Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 49839 words

Chapter 6 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt

Ads the beginning of article before Image

23 Jun 2024

475

Ads at the middle of Article

soshi a zuciyar ta sosai.






Bayan sun koma makaran ta da kwana biyu ranar Safiyya na zaune class ɗinsu sai ga wata ƙawar ta tazo wajan ta kuma ƙawa ga Hajara dan abinda yasa Safiyya ta barta saboda taga ko ina Hajara take itama tana can danshi ta bar ta...












*#VOTE COMMENT SHARE*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*












*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*






~~Wattpad Summy M Na'ige~






*SHAFI NA 12📑*






*__________📖* Bayan sun gaisa sai ƙawar ta Ummi tace,"ina Hafsat kwana biyu na daina ganin ta?".


Sai Safiyya tace, "tana nan lafiya".


Sai Ummi tace, "ki ce dai da dama,wace lafiya ne da ita tana ɗauke da ciki".


Sai Safiyya ta haɗe fuska kana tace, "wani ciki?" tana faɗa ta na hararar ta.




Sai Ummi tace, "Safiyya bari kiji wallahi ba abinda zaki ɓoye min gami da Hafsat wanda ban sani ba, tun farkon haɗuwar ta da Anwar har cikin da ya yi mata ba wanda ban sani ba,ni dai shawara zan baki dan na ga irin cin zarafin da yakema Hafsat ya yi yawa, shiyasa na yanke shawar na zo na faɗa miki abinda ake ciki dan ki nema mata mafita,amma idan zaki saurare ni, dan nasan haliki na rashin kulani shiyasa tun wancan lokacin ban faɗa miki ba amma mikika ce zaki saurareni ko ya ya?".




Murmushi Safiyya tayi mai ciyo kana tace, "ina jinki ki faɗa min".


Sai Ummi tace, "komai na faɗa miki kiyi haƙuri dan na san zakiji zafi sosai".


"Kifaɗa ina jinki"....tafaɗa haka ataƙaice.


Sai da Ummi ta numfasa kana tace, "zaki iya tuna lokacin da Hafsat ta samu saɓani da Anwar? har ta ji ko ganin sa bata sonyi,to ba komai bane ya kawo haka sai rabata da mutuncinta na ƴa mace da ya yi, ta hanyar samata maganin da zai gusar da hankalin ta,ita ko tundaga lokacin ta daina kulashi,ince ma har wajanki ya zo amma ki ka kasa shawo masa kan Hafsat,to da yaga yaki samun nasara gareku sai yaje gun Hajara ya faɗa mata abinda ya ke so tayi masa,ita ko Hajara da son kuɗi tace zatayi masa,to fa tundaga lokacin Hajara tafara bibiyar Hafsat har tasamu ta fara kulata har tayi nasarar rabaki da ita, to fa lokaci ne Hajara ta fara yimata magiya kan ta yarda su shirya da Anwar amma Hafsat taƙi,to da Hajara taga Hafsat ta faye kafiya sai kawai ta kaita wajan wani malami ta faɗa masa abinda ta ke so ya yi mata,bayan ya yi mata aikin da zai sa ta yarda da Anwar, kuma duk abunda yasa ta bazatayi masa musu ba,anyi kuma aiki yaci dan komai sai Anwar yace Hafsat keyi takeyi , koda kowa uwar ta ce tace tayi in har Anwar bai yadda ba bazatayi ba,ya maida ta kamar matar sa, sai yadda yaso yakeyi da ita kuma ba wai dan baya son ta bane a'a yana son ta sosai sai dai yanzu yace bazai iya auren taba saboda taki yarda azubar da ciki,dan haka nake son kije ki nemar mata makarin abinda sukayi mata ko zata samu sauƙin abunda ke damunta".


Hawaye masu zafi ke fita daga idon Safiyya,kallon Ummi tayi tace, "yanzu Ummi kin san komai amma ki ka kasa sanar dani,ashe ba son Allah kikemin ba, dan da son Allah kikemin da kin faɗamin abinda kika sani gami da ƴar uwata".


Ummi tace, "kiyi hak'uri Safiyya wallahi koni ban sani ba sai daga baya,saboda yanzu ita Hajara ta kamu da son Anwar kamar ta mutu shiko yace ko zaman bariki ba zai iyayi da ita ba, bare har ta kai ga aure,to lokacin ne Hajara ke bani labarin yadda ta yi sanadiyar soyayyar su da Hafsat".


