Showing 45001 words to 48000 words out of 49839 words
Chapter 16 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt
uku Hajara mi yasa meki haka?".
*******
Sulaman tun daga lokacin bai sake kiran Hafsat ba, amma sai famar nemar mata aiki yake sabida baya son ya bar ƙasa batare da ta fara aiki ba, dan idan tana aiki albashinta zai isheta har tariƙe kanta batare da ta nemi taimakon kowa ba, kuma cikin ikon Allah ya samar mata aiki a wata asibiti, sosai taji daɗin haka dan haka tace zata cigaba da zama gidan Aunty shemah batare da ta koma hostel ba.
Sai da yaga komai ya dai-data wajan aikin ta sannan ya tattaru nashi da nashi ya dawo ƙasar shi ta haihuwa ciki da kyawar ta.
Ita ma haka ta kasance gareta da har kuka sa da tayi lokacin tafiyarsa.
Haka dai tacigaba da karatu kuma tana zuwa wajan aikin ta, batada wata matsala ko damuwa, matsalar ta itace yanzu Ummar ta take yauwan mafarki a ko da yaushe, dan tunda tazo bata taɓa kewar gida ba sai wannan lokaci, kuma bataji zata iya tafiya ba har sai ta ida phd, dan yanzu shekara ɗaya ce ta rage mata .....
*#VOTE COMMENT SHERE*
*©SUMY NA'IGE*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
~~WattpadSummy M Na'ige~
*SHAFI NA 31📑*
*__________📖* Soyayya mai ƙarfin gaske tashi tsakanin Hafsat da Sulamai, wanda a yanzu ji suke in ba ɗaya guda bazai iya rayuwa ba, kuma duk wani ɗan uwa Sulaiman yasa Hafsat, dan har waya sukeyi da iyayenshi, sosai suke sonta itama haka, kuma yanzu kowani burinsa yaga ya mallaki ɗan uwansa, ita kanta Aunty Shemah har mamaki take a kan wannan soyayya tasu, jira suke Hafsat ta ida karatunta sannan aje ayi maganar aure gidan su.
******
Bayan kwana biyu Abba yaji sauƙi sosai dan har an salame shi yadawo gida, kuma duk da haka Anwar yana kula da su sosai, dan tunda yazo gidan yaga halin da suke ciki suka bashi tausayi dan haka duk bayan kwana biyu ya kanzo yaga yaya suke, kuma sosai yake taimaka musu, dan yanzu har makaranta ya maida su Marwa, Abba ko ya samar masa aiki a company siminti, kuma yanzu alhmdullih komai na Abba ya fara dawo ahankali, kuma ko Yayan Safiyya ba'abarshi a baya ba dan shima sosai yake kula da su Umma.
*A gurguje*
Zahar ciki da fargaba ta ƙaraso wajan da Hajara ke kwanace wadda ta naɗe waje ɗaya kamar ranta zaifi, lokaci ɗaya kamanunta suka canja, ba abinda ke fita bakin ta sai wasu yawu masu yauƙi, knocking ɗin ƙofar Zahara da akeyi ne ya fargar da ita, cikin tsoro da fargaba ta ƙaraso wajan ƙofar ɗakin tana faɗi, "waye?".
Muryar ƴan layinsu taji dan haka da sauri ta ƙarasa jikin ƙofara taɓuɗe musu.
Ko magana basuyi mata ba suka shigo ɗaki dan suga mike faruwa? Hajara da suka gani kwance sai birgima take kamar ranta zai fita.
Ɗayan wanda suka shigo ɗakin ya dube Zahara yace, "Zahara mike faruwa da ƙawarki?".
Jiki na ƙarƙarawa tace, "wallahi bansani ba koni haka na ganta".
Sai ɗayar mace tace, "to wallahi tun bata mutuba ki samu mai napep ya kaita can layi buge ya aje dan wallahi ta mutu ɗakin nan sai ƴan sanda sun tambaye ki".
Sosai Zahara tashiga ruɗuwa, jiki na karkawa tace, "to yanzu ina zan samu mai napep cikin wannan dare?".
Sai ɗayar mace tace, "kizo muje ɗakin Yawale idan zai yadda sai ya ɗauko motarsa ya kaiki inyaso da kun aje ta kujuyu".
Haka ko ta kasance, dan da ƙyara Yawale ya yarda suka je, koda suka je mutane basu fara fitowa ba, dan haka suka ajeta dai-dai bakin ƙofar wani ɗaki suka tahowar su.
