Showing 48001 words to 49839 words out of 49839 words
Chapter 17 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt
to dakiƙa ƙi basu amsa ashe duk abin da ake Sulaiman yana tsaye yana jin komai, irin yadda yaga iyayen sun shiga wani hali danshi yace dasu sabida shi ne zakiƙi auren Anwar amma yasan har ga Allah kina son shi, bayan kwana biyu sai Sulaiman ya kaiku dan ku dube shi aiku nan kuwa ya ƙara tabbatar da tabbas kina sonshi, to bayan kun dawo ne ya yanke shawar zai barwa Anwar ya aureki ko dan a ceto rayuwar sa daga halin da yake ciki, kuma nan yanemi da mu amince masa ya aure Safiyya, haka kuwa a kayi dan ke da Safiyya bawan da muka gayawa sai ankai ku gidajin ku, kuma dan Allah ina roƙonki da kici alƙawarin da kika ɗauka ki tsaya kiwa mijinki biyya da iyayensh".
Yana faɗin haka ya datse kiran.
Tana jin ya katsa wayar ta shige jikin Mumy ta Masa'uda sai kuka take kamar ranta ya fita.
Anwar ko tunda Auntyn shi ta fara magana ya suɗaɗa ya bar ɗakin.
Sai da tayi kuka mai isarta sannan tayi shuru sanadin ciyon kan da ya tasoma mata.
Magani suka bata tasha, ba bata lokaci bacci ɗauke ta.
Itace bata barka ba sai da asuba.
Tashi tayi tayi sallah, bayan ta idar da sallah tajima kan sallaye tana azkar da addu'a Allah yayi mata sauki abinda take kiji kuma Allah ya yaye mata son Sulaiman a cikin zuciyar ta kuma ya bata ikon biyya ga iyayin ta da mijin ta, tana haka bacci ɗauke ta.
Sai kusan ƙarfe goma ta farka, wanka taje tayi sannan ta shirya, beark aka kawo musu amma ita ƙin ci tayi da ƙyar aka samu tasha ruwan tea, bayan sun kammala akace su zo sukai amarya part ɗinta, daya ke gida ɗaya suke da iyayenshi dan sunce basa son yayi musu nisa dan haka suka zauna gida ɗaya.
Part ɗinta suka kaita wannda iya haɗuwa ya haɗu, dan tsayawa faɗar haduwar sa ɓata lokaci ne.
Bayan sun gama shiga ko ina na part ɗin sannan suka zo suka fara shiri tafiya, haba aikuwa Hafsat naganin haka tafara shirin kuka, da ƙyar suka rarrashita ta haƙura.
Amma lokacin da zasu shiga mota saida tayi kuka sosai, haka suka tafi ciki da jin daɗin karamcin da iyayen Anwar dashi kansa yayi musu.
Bayan sun tafi da awa ɗaya sai su Aunty Zainab suka shigo, kuka suka tar da tanayi dan haka suka rarrasheta sannan sukayi mata sallama sannan suka tafi suka barta ciki da kewa.
Anwar ko tun jiya da ya suɗaɗa ya gudu bata sake gininshi ba har yanzu.
Gab da sallar magariba ta tashi taje tayi wanka ta shirya, tana idar da sallah sai gashi ɗakin, a hankali yake taka ƙafar sa kamar wani ɓarawo.
Zama yayi kan kujerar dake kusa da ita, haka yajira har ta gama azkar, saukuwa yayi daga kan kujer da yake zaune ya dawo saman sallayar da take zaune.
Kanta ta ƙara yin ƙasa dashi, lokaci ɗaya wani baƙin ciki ya fara rufe ta amma sai ta dake, sunayen Allah take ta kira a zuciyar ta har tasamu sauƙi abinda take ji.
Shiko rasa abinda zaice mata yayi sabida yana tsoron tace bazata zauna dashi ba.
Sun jima a haka kafin ya buɗe baki yace, "kizo muci abinci dan Allah ba danni ba".
Ya faɗi haka kamar yayi kuka.
Yada take bata ko ɗago ba bare yasa ran zatayi masa magana.
Ruƙonta ya farayi amma sai tayi banza dashi, da taga zai dameta sai ta tashi tabar wajan.
Haka dai taci gaba da kasancewa tsakanin su har tsawo sati biyu ba abinda ke haɗasu,
Yau ma kamar kullum yana parlour zaune yana kallo labaru sai wayar ta shiga rura, number da yagani ne yasa ya faɗaɗa murmushin sa, ɗaukar wayar yayi tare da karawa kunninsa yana faɗin, "ango kasha ƙamshi".
Sai da yayi dariya mai sauti sannan yace, "sosai kuwa, ina fatar kaima kasha?".