Kuma wallah na san yanzu ko kashe Hafsat Hajara na iyayi akan Anwar,dan haka ku ɗau mataki" ...tana faɗa tana tashi tace,


'Kinga tafiya ta dama nazo ne na faɗamiki saboda har gobe kina matsayin masoyiya ta, dan haka sai anjima".....tana faɗa tana tafiya.


Magana Safiya take so tayi mata amma saboda biƙin ciki kasa buɗe baki tayi sai kukan da takeyi kamar ranta zai fita.


Ko lecture basu gama ba Safiyya taje wajan Hafsat tace tazo suje gida.


Hafsat tambayar Safiyya lafiya za su je gida kuma gashi ko locture basu gama ba,Safiyya nuna mata tayi suje gida dan ita ko natsuwa ba ta da , ita ko Hafsat ta kafe bazata jeba,kuka Safiyya ta sanya ma Hafsat tana faɗin sai sunje,kukan da Safiyya ke yi ne ya sa Hafsat jikin ta ya yi sanyi ta yarda zata bita suje gida amma ba dan ranta yaso ba, dan taso Safiyya ta tafi ta barta dan ta naso idan tagama lecture taje gidan Anwar.






Bayan sun fita school ďin suka tsayar da mai napep Safiyya tagaya masa sunan unguwar da zai kaisu,kallon ta Hafsat tayi kana tace, "ina zamuje ne?".




Safiyya batayi mata magana ba har suka kai inda zasuje.






Bayan sun sallame mai napep kana suka shiga wani gida da sallamar su,bayan an karɓa musu,suka gaida wata tshowa, bayan ta karɓa sai Safiyya tace, "lnna ina Malam?Allah dai kasa baiyi nisaba?".




Sai wadda ake kira da lnna tace, "a'a yana ɗakinsa,mikika kawo masa dakike neman sa".


Bata bata amsaba ta wuce ɗakin malam.


Bayan sun gaisa da Malam tayi masa bayani abinda ya kawo ta gami da Hafsat,tana masa bayani tana kuka,sai Malam yace, "ki daina kuka Safiyya,insha Allah komai yazo ƙarshe".


Magani ya haɗa mata dana hayaƙi dana sha harda na wanka ya bata zaitun da habba yace ta rinka shafawa duk lokacin da tayi wanka.


Godiya tayi masa sosai sannan ya tambayeta Mamar ta tace lafiya ƙalau suke.


Har za su fito daga gidan Malam ya ɗauko husunul musulim ya basu ita da Hafsat yace ko wace safiya surinƙa karatunsa,kana yayi musu faɗan da suriƙa addu'o i nema kariya ako wace rana.




Sallama sukayi masa kana suka wuce gida.




Tundaga lokacin suka cika gaba da yimata magani ba dare ba rana, kuma duk abin nan da ake Mamar Safiyya bata san mike faruwa ba,duk da iyayenta ne ke ba Hafsat magani amma bai sa tasani ba.




Kuma cikin ikon Allah yanzu abin yayi ma Hafsat sauƙi sosai, dan yanzu har kiran ta yake amma ba ko da yaushe take ɗauka ba kuma yanzu so ya ke tazo suyi bankwana dan satin nan zai koma gida.....




*#Vote*
*comment*
*Share*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*












*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*








~~WattpadSummy M Na'ige~






*SHAFI NA 1📑*


*__________📖*
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*








*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*






*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION.*








~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~











*SHAFI NA 13📑*




*__________📖* Ko yau suna zaune a ɗakin su ita da Safiyya suna fira sai wayar ta tafara ringing,duba saman secreen ɗin wayar tayi,Hayateenah taga ya bayyana,da sauri ta datse kiran kana ta kashe wayar gabaki ɗaya.


Kallon ta Safiyya tayi tace,"hala waya kira ki ka datse kiran?".


Sai da taya tsane fuska kana tace, "Anwar ne yake dumuna da kira,amma na san maganin sa gobe ko yakira ba zai samu ba".


Har Safiyya ta buɗe baki tayi magana sai suka ji Mamar Safiyya na ƙwala musu kira.
Da sauri Hafsat tace "ga Mama can na kiran mu ki tashi muje".......tana faɗa tana tashi tsaye.


Suna ƙarasowa sai da Mama tayi ma Hafsat wani kallo kana tace, "ga wankin yara can ki ɗauka kiyi har da na Yayan su dan shima ya ce ki wanke masa kayan sa,kuma saura kada ki wanke ya fita".






Tace' "tau Mama zanyi da kyau".




