarsu wadda suka fi so a duniya ta aikata ya keyi
Tun cin dare yake zuba ido amma basu dawo ba,dan haka ko da akayi kiran sallah asuba yaje masallaci ana gama sallah ya dawo .
Bai jima da dawo ba sai gasu sun dawo.
Sallama sukayi bayan Abba ya ƙarɓa suka wuce suka zauna.
Komai Abba bai ce dasu ba kuma suma basuyi masa magana ba saboda ba suga wurin yi masa magana ba, dan fuskar sa haɗe take.
Kallon sa ya maida ga Ammar kana yace, "je ka kiramin Safiyya".
Tashi Ammar ya yi yafice yaje kiran Safiyya.
Mama na fitowa ɗaki bata ce da kowa kamai ba ta fara dukan Hafsat tana faɗin kin ci amana ta Hafsat mikika rasa tana faɗa tana dukanta iya ƙarfin ta.
Tashi takeso tayi dan ta gudu amma takasa saboda bata da wani ƙarfin jiki.
Abba na kallo amma ya yi kamar bai san abbun da ke faruwa ba.
Wani ice Mama ta raramo dan ta bugama Hafsat aikuwa da sauri Marwan ya riƙe yana kuka yana faɗin, "dan Allah Mama kirabu da ita me ta muku ki ka dukan ta, ki dakeni mada-din ta ko lafiya fa bata da komai tayi kuyi mata uzuri mana".
Tun bai kai ƙarshen zan cin ba Mama ta ki feshi da mari har sau biyu.
Abba ne ya yi magana yace "ta ƙyalesu kada ta koma magana ta barshi da su.
Anacikin haka sai ga Ammar da Safiyya sun zo tare.......
Nagaji🤦♀
*#Vote Comment Shere*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
~Wattpad Summy M Na'ige~
*SHAFI NA 11📑*
*__________📖* Bayan ta ƙaraso ta gaishe da Abba da Mama amma kowa bai samu damar karɓa mata ba sai ma tambayar da suka jefa mata.
Abba yace, "Safiyya ashe kin san halin da ƴar uwarki ta ke ciki amma ki ka kasa faɗa mana?".
Tace, "wani hali Abba....!
Ai bata kai ga k'arasawa ba ya da ka mata tsawa haɗi da faɗin.
"Ki bani amsar tambayar dana miki?".
Jikin ta na karkarwa tace, "Abba kayi haƙuri amma ni ban san wane hali take ciki ba".
Mama ce tace mata, "baki san tana ɗauke da ciki ba ne".
Aikuwa Mama na rufe bakin ta, Safiyya ta fashe da kuka mai tab'a zuciya kana tace.
"Wallah Mama ban sani ba".
ta na faɗa tana kuka.
Abba ne yace,
"Ba komai Safiyya kuma ina fatan baki biyema halin taba?kuma daga yau nara baki da ita ka da ta koya miki mugun halin ta, kuma ki sani wallahi bazaki zauna min a gida da wannan ciki ba, dan haka ki tattara kayanki ki koma wurin wanda ya yi miki ciki na bar masa ke har abada, dan wallahi daga yau na cireki daga cikin zuri'a ta, kuma bari kiji minti biyar na baki ki tashi ki barmin gidana ko na illataki" .
yana faɗin haka ya shigewar sa ɗakin sa.
Kuka mai tsanani Hafsat keyi kamar ranta zai fita,rasa bakin magana tayi dan gabaki ɗaya kalaman sa sunyi mata tsauri.
Ko Mama abunda Abba yace yayi mata zafi kuma tasan tunda ya furta to ba abinda zai canja,dan haka taja bakin ta ta kulle amma zuciyar ta na mata zafi.
Safiyya najin abinda Abban Hafsat yace dan haka da gudu taje gida su ta zo da Baban ta.
Tace masa ga Abban Hafsat can ya kore Hafsat.
Safiyya na fita sai ga Abban Hafsat ya fito a ɗakin sa,kallon Hafsat yayi haɗi da antaya mata harara kana yace, "bazaki tashi ki barmin gidana ba?".
Kafin tayi magana Marwan da Ammar suka fara bashi haƙuri,magana yafara musu cikin faɗa yace, "bari ma kuji wallahi duk a cikin ku duk wanda ya taimaka mata ko da bayan idona ne to banyafe ba". sai Mama tace, "a'a ka dai ce ta bar maka gidanka amma ba ruwanka tsakanin ta da ƴan wuna ta, kuma tabar maka gida taje ina Abbansu?, komai zakayi yana da kyau ka dubi gaba dan komu muna da namu laifi....kafin ta rufe bakin ta ya daka mata tsawar da tasa tayi shuru bata shirya ba.
Duban sa ya kai ga Hafsat yace,"ki tashi kibarmin gidana kafin nasa afitar dake".
Ahankali ta tashi ta fara tafiya har ta kai ɗakin ta,kayan ta ta haɗa gabaki ɗaya ta fito tana kuka mai cin zuciya,kallon ta Mama tayi tace, "kinga abinda kika jama kanki kika kuma jamin dan haka......Abba ne yafito yace Mama tayi masa shuru kana ya dube Hafsat yace, "fita ki barmin gidana" yana faɗa yana nuna mata ƙofar fita.
Kuka take kamar ranta zai fita, ta kama hanyar fita Mama ta dube Abba tace, "yanzu barin ta zamyi ta tafi? to ina zata je?".
Sai Abba yace, "tafiki sanin inda zata je" yana kawai nan ya koma cikin ɗakin sa.
Gabaki ɗaya kannen ta kuka suke lokacin da zata fita,har ta kawo bakin ƙofa sai ga Safiyya da Baba ta sun ƙaraso da sauri Safiyya ta ƙarasa wajanta tana faɗin, "ina zakije haka da kaya?".
Tace, "Abba ya koreni yace na bar masa gidan sa,...Baban Safiyya ne ya katse musu magana yace Safiyya taje ta kiramasa Baban Hafsat.
Shiga tayi tafaɗa masa ba jimawa ya fito fuskarsa haɗe ba alamar fara'a.
Bayan sun gaisa da Abban Safiyya sai Baban safiyya ya faɗa masa abunda Safiyya tafaɗa masa tace ya kore Hafsat shin ko gaskiya ne?.
Bayanin da Safiyya tayi masa to shi Abban Hafsat yayi masa kana yace, "wallah bazata zauna gidana da cikiba,Alhaji Abbakar minene banyi ma Hafsat da har zata saka min da cikin, wallah bari gaji yanzu ko ganin ta bana sonyi, gabaki ɗaya Abban Hafsat ya rikice duk yadda Baban Safiyya yaso yayi haƙuri Abban Hafsat yaƙi,kunsan abu ga mai haƙuri idan ya tashi bai iya ba.
Da Baban Safiyya yaga Abban Hafsat yaƙi haƙuri sai yace, "tunda kace bazata zauna gidan kaba to ni zan ɗau Hafsat ta zauna gidana har nayi mata aure.....tun bai kai da rufe bakin shiba sai Abban Hafsat yace, "kada kasoma kace zaka haɗeta da ɗiyan ka dan zata lalata musu tarbiya".
Sai Baban Safiyya yace, "naji kuma na ɗauka Allah ya shirya min su gabaki ɗaya" rigima sukayi sosai da Baban Safiyya kafin su rabu.
Baban Safiyya nafitowa falon Abba dube su Hafsat yayi yace,"ko zo muje gida" yana faɗin haka ya kama hanyar gida sa ranshi a ɓace.
Suna isa gidan su Safiyya sai Baban Safiya ya kira Ummar Safiyya ya faɗa mata abunda ake ciki kuma ya shaida mata cewa Hafsat nan gidan zata ci gaba da zama har Allah ya sauke ta lafiya kuma ya kawo mata mijin aure.
Aikuwa Ummar Safiyya najin ace Hafsat zata dawo gidan da zama ta fara kumfar baki tana faɗi, "itakam gaskiya baza'a kawo mata Hafsat a gida ba salon tazo ta lalata mata tarbiyar yara,wallah bazata yarda ba" sai da ta kai ƙarshin zanci sai Baban Safiyya yace,
"wallahi ba wanda ya isa ya hana Hafsat zama ana gidan, nan ya dinga ci mata mutunci har yace idan tasake cewa Hafsat bazata zauna gidan ba bakin auren ta,ba shiri ta kama bakin ta,Safiyya yace da ita suje ɗakin ta su cigaba da zama ita da Hafsat,ba musu suka je ɗakin.
Bayan kwana biyu da faruwar haka gabaki ɗaya Hafsat bata da natsuwa, gashi ko fita batayi kuma ko takira shi a waya baya ɗauka.
Kuma yanzu ko barci take mafarkinsa take, ko me taki tunanin sa take, gabaki ɗaya ta koma wata iri gashi Ummar Safiyya da ƙannen ta har ma da yayun ta duk sun tsane ta abu ka ɗan sai Ummar Safiyya ta dinga yimata faɗa, sosai abun ke ɓata mata rai amma sai ta dake ma zuciyar ta saboda irin yadda Safiyya da Baban ta ke nuna mata amma daba dan suba da tuni ta bar gidan .
Yau ma kamar haka suna kwance da dare dan har bacci ya ɗauke su tana cikin bacci taji kamar antsaƙure ta,da sauri ta zabura ta tashi,komai bata gani ba, lokaci ɗaya taji tana son taji koda muryar sa ce dan haka ta ɗau waya ta kira koda Allah zai sa ta samu.
Missed call biyar tamasa amma bai ɗauka ba,har taso ta aje wayar ta kwanta sai tace bari ta koma kira,aikuwa tana kira ringing da bai wuce uku ba ya ɗaga tare da faɗi, "wake magana?".
Toilet ɗin dake ɗakin ta shige kana tace, "Hayat nice fa,baka ganeni ba?".
Yace, "oh nagane shin kece?lafiya dai ko?".
Tace, "eh kodama nakirane naji ko lafiya kake?".
Yace, "eh ƙalau nake"...har zai katse kiran tace Hayat kayi haƙuri nasan ko dan mi kake fushi dani amma in har nasamu fita zan zo dan nayi missing ɗinka sosai, kuma kayi haƙuri ka yafemin idan na ɓatama"......tana faɗi tana fitar da ƙwalla.
Gajiya yayi da surutun ta dan haka ya datse kiran batari da yaji sauran zancin ba,daga baya ta lura da ya kashe wayar dan haka taci gaba da kuka dan gani take kamar ta aikata babban laifi fushin da ya keyi da ita.
Washi gari baya sungama aikin su na gida ita da Safiyya sai Mamar Safiyya ta shirya tafita unguwa ta barta daga ita sai Safiyya tace sai ta dawo.
Fitar ta ba da jimawa ba Safiyya ta kwanta barcin rana,aikuwa Hafsat naganin haka taje tayi wanka ta shirya cikin hanzari ta bar gidan, tana fita ta tsayar da mai napep ,basu tsaya ko ina ba sai gidan sa, kuɗi da suka rage mata taba mai napep kana ta shiga gidan.
Parlour tasame shi yana waya, da sauri ta ƙarasa jikin sa tana faɗi, "Missing you Hayatee nah".
Yana jinta jikinsa ya ɗago ya kalle ta haɗe da katsi wayar da yakeyi, dan jinta kawai yayi dan har taso ta bashi tsoro,har ya buɗe baki yayi magana ta haɗe bakin ta danashi tana kissing ďinshi kamar tasamu lolipop,lokaci ɗaya ya fara karɓar saƙon da take aika masa, martani yafara mai dama ta sannan yafara ƙoƙarin rage mata kayan jikin ta,
bayan ya cire mata ya fara romance ɗinta son ranshi,daukar ta yayi ya kai bedroom ďinsa daga can yafara sarrafata yadda yake so,dan kowane buƙace yake da wani.
Sosai hankalin Safiyya ya tashi, lokacin da ta farka bataga Hafsat ba dan ta ɗauka ko guduwa ne tayi sabida abinda mamar take mata,sai da taga kayan ta hankalin ta ya ɗan kwanta.
Tunani tafarayi to ina Hafsat ta tafi ne tasan ba gidan su tajeba .
Shiko ya samu jaka sai yadda yaso yakeyi da ita,tagaji iya gajiya amma takasa buɗe baki tace ta gaji,sai da ya gaji dan kansa sannan ya barta.
Sai da suka ɗan huta ta ƙara shigewa jikin sa,a hankali ta buɗa baki ta fara faɗa mishi abinda ya faru da ita,sannan ta ƙara da cewa, "Hayat ko na ɗauko kayana na dawo nan da zama zan fi samun natsuwa bisa ga inda nake".
Sai da ya kalle ta kana yace, "a'a kada ki dawo dan nima ko wata bazanyi garin nan ba zan koma garin mu dan nagama aikin dana zo yi".
Kuka ta fara masa wai zata bishi garin su,bai kulata ba yaci gaba da abinda yake so da ita.
Roƙon sa tayi ya barta taje gida amma yayi kamar bai jita ba,sai can yace taje ɗin kuma gobe ta dawo.
Wanka kawa tayi ta sanya kayan ta tafito,roƙon sa tayi ya bata ƙuɗi ta hau napep,sai da yagama jamata aji kana ya ɗauko dubu ɗaya ya bata yace taje
Taci sa'a koda ta dawo mamar Safiyya bata dawo ba Safiyya kadai ta isake a tsakar gida tana safa da marwa.
Kallon ta Safiyya tayi tace, "daga ina kika fito?".
Bata karɓa mata ba ta shige ɗaki ta barta tsaye,ɗikin Safiyya tabi ta tace, "dake nake magana kinyi min shuru"
sai Hafsat tace, "mi zance miki to, fita nayi ko so kike na faɗamiki inda naje,to ba aikina kikayi ba bare na faɗa miki" tana magana tana antaya mata harara
Komai Safiyya bata sake cewa da itaba dan tasan ba ida taje sai gidan shegen saurayin ta kuma ta ɗau alwashin sai ta ci mutunci sa duk ranar da ta ganshi.
Ko da dare yaya ba wanda yayi ma ɗan wunsa magana har suka zo kwanciya ,Hafsat a tunanin ta Safiyya bacci take dan haka ta ɗau waya ta kirashi,bayan ya ɗauka ta gasheshi to fa nan suka cigaba da fira amma mafi yawan firarsu ta batsa ce,hirar ce ta dame Safiyya wai a ce ƴar uwar ta ke wannan firar dan haka ta farar kuka har da shisheka, kukan Safiyya da Hafsat taji ne yasa tayi sauri ta katse wayar kana tace, "Safiyya lafiya kike kuka?".
Kyaleta Safiyya tayi dan abin nan na Hafsat yanzu tsoro yake bata, a ce har mutum yayi sanadiyar barin ka gidan iyayenka amma ka kasa barishi wannan wani irin so ne,tana kuka tana tunani cikin zuciyar.
Jin da tayi Stuna in bata amsa mata ba yasa ta ƙaraso wajan ta hawayen da suka Zuni matane ta goge tace, "My Safiyya kiyi haƙuri nasan dan kinji wayar danakeyi ne kike kuka,wallahi Safiyya koni zuciya ta na ƙuna abinda nakeyi dashi amma ya zanyi dan wallahi bani da natsuwa duk banji shiba ko bantare dashi ba, nidai abinda nake so dake kiyi min addu'a kada na mutum ina cikin wannan hali kinji ƴar wuta".
Jikin ta Hafsat ta faɗa gabaki ɗayan su kuka suke mai ciki da kunar rai.
Haka Hafsat taci gaba da zama gidan su Safiyya har aka kuma hutun makarantar su amma duk ranar da tasamu damar fita sai taje wajansa,itako yanzu Safiyya da dare yayi take tashi kuma ta tashe da Hafsat suyi alwala sufara nafil-fili suna kai kukan su ga Allah.
Kuma cikin ikon Allah yanzu Hafsat tarege jin