Anwar bai bashi amsa ba sai yace, "ina amaryar taka?".
Sulaiman yace, "gata kusa dani".
Wayar ya bata yace, "gata ku gaisa". amsa tayi suka gaisa da Anwar sannan tace, "ina Hafsat?".
Rasa mizai cemata yayi sai da Sulaiman yace, "ina amaryar taka su gaisa tace".
Kamar da ɗan tsoro yace, "bari na kai mata".
Sulaiman yace, "wato baku ma tare kenan, ko har yanzu baka sha mansha nu ba?".
Yana faɗin haka shiko dai-dai lokaci da ya shigo ɗakin da take dan haka baiyi magana ba, ƙarasowa yayi wajan da take zaune a hankali yace, "ga Safiyya zakuyi magana".
Tunda aka buɗe ƙofar tasan shine yashigo amma ko mutsi batayi ba bare yayi tunanin cewa zatayi masa magana.
Jin da tayi ya ambace Safiyya yasa ta ɗago kai amma batare da ta kalleshi ba, wayar da ke hannunsa ta karɓa haɗi da karawa a kunninta, sallama tayi Safiyya ta karɓa, bayan sun gaisa, sai Hafsat tace, "Safiyya haka su Abba sukayi muna ko?".
Safiyya tace, "kenan sunyi miki bayani?".
Bata bata amsa ba sai Hafsat tace, "kenan kin san za'ayi haka?".
Safiyya tace, "wallah bansani ba sai da aka kawuni suke min bayani".
Ta kai ƙarshin zanci kamar zatayi kuka.
Hafsat tace, "ni karkimin kuka, wa Yaya Abbas ya aure?".
Naja'atu ƙawarki".
"Wace Najaatu? Kardai kice min Naja'atu Nasir?".
''Ita fah".
Cewar Safiyya.
Ina suka haɗu?".
Sulaiman dake zaune tare da Safiyya yana jinsu sai yace, "kin fah cika mu da tambaya² kibari idan kinzo zakiji".
Marairaicewa tayi tace, "Yaya Sulaiman dan Allah kayi haƙuri".
Bai ce da ita komai ba sai Safiyya tace, "lokacin da mukaje india ne tazo nemana to koda tazo bama nan tunda ga nan yaji yana sonta amma bai gaya mata yace sai mun dawo idan kin amince zaki aure shi to shikenan idan ko baki amince ba sai ya gayama ta, to koda muka dawo yaji haka shine ya gaya mata ba ɓata lokaci akayi komai a kagama".
Sai da Hafsat taje dugon numfashi sannan tace, "kunji daɗin ku".
Safiyya tace, "ba wani jin daɗi biyyace kawai zamuyi ma iyaye, dan haka kema dan Allah duk abinda kike ji ki ajeshi ki tsaya ki kula da mijinki".
Nan dai tayi-tayi mata nasiha, daga ƙarshi kuma suka dawo kuka kafin suyi sallama.
Yana ganin ta fara kuka ya karɓe wayar dake hannun ta, a hankali ya jawo ta jikinsa ya fara rarrashin ta, amma kamar ance ta ƙara, sai datayi mai isar ta sannan tayi shuru.
Haka dai taci gaba da kasancewa tsakanin su bawata jituwa har akayi wata biyu, dan idan ga tayi masa magana to suna gaban Daddy da Mama.
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya.
Yau Monday kuma yau ce ranar da zata fara fita aiki, bayan ta shieya taje ta gaishe da su Daddy da Mama sannan suka tafi ita da Anwar, bayan sun isa asibitin da zatayi aiki, kai tsaye a kayi mata jagora zuwa offce ɗinta, bayan ta zauna tayi ƴan rubuce² sannan ta tashi dan taza gaya wajan marasa lafiya, suna cikin jagayawa ita da wasu likitoce da waɗanda ke nuna mata yadda wajan yake, suna cikin haka sai sukaji kamar ana kiran Anwar, gaba ɗayansu shida ita suka juya dan suga wake kiransa.
Wata mata suka gani kwance saman gadon hospital, sai ɗaga musu hannu takeyi.
Ƙarasowa wajanta sukayi dan suga wacece ita?.
Koda suka zo wajanta amma basu gane taba, da taga alamu basu gane taba tace, "baku ganeni ba ko?".
Atare suka ce "eh".
Kallon Anwar tayi tace, "Anwar kar dai a ce labarin danaji ance ka aure Hafsat da gaske ne?".
Sai da suka kalle juna sannan yace, "eh da gaske ne".
"Allahu akbar, Allah ya nunamin ikonsa, duk yadda nashiga na fita dan kar kuyi aure yau gashi kunyi aure".