Duban ta ta maida ga Safiyya kana tace,"ke ko je ki shirya zan aikeki gidan su lnna"....mahaifiyar Mamar Safiyya kenan.


Tace, "tau Mama bari mu ɗan rage wankin nan sai natafi".




Ai tun Safiyya bata kai da rufe bakin taba Mama ta daka mata tsawa wadda bashiri ta rufe bakin ta.






Hafsat tafiya tayi wajan tulin wankin da ke zobe a ƙasa ta ɗauko ta kai bakin fanfo ta ɗauko kujera dan ta zauna dan yanzu bata iya wani dogon duƙe,aikuwa tun ba takai da zama ba Mama ta daka mata tsawa tari da faɗin, "kada ki zauna kiyi shi a haka,salon ki zauna kiyi min wankin da bai fita ba?".






Sai da Hafsat ta goge hawayen da suka zuba a idon ta kana tace, "wallahi Mama bana iya duƙi sai naji marata ta kulle, dan Allah ki bari na zauna zan fi jin daɗi....ai tun bata rufe bakin ta ba sai ga Abbas Yayan Safiyya ya fito daga ɗakin sa yana faɗin,






"Oh Mama ce zata faɗa kina faɗa?dan baki da kirki baki da tarbiya,ashe rashin tarbiyarki ba wajan bin maza ta tsaya ba harda ciwa manya mutun ci?".






Safiyya na ɗakin su taji duk abinda ke faruwa har lokaci da yayan ta kema Hafsat faɗa,abinda taji ya faɗane yayi mugun ƙona mata rai dan haka bata san lokacin da ta fito ba.






Cikin hanzari tafito d'akin su tana faɗin, "wallahi Yaya kaima baka wuce k'addar da tasame Hafsat ba, da har zaka buɗa baki kayi mata faɗe....... ba ta kai da rufe bakin ta ba taji saukar mari har guda biyu wannda ya gi-gita ta lokaci ɗaya..




Ba ta kai da dawowa hayyacin taba tafara jin saukar duka ta kowane fanni na jikin ta.




Dukan ta yake yana faɗin, "ni zan faɗa kina faɗa ehh?".




Ilata ta taga zayi dan haka da gudu ta yi hanyar d'akin su.






Tana shiga ta kulle ɗaki kana taci gaba da kuka tana mai tausayawa Hafsat.






Koda yaje d'akin yaga ta kulle dan haka ya dawo wajan Hafsat,ita ko tunda taga abinda yayiwa Safiyya ta duk'a haka nan ta fara wanki tana jin ba daɗi ajikin ta.




kallon ta yayi yace, "wallahi minti kad'an nabaki ki kammala Kuma duk basu fita ba hmmmmm Allah kad'ai zai karb'arki a gidan nan"......yana fad'a yana ficewa a gidan gabaki d'aya.






Haka nan Hafsat taci gaba da wanki tanayi tana share hawaye,sosai ta wahala kafin ta kammala,kuma tana kammalawa Mama ta hadata da wanki-wanke da shara da aikin abin ci,aikuwa tana kammalawa sai zazzab'i ya rufeta,sai da Safiyya ta lallab'a taje wani pharmacy ta karb'o mata magani.




Haka dai ta kwana a wannan ranar wahalce.






******


Yau Monday rana school ce kuma babbar rana ce ga y'an makaranta kowa ne ɗan makaranta burinshi yaga ya isa cikin school d'insu cikin lokaci.




Safiyya ce tafito daga d'akin su ta same Hafsat kichen tace, "Hafsat wai mekikeyi a kichen kuma kinsan muna da lecture k'arfe ta kwas kuma yanzu 8:30 gashi ko shiri bakiyi ba,to har yaushe zamu kai school d'in?".






Tace, "kiyi hak'uri Safiyya wallahi Mama ce tasani d'aurama yaran can ruwan wanka kuma gashi wutar ma tak'i ru-ruwa".






Sai Safiyya tace, "kitashi kije ki shirya sai na k'arasa kafin ki fito sunyi zafi".






Tace, "tau Safiyya"..... tana faɗa tana tashi.






Har zata shiga ban d'aki ta watsa ruwa sai ga Mama ta fito daga d'akin ta.






Magana ta fara mata cikin faɗa-fad'a "me zakiyi a ban d'aki? ba aiki nasaki ba ne?".






Har zatayi magana sai ga Baban Safiyya ya shigo gidan.






Kallon Mama yayi da Hafsat dake tsaye yace, "lafiya na ganko haka cirko-cirko?".