Koda mutane suka fito sukaganta yasha da ƙasa, waɗan da suka santa su sukaje school ɗinsu aka nemu ƴan garinsu aka haɗata dasu, su sukayi duk yadda za suyi aka kata gidansu, sosai iyayenta suka shiga tashin hankali lokacin da aka kawo musu ita, ita ba matattaba, ita ba mai rai ba, dan sose take jin jiki.
Koda labari yariske saurayinta, sosai hankalinsa ya tashi kuma duk wani bincike yayi amma bai ganu kamai gami da lamarin ba, dan ko ƙawayen ta antambaya amma bawani abu da akasamu wanda zai nuna ambata.
********
Suna tashi daga wajan aiki yashigo mota, bai tsaya ko ina ba sai bakin ƙofar gidansu Hafsat, yana fitowa ƙanninta suka fara yimasa oyoyo sabida yanzu jinshi suke kamar wani ɗan uwansu, bai ma tsaya wani neman izini ba ya shiga cikin gida bakinsa ɗauke da sallama.
Ummu dake tsakar gida tana girki ta karɓa masa murmushi ɗauke a fuskar ta, kujera da ya gani ce ya zauna kana ya gashe da Umma.
Bayan ta amsa ya tambaye ta Abba, tun kam ta buɗe baki tayi magana suka jiyo sallamar Abba.
Amsa suka yi haɗi da gaisheshi.
Anwar da ya ganine ya faɗaɗa murmushin sa, hannu ya miƙo masa sukayi musabaha kana suka cigaba da firarsu.
Suna cikin haka har Umma ta kammala abinci ta kawo musu shida Abba suka ci, bayan sunci sun ƙoshi suka koma ɗura wata fira, suna cikin haka sai ga Safiyya ta shigo gidan ɗauke da sallama a bakin ta, gaishe da Umma tayi kana ta ƙasara wajan Abba dan ta gaisheshi, har ta buɗe baki tace, "Abba ina wuni"....bata kai da ƙarasawa ba sabida ganin Anwar da tayi zaune gaban Abba, cikin tashin hankali ta buɗe baki tace, mugu mika zoyi muna agida? ina ka kaimin ƴar uwata!".
Tana faɗar haka tazo gareshi haɗi da cungumo masa rifa tana faɗi, "wallahi sai ka nemun ƴar uwa".
Irin yadda yayi mata shuru bai ce komai ba, yasa ta raramu wani icci dan ta buga masa, da sauri Abba dake zaune wanda mamaki yaci kasa ya tashi ya karɓe iccin dake hannuta, amma duk da haka sai da ya shafe wani sashe na jikinsa.
Komawa tayi kamar wata zararriya, koma ɗauko wani tayi dan ta buga masa da ƙyar Umma da Abba suka shawu kanta ta ɗan natsu, lokaci ɗaya ta fara kuka tana faɗin, "mi kazoyi gidan nan? Ko ka ɗauka ta nan ka karasamin ita?".
Gabaki ɗaya kan Anwar ya ɗauri, ga mamaki wanda ya a ddabe shi a zuciya, ahankali ya ɗago idonsa waɗan da sukayi jajar yace, "Safiyya dan Allah kiyi haƙuri ki nunamin wajan da take wallahi da gaske ina sonta, kuma ashirye nake dan na aure ta".
Wata harara ta antayo masa sannan ta fara kici niya ta ƙwace daga riƙon da Abba da Umma sukayi mata, suna cikin haka sai ga Yayan ta Abbas yashigo gidan, aikuwa kamar kar yashigo ta ƙwace daga riƙon da su Umma suka yimata ta faɗa jikinsa sannan tace, "Yaya Abbas ga wanda ya lalatamin Hafsat, shi ne sanadin rushi duk wani jin daɗinta, kuma shine yayi mata ciki kuma daga baya ya guje ta.... aitun bata kai ƙarshin zanci ba sai ga Abbas gaban Anwar zai kai masa naushe, da sauri Abba yace, "Abbas kada kasuma wallahi zan ɓata maka rai!!".
Faɗa Abba ya fara yi masu sosai sannan suka natsu, bayan komai ya lafa nan Safiyya ta faɗa musu komai wanda tasani tsakanin Anwar da Hafsat, sosai su Abba da Umma ransu ya baci, dan ita Umma sabida baƙin ciƙi kasa magana tayi ba abinda take sai kuka baƙin ciki.
Abbane ya dube Anwar da kansa ke ƙasa ba abinda yake sai dana sani da zubar da hawaye yace, "ashe dama haka rayuwar ka take? to ina maka nasiha da kaji tsoron Allah, kasani duk abinda kake Allah na kallon ka, kuma ba abinda zance da kai sai dai nace kaje na barka da Allah".
Tun Abba bai kai da rufe baki ba Anwar ya durƙusa gaban Abba yana kuka kamar ransa zai fita yana faɗin, "wallahi Abba na tuba kodama sharin shaiɗan ne amma wallahi son gaskiya nake mata"....tun bai ka da rufe baki ba Abba da Umma suka shige ɗakinsu suka kulle ransu amatuƙar ɓace.
Abbas nagani haka ya tasa ƙeyar Anwar gaba yace ya bar musu gidansu kuma yaja masa kunne akan kar ya kuskura ya kuma dawo gidan.
Ciki da rashi abinyi Anwar yaja motar sa ya bar unguwar.
Allah ne ya kawoshi ma saukin sa, dan yadda yake jan motar ko gani bai yi, yana yin parking ɗin motar yayi haka ya buɗe marfi motar ya fito wani abu yaji ya dakar masa zuciya, lokaci ɗaya ya dafe ƙijinsa, cikin ƙarfin hali ya fito daga cikin motar dan ya ƙarsa falon gidan, ta ko ɗaya zuwa biyu ya faɗi a farfajiyar wajan lokaci ɗaya numfashinsa ya ɗauke.
Mai gida da ya gama rufe gate yazo ya shiga ɗakinsa yaga Anwar yashe a ƙasa kamar bashi da rai, da gudunsa yazo gareshi, rasa mi zaiyi yayi dan haka da gudun sa yaje wajan wani maƙocinsa ya faɗa masa halin da ake ciki, daya ke koshi abukin Anwar ne dan haka da sauri yazo suka ɗauke shi suka kaishi hospital.
Abbas yana ganin Anwar ya tafi shima ya kama hanyar gida, Safiyya ko ta zauna taci gaba da kuka, Umma ko sai da ciyon ta yatashi sosai tasha wahala kafin ya lafa.
Iyayen Anwar da suka ji Anwar shuru dan haka suka kira wayar sa amma bata shiga dan haka hankalin iyayensa ya tashi sosai, dan haka ba ɓata lokaci suka kama hanyar sokoto dan suje suga ko lafiya ɗan su yake.
Koda suka isa garin sokoto suka samu labarin abinda ya same ɗan su, dan haka basu tsaya ɓata lokaci ba su tafi hospital ɗin da yake, da ƙyar suka samu aka bari suka ganshi sabida har yau bai farfaɗo ba, sosai hankalinsu ya tashi ganin halin da ɗansu ke ciki kuma autan su.
Koda suka tambaye doctor da ke kala dashi dan suji mike damun ɗan nasu, sai doctor ya shaida musu cewa ya kamu da ciyon zuciya saka makon wani abun da yake so ya samu amma bai samu ba, kuma likitan ya shaida musu suyi ƙoƙari su bashi abinda yake so inhar suna son yaci gaba da shaƙar numfashi a durun ƙasa.
Hankalinsu ya tashi sosai, haka dan mahaifiyarshi taji har kuka sai da tayi.
Kwanan su uku sannan Anwar ya farfaɗo daga dogon suman da yayi, bayan ya farfaɗo suka sake yi masa allurar bacci, sai da ya kwana huɗu sannan iyayenshi suka samu ganawa dashi.
Aikuwa yana ganinsu ya fashe da kuka yana faɗin, "Daddy zan mutu, ku taimaka min kuce su bani ita wallahi inasota sharin shaiɗan ne yashiga tsakanin mu amma wallahi har cikin zuciyata ina sonta....tari ya farayi mai haɗi da jini aciki, ruɗewa iyayensa sukayi dan haka da sauri suka kira likita suka shaida masa halin da ake ciki, da sauri suka zo suka fara bashi taimakon gaugawa.
Mahaifayar Anwar kuka take ba ƙau-ƙautawa, sabida halin da taga ɗanta keci, ƴa-ƴanta mata tayi ma waya tace su zo suga Anwar dan yayi nisa.
Sosai hankalinsu ya tashi dan haka su huɗu suka shigo jirgi zuwa sokoto.
koda suka zo suka ga halin da Anwar yake ciki hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, dan haka su yanke shawara zasu fita dashi waje a duba musu lafiyar sa, musamman halin da suka ga iyayayesu sun shiga, dan haka ba ɓata lokaci akayi masa base zuwa ƙasar india.
Yayan su Aminu ɗan Yayan Daddy suka kira suka faɗi masa halin da ake ciki dan haka yace to su haɗu acan india dan yanzu haka baya nigeria.
Cikin kwana ɗaya akayi musu base suka wuce ƙasar india, kuma cikin ikon Allah sai gashi ankawoshi hospital ɗin da take aiki.
Dayaki yanzu suna shiri-shirin kammala karatunsu, dan abu mai wuya ne kesa tayi wata ɗaya ƙasa, dan ita inbanda Sulaiman da gaskiya sai ta ƙara wasu watanni, amma tasan bazai bar ta taƙara koda kwana ɗaya ba bare wata ɗaya dan shi burishi a yanzu duk bai wuce ace ya mallake ta ba amatsayin matar sa.
Zaune take laptop na gabanta tana wani bincike gami da karatun, wayar tace tayi ƙara, kamar bazata ɗauka ba kuma sai ta ɗauku, sunan da taga yana yawo kan screen ɗin wayar ne yasa ta sanya wani murmushi wanda ya ƙarama fuskarta kyau da annuri, ɗauka tayi haɗi da karawa akunnin ta, sallama tayi masa amsawa yayi tare da faɗin amarya ta, i miss you".
Yafaɗi haka tare da rufe idonsa.
Sai da ta sauke ajiyar zuciya kana tace, "miss you too angona".
Shuru ne yabiyu baya, sai can yace, satin nan ne za'ayi bikinku ko?".
"A'a sai wani sati".
Haka tace dashi ata ƙaice.
Gaskiya bazan iya jirin har wani sati ban ganki ba, dan haka ki shiya tarbona daga gobe zuwa jibi".
"Da gaske?".
"Ki zuba ido zaki sha mamaki, wani sanyin daɗine ya mamaye mata zuciya sannan ta buɗe baki cikin marai-rai cewa tace, "My ango nah".
Amsawa yayi yana mai jin wani sanyi azuciyar sa.
Tace, "idan ban saka aiki ba ina so dan Allah".... kuma sai tayi shuru ta ƙasa ƙarasawa .
Yace, "ƙarasa mana ina ji".
Yafaɗa haka da sigar rarrashi.
Tace, "koda-kodama ina so in ba damuwa zan turu maka address ɗin gidansu Safiyya ka dubumin ita da iyayen ta dan Allah ba danni ba".
Ta karasa maganar kamar zatayi kuka.
"Dan wannan ne kike so kimin asarar hawayenki to karki suma, yanzu ki turumin anjima zanje insha Allah".
Wani murmushi jin daɗi ta sanye har shi kansa sai da yaji sautin murmushi, kana tace, yanzu zan turum ma".
Tana faɗa ta da tseki.
Kominti uku ba'ayi ba ta tura masa.
Aikuwa zuwa yamma ya shirya yabi address ɗin da ta bashi har ya kawo gidan su Safiyya.
Yaro aika yace yakira masa Safiyya, Ko da yaro yaje Safiyya na zaune sai aikin tunani take musamman yanzu da Babban ta ya matsa mata sai ta fitar da miji dan aure yake son yayi mata.
Tana cikin haka taji ance ana sallama da Safiyya, gabanta ne ya bada dummm, dan ita batayi dakowa yazo wajan taba.
Mamar tace ace gata zuwa, kallon Safiyya dake zaune Mama tayi tace. "to maza ki tashi kije kin bar mutum waje yana jiranki".
Dan kar ma tayi mata magana yasa tana faɗar haka ta haɗi fuska.
Safiyya da taga alamu haka ba musu ta sanya hijab ɗinta ta kama hanyar waja.
Tsaye ta ganshi nesa da gidan su kaɗan, dan haka ta ƙarasa gareshi bakin ta ɗauke da sallama.
Amsawa yayi sannan tace, "bangane ka ba".
Sai da yayi murmushi yace ko gaisuwa babu? ina fatar kece Safiyya".
Yafaɗi haka ajere.
Kai ta girgiza masa alamar eh".
Sai da ya numfasa sannan yashiga yimata bayani dallah-dallah har sai da ya kammala.
Kuka ta sanya masa sannan ta durƙusa gabansa tace, "dan Allah ka taimaka min ka kaini wajan ta dan girman Allah".
Magana take hawaye sai famar zuba yake akan kuncin ta.
Magana yayi mata yace in har iyayen ki zasu yarda to zai kai ki har wajan Hafsat, sosai taji daɗin abinda yace da ita dan haka tace yazo suje ta kaishi wajan iyayen Hafsat yayi musu bayani ko za su samu natsuwa atare dasu.
Ba musu ko yayarda yaje yayi musu bayanin inda Hafsat take kuma da wajan da take zaune, godiya sukayiwa Allah kana sukayi masa godiya sannan suka ce in akwai yadda za'ayi suna son suje suga ƴar su, yace kar su damu su shirya zuwa jibe sai suwace.
Haba murna tsakanin Umma da Abba ba'a magana dan kamar anyi musu albishir da shiga aljannanh.
Koda Baban Safiyya ya dawo Abban Hafsat ya gaya masa, sosai yayi farin ciki yace shima yana son yaje yaga ƴarsa.
Cikin kwana uku aka yimusu base suka wuce india.....
to asauka lafiya.
*Wai nagaji🤦♀️*
*SAURA KUKI COMMEN AIKO NIK'I ƘARASASHI*
*#VOTE COMMENT SHARE*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
~~WattpadSummy M Na'ige~
*SHAFI NA 34 & 35🔚📑*
*__________📖* Ƙanwar Ummar ta dake zaune ita ta karaɓa musu sannan suka ƙaraso cikin falo, ɗaya daga cikisu tace, "yau zanga matar Yayan Anwar wada akanta ya tashi rasa ransa".
Gabam Hafsat ne ya faɗi tace to miya haɗata da Anwa?.
Ta faɗi haka duk cikin zuciyar ta.
Tana cikin wannan tunanin taji anyaye mata mayafi da ta rufe fuskar ta, kanta ta kara saddawa ƙasa Yayar sa Zainab ce tace, "Hafsat buɗe idonki ga iyayensa".
Gabanta ne ya sake faɗuwa karu na biyu, ana cikin haka sai ga Yayar shi ta riƙo hannusa tashigo dashi ɗakin, zaunar dashi tayi wajan da Hafsat ke zaune sannan suka riƙa ɗaukar su hoto, hanunsa Mamar sa ta riƙo ta haɗa dana Hafsat, lokaci ɗaya suka ji wani yarrrr, addu'ar samun zaman lafiya tayi musu sannan ta fice suma sauran ƴan uwasa haka sukayi sannan suka fita suka bar Aunty Zainab tare dasu.
Sai da tabari duk sun fita sannan Aunty Zainab tace, " Hafsa, to zan gaya miki abinda baki sani ba, tunda sunce sai kinzo na faɗa miki, zan fara baki haƙuri sabida anyi wannan auren bata re da saninki ko amin cewariki ba, dan haka nake mai baki haƙuri bisa ga wannan abin da muka aikata kuma Allah yariga da ya tsara abinsa duk yadda muke so to idan Allah ya kaddara sai muyi haƙuri, ba abinda zance sai dai nace miki yau ke da Anwar kunzan miji da mata....tun bata kai da rufe baki ba Hafsat tace, what!!!.
Tafaɗi haka tari da miƙiwa tsaya tace, "wallahi bazai taɓa yuwa ba, ina Sulaiman?".
Ƙanwar Abbanta ce da tashigo ɗakin dai-dai lokaci da take magana tace, "gashi ko ya yuwu, Sulaiman kuma baruwanki dashi dan yanzu ba muharra miki bane".
Tafaɗi haka ciki da masifa dan ita gwaggo Saratu koda ma masifafface.
Hannu ta ɗura aka tace, "yau nashiga uku dan Allah ina kuka kaimin Sulaiman".
Ƙanwar Mamar tace tace, "kiyi haƙuri ƴa ta, Sulaiman shima yana can da amaryar sa".
Idon Hafsat ta zaro sannan tace, "wani Sulaiman?".
Wannda kika sani mana".
Haka gwaggo Saratu tace da ita.
Jikin ƙanwar Mamar ta Masa'uda ta faɗa tace, "Mumy ya haka ta kasance?".
A hankali ta ƙara janyota jikinta tace, "sai kin daina kuka zan gaya miki".
Ahankali ko ta share hayen ta tadaina kuka.
Waya suka ɗauka suka kira Abban ta sukace ya faɗa mata da bakin sa.
Kiransa sukayi haɗi dasa hands-free ya fara faɗin, "Hafsat bari na tuna miki kafin na gaya miki yadda haka ta kasance, kinsan kimin alƙawari duk inada aka kaiki zaki zauna, kuma kituna hukunci musu alƙawari idan sun saɓa, sannan ya ƙara da cewa, lokacin da iyayen Anwar suka zo suka nemeki da ki aure ɗansu Anwar,