Ta kai ƙarshi zanci da kuka mai ƙunar rai.
Tace, "tun lokaci da kace kana son Hafsat abin baiyi min daɗi ba, sabida sai naga baka dace da ita ba dani kadace, dan haka tundaga lokaci na fara shiga da fita dan kar Hafsat ta amince maka amma ina ƙaddara tariga fata, dan sai da ta amince kuka fara soyayya, hakan ba ƙaramin baƙinciki naji ba, duk da haka banyi ƙasa a guwa ba, sai da naji wajan wani boka yayi maka akin da zai sa kalalata mata rayuwa haka kuwa a kayi to bayan komai ya afku kuma sai Hafsat ta guje ka, to ana cikin haka sai kazo wajena dan nan shirya ku da Hafsat, to a lokacin ne nasamu galabarku har nashiga tsakanin ku na rabaku, to duk da haka ban kyaleku ba, nan dai tagaya musu har ƙarshin zuwan datayi wajan malami da kuma yadda tace yayi mata akan Anwar, to anacikin haka wannan ciyon yasameni ta, a ka mai dani gida naci gaba da jinya, to ina cikin haka aka kawomin hotonan auren ku, to tunda ga nan bansake sanin inda kaina yake ba sai a wannan asibitin.
Tana kai ƙarshin zanci tayi haka tasake magana amma ina, sabida sheɗar ta sai sama da ƙasa takeyi.
Cikin hanzari likitoci suka fara bata taimakon gaugawa.
Tunda Hafsat tagano ko wacece take kuka har inada Hajara ta kawo ƙarshin zance.
Anwar kuwa yana ganin yadda take kuka yaja hannunta yace suje gida sai wani sati zata fara aiki.
Haka suka dawo gida ciki da Mamaki Hajara.
Har dare yayi Hafsat bata dawo dai-dai ba.
Bayan yayi wanka yayi shirin bacci yaje wanta ya rarrashi ta har yasamu taci abinci daga haka dai yayi ta bata magana har yasamu abinda yake so a wannnan dare, sosai ya bata wahala danji yake sai yanzu yasan ta ƴa mace dan da safe har da zazzaɓi sai da tatashi da shi.
Haka dai suka cigaba da rayuwa, sosai yanzu Hafsat ta sake jiki dashi, shiko sai nuna so yake gareta.
Bayan sati ɗaya Hafsat taje asibiti ta bincike Hajara a kace ai tun ranar Allah yayi mata cikawa, sosai Hafsat taji zafi da faruwar haka.
Koda ta dawo gida ta sanar da Anwar amma bai wani nuna da muwa ba, sai dai Addu'ar da yayi mata.
Haka rayuwa tacigaba da kasancewa, dan yanzu soyayya mai ƙarfi ta kullu tsakanin Safiyya da Sulaiman hakama Hafsat da Anwar dan Abin har namaki ya bani.
Koda taje ganin gida tasha mamaki, dan gababki ɗaya Anwar yasa anrushe wannan gidan anyi musu sabo, gaba ki ɗaya koma na gidan ya dawo sabo haka tazo tayi kwana biyu gida koshi da kyar ya barta, koda suka haɗu da Safiyya har cikin Safiyya ya fito haka ma Naja'atu, Hafsat ce ka ɗai keda shigar ciki, dan sai wani kwaɗayi take suko suna tsargowar ta.
Haka dai rayuwar ma'aratan ta kasanci cikin so da ƙauna, bayan shekara ɗaya Safiyya ta haifi ɗanta namiji mai kama da maihaifinsa itama Na'atu ta haifi ƴar ta mace, ita ko Hafsat ta haife ɗanta sak Anwar, murna wajan dangin Anwar da iyayensa ba'a magana kowa faɗi yake Anwar yasamu magaji, bayan angama shagalin biki tace zata kuma gida wankan jego amma Anwar yace shi sam bai san haka ba, da ƙyar iyayenshi suka rarrashe shi ya yarda tatafi.......
*ALLHAMDULILLAH*
To nima Hafsat na tafiya nikuma na aje alƙalamina🤩
fatan alhari gareku masoyan wannan littafi, inama kowa fatan alhairi.
Kuma duk wannada na ɓata ma dan Allah kuyafemin🙏🙏
_Sai bayan sallah idan Allah mai kowa mai komai yasaki haɗamu acin sabon littafe na mai suna *AUREN RASHIN DACE ko kuma SANADIN BARIKI(narasa raina).*_
*Ko huta lafiya🤗*
*#VOTE COMMENT SHARE*
*©SUMY NA'IGE*
*Share*