Sai Mama tace, "aki nasakata shine taki tayi min".






Sai Baba yace, "amma kin san yanzu lokacin makaranta ne kuma zaki sata aki salon su makara,to bawani aikin da zatayi sai tadawo makaranta"......yana fad'in haka yace Hafsata tayi sauri ta shirya su wuce makaranta.






A gurguje ta shirya dan ko beark bata yiba suka Kama hanyar school d'insu.






Takwas saura minti biyar suka isa makaranta,kai tsaye kowa class ɗin su ya wuce, aikuwa bata jima da shiga ba sai ga malamin su yashigo dumin su fara karatu.








Basu jima da fara karatu ba sai ga sak'o yazo daga office d'in sugaban makaranta, bayan d'an sak'on yayiwa Malamin bayanin abinda aka aikoshi na kiran d'aliban da aka umarce shi,malamin ya bada izinin a kira su,nan kowa ya fara kiran su,kuma daga cikin su Harda Hafsat a ka kira.






Bayan ankira sunan su aka umarce su da suje office d'in sugaban makaranta acan ake neman su.






Aikuwa ana faɗin haka gaban Hafsat yayi mummunar fad'uwa, lokaci d'aya wasu hawaye suka fara zoba a idon ta,tunani tafarayi ko korar ta za'ayi sabida batayi jarabawa ba ko sunji labarin tayi cikin shege ne?aikuwa tana kawowa nan a tunanin ta fashe da kuka mai k'unar zuciya, kuma gashi ba mace a cikin wad'an da aka kira dukan su maza ne bare ta samu sauk'in abinda take ji.






Haka taci gaba da biyar su har suka kai office d'in sugaban makaranta.








Gaban tane ya ba da dummmm lokacin da za su shiga offece ɗin,amma ta dake ma ranta had'i da addu'a kana ta shiga.






Office d'in cike yake da malamai har ma da waɗan da ba malaman makarantar ba,sukuwa d'alibai wanɗa da aka kira suna gyefe d'aya suna jiran a fad'a musu abinda yasa ake kiran su,ma fi yawan su maza ne,dan mata ba su wuce uku ba,wajan da mata suke ita ma nan tazo ta tsaya.






Bayan zowan su da mintuna ƙalilan sai shugaban makaranta ya fara jawa bi.






Bayan ya kammala abinda zai ce kana ya mai da duban sa ga d'aliban da suke tsaye yace, "ba komai yasa muka taraku anan ba,sai dan wani abin farin ciki da ya samemu Kuma ya same ku,amma ga wanda yaji yana so ko iyayen shi za subar shi,Wannan abin farin cikin shine gwamnati ce ta ba da scholarship ga ɗalibbai mafi hazaƙa kuma waɗan suka ci jarabawa, suje k'asa she daban-daban suyo karatun master,amma bamu ce dole sai kaje ba, a'a in kana da ra'ayi kuma iyayen ka za su barka to muna maka barka da zowa,Inma baka da ra'ayi ba komai sai kafad'a asa musu son zowa".






"Dan ko wane department zamu d'au mutum biyar mafi ƙwazo a cikin su, kuma waɗan da suka ci wannan jarabawar da ta gudana, amma idan kin san,ko kasan, baza kaje ba ko ba'aza a barka ba to ku faɗamuna,dan haka mun baku kwana uku kuje koyi shawara da iyayen ku sai kozo ku gaya muna dan bama son lokaci ya kule,dan gabaki daya wannan ta fiyar ba zata wuce sati uku ba insha Allah".






Hafsat najin wannan maganar ta sauke wata sassanyar ajiyar zuciya,saboda jin daɗi har da 'yar kwalla ta fitar.






Har suka fara fita bata sani ba saboda ta tafi duniyar tunani.






Wadda ke kusa da ita ta dan ta ɓata sannan ta san me ake ciki.






Da fitowar su cikin office ɗin,cikin zomud'i taje class ɗin su Safiyya dan ta faɗa mata abinda a ke ciki.






Da zowan ta bata tsaya komai ba ta fad'a jikin Safiyya dan ita har ta manta abinda take d'auke dashi sai da Safiyya tayi mata magana a tsorace tace, "Hafsat! baki gudun kijima kanki ciyo ne?".






Ba sarwa tayi kana tace, "My Sufy tashi kiji wani abin farin ciki da ya sameni,yanzu aka aiko kiran mu a office d'in sugaban makaranta, wallahi na d'auka korana za'ayi dan kin san banyi exmas ba,kinga yadda gabana ke famar dukan uku-uku wallahi har k'walla sai da ta zobo min kafin muje,ashe ba kurana za'ayi ba...... nan ta faɗa mata abinda ya wakana,sosai Safiyya tayi murna dajin har da masoyiyar ta cikin wand'an da zasuje waje suyi karatun master,murna da farin ciki wajan Safiyya ba'ace wa komai dan kamar ma tafi Hafsat jin dad'in abin.






Suna gama lecture basu tsaya b'ata lokaci ba suka wuce gida dan su faɗi abin farin ciki da yasa mesu.






Koda sukaje Mamar Safiya tafita unguwa dan haka suka cigaba da aikin su inyaso da tadawo su faɗa mata.






Sai bayan isha'i tadawo kuma ko da tashigo suna sallah,dan haka kai tsaye ta wuce ɗakin ta.








Bajimawa da shigar ta sai suka ji sallamar Baban Safiyya,dan haka da sauri Safiyya taje ta shin fiɗa masa ta barma haɗi da kawo masa abinci da ruwa.






Dan koda ya shigo Hafsat bata ida sallah ba.






Bayan yaci abinci ya koshi kana Hafsat tazo ta gaisheshi haɗi da ɗauke kwanokan da yaci abinci.






Mama ce ta fito daga ɗakin ta tazo ta zauna saman tabarmar da yake zaune.






Gasheshi tayi kana suka fara taɓa fira.






Safiyya ce tace, "Hafsat tashi muje mugaya ma Baba da Mama abin farin cikin da ya samemu".






Sai Hafsat tace, "a'a kije kigaya musu dan gabana sai dukan uku-uku yake dan ji nake kamar baza'abar ni naje ba........












*#Vote*
*Comment*
*Shere*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*












*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*








~~WattpadSummy M Na'ige~






*SHAFI NA 14📑*








*__________📖* Safiyya tace, "a'a ki tashi muje insha Allah za su barki". Ba musu ko ta tashi su kaje wajan da Baba da Mama ke zaune,zama sukayi haɗi da gaishe da Mama.


Ba su jima da zama ba sai ga Yayan Safiyya ya shigo shima inda ya gansu nan yazo ya zauna.


Sai da sukayi ƴan second Safiyya ta buɗe baki tayiwa Baban ta bayanin abinda ke faruwa.








Aikuwa tun bata kai ƙarshin zancin ba sai Mama tace, "tunda muna mahaukwata sai mu barta taje har wata ƙasa karatu ko?ko wannan karatun da takeyi anan gida me tasa ka ma iyayen ta dashi bare yanzu taje wata ƙasa, gaban idon mu ma tayi bare bayan idon mu,dan haka ni ban baka shawara ka barta taje wata ƙasa karatu ba,amma in ka yarda da shawara ta".....tana faɗa tana kallon Baban Safiyya.








Tana rufe bakin ta sai Yayan Safiyya yace, "wallahi ba ina da zata je kawai da ta haihu ka haɗata da liman ɗin unguwar nan dan kaga har yanzu bai sake aure ba tunda matar sa ta rasu kaga sai yayi maneji da ita dan inba shi ba ba mai iya auren ta".






Sai da suka gama faɗar abin da zasu faɗa kana Baban Safiyya ya ɗago da kansa ya dube su ɗay bayan d'aya kana yace,"wannan surutun naku bashi zai sa nace baza ta jeba a'a idan nayi ra'ayi na barta taje ba wanda ya isa yahana taje dan haka kuriƙe shawarar ku har nace zan nemi kubani shawara".






Kallon sa ya maida ga Hafsat kana yace, "naji abinda kuka faɗa amma zanyi shawara zowa safe duk abin da na yanke zan gaya miki" yana faɗar haka ya tashi ya bar wajan batari da ya sake magana ba.






Suma suna ganin ya tashi suka tashi dan sukoma ɗakin su.




Bakin ciki da ta kaici duk ya cika Mama dan shi ko magana ta kasa.






Suna shiga ɗaki ba wanda yayi magana a cikin su har sukayi shirin kwanciya haɗi da addu'a suka kwanta.






Ba jimawa da kwanciyar su wayar ta ta fara ringing amma tanaji ta share sai da akayi mata miss call uku kana ta ɗauko wayar ta duba taga wake damun ta da kira yanzu da dare,ba ƙuwar number tagani har taso taƙi ɗauka sai kuma

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads